Keep on letting your love shine…
RAJA POV.
Zaune yake a falon kakansu wanda mutanen gidan ke kiransa da Baba, Baba Munzali da kuma Kawu Abdullahi ne tare da Baban. Kawu Abdullahi ne ya masa tambayoyi kan yanayin yanda rayuwarsa take a can garin Abuja da ya faɗa musu ya na da zama, sun masa tambayoyi sosai, kafin suka tambayeshi alaƙarsu da Rabi’a.
“Na gamu da ita ne a hanyar makarantar da take zuwa aikatau, kuma daga haka ne muka soma soyyaya, har muka fahimci juna, giftawar wannan iftila’in ne ya kawo mana tsaiku”
Kawu Abdullahi ya gyaɗa kansa a sanda Zaid ɗin ya kai ƙarshe a maganganunsa.
“Ke nan ka san abun da ya faru da ita?”
Kansa a ƙasa ya gyaɗa shi.
“Na sani Kawu, dan ni ne ma da kaina na yi jinyarta a asibitin da aka kwanatar da ita”
Baba Munzali ne yace.
“Kuma kai yanzu kana santa a hakan?”
“Sosai ma kuwa Baba, ina san aurenta a yanda take, abun da ya faru da ita ƙaddara ce,wadda ta wuce fata, kuma san aurenta da nake ne ya sa na biyota har nan…”
Ko kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai, wayar Zaid ɗin ta yi ringing alamun shigowar kira.
“A min afuwa…”
“Ba damuwa za ka iya ɗaga kiranka”
Kawu Abdullahi ya amsa masa. Kansa ya gyaɗa ya na ɗaga kiran.
“Ok”
Kawai yace sannan ya katse kiran, cikin WhatsApp ya shiga, ya buɗe chat ɗin wani contact, a inda aka turo masa wani vedio, buɗe vedion ya yi, kafin a hankali ya matsa ya miƙawa Kawu Abdullahi wayar.
“Ka duba ka ga”
Kawu Abdullahi ya karɓa cike da mamaki, kafin ya danna play, vedion ya buɗe, sannan hoton Habiba dake garƙame a cell ɗin ‘yan sanda ya bayyana, fuskarta ta ji duka ba na wasa ba, muryarta ce ta shiga fitowa raɗau daga cikin wayar.
Hakan ya sa Kawu ya karkata fuskar waya zuwa ga su Baba dan su ma su gani.
“…Ni ce na yi wa Maryam asirin da ya sa Ɗan Lami ya saketa, kuma ni ce na yi mata asirin da ya sakata jinya, har ta kai ga mutuwa, har ila yau ni na saka Ɗan Lami ya karɓo min Rabi daga wajen ‘yan uwan Maryam. Har ta dawowa wuri na da zama, kuma… Kuma ni ce na yi wa Rabin asirin da zai sa idolan wani namiji ya kalleta zai ji sha’awarta, har aka samu wasu suka mata fyaɗe!…”
Daga haka vedion ya tsaya cak, alamun dai ya ƙare ne. Cike da mamaki ko wannensu ya kalli Zaid ɗin dake durƙushe gabansu.
“Kun gane ta?”
Ya tambaya ya na kallonsu, don ya ga kamar ba su fahimci zancen da ake ba. Baki buɗe Kawu Abdullahi yace.
“Na ganeta. Habiba ce… Abokiyar zaman Maryam”
Zaid ya gyaɗa kansa.
“Ƙwarai ita ce… A lokacin da na rasa Rabi’a, na sa aka kamata, don ta mana bayanin inda take, a memakon mu samo bayani kan inda Rabi’a take, sai muka samu wannan bayanin”
Baba ya share ƙwalla ya na kallon jikansa, jini ba ƙarya ba, hatta da yanayin maganarsa irin na mahaifiyarsa ne, shi yanzu ba shi da wani fata godewa Allah, da kuma neman yafiyar Allah, kan zunubansa na baya.
“Matso nan jikana”
Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na matsawa kusa da Baban da ya kira shi, kansa ya shafa ya na faɗin.
“Allah ya mamka albarka, Allah ya ji ƙan mahaifiyarku…. Kuma ni da kaina na baka auren Rabi’a, ba za’a ɗau wani dogon lokaci ba, akwai bikin ɗaya daga cikin ƙannen naka da za ayi nan da sati huɗu, dan haka in Allah ya yarje mana tare za ayi da naku!”
Wani abu ne ya shiga ratsawa tun daga kan Zaid har zuwa ƙafafunsa, farin ciki ya buɗe ƙofar zuciyarsa ya rufta, ƙaunar ‘yan uwansa ta ƙara kama shi, a hankali ya kwanta a jikin kakansa ya na nemawa Momma da Aliyu rahamar Allah.
“Bros”
Cewar Zakar ya na duban Zaid, wanda ke cire takalman kafarsa bayan da ya dawo daga wurin su Baba. Zaid ya amsa ya na cire takalman ƙafarsa. Tare da shigowa ɗan madai-dai cin falon samarin, ya zauna a kan kujera yana dubansu.
“Ya ake ciki ne?”
Sani ya tambaya. Zaid ya yi murmushi.
“Baba ne ya bani aure…”
Zakar ya aje mug ɗin hannunsa ya na zaro ido.
“Ikon Allah… Wai da gaske?”
Zaid ya yi murmushi ya na shafa kansa.
“Da gaske ne mana, kuma kun san wani abun farin cikin ma?, tare da na ɗayar ƙanwar tawa za ayi!”
“Wai auren Nafisa?”
Auwal ya tambaya ya na zaro ido.
“Ban san sunanta ba. Kawai de yace auren nan da wata ɗaya ne”
“Gaskiya muna taya ka murna, amma ai kana nan har zuwa lokacin bikin?”
Cewar Yunus. Zaid ya girgiza kansa.
“Akwai wani aikin da ban ƙarasa ba a Abuja. So dole zan koma, amma biki saura sati biyu zan dawo”
“Ni fa ɗan uwa, ina san wannan ƙanwar taka da kuka zo tare!”
Zaid ya yi shiru ya na kallon Zakar dake wannan batu.
“Rhoda?”
Ya tambaya dan tabbatarwa. Zakar ya gyaɗa kai.
“Of course ita, ina santa, and i mean it”
“She is not musulim, ka bari ta musulunta tukunna”
“Wai har sai ka jira?. To tun da me ya sa bata musulunta ba ?”
Auwal ya ta baya ya na gyara zama.
“Akwai abun da muke jira kafin faruwar hakan, amma ina da tabbacin lokacin shigarta musulunci ya kusa”
“To Allah ya tabbatar, amma dan Allah kar ka bari a yanka ni, dan Wallahi ina santa”
Zaid ya yi dariya ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Idan an yi auren Abuja za ka bita?”
“Abuja kuma?”
Zakar ya tanbaya ya na kallonsa. Zaid ya gyaɗa kansa.
“Ƙwarai Abuja, ma aikaciyar DSS ce”
“Jar uba! Kace ƙanwar taka me zafi ce”
Zaid ya ɓata fuska, ya na kallon Yunus.
“Ban san irin wannan abun Yunus”
“Allah baka haƙuri, wasa ne”
“Rabu da shi sirikina, zan maka maganinsa”
Zakar ya faɗi yana hararar Yunus.
“Har mun zama surukai kenan?”
Zaid ya tambaya.
“Eh mana, na ga dai kai ma ƙanwarmu zaka aura, ni ma kuma ka ga zaka bani ƙanwarka, mun zama surukai”
Gaba ɗayansu suka sa dariya.
RABI’A POV.
“Kin yi shiru?”
Cewar Baba ya na kallonta, ɗagowa ta yi yo da kanta ta kalleshi, yayin da take zaune a ƙasa daga gefensa. Allah ya sani tun bayan zuwan Zaid gidan nan hankalinta ba a kwance yake ba, hatta da baccin dare ba ta samu ta yi, ko na rana ma a firgice take yinsa, duk da ba wai haɗuwa suka yi ba, dan tun bayan zuwansa ba su haɗu ba, kawai de ta na jin tsoron abun da zai je ya zo. Ilai kuwa, yau suna zaune sai ga kiran Baban ya risketa, kan ta zo ya na san ganinta, kuma ta na zuwa suka tarbeta da maganar auren Zaid, shi ne ta musu shiru ta kasa cewa komai, to me za ta ce wai?, tace musu shi ɗin da suka ƙwallafa rai a kai ba mutumin kirki ba ne?, ko ta yi wa kanta ƙarya tace bata san aurensa?.
Haƙiƙa ta ga farin ciki a idon kakansu, ta ga farin ciki a idon Hajiya, kuma ta ga farin ciki a idon kowa na gidan, don kwana uku kenan da zuwan Zaid ɗin, amma kamar yau ya zo, sai nan-nan suke da shi. Ta tabbatar da idan har ta nuna ƙin amincewarta da auren nan, babu wanda zai ƙara kulata, babu wanda ma zai ƙara yin alfahari da ita a gidan. Kuma ita kanta ta san cewa tan na son Zaid, amma halinsa ne kwata-kwata ba ta so, mutum fa?! Mutum ta ga ya kashe a gabanta, ran mutum ta ga ya ɗauka kamar wani kiyashi. Sai de kuma duk da haka babu komai, za ta jure komai a kan ahalalinta, wata ƙila ita ƙaddararta ce ta zo a haka, Allah ya riga ya tsara cewar har ta koma gareshi ba za ta taɓa jin daɗin rayuwa ba, ko wani jin daɗinta na duniya ƙayadajje ne.
Kanta ta ƙara sun kuyarwa kamar ɗazu, ta kasa furta komai, hakan ya sa Baba fahimtar inda ta dosa, tana san auren, amma wata ƙila kunya ce ta hanata furta hakan.
“Na gane…. Ki je ki fara shirye-shirye, dan nan da sati huɗu kema za’a ɗaura aurenki tare da na ‘yar uwarki Nafisa!”
Bayan sati huɗu…
Wakili Family House, Unguwar Jama’are, Haɗejia
Ta ko wani ɓangare na gidan a cike yake maƙil da jama’a, ko ina ka kalla jama’a ne fal, kowa sai kai kawo yake ana ta hidimar biki, domin kuwa yanzu-yanzu aka dawo daga ɗaurin auren jikoki uku na gidan, hakan ya sa gidan ya cika fal da jama’a. Saboda wannan aure gidan har sabon fenti aka sake masa, babba da yaro na wannan ahali na cikin farin ciki.
Daga can ɓangaren samarin gidan kuwa, Zaid ne tare da samarin gidan, jiko da ‘ya’ya, wasu ma bai sansu ba a cikin wata ɗayan, sai yau yake ganawa da su, kuma a yau din ne yake ƙara tabbatar da girma da kuma yawa irin na ahalin nasu.
Daga can gefen kuwa Jagwado, Alandi da Zuzu ne sanye cikin manyan kaya, kai ka rantse da Allah na gari ne, yanda suka haɗe cikin manyan kaya sai zare idanu suke, kowa ya zo sai ya tambaya su waye su? Zaid ne yake amsawa da abokansa ne.
Allah ya sani, ba ƙaramin farin ciki yake ciki ba yau, a yau din nan ya mallaki Ammata a matsayin matarsa, a yau ɗin nan ya zama cikakken mutum, shi kansa ya kasa yarda, wai shi da ya saba rayuwa shi kaɗai, shi ne yau ya wayi gari ya ganshi kewaye da tarin ahali masu matuƙar ƙaunarsa, banda matar da suka ɗauka suka ba shi, har auren gata suka masa, dan kuwa babu wata wahala da aka barshi ya yi a auren, Baba da su Kawu Abdullahi su ne suka ɗauke masa komai.
Lokacin da ya koma Abuja ya siyi wani kyakkyawan madai-daicin gida, wanda yake da niyyar aje Rabi’a a ciki, ya na shirin siyan kayan furnitures Kawu Abdullah ya dakatar da shi da faɗin su ne za su yiwa ‘yarsu kayan ɗaki, kuma hakan aka yi, don a jiya aka cika gidan da kayan furnitures da kuma na kitchen, da ma duk wani abu na buƙatar gida.
Kuma hatta da sadaki Baba ne ya biya masa, shi kansa ba zai iya misalta kalar farin cikin da yake ciki ba, babu abun da zai ce sai godewa Allah, domin kuwa ita ma Rhoda ya na gab da aurar da ita, saboda sun riga da sun ɗinke da Zakar, hujjojjin dake hannunsa kawai ya rage ya miƙa, da zarar ya miƙa su za’a kama Alhaji Bala, kuma kamar yanda suka yi da Rhoda daga zarar an kama Alhaji Bala za ta musulunta.
Sannan sun yi magana da Kawu Abdullah kan daga zarar Rhoda ta musulunta za ayi aurensu da Zakar ɗin. Don haka farin cikin da yake ciki ba me misaltuwa ba ne, baki ya yi kaɗan ya faɗeshi, sai dai kawai ya ci gaba da godewa Allah.