Skip to content
Part 45 of 47 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

RABI’A POV.

Daga ɓangaren Ammatan Raja kuwa, duma suna can nasu ɗakin ana wa amaren kwalliya, cikin wata ɗayan ba ƙaramar rama ta yi ba, don har mutanen gidan sun fara zargin ko auren ne ba ta so, amma ta nuna musu ba haka ba ne. A can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tunanninnika ne birgit ta ko ina, ita kanta a yanzu ba za ta iya cewa ga takamemen abun da yake damunta ba, amma ta san cewa ba ta jin daɗi, duniyar ba ta mata daɗi sam.

Don har zargin wannan auren take, tun bayan rabuwarta da Zaid a Abuja ba su ƙara magana ba, hasali ma rabonta da shi tun ranan da za su islamiyya ta hangeshi shi da su Yunus suna hira, bayan nan ba ta ƙara saka shi a idonta ba, idan za ta ce ga abun da ya ramar da ita to har da kewarsa ma za ta iya shigowa ciki, ta na son ganinsa, ko da faɗa ne ma su ɗan yi, amma wannan zaman nesan ba ya mata daɗi.

“Kai! Amma fa kin yi kyau Rabi’a”

Cewar Rhoda, a sanda aka gama ɗaura mata ɗankwalin farin leshin da suka yi ankonsa ita da Nafisa, kanta ta kalla a mudubi. Tabbas ta yi kyau, dan hatta da wannan tabon yankan na gefe fuskarta an ɓoye shi da hoda, kwalliyar ta bal’in hawa fuskarta. Hannunta ta kai kan ƙashin wuyan da ta yi a kwanankin, ta ɗan ja guntin tsaki ta na jan wayarta.

“Kai ku yi sauri ku fito ga masu ɗaukar hoto nan sun zo”

Cewar Jidda, a yayin da take shigowa ɗakin da gudunta, ta ci uwar kwalliya kai kace ita ma amaryar ce.

“Dan Allah Ummi ki yi sauri ki gama min”

Momi ta faɗa a sigar magiya, ta na kallon me kwalliyar.

“To”

Me kwalliya ta amsa, a gefe guda kuma Rhoda da Rabi ne suke ɗaukar hoto a waya, daga can kuma Kairiyya ce takewa Nafisa da Kulsum hoto a waya.

Haka suka gama shiriritarsu kafin suka fita. Dangi da jama’ar da aka gayyata haka suka riƙa zuba musu ruwan hotuna ana ta Allah sanya da alkairi.

Da yamma kuwa walima aka haɗa musu, amma ba su yi dinner ba, dan Baba yace ba za’a yi ba, duk da suna son yi haka suka haƙura saboda babu yanda za su yi.

10:30 PM.

“Ke wai ina za ki kai ni ne?”

Rabi ta tambaya tana kallon Jidda dake ta janta tun ɗazu, tafe suke a harabar gidan, har ta fara bacci saboda gajiyar da ta yi Jiddan ta taso ta tace mata wai ta zo ta rakata, maganar duniya ta yi amma Jiddan ta ƙi ta amsata. Har ta gaji ta rabu da Jiddan.

Mamaki ne ya kamata a sanda ta ga sun nufi ɓangaren samarin gidan, kuma kafin ta gano abun da ke shirin faruwa, har Jiddan ta buɗe ƙofar wani ɗaki, ta turata ciki, sannan ta ja yo ƙofar ta kulle. Ba tare da ta iya tsayawa ta ga abun da ke cikin ɗakin ba, ta yi saurin juyawa tana bubbuga ƙofar, tare da faɗin.

“Jidda!, ke Jidda! Wai miye ne hakan?”

Daga waje ta ji muryar Jidda na faɗin.

“Tsakar dare mijinki ya kira ni yace ya na san ganinki, shi ya sa na kawo masa ke!”

Dammm!, gabanta ya buga, hakan ya sa ta juya da sauri, ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, kuma idonta bai tashi sauƙa a ko ina ba sai a kan Raja dake zaune daga can gefen gadon ɗakin, waya riƙe a hannunsa, ya kafeta da shanyayyun idanuwansa. Da ƙyar ta iya haɗiyewa wani yawu me ɗaci. A sanda ta ga Zaid ɗin ya miƙe ya na nufota.

Kanta ta kawar gefe tana ƙara matse jikinta a jikin ƙofar, banda lugudan bugu babu abun da zuciyarta ke yi, ƙamshin turarensa da ya cika hancinta ya sanar mata da isowarsa gabanta.

Zaid ya saki wani murmushi ya na ɗaga hannunsa tare da dafa shi jikin ƙofar, ya mata rumfa a tsakiyarsa. Rabi ta ji kamar numfashinta ba ya fita da kyau, kamar ma ba ta shaƙar isaka ne. Kuma hakan be isa ba sai da Zaid ya kai hannunsa ya kamo fuskarta, hakan ya sa ta lumshe idonta ta kuma buɗewa, saboda ji ta yi kamar ya ɗora mata ƙanƙare a kan fuskarta, sakamakon sanyin da ta ke ji na rata jijiyon jikinta, ba shiri ta rintse idanuwanta gam-gam.

“Ammatan Raja!”

Amon muryarsa da kuma sunan suka sa ta ware idanunwata tar, ya ilahi!, ashe haka ta yi kewar jin sunan nata daga bakinsa?, ashe ta yi kewar wannan muryar tasa?, ashe shi kansa ta yi kewar ganinsa?, duk ba ta fahimci hakan ba sai yau, sai yau da take tsaye gabansa, a tsakiyar hannayensa.

“Ba ki yi kewata ba?”

Zaid ya tambaya ya na motsa hannunsa a gefe fuskarta, Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo da kanta ta kalli fuskarsa wadda ta kusa haɗewa da tata, hatta da ɗumin numfashinsa ta na jin sauƙarsa a kan fuskarta, tazarar tsakanin hancinta da nasa bata da wani yawa, hatta da jikunansu sun kusa haɗewa. Ba ta san me ya sa ba, amma ta ga yanda idanuwansa suka ƙara lumshewa fiye da yadda ta sansu a da. Sai de ba za ta bari abun da take ji ya rinjayi kanta ba, ba za ta bari wannan salihar fuskar tasa ta rinjayi tunaninta ba, ita ta san waye shi, ta san ainahin gaskiyarsa. Don haka ta sa hannayenta biyu, ta ture shi zuwa baya.

Sannan ta juya ta shiga fafutukar buɗe ƙofar. Zaid ya tsaya a bayanta kawai ya na kallonta. Babu yanda Rabi ba ta yi ba kan ƙofar ta buɗe ama ta ƙi buɗuwa, hakan ya sa ta juyo ta kalli Zaid dake tsaye a bayanta ya na mata murmushi.

“Ka buɗe min ƙofa,ina san na fita”

Kafaɗunsa duka ya ɗaga mata alamun shi fa babu ruwansa.

“Magana kawai nake so mu yi, da zarar mun gama, zan barki ki koma”

Muryarsa ta faɗa bayan wani lokaci, Rabi da ta ci gaba da kokawar buɗe ƙofar ta juyo ta kalleshi.

“Me kake buƙata?”

Ta tambaya idonta cikin nasa, Raja ya kuma yin murmushi ya na isowa gareta, hannunta na dama ya kama ya shiga janta, duk yadda ta kai da tirjewa sai da ya sadata da bakin gadon ɗakin. Ya zauna a bakin gadon, sannan ta ƙarfi ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Rabi’a ta shiga mutsu-mutsun ƙwacewa, amma fur Raja ya hanata.

“Idan har ba ki tsaya mun yi magana ba, ba zan barki ki fita ba, sai de ki kwana a nan”

Jin maganar tasa ya sa ta tsaya da abun da take, Zaid ya saka hannunsa ɗaya ya kama ƙugunta baya, jin hakan ya sa Rabi jan wata iska, idanuwansa ta ci gaba da kalla, kammar tana shirin gano abun da yake shirin furtawa a cikinsu. Mustu-mutsun ta ci gaba da yi hakan yasa yace.

“Sshhhhh!, ki dena”

Muryarsa ta fito a hankanli cikin duhun daren, kuma amon muryar tasa ne ya haddasarwa Rabi jin kasala, ba ta san lokacin da ta saka hannayenta ta ƙanƙame gaban rigarsa ba.

“Good girl”

Ya faɗi a setin kunnenta, jikin Rabi ya shiga rawa, wani abu ya shiga bi ta kan zuciyarta tun daga samanta har zuwa ƙasa.

“Wani abu nake san nuna miki”

Jin hakan ya sa ta yi saurin kallon fuskarsa. Wayarsa ta ga ya kunna, don haka ta kalli fuskar wayar, tar take iya ganin fuskar Habiba cikin wayar, sannan kuma kar sautin muryar Habiban yake shiga cikin kunnuwanta.

“Ke ce wadda aka cutar, dan haka dole sai da izininki maganar za ta iya zuwa gaba, shi ya sa na buƙaci da na nuna miki. Shin kina san ki shigar da ƙara a kanta?”

Muryarsa ta faɗa bayan da vedion ya kai ƙarshe, Rabi da idanuwanta suke a ƙafe ta kalli fuskarsa, abun da Habiban ta faɗi sam bai ba ta mamaki ba, tun ba yau ba ta san cewa Habiba ce a bayan ko wani abu dake faruwa da su, amma abun da ya ba ta mamakin shi ne, yanda Habiban tace ita silar yi mata fyaɗe, ko da yake ai abun ba na mamaki ba ne, tun da har Yaya ya ƙita ita kuwa me zai ba ta mamaki a duniyar nan.

Jin ta yi shiru ya sa Zaid ya matse hannunsa dake kan ƙugunta ta baya, Rabi’a ta zabura tana ƙara iyowa cikin jikinsa sosai.

“Kin yi shiru?”

“Ba na buƙatar shigar da wani ƙara! A saketa kawai, ta ci darajar Anti Saratu, be side ai ba ma ita ya kamata a kama ba, ga babban me laifi a nan!”

Zaid ya yi murmushi, duk kuwa da ya san cewa hakan za ta iya faruwa. Ita har wa yau a wurinta shi me laifi ne.

“Kar ki damu, za su kama ni ai, dubuna ce ba ta cika ba. Kuma ko sun zo kama ni zan ce su bari sai na yi ajiya tukkuna, sai su kama ni”

Girar Rabi ta haɗe cike da mamaki.

“Ajiya? A ina?”

Hannunsa ya ɗaga zai taɓa fuskarta, amma sai ta janye fuskar tata, sai ya yi murmushi.

“Well! Yanzu ba za ki gane karatun ba, sai nan da wani lokacin… Kuma miye na kawar da fuskar? A zaune kike a cinyata fa!…”

Tunowa da hakan ya sa ta zabura za ta miƙe, amma sai Zaid ya sa duka ƙarfinsa ya dawo da ita, ita kuma sai ta tura shi, kasancewar ya na riƙe da ita sai ya yi baya tare a ita, bayansa ya faɗa kan gadon, yayin da ita kuma take kwance a ƙirjinsa. Fuskarta yake kallo a hankali, yayin da ita ma take kallon tasa fuskar. Hannunsa na dama ya ɗago ya na kama fuskarta, kafin a hankali ya matso da fuskarsa, ya karkatar da ita gefe kaɗan, leɓɓansa masu ɗumi suka sauƙa a kan nata, ba shiri Rabi ta zaro idanuwanta waje gaba ɗaya, ta saka hannunta ta cukukuye gaban rigarsa, ta ƙanƙame yatsun ƙafarta da suka ɗaga sama saboda kwanciyar da suka yi, ta buɗe bakinta ta na shirin yin magana Zaid ya saka harshensa a cikin bakinta, shi kenan kuma!. Ɗan ragowar hankalin nata da ya rage Raja ya ɓarar mata da shi, ya ɗauketa daga wannan duniyar da muke ciki ya kaita wata can da nisa. Ba ta gane komai, ba kuma ta jin komai sai fitar nunmfashinsa a kan fuskarta, babu abun da take gani sai idanuwansa kusa sosai da nata. Kanta ya cilla zuwa wata nahiyar, ba ta fahimtar komai sai Raja da abin da yake mata a yanzu.

“Rabi’a!”

Jidda ta kuma kiranta a karo na barkatai, bayan da suka baro wurin Zaid, amma Rabi fur taƙi amsa mata, don haushinta take ji, duk abun da ya sameta a yanzu ita ta jawo mata, ita ta kawota wurin har Zaid ya yi amfani da damar hakan ya sumbaceta cikin wannan daren. Ƙwafa ta yi a ranta tana goge bakinta da hannunta, ita ji take ma kamar har yanzu leɓen nasa na kan nata ne, ji take kamar har yanzu harshensa na cikin bakinta, sarƙafe da nata harshen, shi take kamar har yanzu hannunsa na kan ƙugunta ne, ji take kamar har yanzu tana kwance a kan jikinsa ne. Ƙafa ta sa ta yi fatali da wannan tunanin da ya addabeta, a sanda suka iso ɗakinsu. Bargo ta ɗaga sannan ta kwanta kusa da Rhoda wadda ke kwance a kan gadonta ta na sharɓar bacci.

A kai a kai take jan tsaki har da ƙwafa, Jidda na jinta amma ta yi luƙus tana mata dariyar mugunta.

<< Labarinsu 42Labarinsu 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×