The one thing that holds more power than ‘I love you’, is ‘I got you’…
No.86, Garki 2, Abuja…
09:00 PM.
RABI POV.
A hankali ta zura ƙafarta ta dama cikin kitchen ɗin gidan, sai kuma ta tsaya ta na kallon irin yawan kayan dake cikin falon, sai da ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, kafin ta sako ƙafarta ta hagu ciki. Kamar sauran sassan gidan, shi ma kitchen ɗin ya haɗu.
A jiya danginta, wato ‘yan uwan mahaifiyarta suka rakota har ɗakin mijinta, kuma a nan suka kwana, ba su tafi ba sai ɗazu da yamma, sun tafi sun barta cikin wannan gidan, bayan da suka mata nasihu kala-kala, sai de kuma ita ba ta jin ko nasiha ɗaya cikin nasihunsu zai yi aiki, don kuwa ba ta jin za su yi wani dogon zama ita da Zaid. Kowa a familynsu burinsa kawai ayi auren, to gashi an yi, ita kuma za ta san yanda za ta yi dan ya saketa, da ta ci gaba da zama da makashi, gwara ta koma can Haɗejian ta ci gaba da zama, . Duk da tasan cewa zuciyarta ba za ta so hakan ba, amma za ta haƙurƙurtar da ita, ta faɗa mata cewar zamanta da Zaid ba zai haifar da ɗa me ido ba.
Motsi ta ji a bayanta a lokacin da ta kai tsakiyar kitchen ɗin, da sauri ta juya ta na kallon bakin ƙofar kitchen ɗin, ganin Zaid tsaye a wurin kuma jingine da jikin ƙofa ya sa ta shiga dube-dube a kitchen ɗin, can ta hango set din wuƙa, ba tare da sake wata shawara da zuciyarta ba, ta rarumo wuƙa ɗaya daga cikin set ɗin, ta nuna shi da ita ido waje.
“Kada ka shigo nan!”
Raja na kallonta ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, hannyensa harɗe a ƙirjinsa, sai murmushi yake zabgawa, don shi a yanzu babu wani abu dake damun ransa, komai nasa ya hau seti, rayuwar ma sai ya ga kamar tana sauri ne. Wai yau Ammatansa ce a cikin gidansa, matsayin matarsa ta aure, halalinsa!. Duk barazanar da za ta masa ba za ta dame shi ba, don shi bai fara santa don ya bari ba, bai aureta don ya saketa ba, ya aureta ne don ya zauna da ita har zuwa ɗan lokacin da Allah ya ɗiba masa cikin duniya. Hannayensa ya ware, tare da zuba su cikin aljihun wandonsa, ya soma takawa zuwa gabanta.
Ganin hakan ya ƙarawa Rabi ƙaimi wurin ci gaba da cuna masa wuƙar a setinsa, sai de kuma ko gezau ba ta ga ya na yi ba, nufota yake gadan-gadan, har ya iso gabanta ba ta bar nuna shi da wuƙar ba, sai zare masa ido take kamar za su faɗo, kuma bai dena tahowa gareta ba har saida ya riski wuƙar, har tana taɓa jikinsa.
Da sauri Rabi ta janye wuƙar zuwa gefe, ba shiri ta cillar da ita can gefe ta na ƙara matsawa baya, shi ma kuma be fasa ba, binta yake ta na ja da baya, har sai da Rabi ta kai jikin wata cabinet.
“Ai ni na san ba za ki iya cutar da ni ba”
Ya faɗa yana kafeta da idanuwansa. Rabi’a ta haɗiye wani abu ta na kawar da kanta gefe, kuma ita kanta ta san gaskiya ya faɗa, ba za ta iya cutar da shi ba sam, ko me zai mata ita ba za ta iya masa koman ba. Amma saboda ƙarfin hali irin nata sai cewa ta yi:
“Me zai hana ba zan cutar da kai ba. Idan ta kama har kasheka ma sai na yi…”
Tana iya jin sautin murmushinsa. Raja ya fitar da duka hannayensa daga cikin aljihu, sannan ya mata rumfa a tsakiyarsu, ya ƙara matsar da fuskarsa kusa da tata dake kallon gefe.
“Ba za ki iya ko da cire silin gashi ɗaya daga jikina ba. Saboda… Kina… Sona, ki yarda kawai. Ko ki yarda ko karki yarda Ammatan Raja… You love Raja… Oh i mean Zaid… Yaya Zaid!”
Ba shiri Rabi’a ta ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, ta rintse idonta gam-gam, ta shiga kokawa da numfashinta dake shirin fita gaba ɗaya, hannunta dake kan rigar jikinta ta damƙeshi tare da rigar.
“You see… Magana ma kawai na miki ta sa kika shiga cikin wannan halin. Ina ga idan na…”
Ba tare da ya ƙarashe ba ya sauƙe hannunsa na dama, sannan ha sako shi ta bayanta, yana turota zuwa jikinsa, hakan ya sa Rabi ƙara ƙanƙame idonta, dan haɗuwar jikunansu sai ya sa ta ji kamar wani irin electric shock ne ya faru tsakaninsu. Kuma hakan be isheshi ya gama wargaza tunaninta ba, sai da ya sauƙe ɗayan hannun nasa ya kama gefen fuskarta da shi. Ya na ƙara kusanta fuskarsa da tata. Allah ne ya ara mata ƙarfin da ta yi amfani da shi wurin turashi zuwa baya.
“Dan Allah ka rabu da ni. Ni ba na buƙatarka a rayuwata, tun ba yau ba na faɗa maka haɗuwata da kai kuskure ne, ka ƙyaleni Zaid, dan Allah ka ƙyaleni!”
Ta ƙarashe hawaye na sauƙo mata.
“Ni kuma ina buƙatarki a rayuwata, ina sonki. Ina…. Matuƙar sonki, dan Allah ki fahimta”
Rabi’a ta share hawayen idonta, sannan a dake tace.
“A haka kake so na? Ni fa ba kamar sauran mata ba ce!. Ina da banbanci da su. Maza biyar… Biyar ne suka haikemin… A haka kake sona?… To ka sani ni ba ni da wannan martabar ta ‘ya mace… Ban mallaki komai ba sai raina, idan ka ce za ka ci gaba da kusanta tata irin haka ina me tabbatar maka da cewar ran nawa ma zan rasa shi nan ba da jimawa ba!” Ta faɗi hakan ne don ta tunzurashi ya rabu da ita, kuma ta na ganin kamar ya manta abun da ya faru da ita ne, don da ace ya na tunawa da ba zai aureta a yadda take ba, shi ya sa ta yi ƙoƙarin tunatar da shi.
Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na shafa sumar kansa, me take so yace ne? Wata hanya zai bi don ya ganar da ita kalar san da yake mata?, da wani yare take so ya yi magana dan ta fahimci kalar son da yake mata?, tun kafin tsautsayin nan ya auku yake santa, yanzu kuma kawai dan ƙaddara ta sameta sai ya rabu da ita?, wannan ba me iyuwa ba ne, santa a cikin jikinsa yake, ba ya jin zai iya rabuwa da santa ko me za ta zama a duniya, kuma ya na fatan bugu na ƙarshe da zuciyarsa za ta yi ya kasance da sunanta ne. Lips ɗinsa ya lasa ya na sakin sumar kansa da ya riƙe.
“Ammata, ni…”
Ya nuna kansa, sannan ya ci gaba.
“Ba dan komai nake sanki ba. Ba na sanki dan kina da wani abu. Bana sanki dan kin mallaki wani abu. Haka kuma ba na sanki dan ina buƙatar ki wadata ni da wani abu. Zuciyarki kawai nake buƙata Adawiyya!. Da zarar kin mallakamin ita zan nuna miki so. Zan nuna miki yanda ake so. Zan koyar dake so. Zan nuna miki yanda ƙaryyayar zuciya, kan haɗe ta dawo me kyau fiye da sabuwa. Zan tabbatar da na ƙawata duniyarki Ammata. Ko da sau ɗaya ne. Dan Allah, ki gwada ni… Ki gwada mallakamin zuciyarki ki ga kamun ludayina. Na roƙeki, Please!”
Rabi ta buɗe idanunwata dake a lumshe ƙwalla wata na bin wata. Idon nata ta sauƙe a kan Raja dake durƙushe kan gwiwoyinsa a gabanta, ya na roƙonta abun da za ta iya mallaka masa cikin sauƙi. Ya Allah! Me ya sa wai ita nata ƙaddarorin basu da sauƙi ne?. Ta san da cewa soyyayar Zaid na ɗaya daga cikin ƙaddarorinta na duniya, wannan haka yake, kuma a rubuce yake.
Durƙusawar ita ma ta yi a gabansa ta na kallon idanuwansa.
“Raj ni ba ni da wani abu da zan baka. Fanko!…. Fanko ce ni, na zama wata kala, saboda kwai ƙaddara ta faɗa min. Ƙaddarar da ba ni na tsrawa kaina ba, ƙaddara ce fa Raj, ƙaddara ce, amma haka Yaya ya guje ni saboda wannan ƙaddarar da ban jarabci kaina da ita ba. kuma na san ko ba Yaya ba babu wanda zai iya aurena a yadda nake, kai ma kawai de ka dage ne. Amma ni da kai ba mu dace ba…”
Kafin ta kai ƙarshen kalaminta, Zaid ya saka hannyensa duka biyu ya janyota cikin jikinsa, tare da haɗe bakinsa da nata, ƙwalla me ɗumi na sauƙa daga idon ko wannensu, Rabi’a ta kama bayan rigarsa gam, dan ji take kamar za ta zame daga hannayensa, kamar ƙasa ce za ta tsage biyu, ita kuma ta rufta ciki.
A hankali Zaid ya saki bakinta ya na rungumeta, tare da shafa sumar kanta dake cikin ɗankwali.
“I adore you Adawiyya, i na sanki ko da ba kya gani. Ina sanki ko da ba ki da ƙafafu. Ina sanki ko da ba ki da hannaye. Adawiyya ko da mutuwa kika yi ba zan dena sanki ba… I love all of you!”
Kalamansa ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar Rabi ba, don tsabar tasirin da suka yi, Rabi’a ba ta san sanda ta ɗago da hannyenta ta ɗora su a kan bayan Zaid ba, ta na ƙara ƙanƙameshi a cikin jikinta, tare da ƙarawa kukanta sauti.
Sai de kuma cikin sakan ɗaya… Biyu… Uku…
A cikin na ukun ta yi sauri ta tureshi, saboda wannan fuskar tasa da ta hango, fuskarsa a lokacin da ya harbi wani bawan Allah. Da sauri ta miƙe da gudu ta bar kitchen ɗin. Ɗakin da yake a matsayin nata ta faɗa tana bankowa ƙofar. Tare da jingina a jikin ƙofa, ta silale ƙasa tana fashewa da kukan da ba ta san daga ina yake fitowa ba, ƙafafunta ta takure a jikinta tana sunkuyar da kanta cikin kuka. Ita da Allah zai ɗau ranta ma da sai abun ya fi mata sauƙi, ƙaddarorinta suna da tsauri, ga su kuma a laye, wata kan wata.
Har ta bar kitchen ɗin kan Raja a sunkuye yake, da ƙyar ya samu ya ja da baya zuwa jikin cabinet, ya jingina da ita, sai sauƙe numfashi yake da sauri-sauri. Zai iya cewa a karo na farko kenan a rayuwarsa da ya yi nadamar shiga aikin DSS, wai me ya sa?, me ya sa komai nasa akan soyyayar Adawiyya yake da wahala haka?, ya tabbatar ba dan wannan aikin ba, da ba za ta ganshi ya harbi wani ba, da ba za ta ƙishi tana masa kallon makashi kamar haka ba. Duk sai ma ya ji ya tsani rayuwar, ji yake kamar kansa na tiriri. Cike da fusata ya ɗaga hannunsa na dama ya na dukan cabinet din dake bayansa. Ya gaji, dole ne ya ƙarƙare aikin nan cikin wannan satin, dole ya kawo ƙarshen komai.
Rabi’a na zaune a falo tana kallo. Jin wani sauti me kama da ƙaran kiran waya ya sa ta juyo ta kalli ƙofar ɗakin Zaid. Mamaki ne ya kamata a sanda ta fahimci cewa tabbas, sautin kiran waya ne ke tashi daga ɗakin, to be fita ba ne ko kuwa?, ita de ta san sassafe ya fice daga gidan, amma kuma yanzu ga ƙaran kiran waya ta na ji, duk yadda aka yi manta wayar ya yi.
Bakinta ta taɓe tare da juyowa ta ci gaba da kallonta, jin sautin kiran wayar na ƙara tashi ya sa ta ƙara waigowa ta kalli ƙofar ɗakin nasa. Ko de wani abu ne yake faru? Ta tambayi kanta a sanda take miƙewa. Ɗakin ta nufa. Sai de bisa ga mamakinta ba ta ga wani abu mekama da waya a ɗakin ba.
Har ta juya za ta fita, ƙaran kiran wayar ya ƙara dakatar da ita, hakan ya sa ta juyo ta shiga bin inda sautin ke fita. Can cikin loka ta ji sautin, don haka ta buɗe lokar, sai ta yi arba da wata kalar waya da za ta ce bata taɓa ganin irin ta ba.
Har zuwa lokacin wayar na ringing, hannun ta kai ta ɗauki wayar, amma kuma babu lamba bare suna. Gaba ɗaya ta riga ta gama shiga duniyar mamakious, wani irin abu ne haka?.
Ɗaga kiran ta yi, tare da kara wayar a kunnenta, shiru ta yi ba tare da tace komai ba, kuma daga ɗayan ɓangaren ma sai ta ji shirun, hakan ya sa ta yi ƙoƙarin sauƙe wayar, sai kuma ta tsinto wani ɓangare na Zaid, wani ɓangare na gaskiyar sa da take tutiyar ta sani, wani ɓangarensa da ɗai-ɗaiku ne cikin mutane kawai suka sani.
“…Lion, umarni ya zo daga sama, duk yanda za ka yi ka yi don ka kawo ƙarshen wannan aikin, oga yace ba zai iya jira sama da haka ba, saboda haka sai ka san yadda za ka yi dan ka miƙo duka hujjojjin da ka haɗa!…”