Heart broken over a love that didn’t even exist…
No.181, Guzape, Abuja…
MISHAL POV.
Zaune take kan gadonta, babban yatsan hannunta na dama sanye a bakinta tana sha. Hannunta na hagu kuma riƙe da wani littafi me ɗauke da rubutun “The Happiest Baby on the Block” .
Kuliya ne ya shigo ɗakim yana dube-dube, tare da faɗin.
“Hafsat ina kika aje min cable ɗin system ɗina?…”
Ba tare da Mishal ta kalleshi ba ta amsa masa da:
“Ka duba drawerta. Yana ciki”
Drawer ya nufa, ya shiga duddubawa, kafin ya samo abun da yake nema, har ya juya ya nufi ƙofar ɗakin, sai ya tsaya ya kalli inda take. Abun na farko da ya fara kalla shi ne, sunan littafin dake hannunta. Wata dariya ta shiga ƙoƙarin ƙwace masa, amma sai ya shanye yana kallonta.
“Mishally!”
Hannunta cikin baki, kuma ba tare da ta kalleshi ba ta amsa da.
“Umm!”
“Me kike ne?”
Ya tambaya yana isowa jikin gadon, littafin ta sauƙe ta kalleshi.
“Littafi nake karantawa a kan yara!”
Ta amsa masa tana maida littafin saitin fuskarta. Dariya ya yi mara sauti, ya zauna a bakin gadon, hannunsa ya miƙa saitin side drawer ya aje cable ɗin da ya ɗauka. Sannan ya dawo da dubansa kanta, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana cewa.
“Yara kike so?”
Da fara’arta ta sauƙe littafin kan cinyarta, har wani farr ta yi da idonta kafin tace.
“Ehen nah!”
Ya yi dariya yana sosa kansa.
“Da gaske kina san yara?”
Sai kuma ta cire hannunta daga bakinta tana ɓata fuska.
“To wai miye na tambayar?”
“Wai da baki nake san yi”
Cikin sakan ɗaya wannan fara’ar da ta ɗauke a ɗazu ta dawo, da rarrafe ta ƙarasa kusa da shi tana ɗora hannayenta a kan cinyarsa.
“Da gaske wai?… Yaushe?”
Kansa ya girgiza.
“Sai bayan kin yi candy”
Fuska ta kuma ɓatawa tana ɗaukewa hannunta daga kan cinyarsa, bakinta ta turo gaba tana juya masa kai.
“To wai kai sai ka sawa mutum rai a kan abu kuma ka zo ka hana shi”
Shi de bai ce mata komai ba, ya ci gaba da kallonta yana murmushi.
“Ni dan Alah ka bani yanzu”
Ta kuma faɗi tana masa fuskar tausayi. Kansa ya kuma girgizawa yana ɗaga kafaɗarsa.
“Dan Allah Love Muffin!”
Ta faɗi tana kamo fuskarsa, idonta ya cika da ƙwallar kukan shagwaɓa.
“A’a fa?!”
“Ni dan Allah ka bani ina so….”
Kuliya na dariya yace.
“Ba matsala ke kika nema ai!”
“Hafsat!”
Kuliya ya ƙara kiran sunanta a karo na barkatai. Mishal dake duƙunƙune cikin bargo tana hawaye ta masa banza tana share hawayen.
“Magana fa nake…”
Ya faɗi yana taɓota. Hannunsa da ya taɓata da shi ta doke.
“Ni ka rabu da ni… Kuma Allah sai ya sakamin… Ashe dama ba kayanka ne baƙaƙe ba ka ɗai, zuciyarka ma baƙa ce”
Ta faɗi cikin kuka tana ƙara duƙunƙunewa. Kuliya ya ƙunshe dariya yana faɗin.
“To me na yi?… Ke ce fa kika ce kina buƙata”
Kuka ta fashe da shi tana rintse idonta gam.
“Allah ban yarda ba… Kuma idan muka haɗu da Anti Adawiyya sai na faɗa mata abun da ka min”
Dariya ya yi mara sauti yana kwanciya a gefenta.
“Ki yi haƙuri to”
“Anƙi a haƙura ɗin… Wayyo Allah na Anna… Wayyo Aki… Wayyo Anti Adawiyya!”
Ta ci gaba da faɗin abun da take faɗi a ɗazu.
“Kuma Allah sai ya mana hisabi, wannan sunansa zalunci, kuma Allah ya hana zalunci…”
Juyowa ya yi yana kallonta, duk da tana lulluɓe da bargo.
“Wai ba a muku biology ne?… Ya kamata a ce an muku a biology”
“An mana ai… Ai an mana, amma ai basu ce da wahala irin haka ba… Wayyo Allahna!”
Ta faɗi tana ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, saboda ƙasusuwanta da suke mata ciwo, ga wani zazzaɓi dake shirin rufeta, wani irin sanyi take ji yana shiga ko wace kusurwa ta jikinta. Kuliya ya yi dariya me sauti a wanna karon.
“Ai da ma ba za su faɗa muku cewar akwai wahala ba”
“Dariya kake min ko?…Ko… Ko?… Ko?”
Ta ƙarashe tana fashewa da wani kukan. A hankali ya buɗe blanket ɗin, har ya samu damar ganin fuskarta, ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye, ga kuma jan da fuskar ta yi, gashin kanta a yamutse, idon nan ma a koɗe.
“Ki yi haƙuri please!… My bad, and I’m truly sorry”
Ya faɗi yana rungumeta daga kwancen da take, dukan ƙirjinsa ta shiga yi, dan ita yau gani take nan duniya bata da maƙiyi kamar shi.
“I hope we can move past this, ko kina so ni ma na yi kukan?”
Sai kuma ta tsaya da dukansa da take, jin yanda muryarsa ta fito a sanyaye. Ta dakata da kukan tana kallon fuskarsa, wadda ya mata yanayin abun tausayi.
“To ni ka min alƙawarin ba za ka sake min ba!”
Cabɗi jam!, ai wannan ai shi ne wasa farin girki, ya faɗi a zuciyarsa, a fili kuma sai ya kyaɓe fuska yana girgiza mata kai.
“Ba zan sake ba”
Hanci ta ja tana kallonsa. Yayin da shi kuma a hankali yake motsa babban yatsansa a gefen fuskarta.
“I hate you Abu Aswad!”
Peck ya mata a goshi.
“Mishallyn Aliyu you are the sun, moon, and stars, i love you more than my morning coffee, my heart is pitter-pattering for you”
Naushi ta kai masa a ƙirji.
“I hate da gaske”
“Ni kuka na ce i love you da gasken-gaske… Jikinki akwai zafi sosai, yanzu ki kwanta, gobe sai mu je mu ga likita”
Kai ta gyaɗa masa tana lumshe idonta.
T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.
ZAID POV.
“Zuwa gobe za a tura takardar ƙara kotu, daga nan za a fara zaman shari’a”
Cewar wata garjejeyar murya da ke futowa daga cikin wata ipad dake aje gaban Zaid da Rhoda. A tare Rhoda da Zaid suka dubi juna. Kafin wannan muryar ta kuma faɗin.
“A yau aka kamo wasu daga cikin waɗanda Alhaji Bala yake hulɗa da su, dan haka kuna cikin haɗari, fatan za ku kula!”
“Ok sir”
Suka amsa masa a tare, kuma daga haka wayar ta katse.
“Yanzu yaushe za ki karɓi musulunci?”
Zaid ya tambaya yana duban Rhoda, a sanda yake rufe ipad ɗin. Rhoda ta yi murmushi.
“Zuwa ranar da kotu ta yanke hukunci, kuma daga nan zan je na duba dangin Mom. Sai kuma…”
Dariya Zaid ya bushe da ita ganin yau ɗaya Rhoda na kunyar furta masa wani abu. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa cikin faɗin:
“Iko sai Allah, abun mamaki Rhoda yau ke kike jin kunyata?”
Duka ta kai masa tana turo baki. Shi kuma ya yi dariya, dan ya san maganar aurenta take san yi.
“Allah Rhoda ke da Ammata kun raina ni, daga na yi abu sai ku kawo min duka… amma ba damuwa, na dena muki wasa”
Ya ƙarashe yana haɗe rai kamar gaske. Rhoda ta yi murmushi tana faɗin.
“Ba ka ji ne ai”
“Ji tsaurin ido, ni fa yayanki ne ba ƙaninki ba?”
“Yi haƙuri to” ya yi murmushi uana ci gaba da kallon ƙanwar tasa.
“Rhoda ki na san Zakar?”
Ya mata tambaya irin wadda ya saba mata a duk sanda magana irin wannan ta haɗosu.
Kanta ta gyaɗa masa tana murmushi.
“Allah ya tabbatar mana da alkairi Cuzzie”
“Me gida Raja wai ina muka shilla ne?”
Cewar Zuzu, wanda ke zaune a back seat na motar Zaid, daga gefensa kuma Jagwado da Alandi ne. A front seat kuma Zaid ne da Rhoda. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa.
“Ba na faɗa muku cewar aikin mu ya ƙare ba?… To wani wuri nake san kaiku”
Daga haka babu wanda ya sake cewa komai cikinsu, har suka ida Rehab, wato gidan da ake kawai mutanen da suke shaye-shaye, ko waɗanda shaye-shayen ya fara taɓawa ƙwaƙwalwa. Su Zuzu ba su fuskanci hakan ba sai da suka ga an shiga da su ciki.
No.86, Garki 2, Abuja…
RABI’A POV.
“Ammatan Raja!”
Zaid ya kira sunan Rabi, wadda ke kwance a kansa tana daddana wayarta. Yayin da shi kuma yake kwance a kan kujera. Rabi ta ɗauke idonta daga kan wayar da take daddanawa ta kalli fuskarsa.
“Au… Ina nufin ‘Yan matan Yaya!”
Nan da nan Rabi’a ta sha mur, dan ya tuna mata da abun da take san mantawa da shi. Harara ta wurga masa tana juyar da kallonta kan wayarta. Zaid ya yi ‘yar dariya.
“Wasa nake. Yanzu faɗamin, menene burinki a da, bayan kun yi aure da Yaya?”
Sai ta ƙara kallonsa cikin rashin fahimta, kuma tun kafin ta furta cewa bata gane me yake nufi ba yace.
“I mean, menene burinki, ko wani fatanki, ko mafarkin da kike, na irin rayuwar da za ki gudanar da shi bayan kun yi aure?”
Ba ta yi mamakin sanin Yayan da ya yi ba, dan a yanda ta fahimci mutum me aiki irin nasa, idan da hali har yanda hanjin jikin mutum ke aiki zai iya bincikawa. Wayarta ta aje a kan cikinsa tana ɗora hannunta kan ƙirjinsa. Idonta na kallon sama ta shiga faɗin.
“Farko dai auren mu, sai kuma mu zauna a wani ɗan ƙaramin gida, ba fa dole sai babba ba, kullum da daddare idan ya dawo, ya riƙa kunna mana wasan ball muna kalla a tv, ko da ba mu da tv a gidan, sai mu kalla a waya, ko ma de ya kasance laptop ɗinsa da shago. Idan wata rana kasuwa ta yi kyau, ya ɗauke ni a bayan mashin, mu shiga zaga gari ni da shi. Ɗan ƙaramin burina kenan. Amma cikin wattanni komai ya wargaje, na tsani Yaya Raj!”
Zaid na wasa da geshin kanta ya furta.
“Wai kekam tsana ba ta miki wahala ne?”
Kallonsa ta yi na wasu ‘yan sakonni, kafin ta miƙe daga jikinsa tana zuro da ƙafafunta ƙasan kujerar. Zaid ya kai hannunsa yana ɗaukan wayarta da ta aje masa a kan cikinsa ya miƙe zaune shi ma. Kallon gefen fuskarta kawai yake, yana san sanin abun da take tunani. Kamar Rabi ba za ta ƙara cewa komai ba, can sai tace.
“A sanda na taso ban san soyyayyar kowa ba sai ta Umma data Yaya Baby. Bayan rasuwar Baby sai ya rage daga ni sai Umma, bayan rasuwar Umma kuma sai na haɗu da soyyayar dangi. Bayan na bar wurin dangina na koma gidan mahaifina a nan ne aka fara koyarwa rayuwata wani sabon darasin da ko da wasa ban taɓa kawo shi a kaina ba. Tsana!, Kar ka yi mamaki idan na ce maka a tasowata ban san tsana ba, dan babu wanda ke nuna min ƙi… Kowa haba-haba yake da ni. Amma daga sanda na dawo gidanmu komai ya sauya, mafarkaina suka durƙushe, komai nawa ya hargitse, babu wanda nake raɓa na ji sanyi sai Anti Saratu. Kowa tsana yake nuna min. Daga baya kuma sai na haɗu da Zara, ita ma ba laifi, tana nuna min tata soyyayar. Bayan wani lokaci kuma sai ga Yaya. Shi ne na miji na farko da ya fara koyar da ni yanda ake so… Shi ne mutum na farko da ya fara buɗemin hanyar soyyaya. A lokacin da muka fara soyyaya da Yaya, a lokacin na fara zuwa Makarantar Brickhall. Daga malaman har ɗaliban makarantar babu wanda bai taka rawa wurin nuna min ƙi ba. Sai mutum ɗaya, wata yarinya ɗaya kacal, ita ce ta nuna min soyyaya. Daga lokacin kuma sai na haɗu da kai…”
Ta ƙarashe tana maida dubanta gareshi. Shi ma kuma ita ɗin yake kallo da lumsassun idanuwansa. Yana nazarin kalaman nata bi da bi.
“Rabin rayuwata ta a kan tsana take Raj, me ya sa ni ma ba zan koyi tsanar ba?, an nuna min cewa ba’a so na, me ya sa ni ma ba zan nuna cewar ba na san wanda ba ya so na ba?…”
“Shhhhhh!”
Zaid ya faɗi yana ɗora yatsansa a kan lips ɗinta. Kusa da ita ya matsa. Ya ɗora hannayensa a kan kafaɗarta.
“Ke abar so ce Adawiyya, kuma ko duniya za ta ƙiki, Adawiyya ni me sonki ne, ina ganin fuskar ɗan uwana a kan taki, haka kuma ina ganin fuskar Momma gwamitse da taki, above all Adawiyya ke ce ‘yar favourite sistern Momma, so please ki dena faɗin haka, da ma rayuwa ba zata iyu ba tare da maƙiyi ba, hatta ɗan adam ɗin kansa ba zai cika ɗan adam ba tare da yana da maƙiyi ba”
Murmushi ta yi ta na kallon fuskarsa, ita kanta a wasu lokutan ba ta san wani kalar so takewa Zaid ba, ita dai kawai ta san tana sansa, tana sansa fiye da yadda za’a iya ƙirgawa.
Hannunta ta ɗago ta kai kan wannan chain ɗin na wuyansa, tare da maida shi cikin rigarsa, a duk sanda za ta ga chain ɗin a waje sai ta sa hannu ta mayar masa da shi cikin riga.
Jikinsa ya ƙara janta, hakan ya bata damar kwantar da kanta a kafaɗarsa.
“Zuwa gobe ki shirya zan kaiki islamiyyar nan”
Kai ta gyaɗa masa domin ta gane wace islamiyya ce, jiya yake faɗa mata cewar yana nema mata wurin karatu a wata isalamiyya nan kusa da su, tun da tace ita ba za ta ci gaba da karatun boko ba.
“Allah ya kaimu goben”
“Ameen”
Zaid ya amsa.
Say i love you to your problems and maybe they will leave you one day too.
No.181, Guzape, Abuja…
MISHAL POV.
“Zauna a hankali!”
Cewar Kuliya yana zaunar da ita a kan kujera.
“Did you feel better now?”
Kai ta gyaɗa masa. Don tun jiya bakin tsiwa da na surutu ya mutu murus, saboda yanzu haka daga asibiti suka dawo, fuskar nan a koɗe, kuma ajeme, ta yi jajawur.
“Na kawo miki abinci?”
Kanta ta girgiza tana faɗin.
“Ni school zan je”
Kuliya ya girgiza mata kai.
“No way Teddy Bear. Ki tambayi wani abun da ban, amma ban da zuwa school”
Daddafawa ta yi ta miƙe tsaye tana kallonsa.
“Ni school zan je to”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa yana ci gaba da kallonta.
“Ba ki ga halin da kike ciki ba ne Hafsat?… Ba ki da lafiya fa!”
Kanta ta girgiza idonta na cika da ƙwalla. Yau za su na da exams, kuma ita za ta iya wasa da komai a duniyar Allahn nan amma ban da exam, ko faɗuwa ta yi a exam har jinya take wani lokacin. Bare a ce result ɗinta ya yi ƙasa da ta biyu, ai ranar kuwa za ta yini tana kuka.
“Ni na warke, kuma zan iya zuwa school ɗin”
Ta faɗi ƙwalla na mata zuba.
“Hafsat! Ba ki ji me na ce ba ne?,babu zuwa school, faƙat!”
Cewar Kuliyan kusan a tsawace. Nan take Mishal ta fashe masa da kuka tana zama a kan kujera.
“Da ma ai na son ba so na kake ba… Da ma na san ka tsaneni, in ka san za ka hana ni zuwa school me ya sa ka min… Ka min…”
Sai ta kasa ƙarasawa tana fashewa da wani sabon kukan. Kuliya ya ɗaga kansa sama. Shi kam Allah ya haɗashi da mata.
“Je ki shirya na kaiki!”
Ya faɗi ya na sauƙe kansa. Ɗif, kukan da take ya tsaya, ta miƙe tsaye a daddafe tana share hawaye. Bayanta ya bi da kallo har ta shige corridor. Ban da rigima irin ta Mishal, me zai sa ta je school a irin wannan yanayin da take ciki?, hatta da tafiyarta ta sauya.
Bayan ta shirya cikin uniform ta fito, ba dan ya so ba haka ya kaita makarantar ya sauƙeta.