Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

If it doesn’t set your soul feel free, then it isn’t love…

No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja

07:30am

“An ya kuwa kina ganin abun nan zai iyu ? Jiya fa ba kiga irin faɗan da muka yi da shi ba, wai ka wai dan na mata faɗa, sai ciwonta ya tashi, ko a ɗakina ma bai kwana ba…”

Muryar Hajjara ta faɗi ta cikin wayar da take da ƙawarta Fati. Tsaye take a jikin wardrobe, yayin da hannunta na dama ke riƙe da murfin wardrobe ɗin, na hagun kuma riƙe da wayar da take.

“Wai baki yarda da ni ba ne ?, na faɗa miki shifa wannan aikinsa ba irin na sauran ba ne, aikinsa ma ya fi yankan wuƙa kaifi, ke hatta da alburushima baya faɗawa aikinsa saurin ci ba, ke de kawai ki yi abinda na ce miki, za ki kira ki bani labari….”

Hajjara ta yi dariya tana rufe wardrobe ɗin, sannan ta juyo tana kallon Fahima da ke wasa a kan gado.

“In dai har kuwa maganin nan ya yi aiki, ni nasan abinda zan baki”

Tana iya jiyo muryar Fatin cikin dariya.

“Za ki kira ki bani labari….”

Daga haka suka tattauna a kan shirin da suke, kafin ta sauƙe wayar, ta ƙarasa jikin side drawer ta buɗe, ta ɗauko maganin da Fatin ta aiko mata. Ta yi murmushi a fili, sannan ta furta.

“Yau zan ga ƙarshen ƙauna!….”.

MISHAL POV.

Tsaye take a kitchen ɗin gidansu tana dafa noodles, sanye take da baƙar skirt ɗinta ta uniform, sai farar long sleeve oxford shirt ɗin da take sakawa a ƙasan suit ɗin uniform ɗin, sai dai babu suit ɗin. Kanta parker cikin ponytail, jelar na reto a gadon bayanta.

Sallamar Hajjara ce ta sa ta juyo ta kalli bakin ƙofa, a zuciyarta kawai ta amsa sallamar, sannan ta ɗauke kanta ta ci gaba da aikinta.

Hajjara ta yi murmushi, ta ƙaraso cikin kitchen ɗin, ta yi birki a gefen Mishal. Sai da gaban Mishal ya faɗi, sannan ta ɗago da kanta ta juya ta kalleta.

Dan ta fita tsayi, da ma girman jikin ne da ita kawai, ba ta cika tsayi ba. Murmushin da ta ga kwance a fuskar Hajjaran ne ya ƙara tsoro tata, duk da ita ba gwanar tsoron ba ce.

Kuma kafin ta yi wani tunanin, Hajjara ta kai hannayenta ta kamo na Mishal dake riƙe da spoon. Da sauri Mishal ɗin ta janye hannayenta tana zaro ido.

Dole ma da wani abun da wannan matar ta shirya, ta daɗe da sanin cewa ba santa take ba, dan ba iyaka jiya ne ta taɓa tada mata da ciwonta ba.

Tana yawan ja mata matsololi da dama, bata santa!, haka take yawan faɗa mata, to me zai sa yanzu tazo tana mata murmushi.

Dakewa ta yi, dan bata san ta ga rauninta, bata san ta gane cewa ta ji tsoronta.

Hannunta ta kai ta kashe gas ɗin, sannan ta ɗauke ƙaramar tukunyar da ta ɗora noodles ɗin, ta juyeta a cikin lunchbox ɗinta ta fice ta bar mata kitchen ɗin, in yaso duk masifar da take ji da ita ta ƙare a kanta, ta ci kanta ta sha baƙin ruwa.

A parlo ta iske Mama Ladi na bawa Daala abinci. Ta yi murmushi tana aje lunchbox ɗinta a kan coffee table. Sannan ta zaga ya zuwa kan sofa, ta ɗauki suit ɗinta a inda ta ajeta, ta saka a jikinta.

“Mama ni zan wuce, ga Baba Ali nan ya zo”

Ta faɗa yayin da take gyara zaman hairband ɗin dake kanta, bayan ta ji horn ɗin motar Baba Alin.

“To a dawo lafiya, banda rashin ji”

Ta yi murmushi tana ɗaukar jakarta, tare da saɓata a bayanta. A dai-dai lokacin Abubakar da Hammad suka sauƙo a tare.

Tana kallonsu har suka ƙaraso cikin falon, ciki-ciki ta gaisheda Abubakar, dan ba wani sosai suke shiri da ita ba, saboda faɗan da yake mata.

“Yaya, gap ɗin nan ya haɗe, yaushe za mu je kasa a cire min braces ɗin nan?”

Abubakar ya miƙe tsaye, kuma ba tare da ya kalleta ba yace.

“Sai mun dawo daga meduguri….”

“Wallahi da gaske nake Aky, ta haɗe fa, idan baka yarda ba zaka iya gan!…..”

“Ya isheni haka! Ke dole ne duk abinda kike so sai an miki ?!, To ba zan kai ki a cire braces ɗin ba!”

Cikin tsawa da ƙaraji yake maganar, ya ma manta waye gabansa, dan haka kawai yake ganin baƙinta yau, maganarta ma baya san ji.

Mama Ladi ta miƙe tsaye mamaki na cinyeta, tasan ba yau ya saba mata faɗa ba, amma kuma ba ya mata cikin masifa haka, kuma ba ya mata faɗa sai ta yi laifi, amma ita a cikin wannan maganar da ta yi bata ga abun lafi ba.

Ba ƙaramar tsorata Mishal ta yi ba, ta ji ƙofofin numfashinta na neman ɗaukewa, amma duk da haka ta daure ta shiga baza idanunta a falon. Tsaye a bakin kitchen ta ga Hajjara na wani irin murmushi me kama da na mugunta.

Dama ita tasan za’a rina, shi yasa sam bata yarda da matar wan nata ba, dan ko abincinta bata ci, ita da kanta take girka abincinta.

“Ka yi haƙuri Aky!…”

Da ƙyar ta furta hakan, muryarta a shaƙe, dan bata san numfashinta ya ɗauke.

“Baki da magana da ta wuce hakan ai, ke kullum cikin aikata laifi, yau kina wannan gobe kina wancan, ni kenan kullum cikin sintiri a hanyar makarantar ku!, Kin girma amma baki san kin girma ba, saboda Allah yanzu yarinya kamar ke ace bata san ciwon kanta ba?, to bari ki ji na faɗa miki idan har baki kama kanki ba, wallahi sai na saɓa miki!”

Har yanzu cikin ƙaraji yake maganar, yayin da Mishal ta runtse idonta tana kawar da kanta gefe, duk da isashiyyar iskar dake falon ita sam bata iya jinta a huhunta, sam bata jin wata iska na kai mata inda ya dace.

“Haba Abbakar? Ya haka dan Allah?”

Mama ta faɗi cikin tausasawa.

Abubakar na maida numfashi kamar wanda ya yi gasar tsere ya kalleta. Kafin a fusace ya fice daga falon.

Hajjara ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, duk ƙaunar duniya sai a ce Mishal, komai Mishal komai Mishal, hatta da makarantar da take ta fi ta Hammad tsada, kuma har mota ya siya mata tare da ɗaukar mata driver, bayan ita nata ɗan a school bus yake tafiya. Koma dai miye yau ranta ya yi fari tunda har ya mata faɗa. Ta kaɗe gefen rigarta ta yi sama, dan taje ta bawa Fati labari.

“Zauna Mishal…”

Mama ta faɗi tana zaunar da ita, tare da sauƙewa jakar bayanta, ta ciro littafi a ciki ta shiga mata fiffita. Kafin ta samu ta dawo hayyacinta.

“Kin sha maganinki ?”

Kai ta gyaɗa mata tana miƙewa, ba tare da tace mata komai ba, ta ɗauki jakarta haɗi da lunchbox ɗinta ta fita.

Mama ta bi bayanta da kallo, zuciyarta cike da tausayin yarinyar.

“Allah ka kawo mata sauyin rayuwa!….”

Wata ƙila ta faɗa a bakin ‘yan amin, wata ƙila Allah ya zaɓeta ne dan ta zamo silar yin addu’ar wani abu dake shirin faruwa kwanaki masu zuwa.

Addu’ar tata, ita ce ta zama silar faruwar wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwarta a ‘yan kwanaki masu zuwa. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryuwar wasu lamura.

Brickhall School, Kaura district, Abuja

09:40am

RABI’A POV.

“Gashi, driverna na bawa saƙo ya siyo min, kuma ya ce ya nema amma bai samo irin wannan ɗayan ba, sai ɗan kwali ya samo…”

Cewar Mishal, yayin da take miƙa mata lalle ɗan kwali.

Rabi’a ta sa hannu ta karɓa. Tsaye suke a bayan ajujuwan makarantar, a ƙofar store, inda ake aje kayan share-share na makarantar.

Rab’a ta juya ta kalli dama da hagun inda suke tsaye.

“A ina zamu yi kenan ?”

“Ga kujeru a can, muje mu zauna”

Kuma da ga haka, suka ƙarasa inda kujerun suke, suka zauna, sannan Rabi ta shiga haɗa lallen. Yayin da Mishal ke dudduba jakarta, a ciki ta ɗauko biscuits, ta buɗe ta shiga ci. Cike da mamaki Rabi’a ta kalleta.

“Bakya azumi ne ?”

Mishal ta yi murmushi, har karafunan braces ɗin da aka sa mata suna bayyana.

“Wahala ce ba zan iya ba, ga zuwa makaranta ga azumi, inaaa!”

Rabi’a ta yi dariya, a kamaninta idan ka ganta sai ka ce tana da wasu shekaru masu yawa,amma da zarar ka yi magana da ita ko na minti uku ne za ka fahimci yarintarta ƙarara.

“Shekarunki nawa ?”

Mishal ta dakata da taunar biscuits ɗin dake bakinta, ta ɗan ɗaga olive green colour eyes ɗinta, tana san ta tuna shekarun nata. Kafin ta sauƙe su a kan Rabi’a dake ɗaure ledar lallen da ta gama haɗawa.

“I’m 17, next year zan cika 18….”

Rabi ta ɗage girarta cikin murmushi tana kallon lallen da ta gama ɗurewa.

“Ki ce babbar yarinya ce…”

Mishal ta yi dariya, wani abu da ba kasafai ta cika yinsa ba.

“Ke fa shekarun ki nawa ?”

“Ki ƙara biyu a kan naki”

“Sha tara ?”

Rabi’a ta gyaɗa mata kai. Ganin ta gama haɗa lallen yasa Mishal maida sauran biscuits ɗinta cikin jaka, tana karkaɗe hannunta, tare da taune sauran wanda ke bakinta.

Ta miƙawa Rabi’a hannunta na dama, sannan Rabi’a ta fara zana mata lallen.

“Wow!, Amma fa ta yi kyau”

Mishal ta faɗi a karo na barkatai, sanda aka gama zanen lallen, ta ɗaga hannayenta sama yafi sau a ƙirga, sai kallon lallen take tana sakewa. Ba za ta ce when last rabonta da ba.

“Nawa ne kuɗin lallen ?”

Sai ta ga Rabi’a ta haɗe rai.

“Shekaru nawa na baki ?”

“Biyu”

Ta masa tana mamakin abinda ya haɗa tambayar da ta mata da kuma wannan batun.

”Kinga kenan ni yayarki ce, kuma ina matsayin yayarki ai bazan karɓi kuɗin lallenki ba…”

“Yanzu mun zama ‘yan uwa kenan ?”

Rabi’a ta gyaɗa mata kai tana murmushi.

“Adawiyya ?”

Zuciyar Rabi’a ta dunguwar a lokaci guda, Adawiyya?!, kaf duniyar nan mutane biyu ne ke kiranta da sunan, Ummanta, da kuma yayarta Baby!.

Unguwar Madallah, Suleja, Niger state

05:30pm

“Wai har sun muku hutun?”

Cewar Saratu, yayin da takewa Rabi ƙananun kalba.

“An musu dai”

Rabi ta bata amsa. Suna zaune ne a ƙofar ɗakinsu, bayan Rabi’an ta dawo daga wurin aikinta ne ta share gidan tas, duk da wahalar rana da kuma aikin da ta je ta yi, ga kuma azumin dake bakinta.

Amma haka ta share gudan tas, kuma bayan ta gama ta ɗora da wanke-wanke. A lokacin Saratun tace mata ta zo su fara kalbar, tun da ta riga ta tsefe.

“Ai har ke, tun da de ba za ki je makarantar ba har sai an koma”

Rabi dai bata sake cewa komai ba, dan tun da ta ambaci kalmar ‘makaranta’, tunaninta ya tafi ɗazu, ta shiga tuna abinda ya faru tsakaninta da sabuwar ƙanwarta a ɗazun.

“Jibi za mu tafi garinmu, a can za mu yi bikin sallah”

Muryar Mishal ɗin ta katseta a ɗazun. Sai kawai ta yi murmushi.

“Ina ne garin ku ?”

“Maiduguri”

Mishal ta bata amsa tana firfita lallen hannunta da iskar bakinta. Rabi’a ta gyaɗa kanta. Tana ƙara tabbatarwa da kanta hasashen da take a kan Mishal ɗin, na kasancewarta shuwa arab.

“Shikenan, na san zuwa yanzu an koma break, bari naje na share inda aka ɓata, ki kula da kanki, Allah ya dawo da ku lafiya, sannan ki gaida Mamanki idan kin koma gida”

Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi, amma maganar Mishal ɗin ta gaba ita ce ta hanata tashin.

“Mamata bata raye, kuma tun a sanda zata haifeni ta rasu, ban san babana ba ma, lokacin da cikina ya rasu, tare da yayana kawai na taso…..”

Rabi’a ba za ta iya cewa ga abinda take tunanin ba a lokacin, tasan dai kawai ta tsirawa ƙaramar yarinyar ido ne, tana nazarin ya akayi ta rayu tsawon shekarunta babu iyaye. Ita da ta rasa iyaka mahaifiya ma kawai rayuwarta ta hargitse bare ita da ta rasa duka biyun.

Kuma bama wannan ba, ba ma ta sansu ba, bata taɓa ganin ko ɗaya daga cikinsu ba.

“Ke Rabi? Tashi ki zo ki soya mana doyar nan!”

Muryar Habiba ta dawo da ita zahiri, a hankali dubanta ya kai kan Habiban dake tsaye a kansu.

“Umma ki bari mana na ƙarasa mata, saura guda biyu fa….”

“Ban yi niyya ba, yanzu nake so ta tashi ta min aiki na….”

Ba tare da Rabi’a tace komai ba, ta shiga ƙoƙarin jan doguwar kalbar dake riƙe a hannun Saratu dan ta miƙe, amma sai Saratun ta mayar da ita ta zaunar.

“Gaskiya Umma ba kya kautawa, Wallahi wannan ba adalci ba ne, yarinyar nan ta je ta yini tana aikin bautar da ba ita take cin kuɗinta ba, dan ke take kawowa, sannan ta dawo ta yi aikin gidan nan, kuma yanzu ta samu ana ɗan mata kalbar da za ta yi adon salla sai ki ce baza’a mata ba ?!”

Habiba ta ɗan sunkuyo tana miƙowa Saratu bayanta.

“Da ke ni mama Saratu, na ce inji didim!, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci….”

Ta miƙe tana ci gaba da faɗin.

“Na taɓo uwr ki Rabi ko?, To baki isa ba, dole sai ta tashi ta soya doyar nan!….”

Kafin Saratu ta sake cewa wani abu, Rabi ta yi wuf ta miƙe tsaye, tana ƙoƙarin ɗaure kanta da ɗankwali. Gashin kanta da tsayinsa ya ragu a yanzu ya kwanta luf a gadin bayanta, har yana reto.

“Gaskiya Umma na gaji!, Wallahi na gaji da abinda kikewa yarinyar nan a cikin gidan, ita ma fa ‘ya ce, kuma ko baabaarta bata raye hakan ba ya nufin a cusguna mata. Umma kema uwar ‘ya’ya mata ce, wata rana gidan wani za muje. Na tabbatar da idan uwar miji ko ‘yan uwansa suka mana haka ba za ki ji daɗi ba. To ita ma kamar haka ne, tana da dangi bayan mu. Dan tsabar san zuciya irin naki yau shekarar yarinyar nan biyar a gidan nan, amma kin hanata ta je ta ga dangin mahaifiyarta, dan kar ta je ta faɗi irin azabar da ake bata a cikin gidan nan su hanata dawowa ki rasa baiwa. Wallahi Umma wannan ba adalci ba ne, ke ba kya tunanin wata ƙila wannan abun da kike shi ne ya zama sannadiyyar tagayyarar mu?, Ita ‘yar taki ta fari, bata jin daɗin aurenta, sannan ni, shekaruna 27, amma na rasa mijin aure, ko sau ɗaya saurayi bai taɓa zuwa ƙofar gidanan yace yana sallama da ni ba, ga kuma Mama, wadda ta lalace da bin maza!…..”

“Ya ishe ni haka Saratu, ki rufa min baki ko na make ki a wurin!”

Saratu ta share guntuwar ƙwallar da ta zubo mata ta buɗe labulen ɗakinsu ta shige ciki.

Rabi’a da ke kiciniyar hura wuta ma ta share tata ƙwallar, saboda tunawa da ta yi da dangin Ummanta, ta tuna yanda suke matuƙarsanta da ‘yar uwarta, sai kuma tunanin Anti Saratun, Allah ya sani kuma ita ma ta sani, ba ƙaramin cutuwa baiwar Allahn nan take da zaman gidan.

Kuma ta san cewa Anti Saratun na matuƙar san aure, dan tasha kamata tana kuka, kan abun da ke damun rayuwarta, sai dai ta zauna ta bata baki har ta samu ta yi shiru.

<< Labarinsu 4Labarinsu 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×