A hankali Zaid da ya dawo daga masallaici ya zauna ɗan nesa da ita. Kallonta kawai yake yana san sanin me ya kamata ya yi?. Ga ɗan uwansa a cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa, ga kuma matarsa da ke cikin tashin hankalin rasa mijinta, shi kansa idan za’a rarrasheshi so yake, dan ba ya so Aliyu ya sake tafiya ya barshi, ji yake kamar ya saka igiya ya ɗauresu da juna, gudun kada wani abun ya kuma zuwa ya gifta a tskaninsu.
Sai de kuma a matsayinsa na namiji, kuma babba, dole ne ya haɗiye nasa tashin hankalin, ya san hanyar da zai bi dan ganin ya kwantar da hankalin matar ƙaninsa.
Bakinsa ya buɗe zai yi magana, idonsa ya sauƙa a kan Rabi’a da Rhoda da suka shigo corridor ɗin ɗakunan.
A hankali Rabi ta yi a jiyar zuciya bayan ganin mijinta cikin ƙoshin lafiya, sai de hankalin nata be gama kwanciya ba sai da ta tafi da gudu ta yi wurin da yake, miƙewa tsaye ya yi yana kallonsu. Rabi ta manta da Rhoda dake bayanta, da kuma Mishal ɗin da hamkalinta bai ma kai kanta ba. Ta yi saurin rungume mijinta tana shafa bayansa. Shi ma riƙeta ya yi da kyau a jikinsa, yana jin kamar ya fashe mata da kuka. A hankali ta sake shi tana ci gaba da duba jikinsa.
“Me ya faru?…”
Ta tambaya tana yawatawa da idonta a kewayen wurin da suke, bata rufe bakinta ba idonta ya sauƙa a kan Mishal dake zaune a kan kujera, ta sunkuyar da kanta ƙasa, gashin kan nata a yamutse, ga jinin da ya fara bushewa a gefen fuskarta. A kiɗime ta zauna kusa da ita tana rungumota jikinta. Mishal na jin kanta ya sauƙa a kafaɗar Rabi ta saki kukan da yake cin ruhinta tun safe. Kukan da Mishal ɗin ke yi ne ya ƙara karya zuciyar Rabi. Mishal na rungume a jikinta ta juyo da kanta ta kalli Zaid dake tsaye yana ƙoƙarin hana hawayensa zuba.
“Raj! Me yake faruwa wai?”
Zaid ya ɗan kawar da fuska yana ɗaga kafaɗarsa.
“Aliyu ne ba shi da lafiya”
Sunansa kawai da ta kira ne ya ƙara karya zuciyar Mishal, ta ƙarawa kukanta ƙarfi tana ƙanƙame Rabi a jikinta. Da Zaid ya ga ba zai iya ɗauka ba, sai ya yi wa Rhoda alama da ta biyoshi, ya kama hanyar barin corridorn.
Duk yadda Rabi ta so Mishal ta kwantar da hankalinta ya gagara. Kukan ma da ƙyar ta sakata ta dena shi. Sai hawayen da take gogewa. Sai wajajen ƙarfe takwas Zaid da Rhoda suka dawo.
Zaid ɗin ya umarci Rhoda da ta ɗauki Rabi da Mishal ta kaisu gidansa, kuma ita ma kar ta tafi, ta zauna ta kwana tare da su. Kamar wata gawa haka Rabi ta miƙar da Mishal ta shiga janta zuwa waje, dan bata ma san inda take saka ƙafarta ba, duk inda aka jata bi take kawai.
Rhoda da Mishal suka shiga mota, yayin da Rabi da Zaid suka tsaya daga can nesa da su. Rabi ta goge ƙwallar idonta ta tausayin mijinta da kuma ƙanwarta, ta kai hannunta ta dafa kafaɗar Zaid ɗin ta dama.
“Ka ci abinci?”
Kansa ya juyo ya kalli fuskarta ta cikin hasken fitilun dake wadace a harabar asibitin. Nan take idon nasa ya cika da ƙwalla. Sai ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya na barin hawayen fita daga inda ya tsaresu tsawon ranar.
“Ban ci ba”
Ya amsa mata a raunane. Rabi ta ci gaba da kallonsa, tana jin ina ma tana da damar da za ta buɗe zuciyarsa, ta cire wannan damuwar da yake ciki. Ƙwalla ta kuma gogewa tana faɗin.
“Na ga ko wanka ma ba ka yi ba. Amma ya kamata ace ka ci abincin”
Sai ya ɗago da lumsassun idanuwansa ya ɗorasu a kanta yana ɗage kafaɗarsa ta dama.
“Adawiyya ta ya kike tunan zan iya cin abinci a irin wanna yanayin da nake ciki, ni yunwar ma kanta ba na ji. Kaina ne kawai ke min ciwo, ji nake kamar zai tarwatse!”
Sai ta ɗan yi tattage tana riƙe kan nasa.
“Ka ga ba?. Yunwar ce ta saka mata ciwon kan, ka daure ka taɓa wani abun, sai ka sha magani, Aliyu ba zai ji daɗi ba idan har ya ji cewar baka ci abinci ba!”
Kiran sunan Aliyin ya sa wata ƙwalla ta ƙara sauƙowa daga idonsa. Rabi ta saka hannyenta ta share masa duka ƙwallar.
“Na san kana da dauriya da kuma juriya, ka ƙara kan wadda kake da ita, Allah zai tashi kafaɗun Aliyu!…”
Da sauri ya saka hannyensa biyu ya kewaye waist ɗinta yana janta jikinsa tare da fashewa da kuka mara sauti. Ita ma Rabin kukan take. Tana shafa ƙeyarsa. Sun jima a haka kafin Zaid ɗin ya saketa ya na share ƙwalla.
“Ki san yanda za ki kwantarwa da…”
Sai kuma ya yi shiru, dan sunan nata ya kwanta masa. Rabi ta kai hannunta na hagu ta kama chain ɗin wuyansa, sannan ta yi amfani da hannunta na hagu ta kama wuyan rigarsa tana janyo shi gaba, kafin ta saka sarƙar a cikin rigar tasa tana faɗin.
“Mishal?”
“Eh Mishal… Ko sallah ba na jin ta yi, dan Allah ki kula”
Kanta ta gyaɗa tana sharar tata ƙwallar.
“Na je na an min gwaji, kuma na ci, dan har training mun fara!”
Bai iya ce mata komai ba, sai kansa da ya gyaɗa, daga haka suka yi sallama, shi ya koma zuwa cikin asibitin. Ita kuma ta nufi motar Rhoda.
Ko da suka isa gidan, wanka tasa Mishal ta yi, kafin ta bata wasu kayan cikin kayanta tace mata tasa. Sawar ta yi, sannan Rabi tace mata ta yi sallah tana zuwa. Sallar ta fara kafin Rabin ta dawo.
A falo ta iske Rjoda kwance a kan kujera tana waya da Zakar, yayin da take sanar masa halin da suke ciki a yau. Ba ta ce mata komai ba ta wuce kitchen. Ta shiga kiciniyar girka musu abinci. Kasancewar babu wani isasshen lokaci, ya sa ta yi gaggauwar girka musu jallof ɗin taliya.
Duka ta jiye musu it a tray, sannan ta fito da ita ta aje a falo, zuwa lokacin Rhodan ta gama wayar tana zaune tana danna wayar tata.
“Bari na kira Mishal…”
Ta faɗi tana nufar ɗakinta. Ko da ta shiga sai ta iske Mishal ɗin zaune kan darduma. Ba ta san me take ba,amma bisa ga dukkan alamu ba sallah take ba. Sai ta shiga cikin ɗakin tare da nufar inda take.
“Ƙanwata!”
Ta kira sunanta tana dafa kafaɗarta, firgiyar da da Mishal ɗin ta yi ya ankarar da Rabi cewar tunani take.
“Kin idar da sallahr?”
Mishal ta gyaɗa mata kai.
“Mishal! A yanzu Aliyu ba ya buƙatar kukanki ko damuwa, addu’a kawai za ki masa, da yardar Allah zai tashi!”
Wata siriryar ƙwalla ce ta biyo kuncin Mishal.
“Anti Adawiyya idan na tuna maraicina sai na ji kamar zan fasa ƙara. Ba ni da kowa fa, Aliyu shi kaɗai ne ya rage min, bayan shi ban da kowa. Idan ya mutu kuma ya zan yi?!”
Da sauri Rabi ta girgiza mata kai.
“Insha-Allah zai warke, zai tashi kin ji?”
Ta faɗi tana jan Mishal zuwa jikinta. Kafin ta saketa a hankali tana share nata ƙwalla.
“Mu je mu ci abinci…”
Mishal ta girgiza kanta. Rabi ta zare mata ido tana faɗin.
“A gidana ba’a min musu, dan haka salin-alin ki tashi mu je mu ci abinci”
Duk da halin da Mishal ke ciki be hanata yin murmushi ba. Tashin ta yi suka fita, a falon suka zauna a kan carpet suka fara cin abincin. Ko rabi ba su yi ba, Rabi ta ji amai na taso mata. Dan haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta da gudu.
“Lafiya?”
Mishal da Rhoda suka faɗi a tare suna miƙewa tare da bin bayanta da kallo.
“Zauna ki ci gaba da cin abincin, ni zan je na dubata”
Cewar Rhoda. Ba dan Mishal ta so ba, haka ta zauna tana ta kallon ƙofar ɗakin Rabin.
“Sannu! Sannu kin ji… Sannu!”
Rhoda ke ta jerawa Rabi sannu, wadda ke ta amayar da taliyar da ta samu shiga cikin. Bakinta ta wanke tana jingina da bango, bayan da ta gama aman.
“Baki da lafiya ne?”
Rabi ta girgiza kai tana dafe cikinta.
“To sannu”
Falon suka dawo, inda Rabi tace ita fa ta ƙoshi, dan haka su su ƙarasa cin abincisu. Babu yadda Rhoda ba ta yi da ita ba kan ta daure ta ƙara abincin, amma tace ita ta ƙoshi. Haka suka ƙyaleta su ma suka ci gaba, da ƙyar Mishal ta iya cin abincin da yawa. Kafin Rabi ta ɗauke trayn ta kai shi kitchen, ta fito tana faɗin.
“Sai mu kwanta ko?”
Rhoda ta miƙe tana faɗin.
“No, ku de ku je ku kwanta a ɗaki, ni a nan zan kwana!”
Rabi ta girgiza kanta.
“A’a… Ke ma zuwa za ki yi mu kwanta, gadon fa babba ne, zai ɗaukemu mu uku”
“Ok, mu je”
Da haka suka koma ɗakin, gadon kuwa tas ya ɗaukesu su ukun, har da sauran space. Rabi da Rhoda ne kawai suka yi bacci, ban da Mishal ɗin da ta kwana ido buɗe. Dan ba ta jin za ta iya baccin, hakan ya sa daren ya mata tsawo, fiye da sauran dararen da suka shuɗe a rayuwarta.
Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja
ZAID POV.
Zaune yake a kan kujera ɗaya dake cikin ɗakin da Aliyu ke kwance. Ya kafe Aliyun da ido, kamar idan ya kira sunansa zau amsa. Hannunsa ya kai ya shafa sumarsa tun daga gaba zuwa baya. Sannan ya dawo da hannun nasa kan bakinsa.
Aliyun dake kwance kan gadon marasa lafiya, ba ya iya numfashi sai da temakon na’urar numfashi. Ba ya jin zai iya ko da rintsawa. Dan gani yake kamar idan ya kumshe idonsa na minti ɗaya, Aliyu zai iya ɓacewa. Haka ya ci gaba da zama a wurin, har zuwa asuba.