ZAID POV.
Yana fita da Rabi’a ba su tsaya a ko ina ba sai wani ɗaki dake kusa da wanda aka kwantar da Aliyu, kasancewar ɗakin babu kowa. Suna shiga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakin ya rufe, sannan ya jingina bayansa a jikin ƙofar. Yana miƙawa Rabi dake tsaye hannunsa, kamawa ta yi, shi kuma ya jata ta faɗo kan jikinsa, ya saka hanyyensa duka biyu ya rungumeta.
Ita ta ɗago daga jikin nasa tana faɗin.
“Ka ji yanda kayan jikinka suke warin gumi?”
Jikin nasa ya shinshina yana faɗin.
“To ya zan yi da rayuwa, larura ta sa na koma ƙazami, kwana ɗaya ban yi wanka ba fa, ga mu yau a na biyu…”
Ta ɗan yi dariya tana mayar masa da chain ɗin wuyansa ƙasan rigar jikinsa.
“Rhoda tace na faɗa maka, ita ta wuce gida, za ta je ta shirya, wai ku haɗu a kotu”
“Uffff! Kin ga Wallahi shaf na manta!”
Ya faɗi yana dafe kansa.
“Abubuwan nawa ne da yawa, kinga kuma ko su kawu Abdullahi ban kira ba, dan kin san ya kamata na sanar da su halin da ake ciki”
Ta gyaɗa kai.
“Haka ne… Abun da ya fi kawai yanzu ka koma gida ka je ka yi wanka, ka sauya kaya, sai ka wuce kotun… Kuma ga abinci nan ma na kawo maka”
Kansa ya girgiza.
“Ba na jin zan iya tafiya na bar Aliyu shi kaɗai”
“Wa ya faɗa maka cewar Aliyu shi kaɗai ne, akwai ni, ga kuma Mishal”
“Idan kuma wata buƙata ta taso wadda dole sai kun buƙace ni fa?”
“Da yardar Allah har ka dawo babu wata matsala da za ta faru”
“Kin tabbata?”
Ta gyaɗa masa kai. Sai da ya ƙara janta jikinsa ya rungume, sannan suka fita a tare. Ganin wata mata da ban a ɗakin zaune kusa da Aliyu ya basu mamaki.
“Ƙaraso Zaid. Wanan ita ce Anna!”
Cewar Aliyun yana nuna masa matar dake sharar ƙwalla. Anna ta juyo tana kallon me kama da ɗanta.
“Zo nan, ai kai ma ɗana ne”
Anna ta faɗi tana miƙa masa hannu. Zaid ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Suka sakata a tsakiya, idan ta juya ta kalli Zaid, sai ta juya ta kalli Aliyu, kafin idonta ya sauƙa a kan Rabi dake tsaye kusa da Mishal.
“Wannan ita ce matar taka kai ma?”
Zaid ya gyaɗa mata kai. Zaid ya ɗan jima a ɗakin, kafin ya musu sallama, bayan ya faɗa musu uzurin da zai je. Har yabkama hanyar barin ɗakin,maganar Aliyu ta dakatar da shi.
“A dawo lafiya Zaid”
Sai da ya juyo ya kalleshi, kafin ya gyaɗa kansa yana fita. Rabi ta bi bayansa suka fita tare har zuwa jikin motarsa. Shiga ya yi, kana ya buɗe ɗayar ƙofar dake side ɗin da Rabi ke tsaye, ya mata alama da ta shigo, shiga ta yi ta zauna.
“Ban sani ba ko zan jima ban dawo ba, saboda ana gama shari’ar, za mu wuce na kai Rhoda karɓar musulunci”
Sai ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsa.
“Me kike so na kawo miki yau?”
“Ba na buƙatar komai, kawai kai nake so?”
Sai ya ɗage mata gira ɗaya yana faɗin.
“Ni da kai na?”
Ta yi dariya tana gyaɗa masa kai.
“In dai ni ne kin samu ‘yan matana, and zan kawo miki kifi, ko shi ɗin ma ba kya so?”
Ta girgiza kanta.
“Ina so”
Zaid ya ɗaga kafaɗa cikin faɗin “To sai na dawo?”
“Ummm”
“Kuma tafiya za ki yi ba tare da kin…”
Tureshi ta yi tana dariya.
“Zaid hoo, baka jin magana Wallahi!”
“To ni ki min”
Juyowa ta yi tana kama fuskarsa, kafin a hankali ta yi kissing ɗinsa.
“Shikenan?”
Ta faɗi tana ja baya. Fita ta yi daga motar, tana rufo masa ƙofar.
“A je a yi wanka, a ƙazan-ƙazan”
Ta faɗi tana leƙo da kanta.
“Lalle kin ci tuwo a kaina Adawiyya, amma zan rama”
Ta bar wurin tana dariya. Ya tayar da motar yana ƙara sinsinar jikinsa.
“Wanka daɗi, wani bai san daɗin wanka ba”
Ya yi waƙar yana juya kan motar.
Believe in your dreams…
Anna da Rabi ne suke tafe, bayan da suka dawo daga wani shago da suka je dan siyan ruwa, duk yanda Rabin ta so Anna ta zauna kan ita za ta je, fir Anma ta ƙi yarda, tace sai de su je tare. Dan ita tausayin Rabin take. A kallon farko da ta mata ta gane cewar tana ɗauke da ciki!, shi ya sa take tunanin kamar ba za ta iya ɗaukan ruwan ba. Amma sai ga shi bayam da suka siyo ruwan ma ba ta bar Annan ta ɗauka ba.
Ba tare da Rabi ta ankara ba, ta ji juwa ta ɗebeta, ta yi baya luuu za ya faɗi, ledar robobin ruwan dake hannunta ta faɗi ƙasa. Anna ce ta yi saurin kamota.
“Sannu!… Kin ga ko?, shi ya sa na ce ki bari na ɗauka, macen dake cikin hali irin naki ba’a barinta ta ɗauki abu me nauyi!”
Cikin rashin fahimta Rabi’a tace.
“Babu komai fa Anna, wallahi ƙalau nake”
Anna ta ɗauki ledar tana dariya.
“Haba ‘yanan, ai mace me ciki ba a rabata da laulayi!…”
Wani shaftareren yanki na zuciyar Rabi’a ne ya yanke ya faɗo ƙasa, wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bomb ya fashe a ƙirjinta, ta sandare a wurin, ta kasa motsa ko da ƙafarta, sai idanuwanta da ta zaro suna duban Anna. Ciki fa?, wai ita ?, ita Rabi’a take da ciki?.
Ganin haka ya sa Anna fahimtar cewa ba ta ma san cewa tana da cikin ba.
”Baki sani ba kenan?”
Kamar wata sokuwa haka ta gyaɗa kanta.
Zaune take a kan ɗaya daga cikin kujerun dake wani corridor, har zuwa yanzu ta kasa yarda da abun da ta ji, wai ita ce take da ciki, to garin yaya, daga sau ɗay!…
Kunyar kanta da ta kamata ce ta sa ta kasa ƙarasawa. Ta yi jigum-jigum, tana jiran fitowar result ɗin gwajin da aka mata. Wata nurse ce ta fito daga ɗakin da take fuskanta, ta shiga kiran sunayen mutanen dake zaune a wurin, da haka har aka iso kanta, ta karɓi nata result ɗin tana komawa baya, tare da zama a inda ta tashi.
Hannunta har rawa yake wurin buɗe takardar. Tar manyan rubutun da takardar ke ƙunshe da su ke sanar mata cewar tana ɗauke da ciki na sati huɗu. Kanta ta sunkuyar ƙasa tana shafa cikinta. A lokacin kuma ƙwalla ta zubo mata. Yanzu kenan ciki gareta?, cikin ma kuma ba na kowa ba sai na Zaid!.
ZAID POV.
Bayan hujjojji da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Alhj Bala hukuncin ɗaurin rai da rai, sauran abokan harƙallarsa kuma, ciki har da Garuje, an yanke musu hukuncin dai-dai da nasa, Usman da sauran abokansa kuma, an yanke musu shekare ashirin-ashirin a gidan kaso. Kuma da haka shari’ar ta zo ƙarshe.
Bayan shuɗewar tsawon shekaru, sai a yau ne Rhoda ta samu adalci kan abun da aka aikata mata, ba ma ita kaɗai ba, hatta da Rabi a yau ne aka sama mata ‘yanci. Daga kotun kai tsaye Zaid ya wuce da Rhoda masallacin da ya yi magana da limaminsa, dan shi yake so ya bawa Rhoda kalimatu shahadah.
No.86, Garki 2, Abuja…
08:00
Rabi da Zaid ne zaune a falo suna kallo a tv. Rhoda kuma na ɗakin da Rabi ta ware mata, dan yau a gidan zata kwana.
“Mts! Ammata na manta da kifinki a mota, bari na je na kawo miki”
Cewar Zaid yana miƙewa tare da barin falon. Rabi ta sunkuyar da kanta ta kalli cikinta. Tun bayan dawowarta gidan take ta neman hanyar da za ta faɗawa Zaid wannan kyakkyawan labarin, amma ta rasa ta inda zata fara.
Kallo ta ci gaba da binsa da shi, har ya dawo hannunsa riƙe da leda, ya buɗe ledar, ƙamshin kayan haɗin da aka yi amfani da su wurin haɗa kifin ya bugi hancints, hakan ya sa ta ji amai ya zo mata. Ba shiri ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta.
Baki sake Zaid ya bi bayanta da kallo, kafin shi ma ya miƙe ya nufi ɗakinta da ya ga ta shiga. Ko da ya isa ɗakin sai ya tarar da har ta faɗa bayi, ta kuma kulle kofar bayin. Maganar duniya mata amma ta ƙi amsa shi hakan ya sa ya juyo, ya na shirin barin ɗakin, idonsa ya sauƙa kan wata takarda aje a kan hijabinta. Don haka sai fasa fitar, ya dawo ya ɗauki takardar ya shiga karantawa.
Sai da Rabi ta gama aman nata, ta wanke bakinta, sannan ta fito. Damm, gabanta ya buga, ganin Zaid tsaye a tsakiyar ɗakin, hannunsa riƙe da takardar da ta manta bata ɓoye ba, kuma ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, wani irin kallo da ta ga yana mata shi ya haɗe kayan cikinta waje guda. Da ƙyar ta haɗiye yawu ta fara takawa tana nufarsa.
“Adawiyya miye wannan?”
Ya tambaya yana nuna mata takardar, sai da cikin Rabi ya yamutsa, jin yanda amon muryarsa ya fito a ƙasashe.
“Ba magana nake miki ba?!”
Ya faɗa cikin tsawa, yana ƙoƙarin saka ƙaton dutse, dan danne ɓacin ran dake taso masa. Abun ya bala’in ɓata masa rai, a matsayinsa na uban ɗan cikinta, kamata ya yi ace ta sanar da shi, amma me ya sa za ta ɓoye masa?.
Sosai Rabi ta tsora, ganin yanda ya buɗe lumsassun idanuwansa a kanta. Hakan wani abu ne da bata taɓa gani ba a tare da shi, nan take ta fara in’ina.
“Ko ba ni ne uban cikin jikinki ba ya kamata ace na sani, ballantana na san da cewa ni ne ubansa, me ya sa za ki ɓoye min?!”
A wannan karon kam ita ma Rabi ranta sai ya fara ɓaci. Dan haka tace.
“Miye laifi na a nan?, ni kai na ban san cewa ina ɗauke da ciki ba, sai bayan da Anna ta ankarar da ni, hakan ya sa na je na yi gwaji a yau ɗin nan, kuma shi ma gwajin ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu. Tun bayan dawowarka nake ta neman hanyar da zan bi na faɗa maka, amma na rasa, shi ne na yi laifi?…”
“A’a kam, ba ki yi laifi ba!. Tun ɗazu na dawo gidan, me yasa da na dawo ba ji faɗa min ba?!”
“Ya isheni haka Zaid!”
Ta faɗi ita ma a tsawace tana kallon cikin idonsa.
“Wai akaina aka fara ciki?. Na ce maka ƙoƙarin gano hanyar da ta dace na faɗa maka nake, amma sai ka hau ni da faɗa?, na ga dai ba wata tara cikin ya yi ba tare da na sanar maka ba!”
“Ya yi kyau Adawiyya, yau kanki tsaye kike kiran sunan, a kan wannan cikin kike gaya mun duk maganar da ta zo bakinki ko?, ki riƙe abunki na bar miki!”
Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya aje mata takardar ba.
Rabi ta zame ƙasa tana fashewa da kuka. Me ya sa ma za ta bari har sheɗan ya shiga tsakaninsu?, kuma ai shi ma ya na da laifi, mi ye na saurin fusatar haka?, tun bayan aurensu ba su taɓa faɗa ba sai yau, hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, har ta kwanta bata dena kuka. Bacci ma a ranar sai ya gagareta. Ta rasa inda za ta sa kanta, musamman idan ta tuna da yanda ta ɗaga masa murya, abun sai ya soketa a zuciya.
Ganin zama cikin kukan ba zai finsheta ba ya sa ta miƙe salin’alin ta nufi ɗakinsa, ƙofar ta tura a hankali tana saka kai ciki. A kunne ta samu wutar ɗakin, shi kuma ya na zaune daga kan gado, ya zuro da ƙafafaunsa ƙasan gadon. Kuma duk da ya bawa ƙofar baya, tana iya ganin yanda ya yi tagumi. Wani kuka me ƙarfi ya ƙwace mata, dan gani take kamar ita ce silar rashin kwanciya baccin nasa.
Da gudu ta hau kan gadon nasa, ta shiga rarrafe a kan gadon, har ta isa inda yake, tana isa dab da shi, ta zura hannayenta ta bayansa, suka kewayo ta gaba, kanta ta kwantar a bayansa tana fashewa da kuka.
Zaid ya rintse idonsa, zuciyarsa na masa zugi, yanzu haka zaman da ya yi na nadama ne, sai bayan da ya zo kwanciya ya ga rashin kyautawarsa kan abun da ya mata, be kamata ace ya ɗaga mata murya haka ba, kuma be kanata a ce ya fusata daga ganin takarda ba. Zaman da ya yi anan yana ta tsara yanda za ayi ya bata haƙuri ne gobe da safe, sai ga shi kuma ita ta zo da kanta dan ta ba shi haƙurin.
“Ka yi haƙuri Raj, na tuba!”
Da ƙarfi ya sauƙe ajiyar zuciyar, sannan ya saka hannayensa a kan nata yana rabasu daga ruƙon da ta masa, sannan a hankali ya sauƙo da ido daga kan gadon, ta dawo gabansa ta tsaya. Ya ɗan ɗaga kansa ya kalleta, fuskar nan sharkaf da hawaye. Sai ya raba cinyarsa biyu, ya zaunar da ita akan ta dama. Tana zama a kan cinyar tasa ta ƙara shigewa cikin jikinsa, tana nanata masa kalaman ban haƙuri. Shi ma rungumeta ya yi, ninkun ƙauna da santa na ƙara shiga cikin zuciyarsa.
“Ya isa haka Adawiyya, ko tsakanin harshe da haƙuri ana samun saɓani. Wannan karon sheɗan ya yi nasara a kanmu, dan haka sai mu kiyaye nan gaba”
Kanta ta gyaɗa masa tana shanye kukan nata.
“I’m sorry too, na faɗa miki maganganu masu zafi”
Kanta ta girgiza tana ɗagowa daga jikinsa. Hannunsa ya kai kan cikinta, yana jin santa da kuma na abun da ke cikinta na ƙara kama shi.
“Ina sonki Ammatana. Wannan babbar kyautar taki ta fi min komai a yanzu”
Ƙara kwanciya ta yi a jikinsa tana lumshe ido.
“Allah alhamdulillah”
Ya faɗi yana ƙara matseta a jikinsa.
“Ina sanki ‘yan matan Zaid”
“Ina sanka Kayali! (Arabic:My choice)”
Sai ya ɗan kalleta kaɗan.
“Da ma ke kika zaɓeni?. Ca nake ai ƙaddara ta zaɓa miki ni”
Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana shirin saka masa kuka, sai ya yi dariya yana ƙara kwantar da ita.
“Ki yi haƙuri. Gaskiya ni me sa’a ne Ammata, a karon farko?”
Kanta ta ƙara cusawa a ƙirjinsa dan tsabar kunya.
“Diary baka da kunya”
Muryarta ta fito daga ƙasan ƙirjinsa. Ya yi dariya.
“Wallahi ji na nake kamar wani sabon mutum, ji nake kamar yau aka haifo ni, duka burikana ɗaya bayan ɗaya suna cika…”
Ya faɗi a setin kunnenta. Sai ta ƙara narkewa a jikinsa tana lumshe ido. dan wani bacci da take ji na shirin kamata.