KULIYA POV.
Kwance yake a kan gadon marasa lafiya na asibti, yayin da Mishal ke kwance a gefensa, kallon fuskarta kawai yake, yana tuna yadda ta yi mirƙisisi kan ita ba za ta tafi gida ba, don ita tare da shi za ta kwana. Baccinta take hankali kwance, kamar tsimma a cikin randa.
Juyawa ya yi yana kallon window, saboda wata iska me daɗi dake shigowa ta windown. A yanzu komai na rayuwarsa ya hau seti, ba ya jin akwai wani buri nasa da rage bai cika ba, komai ya setu, komai ya hau kan hanya, ya samu dangi, ɗan uwa, uwa, mata ga shi har da suruka, shi ko me zai yi in ba godewa Allahnsa ba.
Da ga nan kuma sai ya shiga tsara abubuwan da zai yi idan ya bar asibtin, dan ba zai yi shiru a kan abun da aka masa ba, kuma ya san ko suwa suka masa hakan, dan case ɗinsu shi ne aiki na ƙarshe da ya yi.
Haka Aliyu ya ci gaba da samun kulawar likitoci a asibitin, har zuwa lokacin da ya samu sauƙi, a cikin jinyar da ya yi, ‘yan uwansu na haɗejia duka sun zo sun duba shi, ba ƙaramin daɗi suka ji ba a sanda suka ganshi, kuma shi ma ya ji daɗin ganinsu sosai.
Bayan ya warke ne suka ɗunguma zuwa Hadejia su duka, domin bikin Rhoda, wadda ta zaɓi sunan Rauda a yanzu, dan bayan ta karɓi musulunci aka tambayeta sunan da take so a sa mata, sai tace Zaid ya zaɓa mata, shi da kansa yace ta karɓi sunan Rauda, dan yana kama da sunanta na da, kuma ma’anar sunan ma me kyau ce.
Haka aka sha bikin amarya Rauda da angonta Zakar. Wanda suka ci gaba da zama a haɗejia, kasancewar shi Zakar ɗin a nan haɗejian yake aiki.
BAYAN SHEKARU BIYAR…
No.275, Asokoro, Abuja…
Anna ce zaune a kan kujerar daning, su na magana da Aliyu dake zaune a kan kujerar dake facing ɗinta. Mishal ce ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da tray, wanda ta ciko shi da wasu warmers, ga tulelen cikinta tana turashi gaba.
“Sannu Hafsat. Kai Aliyu ka tashi ka temaka mata mana” cewar Anna.
Kuliya ya miƙe tsaye yana nufarta, trayn hannun nata ya karɓa, sannan ya ƙaraso ya aje shi a kan danning, ya koma inda Mishal take, ya kamo hannunta, tana takawa a hankali har suka iso danning ɗin, ya zaunar da ita a kusa da Anna ya na jera mata sannu, ita kuma ban da gyaɗa musu kai babu abun da take.
“Sai da na ce miki ki bar girkin nan, amma kika ƙi”
Anna ta faɗi tana dubanta, ita dai ba ta iya cewa komai, don tun bayan samun cikin nata ta koma muiskila, sam ba ta son yawan magana.
Ƙofar falon aka turo, Zaid da ya je ɗaukan Rabi’a a NFF (Nigerian Football Federation) centre ya shigo, sannan ita ma Rabin ta shigo tana biye da shi, sanye take da wata kimonoh, wadda ta saka jersyn Super Falcons a ƙasanta. Kasancewar yanzu haka suna training a kan gasar WACON (Women’s African Cup of Nation) da za’a buga nan da sati me zuwa. Dan zuwa yanzu Rabi ta zama ɗaya daga cikin ‘yan ƙwallon da ake ji da su a Nigeria, a taƙaicen-taƙaicewa ma a halun yanzu ita ce kw riƙe da wannan kambun na (Best African Women player). Duk yanda ƙungiyoyi da dama suke son siyanta ta ƙi, don ta ce ba za ta taɓa barin ƙasarta ta koma wata ƙasar ba, saboda mijinta da kuma ɗanta.
“Maman Junior har an dawo?”
Cewar Kuliya dake zubawa Mishal ruwa a cup.
“Wallahi na dawo Papi. Wai Mishal ke kika yi girkin nan?”
Rabin ta ƙarashe tana kallon kayan abincin dake zube a kan danning.
“Sai da na hanata, amma haka ta sulale ta shiga kitchen ɗin ba tare da na sani ba”
Cewar Anna, Mishal ta karɓi ruwan da Kuliya ke miƙa mata ba tare da ta ce musu komai ba.
“Ina Junior?”
Rabi ta tambaya, sakamakon rashin ganinsa a wurin.
“Junior! Junior!…”
Haka ta shuga ƙwala masa kira tana baza idonta, don ganin ta inda zai ɓillo.
Can sai ga wani kyakkyawan yaro dake tsantsar kama da Kuliya ya sauƙo daga kan stairs hannunsa riƙe da Ipad. Rabi ta bishi da kallo tana jinjina kai, wato yana jinta, amsawar ce ba zai iya ba, ita har mamakin lamarin Junior take, ko da ɗiso babu abun da ya baro a hallayar Kuliya.
“Papi na faɗi!”
Cewar Junior ɗin yana miƙawa Kuliya Ipad ɗin hannunsa. Kuliya ya karɓa ya na kallon yaron. Aliyu Zaid Aliyu kenan, a.k.a Junior, a.k.a Kuliya, a.k.a AZA, duka sunansa ne, ɗan auta a wurin kawunsa, kakarsa, mamansa, dadynsa, papinsa da kuma Nininsa.
Zaid ya ja kujera ya zauna yana faɗin.
“Wata ran sai na fasa ipad ɗin nan, in yabso na ga ta tsiyar… In ba wulaƙanci irin na Junior ba, ya za ayi mamansa ta dawo daga training, ta kirashi amma ya wuce wurin Aliyu yana faɗin wai ya faɗi a game?”
Kuliya ya kalli Zaid yana zaunar da Junior a kan cinyarsa.
“Ka fasa, ni kuma sai na sai masa sabuwa, ina ruwanka da sha’aninmu?, mu babu ruwanmu da kowa ba ehe”
“Junior Mama fa?”
Rabi ta faɗi tana kallonsa. Juyowa ya yi ya kalleta da gray eyes ɗinsa da shi kaɗai ne abu ɗaya da ya gado a wurin Zaid, amma hatta da buɗar idonsa irin ta Kuliya ce.
Sai kuma ya sauƙo daga kan cinyar Kuliya, ya tako zuwa wurin Rabi, ya ɗan mata wani gutun murmushi yana rungume ƙafafunta.
“Tafi ka bani wuri ba na so”
“Haka fa ni ma suka haɗe mun kai shi da Papi last week, wai dan suna kallon Film ɗin ‘Tara Dunken’ na zo na sauya, shi kenan suka dena min magan, sai jiya suka kulani”
Cewar Mishal tana aje cup ɗin hannunta.
“Ai ke na sati ɗaya suka miki ma, ni da suka fi sati biyu ba sa kulani fa in ce me?”
Cewar Anna cikin taɓe baki.
“Sorry Mama”
Cewar Junior kamar wanda aka yiwa dole. Rabi ta dunguri kansa tana faɗin.
“Ka dena wannan miskilancin naka, idan ka ce irin halin Papi za ka ɗauko wahala za ka sha, don ma de shi Papi an yi nasarar samun Nini ta seta masa hanya, kai ko sai de ka ci jibga, don dukanka zan fara…”
Shi dai bai ce mata komai ba, sai ƙasan kimonohnta da ya riƙe.
“Nini? Ashe ke kika seta ni?”
Kuliya ya tambaya yana kallon Mishal, ita ko tai masa banza, don ta san idan ta biyashi yanzu sai su zo suna cece ku ce, ita kuwa yanzu a duniyar Allahn nan magana ita ce abun da ke mata wuya, ba ta son yawan magana.
“Sai ku zo mu fara cin abin cin”
Cewar Anna.
“Bari na je na yi wanka tukunna”
Rabi ta faɗi tana ƙwace ƙasan kimonohnta daga hannun Junior. Kafin ta haye sama. Bayan ɗan wani lokaci Zaid ma ya miƙe ya bita.
Kuliya ya ci gaba da tsokanar Mishal, amma ko ci kanka ba ta ce masa ba, har sai da Anna ta masa magana kafin ya shafa mata lafiya.
“Ammatan Raj”
Zaid ya kira sunanta, yayin da take tsaye a jikin mirror tana shafa mai, juyowa ta yi ta kalleshi, shi ma kuma kallon nata yake, yayin da yake tsaye a bayanta.
“Kai wai baka san ka girma ba ne?”
Ta tambaya tana juyawa.
“Girman me?, ɗa ɗaya ne fa da mu kawai, ki bari sai mun tara kamar yara goma haka, sai ki ce na girma, amma ɗa ɗaya ai ya yi kaɗan ya sa na ga tsufana”
Rabi ta yi murmushi tana shafa mai a wuyanta.
“Saura kwana nawa ku tafi ne?”
Ya tambaya yana zuge mata zip ɗin rigarta da bata zuge ba. Rabi na kallonsa ta cin madubin gabanta ta furta.
“One week”
“Mun gode Allah, dan nan da kwana uku visar mu na iya fitowa”
Sai ta gyaɗa masa kai tana juyowa.
“Mu je ko?”
Ya girgiza mata kai yana kama waist ɗinta. Rabi ta ture shi tana faɗin.
“Su Anna na ƙasa suna jiranmu fa”
Ya ƙara kamota yana faɗin.
”To ina ruwana…”
“Dady! Mama!”
Muryar Junior ta kira daga wajen ɗakin. Rabi ta ƙara tureshi tana nufar ƙofar da sauri, sai ta ga Junior ɗin tsaye a waje yana kallonta.
“Me ya faru?”
“Anna tace wai ku yi sauri”
Rabi ta juyo ta kalli Zaid tana watsa masa hararar wasa, kafin ta juyo ta tsugunna ta ɗauki Junior ta sauƙa ƙasa, Zaid ya bi bayansu da kalli yana murmushi, kafin shi ma ya bi bayan nasu ya sauƙa aka fara cin abincin da shi. Labarin rayuwar sabon gidan da suka gina cike da so ƙaunar juna da farin ciki kenan.
Alhamdullullah
END
Assalamu Alaikum
Barkan mu da wannan lokaci, ina so na yi amfani da wannan damar, wurin nuna muku irin godiyata gareku, kan so da ƙaunar da kuka nuna min, a har kullum ina ganin kamar ‘Na gode’ ta yi kaɗan wurin nuna muku jin daɗi na game da yanda kuke support ɗina, my people i can’t thank you enough. Allah ya bar zumunci.
Sannan ina so na yi jan hankali gareku, game da darasin dake cikin wannan littafi. Idan kuka tsaya kuka yi nazari, za ku ga cewar wannan littafin na ƙunshe da illollin fyaɗe, da kuma yanda rayuwar ‘ya mace kan shiga garari yayin da iyayenta suka koreta daga gida, bacin da ƙaddara fyaɗe ta faɗa kanta.
Kun sani, kuma ni ma na sani, fyaɗe ita ce babbar annobar da ta damu yankin mu na arewa gaba ɗaya, shi ya sa nake so, mu tashe tsaye ni da ku, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, wurin ganin mun kawo ƙarshen wannan annoba, domin fyaɗe masifa ne, kuma bala’ine. Ina kira ga duk wani wanda ya san Allah ya wadata shi da wata baiwa, da ya yi anfani da wannan baiwar tasa wurin ganin mun kawo ƙarshen fyaɗe a arewacin nigeria, idan zai iyu, a gaba ɗayan Nigeria ma.
Ni tawa baiwar ta rubutu ce, shi ya sa na yi amfani da shi, wurin ganin na yaƙi wannan annoba da ta damu sauran ‘yan uwana mata. Jama’a mu ƙyamaci fyaɗe.
Say No to Rape❌