Skip to content
Part 7 of 9 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

What she really craves is a wild love, from a steady pertner…

1987

Alhaji Ali Wakili, babban mutum ne me tarin arziƙi. Haifaffen garin haɗejia ne, kuma ya ci gaba da zama a cikin garin har bayan lokacin da ya fara tara iyali. Kasancewarsa mutum me nasibi a harkokin kasuwancinsa, ya sa shi gyara gidansu na gado, ya ci gaba da zama a ciki shi da ‘yan uwansa.

Alhj Ali na da mata biyu, hajiya A’i, yaransu tara da ita mata biyar maza huɗu, matan sun haɗa da Lawisa, Fatsima, Kaltume, sai ‘yan biyun gidan, Maryam da Rabi’a, Mazan kuma sun haɗa da, Abdullahi, wanda ya kasance shi ne na farko, sai Mansur, Haladu da lawan

Hajiya Kande ita ce matarsa ta biyu, yaranta huɗu da shi, kuma dukansu maza ne, Kabir, Sagir, Jamilu da kuma Jibrin.

Duka yaran gidan suna karatu, matansu da mazansu, kuma duk da kasan cewar sun taso a gidan yawa, akwai zaman lafiya a tsakanin yaran ahalin, dan iyayensu jajirtattu ne a kan tarbiyar yaran nasu.

Rana ɗaya da gaba ɗaya ahalain gidan ba zasu manta da ita ba ta kasance Asabat, inda labari ya riske su cewar an yi wa Rabi’a ‘yar biyun Maryam fyaɗe.

Duk wani nau’i na tashin hankali babu wanda bai yi ba a gidan, dan da aka tambayeta ta shin san wanda ya mata fyaɗen?. cewa ta yi bata sani ba, dan hankalinta a gushe yake. Haka aka gama jajjaɓin lamarin kafin aka watsar da zancen, kowa ya ci gaba da lamuransa.

Bayan kwanaki da faruwar lamarin, Alhj Ali ya nemawa Maryam gurbin karatu a garin Suleja, dan haka ta tafi can ta ci gaba da karatunta. Watanta ɗaya da tafiya, alamun samuwar ciki suka fara bayyana tattare da Rabi’a.

Tun tana ɓoye abun har ya zo ya bayyana, har kowa na gidan ya sani. Alhaji Ali ya yi tsallen albarka ya ce sai dai a zubar da cikin. Itama kuma Rabi’a ta yi tsallen albarka kan cewar ba za ta zubar da cikin jikinta ba, hakan yasa shi kuma yace sai de ta bar masa gidansa.

“In dai har ba za ki zubar da cikin jikin ba sai dai ki bar min gidana Wallahi!…”

Haka ya faɗi, a ranar da yake watso mata kayanta ƙofar katafaren gidan nasu. Gaba ɗaya mutanen gudan sun firfito, an tsaya a bakin gate ana kallon abin da ke faruwa.

Babu yanda yayun Alhaji Ali ba su yi da shi ba kan ya yi haƙuri, amma ya ce Wallahi sai Rabi’a ta bar masa gidansa, dan baza’a haife cikin shege a gidansa ba. Ba zata ɓata masa sunan zuri’a ba.

Rabi’a ta tsugunna ta tattare sauran kayan da Abban nata ya watso mata, sannan ta haɗe su a wuri ɗaya, tana ta sharar hawaye. A hankali ta miƙe ta kalli idon Abban nata.

“Da na zubar da cikin jikin, gwara na bar maka gidanka Abba…. Ba zan roƙi ka bar ni na zauna a gidan ka ba, abinda ya sameni ƙaddara ce daga Allah, kuma shi ne zai temakeni na iya cinyeta…..Ni dai buƙa tata ita cee ka yafe min Abba!….”

Ta ƙarashe tana fashewa da kuka, babu wanda bai ji tausayinta ba a wurin, amma banda Alhaji Ali, wanda ya kawar da kansa gefe, ya gwammace da ya sallamarta, da ta ja masa a bun kunya, ace yau a gidansa aka haifi ɗan gaba da fatiha?, kuma ace ‘yarsa ce ta cikinsa?.

“Na san ba lalle ka yafe min ba, amma ni dai ina meneman yafiyar taka, zan yi nesa da kai, zan yi nesa da gida, zan je na haife cikin jikina, kuma zan basu labarin abinda rayuwata ta fuskanta sakamakon fyaɗen da aka min ba tare da san rai na ba…Yaran da aka haifesu ba tare da aure ba suma ‘ya’ya ne, ƙaddara ce ta hukunta zuwansu ba tare da auren ba!…”

Ba tare da ta sake cewa komai ba ta ɗauki sauran kayanta tana ta sharar hawaye, ta kama hanyar barin unguwar tasu.

Sai da ta yi tafiya mai nisa, sannan ta ji muryar mahaifiyarta na ƙwalla mata kira. Cike da mamaki ta juya.

Da gudu ta ruga wurinta tan kuka, suna haɗewa ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana sakin sabon kuka, Ita ma Hajiya A’in kukan take. Kafin ta share hawayenta ta ɗago da ‘yarta. Hannunta ta kama sannan ta danƙa mata wata jaka.

“Akwai kuɗi, da takardun karatunki a ciki, sannan akwai takardun gidana na kano a ciki… Ban ce ki faɗawa kowa inda za ki ba…. Ni dai ina so ki je ki kafa sabuwar rayuwarki a garin kano, idan zai iyu bayan kin haifi yaranki, ki yi aure Rabi’a!…..”

Rabi’a ta ƙara faɗawa jikinta tana sakin sabon kuka.

“Aure be dace da ni ba Mama, sanin kanki ne babu namijin da zai auri macen da ta yi ciki ba tare da aure ba”

Hajiya A’i ta shiga kwantarwa da ‘yarta hankali, tana haɗa mata da nasiha, har zuwa lokacin da suka yi sallama. sallamarsu ta ƙarshe kenan.

Rabi’a ta isa garin Kano lafiya, kamar yanda mahaifiyarta ta buƙata ta sauƙa a gidan da ta bata takardunsa, sai dai gidan babu kayan buƙata a cikinsa. Dan haka washe garin ranar da ta sauƙa a garin Kano, ta fita ta je ta yi siyyayar kayan da zata buƙata na amfanin gidan. Bayan ta samu sati biyu a garin, ta shiga fafutikar neman aiki, cikin sa’a ta samu aiki a wata asibiti, kasancewar aikin nurse ta karanta.

Haka rayuwarta ta ci gaba da gangarawa ita ɗaya, kullum cikin ƙunci da tunanin gida, Allah ya sani tana kewar gidansu, sai dai kuma ba za ta iya rabuwa da cikin jikinta saboda san gidan da take ba.

Sau tari ta kan zauna ta yi tunani a kan rayuwarta, da ma haka duk macen da aka mata fyaɗe ba tare da san ranta ba rayuwarta ke kasan cewa?. Kowa ya na nuna mata ƙyama, saboda kawai Allah ya ɗora mata ƙaddara?.

Watan cikin jikinta tara dai-dai, naƙuda ta tashi mata, Allahn da ya temaketa tana asibitin da take aiki a ranar, dan ba ta wani ɗauki hutu ba. Kuma ita kaɗai take rayuwarta, babu ruwanta da kowa a unguwar da take zaune ko a asibitin. Cikin ikon Allah ta sauƙa kafiya, ta samu yaranta ‘yan biyu maza.

Bayan ta dawo hayyacinta ne ta raɗa musu suna da kanta, na farkon ZAID, na biyun kuma ta saka masa ALIYU.

Ba ta yi taron suna ba, dan bata da wanda za ta gayyata, mahaifiyarta kawai ta kira a waya ta faɗa mata. Hatta da Maryam, ‘yar uwarta, kuma abokiyar tagwaitakarta, wadda ta fi shaƙuwa da ita fiye da sauran ‘yan uwanta bata da masaniya kan inda take. Ita kanta Hajiya A’in taƙi faɗawa kowa inda Rabi’an take ba.

Duk da wahala irin ta renon tagwaye, haka Rabi’a ta reni yaranta ita kaɗai. Sosai take nuna musu soyyaya da kuma basu kyakyawar tarbiyya. A koda yaushe tana nuna musu su so juna.

Haka yaran nata suka taso masu tsananin kama da juna, banbancinsu a hallita biyu ne, shi Zaid yana da ash ɗin ƙwayar ido, yayin da Aliyu tasa take brown, sai kuma totsiyar karen dake a bakin Zaid, wadda shi Aliyu ba shi da ita.

Haka kuma halayensu sun banbanta, dan Zaid yaro ne me sanyin hali, ga haba-haba da jama’a, amma Aliyu mugun muskili ne, babu ruwansa da yawan magana, ga masifa, da saurin fishi.

Kuma har suka yi wayo ta saka su a makaranta, a cikinsu babu wanda ya taɓa tambayarata ina mahaifinsu. Ko a makaranta ma da sunan junansu suke amfani, shi Aliyu amfani da Aliyi Zaid, Zaid kuma yana amfani da Zaid Aliyu.

Tana ƙara nusar da su cewa ba su da kowa sai junansu. Suna primary 5 ne, Zaid ya taɓa tambayarta ina mahaifinsu. Kuma bata ɓoye musu ba, a lokacin ne ta sanar musu da komai da ya danganci ita kanta da kuma su.

Suna da shekara goma sha ɗaya, wata rana sun tafi islamiyya. Rabi’a na kitchen tana girki. Bayan ta gama girkin sai ta manta bata kashe gas ɗin ba. Ta koma ɗakinta ta shiga wanka.

Ta ɗau tsawon mintuna a banɗakin. Kafin ta fito, kuma tana fitowar, ta ji ƙauri na tashi, kamar wani abu na ƙonewa, hakan yasa ta fito falo, don ta duba abin da yake faruwa, me za ta gani?. Gaba ɗaya kitchen ɗin ya kama da wuta, kasancewar a falo kitchen ɗin yake. Har ya bawa falon, yana ƙoƙarin kama ɗakuna, a lokacin hankalinta ba ƙaramin ta shi ya yi ba . Ga shi labulayen ƙofar falon sun kama da wuta, babu damar ƙarasawa jikin ƙofar bare ta buɗe.

Haka ta dawo ɗakinta ta shiga kai kawo na neman mafita. Bata ankara ba har ɗakin ma ya kama da wutar. Ta shiga kiran mutane domin a kawo mata agaji, sai de babu wanda yake ji, bare a kawo mata agajin, kamar yanda take buƙata.

Kuma a lokacin ne, Aliyu da Zaid suka dawo daga makarantar. Tun daga ƙofar falon suka ga wuta na ci, hankalinsu ya tashi sosai, suka shiga kiran sunan mahaifiyar tasu tun da sun san cewar tana cikin gidan.

Jin kiran sunanta da suke ne yasa Rabi’a ta shiga amsawa tana kiran sunayensu, bayan gidan suka zagaya, jin muryar mahaifyar tasu na futowa daga can, dai-dai tagar ɗakinta suka tsaya. Kuka suka ci gaba da yi suna faɗin ta fito daga cikin gidan kada wuta ta ƙonata.

“Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan…idan kuka tsaya wutar zata iya ƙona ku… Ku tafi nace!…”.

Fitar suka yi, sannan suka shiga neman wanda zai temaka ya zo ya fitar musu da mahaifiyarsa.

Kasantuwar unguwar tasu babu kai kawon mutane da yawa, kuma su ba gidan kowa suke shiga ba, yasa saida suka jima, kafin suka samu wasu maza suka shiga gidan suka ga abinda ke faruwa.

Ko da aka kashe wutar har ta gama ƙona ko ina ƙurmus, ta ƙona komai na gidan, ita kanta Rabi’an haka aka fito da ita babu rai a jikinta…

*****  

Present day…

Unguwar Madallah, Suleja, Niger state

RABI’A POV.

Ramadanal kareem, ramadanal kareem!

Watan ramadana, wata mai alfarma…

A hankali waƙar ke tashi ta cikin radion da Habiba ke sauraro. Zaune take a kan tabarma tana dudduba kayan ɗinkinsu Mama na sallah da aka kawo daga shagon ɗinki, don yau jajiberan sallahr. Mama, Fati da Mahmud sun kewaye da ita, kowa na gwada nasa a jikinsa.

Rabi dake zaune daga can bakin murhu tana soya musu kajin da za’ayi miyar sallahr da su sai satar kallon kayan nasu suke.

Don Allah ya sani, tana kewar samun sabon kaya, kayan Mama sun fi mata kyau, ta san da cewar kuɗin albashinta na makarantar da take aiki da shi aka musu dinkunan, amma ita da take shan wahalar aikin ko fallen zani na atamafa roba ba’a samu arziƙin siya mata ba.

Ta juya kanta tana tsame kajin da suka soyi daga cikin mai.

“Salamu alaikum… Rabi wai ki zo in ji Yaya!”

Wani yaro me zaƙin baki ya faɗi yana shigowa cikin gidan. Rabi ta juyo ta kalli yaron. Yaya?, wani mutum ɗaya a duniya da yake santa a yanda take. Yake santa duk da ita ba kowa ba ce. Yake nuna mata so duk da ita bata da komai.

Kuma ita ma ba za ta yaudari kanta ba, tasan cewa tana sansa, dan ba ta ga wani bayan shi ba, to ina ma za ta samu ?, waye zai so ta a haka ?, ta sani cewar ita ba mummuna ba ce, tana da kyau dai-dai nata, amma ai hausawa ma sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka.

“Je ka ce ba za ta zo ba!”

Muryar Habiba ta katse mata tunani, juyawa ta yi suka haɗa ido, a take ta watsa mata wani mugun kallo. Rabi’a ta yi saurin ɗauke kai, wani abu na taruwa a maƙoshinta.

“Rabi! Ɗan siyo min kati dan Allah”

Muryar Saratu ta faɗa, a sanda ta fito daga ɗaki, sai da Habiba ta harareta sannan tace.

“Ba zata je ba, ba ki ga aiki take min ba?”

“To tunda ba za ta je ba, Mama ko Fatima wani ya siyo min a cikinsu”

“Ba ta ta siyo miki, ba inda za su fita”

Habiba ta faɗi a dake. Saratu ta sunkuya tana kallon Rabi’a cikin murmushi, da ido kawai ta mata alamu da ta tafi.

Rabi ta miƙe har da murmushinta ta fita, dan dama da hijabinta a jikinta.

“Mama ta shi ki ƙarasa suyar nan…”

“Wallahi Umma ba zan iya ba, ga Saratu nan, sai ki sa ta ta soya”

“Eh kuma haka ne, Saratu, tun da kin tashi ita me suyar, ke sai ki ƙarasa”

Saratu ba ta ce mata komai ba, ta girgiza kanta tana takaicin halin mahaifiyar tasu da ƙanwarta, ta zauna ta ci gaba da suyar.

“Na yi zaton ba za ki fito ɗin ba ai…”

Sassanyar muryar Yaya ta faɗi, yayin da yake kallon fuskar Rabi’a. Ta ɗan yi murmushi kaɗan tana sinnekai.

“Umma ce ta sa ni aiki, shi yasa”

Ya langwaɓe kai gefe yana faɗin.

“Allah ya bani kuɗin da zan aureki Rabi’ata, dan na gaji da ganinki kina wahala a banza, Gwara na aureki ki je can gidana ki yi bautar me lada!…”

Ƙwalla ta taru a idon Rabi’a, amma sai ta shanyeta, don ko kaɗan bata so ta zubo.

“Gobe sallah, me kika tana da min ?”

Ta ƙara sunkuyar da kanta. Warin wannan bolar na cika hancinta, don Allah ya sani bata san zama a ƙofar gidansu.

“Babu komai”

“Na sani ai, shi yasa ni na samu na ɗan ɗinka miki kala ɗaya da hijabi, ki yi haƙuri ba yawa Honeyna!”

Abubuwa biyu ne suka karya zuciyar Rabi’a lokaci guda, ɗinkin da yace ya mata, da kuma sunan Honeynsa da ya kirata da shi, wannan ƙwallar da take ta ƙoƙarin riƙeta ta sauƙo mata.

Ta ɗago da kanta ta kalli fuskar Yayan, sannan ta kalli kedar da yake miƙa mata.

Tsabar murnar samun sabon kayan da take ranar kasa bacci ta yi, daga ta ɗan jima a kwance sai ta miƙe zaune ta janyo ledar kayan ta duba su, ta kuma mayar wa.

Allah ne kaɗai yasan yanda ta yi farin cikin samun kayan, shi yasa a har kullum take taya Yayyan da addu’a kan Allah ya buɗa masa, har ya samu kuɗin da zai kawo a aura masa ita. Duk lalacewr auren yafi zaman gidansu.

“Ka zo?!…”

Kamar daga sama ta ji muryar Mama, hakan yasa ta buɗe idonta dake a lumshe, ta cikin net ɗinta ta hangi fuskar Maman, wadda ta yi kwalliya a cikin daren Allah ta ala.

Wasu tsukakkun riga da wando ne a jikinta, ga kitson attachment ɗin da takanas ta tashi ta je aka mata shi, ta zube shi a bayanta, ta caɓa wata uwr kwalliaya, kamar me shirin zuwa gidan bikin, gidan bikin ma irin na kece rainin nan.

“Ka ɗan ƙara matsawa gaba… kasan ni bana san sa ido, kar ka ga dare ya tsala, akwai munafukai masu bacci da ido ɗaya”

Ta kuma faɗi ta cikin wayar da take.

“Ok to bari na fito…”

Kuma daga haka Maman ta sauƙe wayar da ke riƙe a hannunta, ta gyagyyara jikinta, sannan ta kashe wutar ɗakin ta fita.

Rabi ta ƙara dunƙuƙunewa a cikin bargonta, don bata ma so Maman ta san cewa ta farka. Abin da ake zarginta da shi, shi ne ‘yar mai zargin nata ke yi.

<< Labarinsu 6Labarinsu 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×