Skip to content
Part 8 of 9 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

No.181, Guzape, Abuja.

10:00pm

KULIYA POV.

A hankali ƙafafunsa suka taka cikin falon gidan. Abu na farko da ya yi shi ne kunna wutar gidan gaba ɗaya.

Kafin ya ƙaraso cikin falon, ya sauƙe ledojin da ya shigo da sua kan sofa. Sabbin kayan da ya siya zai saka idan zai je idi. Kuma kafin ya taho gidan nasa sai da ya biya ta gidan Anna, ya kai mata nata kayan idin. Sai ledar da Annan ta saka masa abinci a ciki, don haka tace yana buƙatar ya riƙa cin abincin gida, ba na kanti ba.

Kuma haka ɗin ne, bayan farin ruwan sanyi da ya sha a office lokacin da aka yi buɗa baki bai saka komai a cikinsa ba. Dan shi ba iya girka abinci ya yi ba, idan har ba gidan Annan ya je ba to sai dai ya yi order a wani restaurant da ya saba siyan abinci.

Idan kuma aiki ya sha masa kaibama ya samun damar cin abincin. Dan bai damu da shi ba, shi yasa ulcer tai masa kamun kazar kuku.

“Ayra!, Ayra!….”

Muryarsa ta shiga kiran sunan a hankali, kamar ba shi ba, yana yi yana dudduba ƙasan kujeru.

Da gudu kuliyar tasa ta fito daga ƙasan wata kujera, sannan ta iyo kansa. Wata hallita ɗaya a duniya bayan Anna da take iya ganin farin haƙorinsa cikin murmushi ko dariya. Shi kansa yaan cewa ba kasafai yake murmushi ba ma balle a je ga dariya. Murmushin ma baya yi sai idan ya yi nasara a aikinsa.

A ƙasa ya zauna, sannan ya kamo kuliyar tasa yana shafa kanta.

“Kina jin yinwa ko ?”

Ya tambaya kamar yana magana da mutum, don shi ɗaukarta yake kamar ƙawa, saboda bayan me gadin gidan, sai wata tsohuwa dake zuwa tana masa shara a gidan duk sati, babu wani abu mai rai dake rayuwa a gidan sai ita.

Ledar da Annan ta saka masa abinci ya janyo, sannan ya fiddo da abincin da Annan ta zuba masa.

Ya buɗe flask ɗin, ya zubawa Kuliyarq a murfin flask ɗin, ya tura mata gabanta, nan take ta hau ci.

Shi ma gefe ya koma ya zauna ya fara cin nasa abincin. Yana tunanin yanda ayyuka za su masa yawa a satin nan, dan abokinsa kuma abokin aikinsa ya ɗauki hutun bikin sallah. Saboda haka duka ayyukan Abubakar ɗin shi ne zai ƙarasa. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Yana kai lomar abincin bakinsa, idonsa a kan Ayra, yadda take ta famar cin abincin ne kaɗai zai nuna maka cewar a matse take da abincin.

Bayan sun gama cin abincin, ya ɗauki Ayra tare da ɗorata a kan kafaɗarsa, sannan ya ɗauki sauran kayan nasa na ledar, ya shiga ɗakinsa.

A kan gado ya zube ledojin, kafin ya aje Ayra kusa da ledojin, Ya juya zuwa walk-in closet ɗinsa. Bayan ɗan wani lokaci ya fito, ya shiga banɗaki.

Wanka ya yi, ya fito bayan ya sauya kaya. Daga suit ɗin da ya shigo da ita zuwa wasu baƙaƙen shirt da wando na pyjams.

Ya dawo ya zauna a kan gadon yana fitar da kayan idin nasa. Kamar yanda ya saba duk shekara, baƙar shaddace guda ɗaya, sai wani baƙin voil, hulunan ma baƙaƙe ne babu ratsin wata kala ko guda a jikinsu. Haka takalman ma baƙaƙe ne guda biyu, dan shi ba wasu manyan kaya yake sawa ba, sai lokaci irin wannan idan ya zo, hatta da sallar juma’a ba da manyan kaya yake zuwa ba.

Miƙewa ya yi ya koma closet ɗin. Wani abun mamaki shi ne, gaba ɗaya kayan cikin closet ɗin baƙaƙe ne, kamar na mai shirin zuwa jana’iza.

A rayuwarsa ba ya saka wani kaya mai kala, duka kayansa a duniya baƙi ne, motarsa baƙa, kayan sakawarsa baƙaƙe, hatta da case ɗin wayarsa baƙi ne. Bayan ya aje kayan, ya fito ya zauna a kan work table ɗinsa, ya shiga yin sauran aikin da ya dawo gida da shi.

*****

Dambuwa road, Maiduguri…

MISHAL POV.

Zaune take a ɗakin da yake a matsayin nata. Don ba yau suka saba zuwa Maidugurin ba, hasalima suna zuwa akai-akai. Kuma idan sun zo ɗin a babban family house ɗinsu suke sauƙa.

Duk da kasancewar gobe sallah, amma gidan har yanzu be rabu da zuwan baƙi ba. Tun daga hayaniyar dake tashi a gidan za ka gane hakan.

Ba su dameta ba, Don Kullum ba ta fita, tana ɗaki, bata san ta fita su haɗu da Yazid. Yazid?, wani mutum da ya so lalata mata rayuwa, wannan mutumin da duk duniya bata tsani wani mahaliƙu kamarsa ba.

Shi ne wannan mutumin da a sanadiyyarsa ta gamu da ciwon hysterian da take da shi a yanzu. Kuma dan abun a family ya faru, haka aka rabu da shi ya ci gaba da yawonsa. Yana shiga cikin ‘yan uwa kansa ɗage a sama, kamar bai aikata komai ba.

Ita kuma da aka yi ƙoƙarin cutarwa ita ce ke ɓuya, ita ce ke ɓoye kanta da barin shiga dangi, har yanzu gani take kamar idan ta idan ta shiga cikinsu suna ganin wannan tabon a jikinta ne. Duk da Allah bai sa ya haike matan ba, amma tana jin zafin abinda ya mata a ranta. A duk sa’ar da za ta ganshi ji take kamar ta fasa ihu, a wasu lokutan ma ganin nasa kawai shi ne ke tada mata ciwonta.

Ta ɗan ja gutun tsaki tana ci gaba da buɗe littattafanta. Ita ta tsani aikin makaranata, dan de ba ta san ɗan uwanta ya yi asarar kuɗin da yake kashewa a kan makarantar ta a banza, amma da ba za ta na maida hankali ba.

Gashi dai hutun sati ɗaya a ka bayar, saboda ba ƙarshen term ba ne, a tsakiyar term aka basu hutun, amma sai da suka haɗo su da holiday project.

Kuma tun barowarsu Abuja abun da take ta ƙoƙarin yi kenan. Amma har yanzu ta kasa gamawa.

Ta kuma jan wani tsakin tana ture littatafan, duk aikin ya gundureta, fita take san yi, bata san zaman gidan gaba ɗaya. To amma ta fita ta je ina ?, ta san in ma fitar ce ba za’a barta ta fita ita ɗaya ba, dole za’a haɗata da wani.

“Baby!”

Kamar daga sama ta ji muryarsa yana kiran sunanta, sunan da kaf duniya babu me kiranta da shi sai ‘yan gidansu. Tasan da cewa za su zo, amma ba ta san cewa yau za su zo ɗin ba.

Da sauri ta miƙe ta fita daga ɗakin, a falo ta same shi yana ta nemanta. Yana ganinta ya sakar mata wani kyakkyawan murmushin. Da gudu ta ƙarasa kusa da shi, kuma tana zuwa jikinsa ta ɗale shi, duk tsayinsa amma saida ta riƙe masa wuya.

“Tun sanda muka zo nake ta nemanki”

Wannan dakakiyar muryar tasa ta faɗi. Ta yi kewarsa da ma duk wani ɗan gidansu, dan za ta iya cewa duk familynsu babu wanda take so kamar ‘yan gidansu, duk da su ma a Abuja suke da zama,amma bata gajiya da ganinsu.

Sunansa Arman, ɗa ne a wurin cousin ɗinta Nimra, wadda ta kasance soja me riƙe da muƙamin general na nigeri. Yaranta uku Arman, Iqra sai Ijaz, kuma gaba ɗaya yaran nata sojoji ne. Wani abu dake ƙara burgeta da gidansu kenan.

“Ina Iqra da ijaz?”

Ta tambaya tana sakinsa. Kanta a sama wurin kallon fuskarsa, sbd tsayin da ya fita. Kasancewar shi dogo ne, ita kuma gata ba wani tsayi gareta ba.

“Suna waje, har da su Ammy muka taho”

Zuciyarta kamar ta fito waje don murna, Allah ya dubeta yasa ba za ta yi bikin sallah lami ba, dan tunda har duka mutanen gidansu suka zo, to shikenan, matsalarta ta zaman kaɗaici ta yanki.

Unguwar Madallah, Suleja, Niger State

07:44am

RABI’A POV.

Ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, kallo ɗaya za ka mata fahimci hakan, saboda daga kun haɗa ido za ka ga ta maka murmushi, duk da dama ita gwanarsa ce. Amma na yau ya fi na kullum. Jin kanta take kamar kowa, yau Allah yasa ita ma ta saka sabon kayan da za ta tafi idi da shi.

Saɓanin sauran shekarun da ta shafe a gidan, a da sai dai Saratu ta bata kunce ta saka. Amma yau ita ma gata da nata sabon kayan, sai dai duk da haka bata da takalmin sakawa, shi yasa Saratu ta bada ɗaya daga cikin nata, Da murnarta ta zangari takalmin ta saka.

Tun da ta fito daga wanka ta saka kayan Mama ke binta da kallo, amma ba ta ce komai ba, har suka shirya suka fito dan tafiya wurin idi.

Rabi ba ta san sanda Mama ta dawo gidan ba, ita dai kawai ta farka ta ganta. Kuma ba ta ce komai ba, ta ja bakinta ta yi shiru, tun da har uwrta tasan abin da take.

A bakin ƙofar ɗakinsa suka ga babansu, kowa a cikinsu ya wani ɗauke kai babu ma mai shirin gaishe da shi, sai Saratu da ita, kuma shi ma bai wani amsa musu da mutumci ba, sama-sama ya amsa su.

Ita kuma Rabi ba ƙaramin mamakinsa take ba, kusan kwanansa huɗu baya gidan, ko jiya har suka kwanta ba ta ga dawowarsa ba, wata ƙila ma da asuba ya dawo, don ba ƙaramin aikinsa ba ne. Mutumin da ya taɓa kawo karuwa cikin gidan matarsa ta auren sinnah, ai fiye da haka ma zai aikata..

“Ah-ah, Karfa, a ina kuma kika samo sabon kaya ?, in ji dai ba sata ki kai ba?”

Muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta juyo da sauri ta kalleta. Rabi ta tsorata, dan jiya basu san an bata wani kaya ba, tana shigowa da ahi ɗaki ta shige, Anti Saratu kawai ta nunawa.

“Saurayinta ne ya kawo mata, ba sata ta yi ba”

Saratu ta bata amsa.

“Shiya munafuka! Ashe jiya da kika je siyan katin tsayawa ki kai a lungu ya gama lalube ki sannan ya baki kaya?”

Habiba ta faɗi cikin kama baki.

“Ai ni na jima banga baƙar munafuka irin wannan yarinyar ba, kin ga fa jiyan da ta dawo, ɓoye kayan ta yi a cikin hijabinta, dan kada mu gani”

Mama ta faɗi tana aika mata harara.

“Ya isa haka dan Allah, to duk sharrinku a ƙofar gida ya bata, da za ku ɗorawa marainiyar Allah shari, dan Allah Umma ku riƙa duba baya, idan an giram a san an girama”

“Kan abu ta kaza-kazacan!, Saratu! Ni ki ke faɗawa irin waɗanan maganganun ?…..”

Sararu ta juyar da kanta gefe daga barin kallon Umman, ta kalli Rabi wadda hawaye suka wanke mata fuska tun a sharin farko da aka laƙa mata.

Hannunta ta ja suka fita daga gidan, dan ta ga kamar su basu da niyyar zuwa idin, su da suke da niyya gwara su yi sauri, don kada su rasa.

Da sauri Ɗan Lami ya bi bayansu, dan ko ba komai yasan akwai ‘yan kuɗaɗe a hannun Saratu, shi kuma kuɗaɗen da ya ara sun ƙare kaf, bai ta shi da ko sisi ba. Kuma gashi yana san zuwa idin, ko ba komai Saratun za ta masa kuɗin babir.

“Umma da alama fa sai kin ɗau mataki…”

Cewarta,

Ni kuwa na ga hakan, kada ki damu, zan ɗau ƙaƙƙwaran mataki kuwa”

“Ke Fati, uwr me kike a ɗakin ne?, dallah ki yi sauri ki fito”

Mama ta faɗi cike da masifa tana kallon ƙofar ɗakinsu, Habiba ta shiga soshe-soshen ƙeya.

“Amm, Mama na ce Alhajin jiyan nawa ya baki ?”

Mama ta juyo ta kalleta tana haɗe rai.

“Ni ba na san bita da ƙulli, dubu hamsin ne, ya ce babu kuɗaɗe a hannunsa, zan baki dubu biyar kawai…”

Habiba ta yi murmushin yaƙe.

“Haka ne, amma dai an kinsa dai ko kuɗin ɗinki shaddara da na ɗinka miki a sallar nan ya fi dubu biyar…”

“Ni fa Umma na gaji da gorin da kike min!, kawai dan kina min ɗinki sai ki kafa bina da bita da ƙulli?… Da na ce dole sai kin min ɗinki?… Idan ba ki min ba ma samari na za su min ai!”

Kamar Maman ita ce uwa haka takewa Habiban faɗa.

“Haba Mama, abun fa ba na ɓacin rai ba ne, ki kwantar da ranki mana”

Mama ta ƙara juya kai tana huhhura hanci.

Ƙarshen zamanin kenan, dama an sanar da mu cewa; baiwa za ta haifi uwar gijiyarta,to ga kyakkywan misali nan Habiba da Mama.

Sannan an ce abun da ka yi shi za’a maka, hakan ce ke faru da rayuwar gidan Ɗan Lami, amma shi sam bai lura da hakan ba, dan ba iyalan nasa ne a gabansa ba.

(Allah ya fihsemu turba mai kyau🙏).

Bayan an sauƙo da ga idi, Saratu da Rabi gida suka dawo, in da Mama ta wuce yawon gantalinta, Habiba da su Fati ma gidan suka dawo.

Kuma tana dawowa ta laftawa Rabi aikin abincin sallah, haka Rabi ta cire sabon kayanta ta hau aikin ba ji ba gani, duk da Saratu na tayata da wani abu.

Da haka har suka yi suka gama, kuma bayan sun gama ba’a bawa Rabin abincin ba, sai kusan la’asar aka ɗan zuba mata kaɗan a kwano, wai duk dan a ƙuntata mata.

Naman da kajin data soya ma ba’a saka mata ba, sai wanda Habiban ta ci ta bari, kuma ita hakan bai dameta ba, don bata damu da cin kaza ba, tafi san kifi, kaza bata birgeta a rayuwa.

Duk da haka sai da Anti Saratu ta ɗiba mata naman ta bata, tace mata ta ci, ai da kuɗin da ta nema aka sayi naman. Bata san yi mata musu shi yasa ta ci ɗin, ba wai don naman ya mata daɗi ba.

Da la’asar Zara ta shigo gidan tace ta zo su je yawon zaga gari, da farko sai da Habiba ta hana, amma da Saratu tayi uwa tayi makarɓiya sai ta haƙura ta barta.

A wurin Rabi wannan sallahr ta musamman ce. Saboda tana cikin farin ciki, komai na tafiya mata dai-dai. Har ta fara ganin kamar wahalarta ta ƙare a rayuwa.

Abun da ba ta sani ba shi ne; wasu abubuwan ma yanzu ne suka soma, wata wahalar ma bata shigeta ba tukkuna, wani ciwon ma bai sameta ba har yanzu!.

Wani sabon kukan ƙunci da damuwa na nan tafe a gaba. Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa, akwai damuwa da iftila’i a rayuwa, akwai damuwa a akan wata damuwar.

Ƙaddarar kowa da ban ce, kamar yanda Labarin kowa yake da ban. Labarinta yanzu zai soma, haka mahaifiyarta ta faɗa. Kuma yanzu zai soma ɗin.

Don ba ayi komai ba ma, labarinta zai sauya tare da faruwar wata ƙaddara mai zuwa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, ƙaddarar da za ta sauya komai, ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu abubuwan.

<< Labarinsu 7Labarinsu 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×