Skip to content

Lamarin Duniya | Fasaha Haimaniyya 1

3
(2)

<< Previous

Bismillah da sunan Allah Rahimi

Shi yai akuya kuma shi yai raƙumi

Ba ya gajiya balle ma yai gumi

Ba ya damuwa balle yai tagumi

Shi yai Bauchi kuma yai Gumi

Ba ya ƙaunar duk wani azzalumi

Tsira da amincin Allah mai yawa

Gun sahibi abin son kowa

Manzon Allah abin son kowa

Har alihi sahabu gaba ɗaya.

*****

Da ba ka ayau kuma ka yo wanzuwa

Yau ga ka a baina kana yin rayuwa

In ka ji ƙishi a gefe ga ruwa

Babu yunwa kuma ba ka da damuwa

Ka saki jiki kana yin rayuwa

Kan lahira fa ba ka komuwa

Kullum buri yana yin hauhawa

Ka ɗau harka kana cin kasuwa

Ko ka noƙe ba ruwanka da kowa

In ka so ka zamo abin son kowa.

*****

Watarana a ganka kana yin dariya

Kana shagali jin daɗin duniya

Ka sayi gida ga tarin dukiya

Ka hau mota kana bin hanya

Kana harkarka ba wata tankiya

Mulki ya sa kana yin fariya

Ka ɗau ƙarfe ana ta hatsaniya

Kai ne caca kai ne shan giya

Kai ne bin ‘yan matan duniya

Kai dai kawai kana ta fagabniya.

*****

Ko da kullum kana annashuwa

Ko kuma kullum kana a damuwa

Ina talaka da ba shi da dukiya?

Ko tajiri mai tarin dukiya

Aure kike yi ko ko budurwa

Lebura kake ko ɗan kasuwa

Ko da rini kake ko fawa

Ko da tuwo kike siyarwa

Ko ka shina ko kai mantuwa

Watarana tabbas za ka macewa.

*****

Ya ‘yan uwa mu zam gyaran hali

Don rayuwarmu tana da dalili

Mu sani dukkanmu muna kan hanya

Kuma za mu tafi babu ragin ɗaya

Fatan kowa ya zam dacewa

Da yin kalima a loton mutuwa

Sai dai kowa ba ya son mutuwa

Kuma za ta zo babu makawa

Alheri munka yo ko sharri

Za mu yi jawabi a kabari.

*****

Ya Allah sarki na roƙe ka

Ka yi gafara ka yafe laifuka

Ka yi rangwame ka yafe mu duka

Ka ƙara mana son addininka

Da Imani da tsantseni duka

Da bin koyarwar manzonka

Ka samu cikin ceton manzonka

Don ni’ima cikin falalarka

Ka sa mu cika muna bin addininka

Ran lahira mu tashi a addininka.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×