Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Darajar marubuci,

Masani mai azanci,

Ta fa zarci-,

ta duk wani mai sanarwa da Hausa.

– Aminu Ladan Abubakar (ALA)

(Wakar Inuwar Marubuta)

TUNAWA

Iyayenmu da suka rigaye gidan gaskiya, da sauran ‘yan uwa musulmi baki daya.

DOMIN

Ameena Sani Fagge

MANAZARTA

Jameelu Haruna (Jibeka)

JIGO

Abdullahi Yusif Fagge, Ahmed Yusif Amo, Sama’ila Yusif, Hassan Hussaini Aliyu, Muhd. Y. Rayyan, Hayat Muhd Fagge

YABAWA

Bashir Reader, Ibrahim Muhd. Indabawa, Auwalu Danborno, Muhd. Lawal Barista, Aminu Ala, Shehu (Harafi), Iliyasu (Maikudi), Tasi’u (Sheara), Nazir Adam Salih, Nasir NID, Habibu Darazo, Ibrahim Daurawa, Abdul’Aziz Sani, Bashir Basad. Da sauransu.

A KARKASHIN

Inuwar Marubuta Littattafan Hausa (Hausa Authors Forum)

*****

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.

Farkon Labarin

1980

Daga can gefen bolar, za ka iya hango matar da ‘ya’yanta uku, a tare da ita. Biyun dake rike a hannunta maza ne, ‘yan-biyu Hassan da Hussaini, wadanda suke amsa sunayen Abba da kuma Samir daga gare ta. Goye a bayanta kuwa, ‘yar budurwa ce, kanwa ce ga ‘yan-biyun, masu shekarun da ka iya zama uku zuwa hudu, sunan ta Samira, ita watanni sha hudu ke nan da samuwarta a duniya, da alama ita ce Gambonsu.

Kamar yadda matar ke fara a launin fata, kyakkyawa a siffance, to haka ma ‘ya’yan suke, sai dai kuma in ka dauke wannan baiwa da Ubangiji ya yi musu ta kyau, to duk abin da suke ciki a yanzu cikin muni yake, ban da hali.

Da farko dai a gefen bola suke, kuma ga dukkan alamu kai tsaye cikin bolar suka nufa. Wannan ke nan, sannan kuma abu na biyu, suturun dake jikin dukkansu, daidai take da suturar da za ka gani a jikin mahaukaci tuburan, abin bai tsaya nan ba sai da ya zarta zuwa ga jikinsu da yanayinsu.

Fatar jikinsu dai ta nuna, ta hanyar dafewa da yamutsewa da ta yi, haka nan yanayinsu tattare yake da alamomin damuwa da kuncin rayuwa, wadannan abubuwan kuwa suna da tarin nasaba da halin da halittun hudu suke ciki, na kunci da takaicin rayuwa.

Jama’a da dama sun san matar mai suna Umma Maryam, kamanninta da yanayinta, uwa-uba ga kananan ‘ya’yanta ya kan sa dole a tausaya mata da ‘ya’yanta, ko a tausayawa rayuwarta, to sai dai kuma da yawan mutanen sun dauketa a matsayin mahaukaciya, za ta iya yiwuwa haka ne ko ba haka ba ne, kama da wane dai ba ta wane.

Kamar ko da yaushe da ta isa gab da shiga cikin bolar sai ta tsaya, sannan ta durkusa ta kwashi ‘ya’yan nata hagu da dama ta rungume, kana ta ci gaba da shiga bolar kai tsaye. Allah sarki uwa kenan, ita a ganinta shigar yaran cikin bolar na iya kawo musu matsala musamman ko gurin taka wani mugun abu a kafafuwansu marasa takalma, duk da ita kanta kafar tata ba takalmin kirki.

Haka ta tsattsalaka har zuwa can jikin wata katangar kango dake rave da bolar. Gurin da ta tsaya a share yake, duk da cewar kewaye yake da bola tsibe, to hakan dai shi ke nuna cewar muhallin na Umma Maryam ne da ‘ya’yanta.

Ta sauke ‘yan ‘ya’yanta biyu, Samir da Abba, sannan ta ajiye daurin buhun tsummokaran da ke kanta gefe guda, kana ta sunto Samira ‘yar jaririya dake bayanta, ta iya zama don haka ta zaunar da ita bisa zanen goyanta. Tuni Samir da Abba suka zagaye autarsu, yaro ke nan, da alama wasa za su yi mata.

Umma Maryam ta sami guri ta zauna, ta sanya diyanta a gaba cikin kulawa. Zamanta ke da wuya ta jawo buhun nan da ta sauke, ta kwance buhun, ta dauko wata bakar leda daga ciki. A cikin bakar ledar ta dauko wani burodi rabi, tare da gyada mai gishiri, sai kuma ruwa da ke daure a leda ta daban.

Ta gutsira burodin gida hudu, Abba, Samir da ita, kowa ya mallaki gutsire daya, sannan ta ajiye dayan, ko dan Samira ba za ta iya ci ba? Daga bisani ta kwance ledar gyadar ta ajiye a gabansu. Sai bayan da ta dan debi gyadar, ta afa a baki hade da burodin, kana suma ‘ya’yan suka yi koyi da abinda ta yi.

Daga haka kuma sai hawaye ya biyo kan fuskarta, ya ziraro zuwa kumatunta. Tsabar bakin ciki da kunar zuci ke tattare da hawayen, kuma dafe a fuskar tata.

Abba da Samir ba su lura da hakan ba, suka ci gaba da cin abincin, har suka kammala ta ba su ruwa suka sha. Kana suka juya ga autarsu, don yin wasanninsu.

Ita kuma Umma Maryam duk kokarin da ta rinka yi ga zuciyarta, don kawar da wannan lamari na tsananin damuwa da tsayar da hawayen, musamman don kada ‘ya’yanta su lura hakan bai yiwu ba. Ya za ta yi? Dole ta ci gaba da fitar da hawayenta cike da kunar rai.

Abin da ba ta so ba, Samir ya lura da halin da take ciki, sai ya tsaya ga barin wasan da yake yi, yana kallonta cike da damuwa, wannan ya sa Abba shima ya dube shi tare da lura da halin da mahaifiyarsu ke ciki. ‘Yar auta ma dariya ta tsaya, saboda tsayawar wasa daga ‘yan uwanta.

Yaran suka isa ga mahaifiyarsu, suka fada jikinta. Samir na shafe mata hawaye, shima sai ya fara hawayen cikin tsananin damuwa, cewa ya yi.

‘Umma wa ya ba ki kuka?’

Ta cije leventa, cijewa ta tsananin takaici, ji ta yi ta kasa magana, amma ba zai yiwu ba, yara ne, kuma kanana, dole ta kwantar musu da hankali, kar su taso cikin damuwa. Ta rinka shafa kansu, kamar za ta hadiye su ‘Ba komai, ku yi wasan ku, ai ba komai, kun bar kanwar taku kar ta yi kuka. Kar…’Zuciyarta ta tuke, matukar tukewa, tabbas ta gode Allah da ya ba ta ‘ya’ya gudan jininta, kanana amma sun fara damuwa da damuwar ta, ji ta ke a kullum kamar ta hadiye su, ina ma ace za ta iya da ta daina shiga damuwa don suma kar su rinka shiga, kar su san wani abu damuwa, kar su damu. Amma ba hali. Shin da ace ba ta da ‘ya’ya wane ne zai damu da halin da take ciki, har ya rinka tambayar ta me ke damun ta?

Ta rukunkume su, ta sa hannu ta dauko auta ta hada su uku a kirjinta, ta rufe tana shafar kawunansu, hawayen ya valle. Ita kadai take jin abin da take ji a ranta, sai kuma Allah da ya halicce ta.

*****

Da yake rana ce ta Litinin sai ya zamo kasuwar Singa (kasuwar hada-hadar kayan abinci) ta cika, saboda ana sauke kaya sosai a ranar. Kamar jiya matar na dauke da autarta Samira goye a baya, kanta kuma dauke da buhun tsummokara, ‘ya’yanta biyu a gabanta, suna tafe, hannun hagunta kuwa rike da wani tsohon kwano, wanda ke dauke da tsabar kudin da ba su fi shida ko bakwai ba, don har da ‘yan ficikoki.

Da ya ke ‘ya’yan nata ba su da kiriniya sai ya zamto ba ta cika samun matsalolin ratsa jama’a da ta ke yi ba daga wannan shagon zuwa wancan.

Da alama yaran sun saba, domin su suke nufar kowane shago ita kuma ta rufa musu baya. Idan suka je suka tsaya, ita kuma sai ta fadi abin da ya kawo su.

‘Alhaji a taimaka mana da sadakar abin da zamu ci abinci.’

Alhajin ya dubeta sosai kamar me mamakin abin da take fada, kana ya dubi su Abba dake gabanta, sai kuma yanayin fuskarsa ya sauya, ya jawo wata leda a gefensa. Naira hamsin ya dauko ya mika mata. Abba dake kusa da shi ya sa hannu biyu, ya karva yana godiya.

‘Allah ya biya da alkairi.’ Umma Maryam ta fada, kana suka wuce.

Alhajin da ya ba su sadakar ya dubi wani tsoho da ke zaune kusa da shi, da alama daya daga cikin yaran sa ne.

‘Ashe matar nan tana nan?’

Tsohon ya amsa ‘Ka san tana yawo da yawa, jiya ma a kasuwar Kwari na ganta.’

Suka dan yi shiru.

‘Ni kam ina tausaya mata, baren ma ‘ya’yanta. Ko daga ina ta fito? Akwai alamun aikin sammu ko sihiri ne ke walagigi da ita da ‘ya’yanta. Amma ana zaluntarsu, gashi ma da alama ta haukace gaba daya.’

‘Ta haukace mana, amma akwai wasu lamura na ban mamaki tare da ita. Domin a haka yadda take, a haka take kokarin baiwa ‘ya’yan nata tarbiyya, har karatu take koya musu, domin na tava ganin ta a bakin kasuwar nan tana koya musu karatun Kur’ani. Sai dai kuma a jita-jitar da nake ji, an ce a garin nan take, kuma matar wani babban mutum ce…’

Alhajin ya nisa. ‘Allah ya kyauta.’

Umma Maryam sun ci gaba da neman taimakon abin da za su ci, idan har sun samu to shi kenan, sai kuma wani lokacin, ba ta san ta yi ta yawo ba wai don tarawa ko wanin hakan, a tsarinta idan ta samu na abincin shi kenan.

Dukkanin lamarin ya faru ne daga karfe sha biyu na rana, zuwa hudu da rabi na yamma.

Kai tsaye da suka nufi kofar (gate) din dankareren gidan, aka bude musu kofa. Umma Maryam da diyanta suka shiga, har da sallama ta yi ga maigadin, ko kallon kirki ba ta ishe shi ba, bare amsawa.

A fasalce da bayyane gidan kato ne sosai, kayatacce sosai, dankarere sosai mai tattare da tsari iri-iri, kwatankwacin gidan miloniya. Kayatacce da fulawoyi, tsarin jerin motoci reras.

Kai tsaye, ainihin ginin gundarin kyakkyawan gidan suka nufa. A duk lokacin da suka doshi wannan guri mai gadin ya kan ji kamar ya je ya fatattako su, sai dai ba dama, ko mene ne dalili?

Bai fi taku tara tsakanin su da kofar shiga cikin katon falon gundarin gidan ba, kofa ta bude, kamar yadda kofar da ta bude take da tsananin kyau da kayatuwa, haka babbar matar da ta fito daga cikin falon da diyanta suke da tsananin kyau da kayatuwa, cikin kayatattun kaya, tun daga kan yari, riga, zani, mayafi, jaka zuwa takalmin kafa, ga uwar kenan da ‘yar kankanuwar ‘ya gareta mai kama da ita kwabo da kwabo, to haka shi ma daya dan nata wanda ya dan dara ‘yar kadan ya ke.

Namijin yana rike a hannun dama, macen kuma a hagu na matar. Fararen kayan boyel ne a jikinsu, sun yi anko, amma dukkaninsu suna sanye da bakaken takalma ne. matar babbar mata ce, Hajiya, mai dauke da shekaru kamar ashirin da takwas zuwa talatin, akasin ‘ya’yan masu shekarun da suka fara daga biyar ne zuwa kasa.

Umma Maryam ta ja, ta tsaya, daga ita har ‘ya’yanta, kallon Hajiyar da diyanta suke. Umma Maryam na dauke da murmushin dake nuna farin ciki da masaniya ga ganin Hajiyar. Haka shima Samir cikin irin wannan hali yake, shi kam Abba ko dubansu bai kuma yi ba, tun kallon farko, to ita autar da ke baya ba ta ma san abin da ke faruwa ba.

Kicin-kicin Hajiya Kilishi ta yi da rai, ta murtuke fuska, babu alamun rahama tattare da ita. Face tsaki da ta yi, ta tsartar da yawu, ta ja diyanta zuwa ga ajiyayyar motar da ke jiran su, kirar Jeep fara mai bakaken kafafu (tayoyi).

A hannun Samir akwai guntun burodin sa da bai kammala cinyewa ba, ya dubi Zuhra da ke waigo shi, ya kwace daga hannun uwarsa, ya nufe ta. Yaro kenan fadi ya ke.

‘Jarah…ungo…ungo…’ Busasshen burodin yake mika mata, rashin sanin da ya yiwa jelar rakumi ta yi nesa da kasa, da dan gudun sa ya kai gare ta.

‘Un…go…ungo bilodi.’

Karamar yarinyar ta callara kara, tare da kai masa duka da dan hannunta shafal. Uwar ta juyo a gaggauce, cikin fushi da zafin nama. Marin da ta fallawa Samir ko babban barde irin sa za ta yi masa. Karfin marin ya sanyashi kifewa a kasan Hajiya Kilishi, ta kai masa duka da kafar ta, tare da tsarta masa yawu, ba ruwanta da cewar yaro ne, a ganinta koma dan tayi ne.

Umma Maryam tana kallo, da marin da dukan duk kamar ita aka yi wa, tsakanin da da mahaifi sai Allah, fashewa ta yi da kuka. Abba kuwa ganin dan uwansa cikin wannan hali ya sa shi tahowa da gudu, shima kuka yake, gashi yaro a tunaninsa ko zai kwaci dan uwansa ne? Ko kuma wani abin zai yi? Yana zuwa dai shima ya sami nasa marin, da hankadewa, daga Hajiya Kilishi. Ko kadan ba ruwanta da wani yara ne, dukansu ta ke kamar yadda za ta doki uwarsu.

Yara biyu, Samir da Abba a kwance suna kuka, can a tsaye ba tare da motsi ba uwarsu ce ita ma kukan take. Nan kuma Hajiya Kilishi cikin fushi ta zaro hankici, ta share hannunta, sannan ta bude motar ta sanya ‘ya’yan nata. Zuhra a gaba dake ita karama ce, Kabir a baya, bayan ta rufe ta zagaya ta hau. Ta tashi motar, ta tura giya, ta fincike ta zuwa wangamammiyar kofar gidan, ta fice.

Abubuwan sun faru ne a kan idon Alhaji Masa’ud, dake can saman bene yana kallo, shi ma murna ya yi da abin da matarsa ta yi wa ‘ya’yan Umma Maryam.

Haka nan akan idanun Bazuye maigadi da abokin sa duk lamarin ya faru.

Bayan rufe kofar, ya koma kusa da abokinsa Mati ya zauna.

A can saman, Alhaji Masa’ud shi ma ya koma ciki, cike da murnar wulakancin matarsa ga su Abba.

‘Uhm.’ Mati ya yi gyaran murya.

Bazuye ya dube shi a kaikaice ‘Ina sauraron ka.’

Ya san shi da tambaya, ya kuma san ba zai kyale ba.

Ai kuwa sai cewa ya yi ‘Wai ba ka ba ni labarin wannan mahaukaciyar ba, Umma Maryam da Alhaji ya ba ta guri a gidansa alhalin ba so ya ke ba, shi da iyalan sa sun tsane ta da ‘ya’yan ta.’

Bazuye ya yi kumburi a tunanin sa murmushin fushi ne ‘Kai ma ka fada, ai ni abin yana sanya ni takaici. Kamata ya yi ace tuni Alhaji ya rabu da matar nan amma ya ki, ya kyale ta, ai ko kawar da ita ya sa a yi, abu ne mai sauki, amma ya bar ta…’

‘To ya suke da ita?’

‘I to, abin da yawa mutuwa a kasuwa, ba na ce ba, amma ina tunanin…kai ba na ce ba, amma ni a ganina ko ma ya ya suke, ya kamata ace ya yi maganin abin. Kai ni ban ma tava ganin mutumin da ya ke zaune da abin da yake ki a rayuwar sa ba, kuma yana da ikon rabuwa da ita. Na dai rasa kan wannan abu.’

Dukkanin al’amuran sun faro ne a 1980, a lokacin su Samir, Abba, Samira, Zuhra, Kabir suna kanana.

Babi Na Farko

2005

Samarin biyu suna zaune ne a can gefen gidan, muhallin da shi kadai ne kawai suke da damar zama, daga shi sai dan tsukukun dakin da aka ware musu a babban gida, sai kuma idan waje za su fita.

Allah da ya raya Samir, Abba, Samira da mahaifiyarsu Umma Maryam, shi ya baiwa Alhaji Masa’ud damar kara gyara gidan, ya fi da kyau sosai.

Shekaru da dama har yanzu Bazuye ne ke gadin gidan, ba a sauya shi ba. Haka nan Hajiya Kilishi dai ita ce matar gidan, ba a yi mata kishiya ba, bare a rabu da ita. ‘Ya’yanta biyu, Zuhra ‘yar gata, ‘yar shagwava da Kabir, su ne ba ta kara samun wasu ba. Allah shi ke da ikon mutum da aljan.

Abba ya dubi yayanshi Samir.

‘Yaya, ya kamata ka yi tunani dangane da wannan al’amari, ka yi tunani dangane da matsayinmu a wannan gida, da halin da muke ciki, ka duba ka fitar da abin da ya dace, ka yi abin da ya kamata.’

Samir ya yi ajiyar zuciya. A dukkanin saninsa, da kuma nazarin abin da mahaifiyarshi da ‘yan uwanshi, kuma kannenshi suka guje masa gaskiya ne, dari bisa dari, kuma haka ne. To amma kuma, ya ya zai yi da so, so mai tsanani, son da bai san ya zai yi da shi ba. Shi kansa ya yi kaico da wannan son da ya shige shi, son wadda bai dace ya so ba. Shi kam, wannan son ya zame masa mugun ciwo.

Yana cikin wannan tunani alhalin kaninsa Abba na zaune a gefensa zumbur ya mike. Da ya mike din bai san dalilin mikewar ta sa ba sai bayan da ya mike din, sai ya kai idanunsa gurin da suka haddasa masa mikewar.

Mota, kirar Rio Sorento, ta gama tsayawa a harabar gidan, taku goma tsakani da inda su Samir ke zaune. Minti hudu bayan kashe motar, yarinya mai kyau ta bude kofar motar ta fito, hannunta rike da littattafai. Daga makaranta ta dawo, Zuhra ce.

Cikin doki Samir ya yi taku biyu daga inda yake tsaye, kai tsaye gurin ta ya nufa, daga bisani ya tsaya, ko mene ne dalili? A zaune a inda yake shi kuma Abba ya kufula iya kufula, yanzu fa ya gama yi wa yayan nasa magana akan ya rabu da shisshigewa yarinyar nan, ko don gujewa irin wulakancin da suke ciki, amma wai ga shi ya mike zai je gare ta, daga ganin dawowar ta, alhalin shi kansa ya san abin da zai riska. Don bakin ciki kasa motsi Abba ya yi.

A can bakin kofa, idanun Bazuye na kan duk abin da ke shirin faruwa, kwafa ya yi, ‘Mayu, tsinannu.’ Ya ce a ransa, kuma da su Samir ya ke.

‘Sannu da dawowa.’ Samir ne ya ce da Zuhra.

Ta yi tsaki, ta kalleshi a yamutse ‘Kai dai Allah wadaranka, wulakantacce.’ Ta tsarta masa yawu, ta wuce abinta.

Murmushi ya yi, ya shafo yawun nata ya lashe, bai motsa daga inda yake ba, face bin ta da kallo da ya yi, babu kiftawa bare dauke kai.

Abba da ke zaune, haushi ya sa ya ji kamar ya tashi ya bubbuge yayan nasa, amma babu dama, sunkuyar da kansa kasa ya yi kawai yana hawaye, zuciya na cin sa.

Daga gefe, kofar shigowa cikin gidan kuwa, Umma Maryam ce da Samira, suka dubi juna cike da mamaki da takaicin abin da idanun su ya gane musu ya faru tsakanin Samir da Zuhra. Dawowar su kenan daga gurin me magani, inda suke karvowa ita Umma Maryam din maganin ciwon hakarkari dake damunta. Ta samu sauki da jin dadi a zuwan ta din, amma ga shi ta riski vacin rai.

Suka tako a hankali, cikin halin takaici har zuwa ga inda Samir ke tsaye, Umma Maryam ta kama hannun sa, ta ja shi zuwa inda Abba ke zaune, ta zaunar da shi, ita ma ta sami guri ta zauna, Samira ma ta samu guri ta zauna, har wannan lokacin Abba bai dago kai ba, zuciyar sa tafasa ta ke.

Umma Maryam ta dubi Samir, duba na nutsuwa, kafin ta bude baki ta fara da cewa.

‘Dukkaninmu nan da ka ganmu ba wai muna ki ne ga abin da kake so ba, ba wai muna nuna rashin amincewa ko kulawa ba ne ga abin da kake so, face dai a zahiri muna guje maka ne abin da yanayi ya janyo mana na kaskanci da wulakanci. Kana sane, kamar yadda mu ka sani cewar a yadda muke din nan, cikin hali mai muni, su kuma su Zuhra da iyayenta da ‘yan uwanta suke, halayyar su da yanayin su yake, ka san lallai ya kamata mu gujewa halin da ka ke neman shiga.

‘So ne, mun lura kana neman afkawa ga son wannan yarinya, to amma ya kamata ka yi la’akari da yanayi, ka yiwa kanka kiyamullaili ka jure, ka daure ka kawar da kanka gare ta. Kar ka dauka ba zai yiwu ba, ko ba za ka iya ba, a’a za ka iya, ko ba ka daina ba za ka iya daurewa ka danne, musamman bisa la’akari da irin wulakanci da cin mutunci, da musgunawar da suke yi mana, a karon banza ma sun wulakanta mu bare kuma kai ka kai kanka ga son ‘yar su, yarinyar da kullum kwanan duniya ba mu da sake ko shakatawa, ta vangaren ta.

‘Mune makiyan su, mune wulakantattunsu, mune koma bayansu a duk fadin duniya alhalin ba wani abu suke ba mu ba, ba a kan su muke zaune ba. Don haka ya dace ka lura da wannan lamari, ka duba, duba managarci, ka ga me muke gujewa, mene ne ke hana mu goyon bayanka ga wannan al’amari alhalin mune kan gaba gurin kin abin da ka ke ki, da son abin da ka ke so. Haba Samir, ya kamata ka yi hali, ka yi hali….wannan ba halin gado ba ne…’

Ita da take maganar kuka take yi, haka nan ‘ya’yan nata, har Samir din ma kuka yake. Bare ma da yake ita idan tana magana cikin nasiha mutum kan sami kansa cikin halin nutsuwa, sauraro da sakankancewa.

Abba da Samira sun damu matuka, ba sa son ganin mahaifiyarsu cikin wannan hali, ba sa nutsuwa musamman ma da yake halin yakan taimaka gurin tashin cutar ta lokaci-lokaci.

Tunanin Samir ya bambanta da na kannenshi, shi a gurinsa ko kadan bai yi tunanin zai ragu ga son Zuhra ba, don haka nasihar mahaifiyar ta su kamar waka ta zame masa, shi tuhumar mahaifiyar tasa ma yake yi, dangane da wasu maganganu da ta yi.

A ganin shi, da mahaifiyarsu ke cewa su Zuhra ba sa yi musu komai, ba gurin zama, ba abinci, ba abin sha, to ya yarda ba sa ba su abinci, amma ai yanzu a gidan su suke zaune. Hakan ya sa ya yi tunanin zai tambayi mahaifiyarsu wasu al’amura, to amma ganin halin da suka shiga ya sa dole ya kyale a yanzu.

Sun jima a zaune jigum cikin wannan halin da suka sami kansu, kowannen su akwai irin tunani da nazarin da zuciyarsa ke masa, duk da uku daga cikin su nazarin su da tunanin su ya kusan zama guda. Daya ne ya bambanta.

Rayuwa irin ta su Umma Maryam, rayuwa ce mai ban mamaki, mai abin al’ajabi. Rayuwa mai muni da takaici, a yalwataccen gidan kunci, gidan takaici.

Ita da ‘ya’yanta sun rayu shekaru masu dama cikin kunci, a inda ba a son su, an tsane su. A cikin wannan hali ‘ya’yan uku suka yi karatu kala biyu, boko da arabiya. A Arabiyya sun yi zurfi, don har an yi sauka da su a makarantun allon da Umma Maryam ta sa su, boko ne dai dukkaninsu sun gama firamare, amma ba su samu ci gaba ba. Sai dai mafi yawa daga karatun nasu, sun same su ne daga gurin mahaifiyar su, Umma Maryam da yake ita ta sami kowanne vangare, digiri gareta.

*****

Saurayin da budurwar duk kyawawa ne, hakanan kujerun da suke zaune a kai ma, to ita ma bishiyar fulawar da suke karkashin ta ma kyakkyawa ce.

Zuhra ta kada fararen idanunta, ikon Allah, sai ya zamana kamar yadda take kyakkyawa, kamar yadda idanunta suke farare haka ma sutturunta suke farare tun daga kasa har sama, don haka sai ta zama zarah cikin wata da taurari a tsakiyar farin gajimare.

‘Hasken zuciyata, yau na ga mulki ake ji.’ Nazi ya fada da haskakakkun murmushin sa.

Ta watso masa nata samfurin hade da fari, a lokaci guda ta kalli cikin idanun sa. Hakan ya hadu ya haifar da wani shauki mai tsima jiki a gare shi.

Tun daga yanayi, magana, mu’amala da kasancewar su tare Zuhra idan suna tare da Aliyu jin ta take tamkar a cikin aljanna, idan tana kallon sa ba ta son ta daina, idan yana magana ba ta son ya yi shiru, idan suna tare ba ta son rabuwar su, idan ya yi murmushi ji take kamar ta shide, idan ya kalleta yanayin ta na rikita.

To shi ma haka yake samun kansa cikin irin wannan hali, har ma ya kan yi tunanin ya fi ta son ta, ita ma wannan tunanin take, haka nan mutane kan yi tunanin ko a tsakaninsu wane ne ya fi son wani. Su kan su, jin su suke kamar za su narke wa junan su. Gida da waje, masallaci da makartanta, daya bai gajiya da tunanin dan uwansa. Wasu na ganin sune Laila da Majnun na rayuwar Hausawa.

‘Humh, bari kai dai. Yau ji na nake kamar in buda zuciya ta in sanya ka, in rufe, ka kwanta, in tafi da kai cikin gidanmu, in fada kan gado in rufe kaina da lallausan bargo.’

Ita da ta fadi maganar, ta fi wanda ta gayawa tsimuwa da dokanta a cikin zuciyarta.

Ya kalle ta da ninkuwar murmushin kauna, a nutse kuma a hankali ya sake dubanta, bai daina murmushin ba. Kamar kullum ta san abin da yake nufi, don haka ta ba shi hadin kai, ta sakar masa murmushin nata a sanyaye. Ya mayar da hankalinsa gaba daya gare ta.

Masoyan biyu suka kurawa juna idanu cikin doki, kulawa, kauna, so da shaukin juna, tsawon lokacin kowannensu yana kallon tsakiyar idon dan uwansa, ba komai suke gani ba face tsantsar so da kauna. Kamar mintuna goma a tare suka yi ajiyar zuciya, suka kawar da kawunansu daga junansu.

‘Brother Kabir ya yo min waya dazu mun gaisa.’ Nazi ya fada a sanyaye.

Zuhra ta kalle shi a takaice, cikin murmushi.

‘Allah sarki Yaya Kabir, mutanen Amerika, muma ya yo mana waya dazu da safe around 9 mun gaisa, har yana bamu labarin kungiyar dalibai Musulman makarantarsu na can, za su yi tarurruka da ziyarce-ziyarcen kasashe a wannan satin…’

‘Yaushe za mu je kasar nan?’ Nazi ya tambaye ta cikin shaukin zuci.

Shiru suka yi suna kallon juna, take suka kara komawa halin da suka bari na dazu. A nutse Nazi ya mika hannu ya ciro wani kati a aljihun sa, maimakon ya dubi katin sai ya mika mata, ta dubi kalaman kaunar da ke jiki da kulawa da soyayya.

Kamar an koro shi, Samir ya shiga kewayen lambun shakatawar da su Nazi din suke zaune. Ya riske su a cikin halin da suke, hankalinsa ya yi matukar tashi, kishi ya turnuke zuciyarsa, ya yi duru-duru kamar ya koma inda ya fito ya gaza, ya dube su sosai. Sun shagala a fagen soyayya da kauna, shi kuma ya shagala a fagen kiyayya da kunci, sun shagala cikin farin ciki, shi kuma ya shagala a cikin bakin ciki.

‘Kai sake ta mana!’

A firgice masoyan suka mike, matukar razana kam, sun razana, a tsammanin su Alhaji ne, amma akasin haka sai suka ga wanda ba kowan-kowa ba a gurinsu. Hakan ya hada da razanar da su da bakin ciki ya kawo su iya wuya. Tun kafin wani lokaci a zucin su suka ji kamar su hadiye shi danye.

A tsaye, da yake ya kasa motsi face kura musu idanu da ya yi, idanu masu siradin kwalla, masu tsantsar kauna da kishi.

Shiru na mintuna, wanda daga bisani tsiwa da tsananin fadan da aka tattaro guri guda, suka biyo baya daga bakin Zuhra, mai neman kuka ne bare an jefe shi da kashin awaki.

‘Wane ne kai?! Mene ne gamin rayuwarmu da taka?!” Ta yi kwafar bakin ciki ‘Allah da ya halicce ka ya tsine maka albarka. Wallahi daga yau sai ka san ka tafka kuskure na neman shige mini hanci da ka ke..’

Duk irin cin mutunci, wulakanci da tsiwar da Zuhra ke yi ga Samir bai daga ido ya kalleta ba, bare ya tamka mata, face ma da ya ke jin zuciyar sa na tsananin kara jin soyayyar ta, sai kuma rawar da jikin sa ke yi.

So so ne, so ba shi da tabbas. In ban da so duk irin munin halin da ya ke ciki babu abin da zai sa Zuhra ta yi masa wulakanci irin wannan. Vacin ran Samir bai fito fili ba sai a lokacin da Nazi ya furta na shi furucin gare shi.

‘Da alama kai dabba ne, dan dabbobin mutane.’

‘Saurara ka ji!’ Samir ya daka masa tsawa ‘Ba ka isa ka gaya min magana ba alhalin ka shiga rayuwa ta, ka shiga soyayyar wacce na ke so…’

Shi da kansa ya katse kansa, ya yi shiru ga barin zancen da ya ke yi a lokacin da maganar Zuhra ta ratsa kunnensa. Idan tana magana nutsuwa ya ke yi, sakankancewa ya ke yi, ya kuma saduda, ya gaza yin komai. Don a wani abu mai kama da mafarki sai ya rinka jin muryarta da tsananin zaki a lokacin da ko da zagin iyayensa ta ke yi.

‘Har ka isa ka bude baki ka ce kana so na? Kai din banza, marasa asali….’

Wani abu ne ya tsirgo tun daga tsakiyar kan Samir har karshen dan yatsan kafar sa na dama. Bai gama warwarewa ba ya jiyo batu daga bakin Nazi.

”Ya’yan tsiya, ma su shiga rayuwar da ba ta su ba. ‘Ya’yan da ba su kamata da rayuwar al’umma ba…’

Cikin fushi, a harzuke Samir ya taso kan Nazi. Kyakkyawan mari daga Zuhra gami da tsarta yawu ne ya katse masa hanzari, sannan.

‘Me za ka yi? Wulakantacce, dan mahaukaciya, dan titi, wanda aka tsinci cikinsa a kan hanya, a yawon bola…’

Kikam ya tsaya. A yanzu kwakwalwarsa ta rikice, tunaninsa ya damule, babu nutsuwa, babu kwanciyar hankali a tare da shi, ba shi da wani zavin kyakkyawan tunani guda daya. Yana da zuciya, amma akan Zuhra tun tsawon wani lokaci, tun lokacin da ya tabbatar da son ta gareshi, ya sakwarkwace ya susuce.

A can tsakiyar cusasshiyar kwakwalwar sa, ya jiyo ci gaban kalaman yarinyar da soyayyar ta ya zamar masa babbar cuta.

‘Ka yi na karshe, daga yau babu sake, rayuwarku ta kare a gidan nan. Wallahi sai kun bar mana gida,…. Idan ba ka sani ba yau in sanar da kai cewar, uwar nan taku karuwa ce, karuwanci take ta same ku, ta haife ku, bakin ciki da rashin abinci da talauci ne ya mayar da ita mahaukaciya….’

Wani dum! Dum!! kawai ya ji a cikin kwakwalwar sa, daga nan kuma sai dif! Babu wani sauran abu da ya ci gaba da ji.

Launin So 2 >>

1 thought on “Launin So 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×