Kowane taki ana tunani da sa ran mutuwar Samir, sai dai abin da yake baiwa kowa mamaki shi ne idan aka yi masa maganar Zuhra sai a ga jikin nasa da sauki, har ma ya kan samu ya yi hira, musamman hirar da ta shafe ta, amma bayan wannan to fa sai dai rikicin jiki da radadin zuciya da ke addabar sa. Wannan abu yana damun su Umma Maryam, Alhaji Yusuf da Samira har ma da Kabiru.
Hankulansu sun tafiyu wurin nema masa lafiya, don haka shi Alhaji Yusuf bai damu da neman halin da kaninsa, wanda ya zalunce shi yake ba. Ya dai yi mamaki yadda halin Kabir ya bambanta da na mahaifinsa, wanda shi yana da adalci, karimci, lamarinsa bai damu da abin duniya ba.
Sun yi mamakin soyayya irin ta zuciya wadda ta hada Samir da Zuhra, Kabir da Samira, alhalin ga halin da mahaifinsu Alhaji Masa’ud, wanda babu ruwanshi da ‘yan uwantaka, babu ruwanshi da zumunci da aminci, kuma azzalumi.
Ranar Lahadin ta zowa su Alhaji Yusuf da tashin hankali mai tarin yawa, domin jikin Samir ya tsananta har ma ba a tunanin zai iya kara duk minti na gotawar agogo.
Babu shakka rayuwar Samir tana cikin tsananin barazanar da duk wanda ya gan shi, to ya kamata ya tausaya masa. Hakan ya sa wadanda suke tare da shi, hankalinsu ya tashi matuka, suka kuma tausaya masa, matukar tausayawa.
Kowannensu idan ka ganshi ido ya raina fata, addu’a suke yi masa na samun sauki, da rangwame. Shi kansa likitan yana tausayi ga rayuwar Samir. Sa wa ya yi su Alhaji Yusuf su rinka yi masa addu’a. Dukkaninsu kuwa sun kewaye gadon nasa, bayan ruwa da aka sa masa da allurai da magunguna da ya sha, gumi ne sharkaf a fuskarsa, wani irin numfarfashi yake yi, idan ya yi na tsawon dakika arba’in, sai ya yi dif, kamar ba zai kuma yi ba, kai sai sun yi zaton ma rai ya yi halinsa, sai kuma su ji ya yi ajiyar zuciya, ya ci gaba da numfarfasawa, ya kan iya bude ido da kyar, kuma a juye, sai kuma ya rufe, ya sake budewa, haka ya ke yi a gabansu.
Abba ne a gaba Zuhra tana biye da shi a lokacin da suka shiga harabar dakin asibitin da Samir ke kwance.
Babban abin da zai ba da mamaki shi ne, yadda yarinyar da aka baza hotonta a ko ina ana nema, ga ta ta ratso har zuwa asibitin nan. Wannan ya faru ne saboda halin da ta shisshiga na jigata, wahala da kunci, wanda ya sauya mata kamanni, ba ita ba, hatta shi kansa Abba zai yi wuya kai tsaye ka gane shi.
Sai dai duk da haka wannan bai hana Sifiritanda Inuwa Lambu gane su ba, wanda tun a jihar Kaduna ya riske su, ya gan su suna kokarin neman hanyar dawowa gida. Shi ya zame musu jagora da taimakon Kabir, wanda shi ne ya baiwa Sifiritandan wannan kwangila, na nemo masa su Abban. Wanda duk wani abu da ke faruwa S. Inuwa Lambu yana buga masa waya, ya sanar da shi halin da ake ciki.
Ya sha walaha, tare da aiki da hankali kafin ya sami sa’ar gano su. Da ya sanar da Kabir samo su din, sai ya ce masa ya yi shiru, kar ya gayawa kowa, kawai su zo asibiti yana nan. To shi ne S. Inuwa Lambu ya kawo su, ya tsaya a wajen asibitin yana kallon su har lokacin da suka bude kofa suka shiga cikin dakin sannan ya juya, yana murmushi.
Isar Abba da Zuhra a bakin gadon da Samir ke kwance, ya yi daidai da farfadowarsa.
Alhaji Yusuf, Umma Maryam, Samira har da Kabir, bin su da kallo kawai suka yi, ya kamata ace sun yi murna sun nuna ta a zahiri, amma babu hali, saboda halin da Samir ke ciki. Sai dai hawaye da suka shiga zubowa daga idanun Umma Maryam da Samira, shi kuwa Alhaji Yusuf kwalla ce ta taru a idanunsa.
Sun dade suna kallon su Abba da Zuhra, wanda har suka fuskanci cewar akwai wata alaka ta soyayya mai karfi a tsakaninsu, wanda idanunsu ke nuna irin launin son da yake dafe a zukatan nasu.
Samir da ya bude idanunsa, bai kuma rufewa ba saboda ganin fuskar Zuhra da ya yi.
Fuskar da ya dade yana marari, yana doki, ya shaukanta, da son gani. Ya shiga wani hali saboda rashin ganin ta, to ga ta yau ya gan ta, sai me? Ji ya yi, ya samu sauki, sai dai rashin kwarin jiki. Ji ya yi an sauke masa kashi tamanin da tara cikin dari na makuntacin halin da yake ciki na rashin lafiya.
‘Sannu….sannu.’ Zuhra da Abba suka hada bakin cewa da shi hakan.
Kallon su kawai Samir ya ke yi. Ya san abin da ke tsakanin Abba da Zuhra, hali ne da zai iya kwatantashi zama na tsakanin ruwa da wuta. To amma a yanzu ya lura babu wannan, wani yanayi mai karfi da ya lura da shi, shi ya fara tada masa hankali, ya kasa magana, kawai sai ya kwanta, ya rufe idanu. Da ya sani da bai rufe idon na shi ba, domin a lokacin zuciyarsa ta gaya masa abin da ya so ya faru, a zahiri. Gani ya yi soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Abba da Zuhra.
‘Wayyo Allah, wallahi ni na ke son ki.’ Haka ya fada da karfi, a gigice, take ciwo ya dawo danye shakaf.
Sai da likita ya yi masa allurar barci, sannan hankali ya kwanta.
A cikin dakin, yanzu ya rage daga Samir da ke kwance a gadonsa na marasa lafiya, sai Abba da Zuhra da suke zaune a kujerun can kuryar dakin a kan kujerun roba guda biyu. Kallon juna suke yi, haka nan hira suke yi.
Umma Maryam da Samira suna waje, Kabir da Alhaji Yusuf sun fita neman abinci da kuma wata unguwa da Kabir ya nemi Alhaji Yusuf din ya rakashi.
A kwancen da Samir yake ba barci yake yi ba, yana kwance ne cikin hali mafi tsanani, da kunar zuci, da wanda hirar su Abba ke rura wa a zuciyarsa.
Abba ya yi murmushi, yana kallon Zuhra. ‘Makiyi ya kan zamo masoyi a rayuwa, haka nan masoyi kan zamo makiyi, idan wani juyin ya zo. Don haka Annabi (S.A.W.) yake cewa a yi soyayya don Allah, haka nan a yi kiyayya don Allah.’ Ya dan yi shiru, kafin ya dora da fadin.
‘Ban tava zaton idanuna za su kalle ki, fuskata dauke da murmushi ba. Ban tava zaton bakina zai fadi kyakkyawan kalami a gare ki ba. Amma a yau ga shi duk wani kyakkyawan kalami da na furta miki gani nake ba su kai kalaman da ya kamata in gaya miki ba, gani nake na takaita, iya takaitawa.’
Zuhra ta yi murmushi tana kallon sa, ‘Ni ba na so ka rinka maimaita wadannan kalaman, abin da ya wuce, ina ganin ya wuce din. Ka san zuciya yadda ta ke da abin da aka dasa mata. Shi ma mahaifin namu ina fatan ya gane.’
‘Yauwa ni fa ina ganin idan ya san dawowar mu da tuni ya nemo inda muke.’
‘Kwarai kuwa, ni ina jin tsoron ma abinda zai biyo baya.’
Suka yi shiru gaba daya kamar masu nazarin abin da zai biyo baya. Can Zuhra ta nisa, wani murmushi ne ya mamaye fuskarta.
‘Idan komai ya yi daidai ai sai batunmu ko.’
‘Batun me?’ Abba ya bukata.
‘Batun da muka yi a kusa da bishiyar kwakwar nan da ta bamu tsoro.’
Ya tuna batun, amma ya yi kememe a zuwan bai tuno ba. ‘Sai fa kin tuna min.’
‘Haba Malam, batun zama daya mana.’
Ya gane, amma sai da ya kara tsonakar ta. ‘Zama daya kamar ya ya?’
‘Aure mana’ Ta fada da shagwava.
Suka yi dariya gaba daya. Sai bayan da suka yi tsaka da dariyar tasu ne, sai suka tuno, inda suka dubi vangaren da Samir ke kwance, suka yi ajiyar zuciya, Allah ya taimake su barci ya ke yi. Sai kuma suka yi mukus.
Sun makaro, domin Samir kam ba barci ya ke yi ba, zuciyar ce ke tafasa. Ya fahimci inda kannen nasa suka dosa, domin ko shakka babu soyayya ce mai girma a kalamansu. Gumi ya yi masa sharkaf a fuska, kuna ta yi masa makil a zuciya.
‘Kanwata ko zamu fita waje.’ In ji Abba ga Zuhra.
Ba ta yi alamun tashi ba. ‘Gaskiya yanzu na tabbatar zama da dan uwa da zuciya daya ya fi komai dadi.’
Abba ya yi dariya ‘Musamman ma idan akwai soyayya a tsakani.’
Suka yi shiru kafin Abban ya zarce da fadin, ‘Dazu da ki ke batun aure, a ina ki ka ga an auri mara sana’a, mara zurfin ilimi.’
Ta harare shi, ‘Wane ne ba shi da ilimin? Kai ka dauka ilimin boko shi ne ilimi kawai? Ai ilimin addinin yana gaba. Kuma sana’a, ai yanzu na san idan komai ya daidaita, kai din babban oga ne, na san ka da gwarzanta ka fa.’
Suka yi dariya, kana Zuhra ta mike da nufin su fita waje. Da Samir zai iya to ya so ya bude idanunsa ya kalli matasan biyu, da yadda za su fita daga dakin.
*****
Dukkanin yadda Kantafi ya baiwa Alhaji Masa’ud shawarar yadda zai yi haka ya yi. Jakar da ke makare da zambar gwala-gwalai da lu’u-lu’u ta tsabar kudi Biliyan shida, ya tura ta a bayan motar tasin, kamar yadda dan tasin ya ba shi umarni, don ya kai shi filin jirgin inda zai tashi zuwa Andulus.
Dukkanin tsarin Kantafi ne ya yi masa, a matsayin kwangila ta miliyan daya. To sai dai shi ma Kantafin ya yi nasa tsarin, na tsara yaransa da mutanensa, ta yadda za su sami hurumin dauke masa jakar su musanya masa da wadda yake so, ciki har da dan tasin.
Alhaji Masa’ud ya shiga motar, ‘Mu je.’ Ya ce da dan tasin.
Dan tasin ya sa giya, gami da amsawa ‘To yallavai.’
Tiryan-tiryan suna tafiya, sun yi shiru babu mai magana. Alhaji Masa’ud tunani uku yake. Matarsa dai Hajiya Kilishi ta dade da sauka a Andulus, shi ta ke jira. Matsalarsa ita ce ‘ya’yansa, duk da Kantafi ya yi masa alkawarin zai nemo masa su, ya tura masa.
Hankalin dantasi ya kwanta, a lokacin da ya cunkuson motocin da ke gabansa. Don haka ya dan tsaya a hankali, yana bin bayan motar da ke gabansa. To a lokacin ya fara yiwa Alhaji Masa’ud hirar dauke hankali.
Su kuma mutanen Kantafi su biyu, a lokacin ne daya ya fito daga cikin motar da ke biye da bayan motar tasin, ya bude but din motar kamar yadda tuni dantasin ya gama budewa, ya dauke jakar da ke cikin but din, ya sauya da irinta, ba bambanci da wadda ya sauya din.
Da cunkuson ya ragu, dantasin ya ja su zuwa filin jirgin sama, su kuma miyagun biyu suka sauya hanya, zuwa inda aka umarce su, su bi, su je, su ajiye jakar. Wani kango aka ce su ajiye ta. Hakan kuwa suka yi, suka ajiye suka yi tafiyarsu, don sun cika aikinsu.
Sai dai wautar da suka yi, ba su san mene ne a cikin jakar ba, kamar yadda ba a gaya musu ba, domin da an gaya musu ko sun sani, to da ba su ajiye din ba, da suma sun yi nasu gun da ita.
Wanda ya ba su aikin da umarnin ajiyewar, yana voye ne a nesa da wurin yana kallon wurin, yana jiran su kawo, su tafi, shi kuma ya zo ya dauka, lokacin da ya yi tsammanin zuwan su, ba su zo ba, saboda cunkoson ababen hawa, har ya gaji. Don haka ya yi nufin ya tsallaka titi ya samo dan abin sanyi ya jika makogoronsa. Tsautsayi ne ya kira shi, domin yana kokarin tsallaka titin wani mai mota da ya shawo giya ya yi tafiyar ruwa da shi.
Karaya biyu a kafa da munanan raunuka, a ko ina na jikinsa, ba kowa ba ne zai gane Kantafi ba yadda fuskarsa ta wadatu da jini. Yana ji, yana gani a cikin wani hali aka kwashe shi zuwa asibiti.
A irin wannan lokaci ne, Alhaji Yusuf da taimakon Kabir suka je ainihin dukkanin gurin da za su je don neman kanin nasa, ba su same shi ba, sai labarin cewar ya sayar da dukkanin wata kadara, ya kwashe dukkanin kudade na ajiye da na banki, ba a san inda ya nufa ba. Alhaji Yusuf ya sallami Kabir, cewar ya koma shi zai je wani waje.
Alhaji Yusuf da kanshi, ya nufi gidan Kantafi, yana da masaniyar gidan, da ya je baya nan. Ya jejje dukkanin inda ya ke da masaniyar suna zuwa babu su, ba labarinsu. Ya tuno da kangon nan, ya tuno cewar idan rakumin ka ya vata ba laifi ba ne, idan ka duba cikin akurki.
Da ya je kangon bai ga alamar su ba, har lekawar daya yi bai gan su ba, face akwati da ya gani, ya yi sha’awar ya dauki akwatin, ya je ya yi cigiyar mai ita a gidan rediyo. Sai kuma ya yi tunanin, ya bar ta inda ya gan ta, ya juya zai tafiya, sai ya ga babu adalci idan bai je da ita yayi cigiyar ba, domin ta ya ya me ita zai san inda take. Ya kinkimo ta da kyar zuwa waje.
*****
A bakin kofar shiga asibitin, Alhaji Yusuf ya hadu da Kabir.
‘Ina ka bar motar?’
‘Tana ciki.’ In ji Kabir.
‘Ya, na ga kamar ranka a vace.’
Kabir ya dan yi shiru, kafin ya ce.
‘An tabbatar min da cewar su Abba da Umma kasar suka bari.’
‘Inna Lillahi, wa inna ilahir raji’un, kana da tabbacin hakan, ko kuma dai yana wannan garin?’
‘Gaya min aka yi, ba ni da tabbaci.’
‘Daman ina son ka rakani gidan rediyo mu bada cigiya, sai mu hada da cigiyar inda suka shiga.’
Kabir ya karvi jakar da ke hannun Alhaji Yusuf, suka shiga cikin asibitin don su shiga motarsa su je.
A bakin motar ne, Abba ya karaso da sallama. Ya mikawa mahaifin sa takarda.
‘Wani ne ya kawo, ya ce a baka.’
Alhaji Yusuf ya amsa da mamaki yana kallon sa, bai ce komai ba ya bude don karantawa.
Daga Alhaji Kantafi
Ba rubutuna bane, sawa na yi aka rubuta. Ba sai ka yi mamakin cewar na san kana raye ba, ko ka fito daga fursuna. Ka san dai mu’amalata da kaninka, Alhaji Masa’ud. To dukkanin wani makirci da zalunci da ya yi maka a matsayin a mallake dukiyar ka, har ya mallake din ina da masaniya.
A karshe dawowar ka da dawowar dansa Kabir ta zamar masa barazana a rayuwarsa, wanda dole ta sa idanunsa suka rufe, ya nemi shawara ta, ni kuma na ba shi gurguwar shawara, na gina masa gadar zare wanda ya hau ya fada. A zahiri na sa ya sayar da komai ya tattara duk wata kadara da tsabar kudi an mayar da su gwala-gwalai da lu’u-lu’u ni kuma na sa an dauke su an musanya masa da jaka mai dauke da miyagun kwayoyi, wanda ina da tabbacin yanzu haka yana can hannun jami’an tsaro.
Sai dai kash! Nima da na yi hakan na gamu da gamona wanda ina da tabbacin ba zan kara kwana a duniya ba. Don haka nake yi maka albishir na cewar dukiyar da ainihinta taka ce suna kangon titin Inuwa Dikko da yake daf da gidan gonar Madaki, ka je ka dauki abar ka. Jaka ce baka, mai ratsin zaiba da farin madauki, mai jan zare a jikin madaukin nata.
Kar ka manta da sunana Kantafi masomin asara, nima kam na yi asarar.
Alhaji Yusuf ya dubi jakar da ke hannun Kabir, ya karveta, ya mikawa Abba, sannan ya mikawa Kabir takardar, tun kafin ya gama karantawa, Alhaji Yusuf ya ce. ‘Zo mu tafi filin jirgin.’
Da hanzari suka shiga motar, suka dauki hanya. Anan suka bar Abba dauke da jaka da bai san irin makudan da ke cikinta ba.
Ba su yi nisa da asibitin ba, rediyo ta sanar da su halin da ake ciki.
Jami’an tsaro na fararen kaya dake filin jirgin sama sun sami sa’ar cafke dan kasuwar nan Alhaji Masa’ud yana kokarin fita da miyagun kwayoyi. A yanzu haka jami’an tsaron sun tunkuda keyar sa zuwa babban ofishin su da ke Bompai don gudanar da bincike.
Alhaji Yusuf da Kabir sun yi gumi sharkaf. Ba tare da magana ba Kabir ya juya kan motar zuwa hedkwatar ‘yan sandan.
Mummunan labari suka riska na cewar tuni ma jami’an suka mika shi kotun tafi da gidanka ta ma’aikatan, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar da tarar dubu dari biyu, ko shekara goma ba tara.
Tun da ta ji shiru na tsawon awanni ashirin da takwas, kwana daya da awa hudu, hankalin Hajiya Kilishi ya tashi, ta san lamarin babu lafiya, rashin isowar mijinta Alhaji Masa’udu ta san akwai bayani a kasa. Kamar yadda suka yi cewar ta yi gaba shi zai biyota daga baya, to rashin biyowar a lokacin da ta sa rai, ta san ba lafiya ba.
Sai dai kafin ta kai ga nisa ta sami amsar tunaninta, sako ta samu ga abin da ya faru ga mijin nata, an kamashi a filin jirgin sama da akwatin miyagun kwayoyi.
‘Na shiga uku na lalace, wayyo Allah!’ haka ta iya fada, ragowar abin da ya biyo baya suma ne.
*****
Sai da kyar Alhaji Yusuf, Umma Maryam, Kabiru da Abba suka sami dama da izinin ganin Alhaji Masa’udu a inda yake a kulle.
Ya kura musu idanu kamar mai kokarin tuno inda ya sansu, musamman ma ya fi kallon yayansa Alhaji Yusuf. Idan ka nazarci fuskarsa, idan ka lura dashi, yana tattare da yanayin nadamar dole, sai dai baya fatan yinta a zahiri. Hawaye ne ke kokarin fito masa daga idanu, amma yana ta kokarin hanawa, to ba zai hanu ba, domin ya taru a idonsa ya bayyana kowa yana gani. Cikin takaici ya kawar da fuskarsa daga kan fusakun da ke gabansa, ya sa hannu, ya share hawayen da kyar. Ya dawo da ganinsa ga yayansa Alhaji Yusuf, babu alamar jin nauyi ko nadama a tare da shi.
‘Mene ne kuma na zuwa gurina a yanzu?’
Alhaji Yusuf ya dan girgiza kai, kana ya dubi hagu da damansa inda su Umma Maryam, Abba, Kabir da Samira suke zazzaune.
‘Ka kwantar da hankalinka, ba wani abu bane, ka dai san wane ni, kuma ka san su wane ne zaune a gabanka yanzu.’
Ya yi tsaki ‘To sai me kuma? Bari ka ji Yusufu yanda ka san rabuwar wuta da ruwa, haka rayuwata da taka ta rabu. Kar ka yi tunanin akwai ‘yan uwantaka a tsakaninmu, babu ita, na dade da sa almakashi na katse shi, babu ni babu kai.’
Alhaji Yusuf ya yi murmushi ‘Ba a katse ‘yan uwantaka Masa’udu. Ya kamata ka yi nadamar halin da kake ciki a yanzu, idan ta ni da iyalina ne babu matsala mun yafeka…’
‘Ba na bukatar yafiyarka, kai ba ka isa ka ce ka yafe min ba, me na yi maka na yafiya? Babu, da za ka gane to da ka zare lamuranka daga nawa, iyalinka da nawa ka rabasu. Sannan kuma dukiya da kake tunanin taka ce na karve to ta salwanta, don haka sai ka san abin yi…’
Alhaji Yusuf ya yi murmushi, lallai kanin nasa yana da taurin kai, ‘Dukiya sai abin da ya tavu amma ta dawo hannun da ya kamata….’
Masa’ud ya kalleshi ‘Me ka ke nufi?’
‘Abin da ka yi tsammani. Shawarar da abokinka ya ba ka ita ka bi ka tattara komai, kamar dai yadda ku ka kulla to a karshe Allah da taimakonsa an tattara komai sun fado gurin mai su.’ Ya nuna kansa.
Alhaji Masa’ud ya fahimci abin da yake nufi ‘Kai ka kulla min makirci kenan?’
‘Ba ni na kulla maka ba, abokinka ne da kuma kai kanka, ku ka kullawa makircin da ya sameka, kuma sai Allah ya yi hukuncinsa, ka san shi ne mawaarwarin makirci…’ Ya ba shi labarin dukkanin abin da ya faru.
Gumi ya rufeshi ruf, mai zafi, ya kalli dansa Kabir. Yana shirin yin magana, S. Lambu ya karaso, yana dauke da jakar kudin da su Abba suka kwato daga hannun ‘yan ta’addan nan, ta kudin da Alhaji Masa’ud ya aika musu domin karvar ‘yarsa Zuhra. Da ya zo gaban Alhaji Yusuf ya dire akwatin.
‘Akwatin kudin da Alhaji Masa’udu ya aikawa ‘yan ta’addan da suka tsinci su Zuhra da Abba ne, ga ta nan.’ Ya mikawa Alhaji Yusuf din ba tare da ya dubi Alhaji Masa’udu ba, ya dafa Kabir. ‘Kabiru ya za a yi sai mun hadu?’
Kabiru ya dubi mahaifinsa, yana kokarin yin magana kamar yadda shima Alhaji Yusuf din a kufule yake yunkurin yin magana, amma sai ma’aikacin fursuna ya karaso a lokacin yana sanar da su cewar, lokaci ya yi na barin gurin. Babu yadda za su yi, dole suka rabu, Alhaji Masa’ud bai daina kallon yayansa ba har aka shiga dashi ciki, yana tunanin irin makircin da ya kulla wa yayansa, yana tunanin halin da yake ciki, da yadda ya tafiyar da rayuwarsa gaba daya. A ransa bai yi nadama ba.
‘Zan yi maganinka Yusuf, za ka gane kurenka.’
Allah sarki bai san cewar mugun halinsa, shi zai bi ba.
Su hudun da suka baro gidan, mazan wajen Alhaji Masa’ud asibiti suka nufa, a halin tafiyarsu ne Alhaji Yusuf ya ke lallashin Kabir, da nuna masa halin rayuwa da kaddarar rayuwa yadda take. Haka nan da suka isa asibiti, Umma Maryam ta ci gaba da lallashin Zuhra, saboda halin rayuwar da iyayensu suke ciki.
Alhaji Yusuf ya yi alkawarin tallafar rayuwar su, a matsayinsu na ‘ya’yansa. Ya kuma yi alkawarin zuwa Andulus domin taho da Hajiya Kilishi.
Dukkaninsu, a gaban gadon Samir suke, wanda yake a kishingide, wasu a tsaye, wasu a zaune, hankulansu na kan Zuhra da Abba, wanda Abban ke rarrashin ita Zuhrar. Zuciyar Samir a kone take, ta gama tafasa, soyayyar Zuhra ta yi illa a zuciyar tasa, a karshe ta shafi sassan jikinsa, zuciyar ta kuma rikice masa ta haifar da kawo karshen rayuwarsa, a ransa cewa yake ‘Zuhra ina sonki, ina kaunarki, ki soni don Allah, domin kalmar La’ilaha illallahu Muhammadur Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Salam.’ Da karfi ya fadi kalmar, daga nan babu shi, ya mutu.
Dukkaninsu sun ji kalmar, don haka hankulansu ya kai kansa, sun lura da ya rigamu gidan gaskiya, Allah ya ji kansa, amin.
Na kammala.
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Mu hadu a:
Kushewar Badi…sai badi