Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Babi Na Biyu

Gurin nan dai, da suka saba zama na cikin bola shekara da shekaru, tun su Samir suna kanana, anan suke zaune su hudun. Uwar, Umma Maryam da ‘ya’yanta Samir, Abba da Samira.

Umma Maryam zaune kan tarin busasshiyar bola, ‘ya’yan nata zaune a kasa, Abba da Samira a vangaren hagu, Samir a dama, kowannensu akwai kuka a tare da shi.

Kodayake, tun lokacin da ‘ya’yan suka fara girma sun yi kokarin hana mahaifiyar tasu fita yawon bara da zuwa bololi, amma ta ce ita ba za ta daina ba, bisa dalilin da ta sanar da su cewar, zuwa bara dai don ta samar musu abinci ta ke yi, bola kuwa a cewar ta nan ne kadai take zuwa ta samu nutsuwa a ranta, domin nan ne gurin da ba wani wanda zai kore ka, ko ya yi maka korafin ka tsare masa guri. To wannan ya sa wani lokaci ma su da kan su suke rako ta, a vangaren bara kuwa sukan yi kokari su su fita ko dako ko neman taimako su samo musu abin da za su ci, amma hakan bai hana Umma Maryam zuwa barar ba, domin ta fi jin tausayin ‘ya’yan nata fiye da ita kanta da kuma yadda suke tausaya mata.

Ikrarin da Zuhra ta yi, shi ne ya tabbata, ko wuni ba su kara yi ba, bayan dogon wulakanci da cin mutumci har ma da mari, Alhaji Masa’ud ya fatattake su daga gidan. Shi ne Umma Maryam ta kamo hannayensu da ‘yan kayan su kai tsaye suka doso bola, kuma suka zauna anan. Mene ne sirrin zaman su a bolar?

Umma Maryam ta kurawa Samir idanu, ga shi tana son yi masa magana, tana son fada masa abin da ke ranta ta gaza, tsananin kama da ya yi mata da mahaifin su, mijin ta, rabin ranta, ya sa ta kasa furta komai, sai ma fashewa da kuka da ta yi.

Tsawon mintuna hamsin da biyu, babu magana, sai daga baya dan kwarin ran Samir ya kawar da shirun ta hanyar sanar da ita abin da Zuhra ta gaya musu a matsayin ‘ya’yan shegu. Ya kuma yi mata tambayar da ta kassara rayuwarta, ta sa ta ninkuwa cikin kunci, tambayar da ta tado mata da tsohon mikin zuciyarta.

‘Umma idan mu ‘ya’yan shegu ne, ki gaya mana mu san abin da za mu yi…’ Samir ya yi tambayar da muryar kuka.

Abba da Samira kuwa suna kuka suna kallon mahaifiyarsu, a tunaninsu maganganun yayan nasu da tambayar ta sa ga mahaifiyar su na iya tayar da cutar asma da ciwon kirjinta, Allah ya sa hakan ba ta faru ba, don ita Samira ma rungume mahaifiyar tasu ta yi, daga gefe.

Ta dade tana kuka mai ratsa zuciya da sanya tsananin tausayi, kafin daga bisani ta fara baiwa ‘ya’yan nata labarin rayuwarsu, ita wace ce, wane ne mahaifinsu, daga ina suke?

‘Ku ba shegu ba ne……’ Ta fara ba su labarin, muryarta a tausashe, kuma a nutse.

”Ya’yan halak ne ku. Kuma mahaifin ku yana nan da ransa.’ Da ta fadi haka sai ta shiga zubar da sabbin hawaye, amma hakan bai hana ta ci gaba da ba su labarin ba.

‘Asalin garinmu Bichi. Alhaji Yusuf, mahaifinku hamshakin mai kudi ne, attajirin da ya yi fice a wannan gari na Bichi, ya sami kudin sa ne da yake gwarzo ne a vangaren noma da kiwo. Gidanmu babban gida ne, wanda saboda kirkin mahaifinku kullum a cike yake da mutane, mabukata da almajirai.

Ta saki ragamar labarin da cewa.

‘Tun Alhaji Yusuf yana karami, mahaifansa suka mutu ta dalilin wata cutar yunwa da aka tava yi, don haka ya taso daga shi sai kaninsa mai suna Masa’udu, kuma ba su da wasu ‘yan uwan kirki. Haka suka taso cikin maraici da rashin kulawa.

Alhaji Yusuf ya zamo mutum mai kirki, a yayin da kaninsa Masa’udu ya zamo maketaci, mamugunci, to haka suka taso. Allah cikin ikonsa ya azurta Alhaji Yusuf, wanda tun kafin ya zama mai kudi ya yi aure, ya auri Umma Maryam, shi ma kaninsa ya yi aure. Saboda kokarin neman na kansa, da kokarin riko da addini ne ya sa Umma Maryam ta aure shi. Haka shi ma a daidai lokacin kanin nasa ya yi aure, kuma duk wani taimako da tallafi yana samu daga gurin mahaifinku.

‘Wata rana, bayan shudewar wasu shekaru, Umma Maryam na zaune a falo dauke da Samir, Alhaji Yusuf ya shigo, ko da ta gan shi da yanayinsa ta san akwai wani abu, a tare da shi, ta yi masa sannu, ta kuma tambaye shi abinda ya faru.

Mutum ne mara fushi, da saurin saukowa, amma a wannan lokacin ya hau da yawa, ya dube ta ya ce. ‘Maryam zan kori Mudan ne daga ma’aikata ta.’

Mudan, wani babban yaron Masa’udu ne.

Ta shiga ba shi hakuri, a lokacin. Ya tsayar da ita da cewa ‘Kar ki damu Maryam, abin ne ya yi yawa, fitinar ta shi ta yi yawa, duk ya dagula min lissafi, ya lalata min al’amura, ni da ma’aikata na da abokan harkokina, don haka wannan ita ce kawai masalaha.’

‘Rufe bakin sa ke da wuya suka ji sallamar Masa’udu. Ba su gama amsawa ba sai ga shi ya shigo har in da suke, da yake yana shigowa. Ya dube su shekeke, ko zama bai yi ba.

‘Alhaji gurin ka na zo.’ Ya fada da wata irin murya ta fushi.

Alhajin ya amsa masa da cewar yana jin sa, kuma yana sauraro.

Cikin tsaurin ido yake magana, yana cewa ‘Na ji wani kishin-kishin ne na wai za ka kori Mudan daga aiki.’

Fuskar Alhaji Yusuf ta nuna alamar yadda har kanin sa ya samu labarin nan. Lallai mutanen duniya munafurci ya yi musu yawa.

‘Kwarai kuwa.’ Ya amsa masa.

Kawai sai ya fashe da dariya, ya ci gaba da cewa ‘To wallahi kul ka aikata hakan, yin hakan daidai yake da tagayyarar rayuwarka don haka akul dinka, ka yiwa kanka kiyamullaili.’

Abin ya baiwa Alhaji mamaki, bai iya ma cewa komai ba, face kallon Masa’udun da yake yi. Shi kuma yana gama maganarsa sai ya yi ficewar sa cikin gadara ya bar su nan cirko-cirko. Shiru na tsawon lokacin kafin Alhaji Yusuf ya yi ajiyar zuciya, kafin ya ce komai Umma Maryam ta riga shi da fadin ‘Report ya kamata ka kai ofishin ‘yan sanda Alhaji.’

Huci kawai ya yi. Bai ce komai ba, alamun tunani ya ke yi, tunani mai zurfi. Can daga bisani ya nisa, ya dubi matarsa yana cewa, ‘Za a yi hakan. Kuma barazanar sa ba ta isa ta sa na fasa abin da na yi nufi ba….Lallai duniya ta lalace da mutanen cikinta.’ Ya jinjina abin a zuci, ya ci gaba da fadin ‘Dole ne in kori Mudan daga kamfanin nan.’

Abin da Alhaji Yusuf ya nufa bai kuskure ba. Kwana biyu tsakani, da hannun sa ya baiwa Mudan takadar sallama. Yaron da yake ya samu sake, kuma fitsararren yaro ne, cikin gadara ya bude, ya karanta takardar, shi ma daman ya samu labarin korar. Babu irin gurvatacciyar maganar da bai gayawa Alhaji ba a wannan ranar.

Haka shi ma, Masa’udu da ya sami labarin bayar da takardar, a ranar babu irin cin mutuncin da bai yi wa yayan nasa ba, ya kuma jaddada kudirin sa na cewar sai ya tagayyara rayuwar yayan nasa. Sati uku da yin haka, wata rana da ta zamo ta Asabar, Alhaji Yusuf da Umma Maryam suna kwance, labarin tashin gobara a daya daga cikin kamfanoninsa ya riske su. Da yake dare bai yi sosai ba suka bazama zuwa gurin da abin ya faru.

A kofar kamfanin da suka tsaya, don duba abin da ke gudana aka sace motar da suka je da ita, hankalinsu ya yi tashin da ba su san irin sa ba, duk da sun san kaddara ce da Allah zai iya jarrabar dukkan bayin sa, ya sa suka yi ta maimaita Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Suka juya zuwa gida a wata tasi, wani karin tashin hankali, tun kafin su je ga unguwar su labarin kamawar wata gobarar a gidan su na kwana ya riske su. Goma da ashirin ke nan. Lallai haka yake, kamar yadda Allah kan yi bature a dare daya, haka ya ke yin bakar fatar almajiri a dare daya.

Lamarin da a lokaci guda ya tarwatsa ginin rayuwar Alhaji Yusuf da iyalansa, wanda kanin sa Masa’udu ya haddasa, ya kulla a cikin sati uku. Wani abu da ya yi, wanda daman ya shirya wa hakan, shi ne, sai da duk ya kwashe takardu da tsabar kudin Alhaji kaf, da takardun gidajen sa guda biyu wanda yake ciki da sabon da ya gina da takardun kadarori, sannan ya haddasa gobarar.

Allah mai yadda ya so, cikin dare daya suka zama ba su da komai, ba su da wani tudun dafawa. Shi kuma kanin sa Masa’udu ya zamo hamshakin mai kudi.

Wanda ke zaune a dankareren gida sati daya da ya wuce, yanzu shi ne zaune da iyalansa a bakin wata rumfa cikin wani mawuyacin hali. Kayan jikinsu a yayyage, sun yi bakikkirin. Samir, (lokacin yana yaro) kuwa kowanne lokaci sai kuka yake yi, saboda yunwa. Yanzu ne Alhaji Yusuf yake ganin ashe mutane ba su damu da rayuwar mutum ba face kawai sun damu da abin da yake da shi. Wannan shi ake cewa duniya sai sannu.

‘A inda suke a bakin kasuwar a wulakance, a haka mutane ke zuwa su gan su su wuce su, da wadanda suka san su da wadanda ba su san su ba, babu abinda yake hada su da su face sadakar naira biyar ko goma, ko kuma ruwan sanyi ko mangwaro.

Allah ya yi Alhaji Yusuf da zuciyar nema don haka ya yi tunanin ya kamata ya tashi ya nema din, musamman don iyalansa da suke neman shiga wani hali. Me ya kamata ya yi?

Da ya fara shiga kasuwa, yana tunanin abin da ya kamata ya yi, sam rasawa ya yi – babu wani abu da zai yi na kai tsaye ba tare da tsangwama ko hanawa ba face dako. Dako ne yake da saukin da za ka tunkara ba tare da tsangwama ko ki ba. Yana cikin wannan tunani ne ya lura da wata mata Bayarabiya da a gaban ta akwai daurin kaya, da alama kuma mai daukar mata ta ke bukata, don haka ya matsa gare ta.

‘Dako ne?’ Ya ce da ita.

Bayan kallon sa da ta yi ta amsa da ‘e’.

Alhaji Yusuf ya dauka ba tare da ya tsaya ta dora masa ba. Yana da karfin daukar. Rayuwa kenan, mai sawa a dauka yau shi ne ya dauka.

Can bakin kasuwar ya kai mata, ya ajiye a inda ta bukata. Naira biyar ta mika masa. A ka’ida ya fi haka, amma ta ya ya zai nuna mata hakan? Babu! Kuka ne ya zo masa, cikin hanzari ya kawar da shi, domin yin hakan alamu ne na fushi ga yin Ubangiji, ya yi gaba cike da tunanin ya ya zai yi, da iyalinsa? Naira biyar ta yi kadan matukar kadan.

Bai san abin yi ba, yana dai tafe yana tunani, har zuwa wajen wani taro da ya ja hankalinsa. Hakan ya sa ya dan matsa zuwa gurin don ganewa idanunsa abinda ake yi.

Dambe ake yi. Tun da farko, ba yanayin yadda kartan ke kirvar junansu ne ya ja hankalin Alhaji Yusuf ba, domin shi ko kadan wannan ba ya cikin tsarinsa. Yadda ake watsi da kudi shi ne lamarin da ya ja hankalin sa matuka. Abinda yake nema ne don ya ciyar da iyalin sa bai samu ba, ya ga ana watsi da su kamar yayi ko bola.

Ransa ya biya – hankalinsa ya tashi, tunaninsa ya zurfafa. Ya kamata ya gwada wannan sana’a don ya ciyar da iyalan sa, kada yunwa ta yi musu illa. Yana sane da cewar sana’a ce mara kyau, to amma yana cikin hali mawuyaci mai muni. Ya ya zai yi?

Ko kadan bai yi mamakin yadda tunanin nasa ya dauki dogon lokacin da har sai da aka gama damben ba. Idanuwansa sai gane masa tarin kudaden da aka zuba wa wanda ya lashe damben suka yi. ya yi ajiyar zuciya mai nauyi, ya kalli dan-damben da ya lashe kudin, har hada ido suka yi.

Alhaji Yusuf bai yi kwauron baki ba, bayan watsewar da aka yi ya isa ga wani Alhaji da ya lura, ya kuma fahimci shi ne maigidan dan-damben nan da ya yi nasara. Kai tsaye ya isar masa da kudirin sa na son shi ma ya zama daya daga cikin ‘yan-damben nan. Sannan kuma ya sanar da shi gaskiyar lamarinsa da halin da yake ciki.

Alhajin ya yi mamaki, ya ba shi dariya, ya kuma ba shi tausayi. Don haka ya nuna masa babu komai, kuma zai saurare shi jibi. A karshe ya kawo naira metan ya ba shi.

Hakan ya sa Alhaji Yusuf jin dadi na gaske, ya kuma kara masa kwarin gwiwar yin damben a rayuwarsa a matsayin sana’ar da zai ciyar da iyalinsa. A ganinsa ‘yan-dambe suna da kirki, kuma za su zamo ababen harka na kwarai. Sannan kuma harka ce da karfinka ne zai samar maka biyan bukata, babu wani da zai kawo maka cikas. Idan ka cinye a ba ka kudi, idan ba ka ci ba ma a ba ka gwargwadon naka.

Ya nufi gurin iyalinsa, cike da gamsuwa.

Halin kuncin rayuwar da yake ciki shi da iyalin sa ne suka sanya shi ya yi jan halin dauriyar tunkarar kowanne kato don yin damben. Ba shi da wani zavi, ba shi da wani shiri face na neman abin da za su ci da iyalansa, sai kuma addu’a da neman taimako daga Ubangiji Allah.

Ya yi dar, ya damu, damuwa mai yawa, yau shi ne za su yi fadan dambe da wani girdeden kato, don ya sami abinda zai ciyar da iyalin sa. To idan ya mutu fa?

Shi kam, kaf a zuciyarsa da ilahirin kwakwalwar sa ba shi da wani tunani face guda uku, Allah da Manzonsa da kuma iyalansa.

Ya juya ga katon da za su kara. Shi kam ganin shi ya ke kamar wata dukiya da zai juya yake. Jin kuwwar mutanen da ke ta ihun zugawa ya ke kamar karar wayar salula na sanar da shi shigowar wata harka da zai sami abin da zai ciyar ya ci, ka da ya tagayyara. Tunaninsa iyalansa, maganar zucinsa addu’ar sa.

A cikin wannan hali ne, alkalin wasan ya ba su damar yamutsawa. Alhaji Yusuf ya saba da aikin karfi tun asalin sa, ya iya dambe da kokawa da yake a kauye ya taso. Don haka ya tuno su, ya kuma shiga katon nan da su. Sai dai damben da ba na yanzu ba ne, damben da ya yi, ya sani ba irin wannan damben ba ne da ake shirya wa, ake tsimuwa.

Haka suka yamutsa. A turmi na farko Alhaji Yusuf ya gane kurensa, ya daku iya dakuwa, sai dai ba a cinye shi ba. Haka a turmi na biyu. Amma a turmi na uku sai ya sami nasara, da taimakon Ubangiji ya shammaci katon nan, ya yi masa kwaf daya a fuska, ya kayar da shi.

Lamarin ya yi matukar baiwa mutane mamaki, ciki har da Alhaji Mato, Alhajin da ya karvi Alhaji Yusuf, wanda a tunaninsa za a yiwa Alhaji Yusuf din kwaf daya ne ya mutu, kowa ya huta. Kai shi kansa Alhaji Yusuf din ya yi mamakin kansa da wannan lamarin.

Sai dai kuma Alhaji Mato ya yi murna, da yake shi ya kawo Alhaji Yusuf din, kuma ga shi ya kashe masa yaron Sambo Gwanki, abokin adawarsa. Ya yi ta murna yana hadawa Alhaji Yusuf kudaden likin da aka yi masa da kansa.

Saboda murna ma kin karvar komai ya yi daga cikin kudin gasar da kudin likin da aka yi ya hadawa Alhaji Yusuf makudan kudade. Ya ba shi yana murna.

A vangaren su Sambo Gwanki kuwa, bakin ciki kamar me, don su a tunanin su ma tsafi ne mai karfi Alhaji Yusuf da Alhaji Mato suka yi. Don haka suka kudiri niyyar in har zabo na yawo to fa kere ma na yawo wata rana za a hadu.

A cikin unguwar dake makotaka da kasuwar da su Alhaji Yusuf ke zaune, Alhaji Yusuf ya kama daki, a wani gidan haya mai dakuna da ‘yan haya. Ya sayi kayan abinci.

Zaune yake a gefen tabarma, matarsa Umma Maryam dauke da Samir a hannu zaune a gefensa.

Abubuwan da ta gama fada masa sun shiga zuciyarsa, kuma ya yarda da hakan, ya gamsu da bayanin matar tasa.

‘Ai tun da ki ka ga na sayi wannan kurar kin san na daina dambe. Ki kwantar da hankalinki.’

Ta ji dadin abinda ya fada gare ta. Ta shiga share masa hawayen da ke fita daga fuskarsa. Suka kurawa juna idanu cike da wani lamari da ke kwance a zucin su.

Kudin da Alhaji Yusuf ya samu, ya sa Alhaji Masa’ud a cikin bakin ciki. Kamar an yi masa mutuwa ta gaba da baya, hagu da dama. Ya kasa zaune bare ya tsaya, duk komai ya dagule masa. Zuciyar sa ta takura, kwakwalwarsa ta yi zafi, zafi mai yawa.

Ya hada mata abubuwa da yawa, ya saka ya warware, ya kulla ya kunce, me ya kamata ya yi a yanzu?

‘Ganin bayan yayan nasa Alhaji Yusuf. Ganin karshen rayuwar sa shi ya kamata na yi’ Ya fada a kunnen zucin sa. Domin ya san yayan nasa da kashin arziki, yanzu ya havaka ta dalilin wannan kudi da ya samu.

Ya amince da wannan shawarar dari bisa dari, ya yarda da ita, ya kuma gamsu. Me ya rage.

A nasu vangaren su Alhaji Yusuf ba su san suna barci ne wani yana yi musu numfashi ba, Alhaji Yusuf da Umma Maryam da diyansu, suka wayi gari da asuba, an yashe musu komai na dakinsu. Abin da ya yi saura kawai shi ne kayan jikinsu, sai tabarmar da suke kai.

Wannan abu, abin mamaki ne, ba ga su kadai ba har ma ga kowa da kowa, musamman wanda ya ji labarin. Wasu suna tunanin aljanu ne suka yi aikin. Wasu kuma cewa suke yi karya ne, ba sata aka yi musu ba, su dai su san yadda aka yi suka voye kayan su.

Don rashin adalci har kurar ruwan sa dake kofar gida an sace.

Kuka Umma Maryam ta rika yi – kasa lallashin ta Alhaji Yusuf ya yi, yana kukan zuci shi ma. Da ya nutsu a tsawon lokacin awanni uku, sai ya gano an yi amfani da hodar sa barci ne, bayan an hura musu, aka yi musu wannan mummunar satar ta kassara rayuwa.

Allah shi ke yin yadda ya so, da yadda ya ga dama.

Can suka takure a lungun dama na dakin, Alhaji Yusuf ne ya ke da karfin halin yin magana.

“Zan koma dambe, Allah zai mayar mana in Allah ya so ya yarda.’

Umma Maryam ba ta so, ba ta son wannan bakar sana’ar, idan aka kashe mata shi ko aka nakasa mata miji, ya ya za ta yi kenan?

Ta kuma fashewa da kuka – ya ci gaba da rarrashin ta.

A ranar da ya ce zai koma sana’ar dambe, a ranar Alhaji Masa’ud ya sami labari. Duniya ba gaskiya, mai yawan magulmata. Hakan ya ba shi dama ta musamman da yake bukata, bai yi kasa a gwiwa ba Alhaji Mas’ud ya sami su Sambo Gwanki.

Abin da yake so, yake bukata shi ne ko ba a garin nan ba, a samo kwararren dan dambe, kakkarfa, kuma garsamemen katon da zai kawar da rayuwar Alhaji Yusuf din. Ya yi alkawarin biyan kudade masu tarin yawa, daga kan shi dan damben har zuwa su Sambo Gwanki.

Mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki, wanda aka samun ya dade zuciyarsa cike da tsanar Alhaji Yusuf din, yanda shi Alhaji Yusuf din ba dan dambe ba amma ya sami damar cinye su a karonsa na farko, don haka a ganinshi koma baya ne da tozarci ga lamuransu, su ‘yan dambe. Hakan ya sa ya bayar da goyon baya na musamman ga kudirin Alhaji Masa’ud.

Ba sai sun je wani gari ba, anan ma akwai Shago Mai Sango wanda baya yin dambe, baya karo da kananan arna sai manyan ‘yan-damben da suka gagara, suka havaka aka sansu, aka yarda da jarumtar su a fagen dambe, to su yake karawa da su. To bare wani dan tsako da ba ma harkarsa ba ce dambe.

Shi kansa lokacin da aka yi masa bayani, shi Shago-Mai Sangon, abin haushi da mamaki ya ba shi. Ya ma za a yi ace wai shi ne zai kara da wani da ba turkunuku ba. To amma da suka lallaveshi, suka gaya masa nufinsu da irin kudaden da suka ware masa, sai ya amince ya yarda zai yi masa kwaf daya ya karvi dirhaminsa.

Da ya amince su kuma suka ji dadi.

Karo na gaba

A washe-garin ranar da za a kara damben su Alhaji Yusuf a ranar gwamnati ta yi sanarwar dakatar da duk wata harka irin wannan, ta dalilin cewar ana samun mafakar gurvatattun matasa da haifar da wasu a gurin. Don haka akwai bukatar a tsaftacce harkar, kafin a ci gaba da yi, wadda kuma ta yi vacin da ba za ta tsaftatu ba, sai a hanata gaba daya.

Wannan bai sa an fasa yin damben ba, a tunanin mutane irin na wannan kasa shi ne, idan aka sa doka ba lallai ne ta fara aiki a ranar ba. Wani lokacin ma idan ba su daina ba sai dokar ta bi ruwa. Idan har ma ba kamu aka zo ana yi ba. Don haka suka ci gaba da harkokinsu.

Kai da gani babu gami, kuma shiri ne don kawar da wanda ake son kawar wa. Katon da ke gaban Alhaji Yusuf ko kadan babu gami, ruwa ba tsaran kwando ba ne.

Tun kafin a bayar da umarnin fara damben, katon nan yake neman yiwa Alhaji Yusuf kwaf daya, don a ganinshi kar ya vata masa lokaci. Allah sarki, shi kuwa Alhaji Yusuf idanunsa a rufe suke, halin da suke ciki shi da iyalinsa shi ne abin da ya fi damun sa, bai lura ba, bai kuma damu da irin girman katon da ke gabansa ba, tunaninsa Allah, fatansa fita daga halin da suke ciki.

Ya san lokacin da aka bayar da umarnin fara karawa, amma bai san lokacin da aka fara din ba, domin tun kafin alkalin damben ya matsa, abin ka da wanda ke hanzari, katon nan ya yiwa Alhaji Yusuf varin makauniya da hannunsa mai kama da faranti.

Taurari suka watsu a idanunsa, juwa ta samu a kwakwalwarsa, radadi ya watsu a jikinsa. A wannan lokacin ya kuma jin karin duka, ya kara ji ba kakkautawa daga katon nan. Zafi kan zafi wai kunama ta harbi gyambo.

Cikin wannan hali, tsautsayi wanda bai wuce ranar sa, ‘yan sanda suka halarci gurin, ba su saurarawa wadanda suka riska ba, suka yi awon gaba da su, ciki har da Alhaji Yusuf wanda bai san a halin da yake ciki ba, a sama yake ko a karkashin kasa, Allah masani.

Bayan ya sauke wayar daga kan kunnen sa, sannan ya dubi mutumin da ke gefen sa, gajere ne, fari, mai matsakaicin kauri, sunan shi Alhaji Bello Kantafi – ya cafki wannan sunan ne saboda yadda ya ke haifar da asara ga abokan harkokinsa na yau da kullum, aboki ne ga Alhaji Masa’ud, wanda a yanzu suke tsaye tare.

‘A tunani na kana da fahimta gwargwado, amma sai na ga ba haka abin ya ke ba. Don haka abu na karshe da zan gaya maka anan shi ne, na san komai tsakanin ka da yayanka Alhaji Masa’udu da kuma iyalin sa. Ma’ana yadda ka kassara rayuwar sa da ta iyalansa. Idan ba ka gane ko fahimta ba, bari in zayyane maka komai. Sai dai kafin nan kar ka manta cewar suna na Kantafi. To ina farin cikin sanar da kai cewar ina da hujjojin da idan na bayyana su, to rayuwarka za ta wulakanta, ta ci gaba da faruwa a gidan maza tare da ayyuka masu tsanani, shin kana son haka…?’

Alhaji Masa’ud bai ce komai ba, face kallo. Ganin haka ya sa Kantafi ya dora da cewa.

‘Don haka sai ka zavi daya, ko ka biya bukatar Alhaji Bello Kantafi ko kuma ka yi taka-tsantsan da rayuwar matar mamacin nan da marayun Allah da ka jefa a munin hali, wannan sinadari ne na farko da zan gaya maka, idan kunne ya ji to…’

Bai karasa ba ya wuce a fusace zuwa inda ya ajiye motarsa, ya shige.

Lokacin da Alhaji Bello ya furta kalmar ‘sinadari’ a lokacin gaban Alhaji Masa’ud ya yi mummunar faduwa. Domin an camfa Alhajin da cewar duk lokacin da ya furtawa mutum kalmar ‘sinadari’ to ba shakka sai ya yi masa sanadin tafka mummunar asara, duk da a wannan lokacin sinadarin ta zo a wani yanayi, to amma sanin hali wanda ya fi sanin kama.

Sannan shi kam a gare shi, ko me Alhaji Bellon zai yi sai dai ya yi, amma ba zai dauki kudi har miliyan daya da dubu dari ya ba shi ba haka kawai, ba aikin fari balle na baki.

‘To mene ne abin da ya kamata in yi?’ Ya tambayi kanshi. Tsawon lokaci yana nazari, yana tunani kuma yana hange. Can ya nisa bayan ya yanke shawarar gara ya nemo Umma Maryam da ‘ya’yanta da ya wulakanta, ya kora, ya dawo da su, ya ci gaba da zama da su har ya sami dabarar kawar da su daga doron kasa.

Wani abin mamaki da ya ke ji a zuciyarsa shi ne, duk irin miyagun halin Alhaji Kantafi da zaluncin shi wai shi ne yau yake ikirarin idan bai samu wadancan kudaden ba, to ya gwammace a killace su Umma Maryam da diyanta. Wannan abin, abin mamaki ne, an gasa nama an jefar.

Wannan dalili shi ya sa Alhaji Masa’ud ya binciko Umma Maryam da ‘ya’yanta ya mayar da su gidan inda suke, zama da magaji an ce ya fi zama da magajiya.

Da ta kawo nan ga labarin da take baiwa ‘ya’yan, sai gurin ya yi tsit – daman tuni kowannensu ya jike da hawayen kuka, kowannen su ya yi zurfi a tunani mai kunci, ban da mutum daya, Allah daya gari bamban.

A zuciyar Samir babu komai face tunanin yadda zai nemi kudi, don ya dauki fansa a kan kanin mahaifinsa, Alhaji Masa’ud. Lokaci guda kuma ya hadawa zuciyar tasa tunanin, don haka ya shiga nazarin irin sana’ar da ya kamata ya yi. A gurguje ya karade sana’o’i a zuciyarsa da dama ya auna su, ya ga suna da matukar wahala a gare shi, face wasu daidaikun sana’o’i da ya hango, a ciki ya ga ba laifi ba ne idan ya yi gado, ya gaji mahaifinsa wanda a yanzu ba su san inda yake ba tsakanin gidan mahaukata da gidan kaso.

A lokaci guda kuma zuciyarsa tana kara masa tabbacin lallai-lallai sai ya mallaki Zuhra a matsayin matarsa, kowa da kiwon da ya karve shi.

Zuciyar Samir kenan, ko a wane hali zukatan ragowar ke ciki?

<< Launin So 1Launin So 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×