Babi Na Uku
Yadda Ubangiji ke yin yanayi mabambanta, sanyi, zafi, damina, rani hakan ya kan yi ga lamuran mutane, ta zamantakewa ne, mu’amala ne da sauransu.
Kacokan din lamuran Zuhra ya sauya, a da babu wanda ta fi tsana irin Samir, wanda shi ne ta fifita tsanar shi a ranta, wanda ta dauke shi a matsayin wata mummunar halittar daji dake barazana ga rayuwarta.
Yanzu kam idan da akwai wanda ta tsana, to bai wuce Abba ba, daga shi ko sai mutuwar ta. Ta tsane shi ne, bayan tsana ta gado da ta gada, sai kuma tsana saboda irin gani-ganin da yake yi mata, da irin kallon tsanar da yake yawan yi mata.
Tun da mahaifinsu ya dawo da su Umma Maryam din, Abban ya ke mata wannan kallon, sai ta kai ta kawo kullum Allah-Allah ta ke yi gari ya waye ta fito harabar gidan kawai don ta yi masa wulakanci, to ita a ranar ta fi kowa jin dadi.
Ire-iren wulakancin da take yi masa ban da sa aiki na musgunawa, na wulakanci da kaskanci, duk bai fiye gamsar da ita ba domin ta ga ba ya canzawa, face idan ta sa mahaifiyar sa aiki, ko ta wulakatata to a lokacin ne ta ke ganin hawayensa, to ita a ranar sai ta ji dadi, ta je ta kwanta da farin ciki.
Abu guda da Zuhra ta gaza sani har yanzu shi ne, dalilin da ya sa mahaifinta ya dawo da su gidan. Ta san sun tsane su, to mene ne gamin su da su? Mene ne gamin kifi da kaska? Ita dai ba ta da masaniya, abu daya kwai shi ne ta kan ji kishi-kishin, wai ‘yan uwansu ne.
To shi ma haka abin ya ke a gurin sarkin zuciya Abba, ya rasa dalilin da ya sa mahaifiyarsu za ta ce su jure wulakancin Alhaji Masa’ud da iyalansa, kuma su rinka yi musu biyayya alhalin babu wani abu da suke musu n ban da dan dakin kwana da suka ba su, sai tarin kayan wulakanci, da taimakon musgunawa da kaskanci.
Kullum da bakin ciki ya ke kwana, da shi yake yini, abin har ba a cewa komai, yana da dakakkiyar zuciya amma kullum sai ya yi hawaye, ba shi da damar bijirewa saboda mahaifiyarsa mai hakuri ce.
Ita kanta kanwar sa Samira, halin su daya, abin na damunta matuka. Babban Yaya ma haka, sai dai shi soyayyar sa ga Zuhra ita ce gaba.
Karfe hudu ne na yamma, Abba ya kammala wankin motar da Zuhra ta sa shi. A lokacin ta fito domin tafiya. Zuciyarta ce ta raya mata yin wulakanci. A can gefe ta hango shi zaune kai a duke, Samir kuma tsaye yana kallon Zuhra da murmushin ‘yan samari, washe baki yake da motsawa gami da shirin fadin barka da fitowa gareta. Ya kuwa fada din.
‘Barka da fitowa.’ Ko a jikinta an tsikari kakkausa, a ganinta shi da kiyashin da ke kasan kafarta duk daya suke. A yanzu dukkanin tunanin ta da ke gwamutsuwa a zucin ta bai wuce na irin abin da za ta kaffasawa Abba ba.
‘Ya iya mota.’ Ta ce a ranta. Tabbas ta tava ganin shi ya gyarawa motar cefane fakin kwanaki, wanda har sai da ta yi masa hukunci. Ta so ta san yadda aka yi ya iya mota, sai dai ba wannan bane a gabanta a irin wannan lokacin. To in haka ne kuwa, bari a yanzu ta sa ya dauke ta, tafiya mai nisa za su yi, ta baro shi a can. Lallai in ta yi masa haka ta wulakanta shi, kai tsaye ma zai iya vata, ka ga shi ke nan lamari ya yi mata yadda take so, bukatar ta ta biya. Ta ji dadi da wannan tunani nata, ta dade tana neman hanyar salwatar da shi, yau ga shi cikin ruwan sanyi ta samu dama mai kyau.
Ta ci gaba da takawa sannu a hankali zuwa ga muhallin da motar take, ta bude ta da dan hanzari kana ta zaro mukullin motar ta dago, ta kalli inda Abba ya ke. Ta yi sa’a sun hada ido.
‘Zo nan.’ Kiran shi ta yi a gadarance.
Ya kalleta da idon tsana, ba zai je din ba, in dai akan kansa ne, to amma a dangane da umarni daga mahaifiyar sa, dole ne ya je. Ya mike, ya je gare ta, bai yi magana ba, ya tsaya kawai. Kallon da ya ke yi mata bai sauya ba.
‘Unguwa za ka kaini.’ Ta ce a takaice, har yanzu da gadara a maganarta.
Abba ya maimaita abin da Zuhra ta ce a ransa, yayin da ya ke kallon makullin da ta ke mika masa na motar da ke gabansu. Ya yi niyyar ce mata bai iya mota ba, ya sauya tunani don ganin hakan ba shi da wani amfani. Sai dai kuma ko tantama baya yi, ya san akwai dalilinta na yin hakan gareshi, dalilin kuwa bai wuce na wulakanci ba.
Ya karvi mukullin, babu ruwan shi da sanin inda za su, in ta gaya masa ruwanta, idan ba ta fada ba, ruwanta. Sai dai ta gaya masa din, tun kafin su shiga mota.
‘Ina fatan ka san hanyar Zariya ko?’
Bai gyada kai ba bare ya yi mata magana. Ita ma ta san da hakan.
‘Nan na ke so mu je, mu dawo.’
Suka shiga, tana baya ta harde. A tunanin Zuhra da tsarin ta shi ne, idan suka nausa Zariya za ta karve mukullin motarta, ta dawo ta bar shi a can, idan ta yi masa haka ta san ba wani gari ya sani ba don haka zai iya vata, bai ma san Kano ba, bare Zariya.
Amma bayan da suka fara tafiya, sai ta ga ai Zariya ta yi kusa, me zai hana su zarce nan. Idan suka yi doguwar tafiyar ta wuce Zariya, ta wuce Kaduna da Abuja za ta iya zuwa inda ya dace ta salwantar da shi, hankalin ta kwance, ta dawo, ba mamaki a haka ta karar da ragowar su Umma Maryam, Samir da kuma Samira, ka ga shi ke nan ta hutar da iyayenta zama da miyagu.
Wannan tunani na Zuhra ya gamsar da ita matuka, har ma ta dada da tunanin idan har da isasshen lokaci, to me zai hana ta zarce da shi zuwa garin arna ta watsar da shi a daji, inda take da tabbacin ta salwantar da shi kenan, in ko haka ta faru, babu wanda zai kai ta farin ciki.
‘So nake ka bi hanyar Zariya, har sai na ce ka tsaya. Kuma ina son ka yi sauri ba wai tafiyar ‘yan mata ba.’
Abba dai bai amsa ba. Tafiya ta mika. A lokacin da suke tafiya bayan da suka gifta garin Kura, anan Zuhra ta tabbatarwa kanta lallai Abba ya iya mota fiye da zaton ta. Hakan ya kara mata farin ciki, za ta yi nasarar kawar da babban wanda ta tsana a rayuwarta. Shi kuwa bai san ma abin da take kulla masa ba.
Yanzu ne Zuhra ta fara yin wani tunani a ranta. Tunanin da tun da take a rayuwar ta ba ta tava yin irin sa ba. Abban nan fa da yake jan ta, ta ke sa ran nan da dan lokaci ta rabu da shi, ya halaka ko ya salwanta, wai fa jinin tane?
‘Ta ya ya?’ Ta ambata a ranta, ta ya ya, ya zama jininta.
‘Ba zai yiwu ba.’ Ta ci gaba da batu a ranta. Kai ko ma dan uwanta ne, jininta, to ta tsane shi, tsana mai yawa. Kuma za ta iya salwantar da rayuwarsa, babu abin da ya shafe ta.
A cikin tunaninta, idanunta na gane mata itatuwa, gidaje da motoci da suke ta wucewa kamar iska, tuki mai nutsuwa da gudu mai yawa. Ta ya ya Abba ya kware haka? Shi ne ba ta gamsu ba, da ace za ta ajiye son rai da ta yaba masa ta vangaren iya tuki a nutse, amma ita ba wannan ba ne a gabanta, tsanarsa ma ta kara yi.
Lokaci bai gushe da motsawa ba, haka itama tafiya ta ci gaba da garawa, suka wuce Zariya, Kaduna da Abuja, Abba bai saurara ba, Zuhra kuwa ba ta ce ya dakata ba, awanni suka mika su ga bayan garin inda Zuhra ta gamsu da muhallin da take bukata don ajiye Abba.
Dajin da yanayin gurin ya ba ta tsoro da mamaki matuka, ita kanta ba ta san wane gari ba ne, don haka ta gamsu da gurin don jefar da Abba cikin dabara.
‘Za ka iya tsayawa anan.’ Ta umarce shi.
Ita kanta ta san ba zai yi mata musu ba, zai aminta da umarninta. Ya tsaya din kuwa a gefen hanya daf da tarin wasu bishiyoyin dajin ya tsaya. Jefi-jefin motoci na wucewa can da can, daga inda suke tsaye babu gari a kusa, sun dai wuce wani dan gari mai tazara da yawa a bayansu. Abba ba zai iya sanin yawan tafiyar da za su yi ba, kafin su riski wani garin daga nan.
Ta bude a hankali, ta fito daga motar, kallonshi ta ke yi – shi ma ya fito kafin ta umarceshi da yin hakan. Ta mika masa hannu.
‘Ba ni mukullin motar.’
Har yanzu tunanin, yadda za ta yi da shi take. Kamata ya yi ta wulakanta shi kuma ya san wulakantashi ta yi, kafin ta tafi, ta bar shi sai dai tana jin tsoron kar ya bijire mata, shi ya wulakanta ta a nisan duniya, sai yanzu ta fahimci idan ta yi wasa za ta iya yin kuskure, ta yi daurin gwarmai. A ranta, ta ce kawai ta karvi motarta ta gudu, ta bar shi, ta san ko banza shi da gida sai a darussalam.
Haka nan ta san dole ne zai wulakanta, kamar yadda ta ke so, kafin ya mutu, ba mamaki ya haukace, ba mamaki ‘yan iskan gari su kassara shi kafin mutuwarsa. Haka ya yi, ta raya wa ranta tana mai jin dadi.
Ta maimaita ‘Ba ni mukullin motar.’
‘An hana ki!’
Ta ji kamar haka ya ke shirin fada, don haka hankalinta ya fara tashi.
Ta dube shi ta kara furta abin da ta fada tun farko, saboda jin ya yi shiru bai amsa mata ba.
‘An ki a baki!’ Ya fada, wannan lokacin a zahiri ba a tunanin Zuhra ba.
Gabanta ya yi mugun faduwa. Karo na farko ke nan da ya yi magana, tun daga gida. Lallai ta faru ta kare, an yashe mai dami daya. Ta yi dauriya, da jajircewa ta dubeshi da gadara.
‘Cewa na yi ka ba ni mukullin motata.’
Ya jaddada mata ‘Cewa na yi ba zan ba ki ba.’
Da farko ta dauka abin da take ji, karya kunnuwata ke fada mata, amma yanzu ta gaskata abin da take ji daga bakin Abba da kakkausar muryarsa. Me ya dace da yin ta ke nan?
Ta yi juyin duniyar nan don ya ba ta mukullin, amma ya ki ba ta. Nufinta ya tarwatse kenan, reshen da mujiya ke kai na neman juyewa da ita. Tsawon lokaci suka yi a tsaye, babu uhm bare um-um.
Zuhra ta ga lokaci na gushewa, lamari na neman sauyawa a gare ta. Dole zuciyarta ta sauko, ta fara karaya, tana kissima adadin nisan su da gida, da kuma yanayin Abba da ta ke gani a yanzu, ta tsumu da bakin ciki.
‘Mu koma gida.’ Ta ba shi umarni, har yanzu da gadara a tare da muryarta.
Murmushi ya bayyana a fuskar Abba, karo na farko kenan a sanin Zuhra.
‘Yaushe?’ Ya tambaye ta.
Tambayar ta kuma ruda ta. Me yake nufi?
‘Yanzu na ke son mu koma gida.’
‘Ai ke da komawa gida kuma, sai a darussalam in ana komawa.’ Karsashin muryar ta shi ya razana Zuhra.
Ta tuno da abin da ta kissaima ranta na ganinta cewar shi da komawa gida sai a Darussalam, to ga shi yanzu ya fadi hakan gareta. Cikin tsiwa ta dubeshi.
‘Wallahi karya ka ke, ba ka isa ba, kai din banza, sai ka ba ni makullin motata na tafi gida…’
Ya yi dariya cikin takaici.
‘Abin da ki ka raya a zuciyar ki, abin da ki ka kudira da niyyar yi shi ne zai faru a kanki, don haka da ma za ki saduda, ki yarjewa ranki cewa kin baro gida, kuma kowa ya bar gida, to gida ya bar shi. Ki daura damarar karasa gadararriyar rayuwarki a nan, kamar yadda ki ka shirya gare ni. Ramin mugunta ne ki ka gina daidai da ke, kin kuma shiga, ga shi ya yi cif-cif da ke, don haka sai zama.
‘Abin da ba ki sani ba ne, wannan ranar na dade da neman zuwan ta, Allah da ikonsa sai ga shi Allah ya karvi addu’ata, daman shi maji rokon bawansa ne, ke da kan ki kin taimaka min na samu zuwanta daidai da yanda nake so, don haka sai ki shirya wa biyan bashi, don kuwa kowa ya ci bashin maigari sai ya biya shi.’
Maganar Abba ba karamar tsuma zuciyar Zuhra ke yi ba, lallai ta dauko ruwan dafa kanta. Mene ne mafita? Guri ko in ce gari da nisa bare ta gudu, idan mota ta tara ina kudin, kai da alama ba zai bar ta ma ta gudu ba, ta karanci hakan a cikin idanunsa.
‘Ba ka isa ba, kuma karya ka ke yi.’
Duk tunanin da ta ke yi, Abba yana gefe ko kallon ta bai damu ya yi ba a yanzu, shi dai ya tabbatarwa kansa dole ne ya kawo karshen wulakancin Zuhra garesu, kuma ya rama gashin kumar da ta ke musu. Ba zai bar ta ta koma Kano gidansu ba, ko da kuwa hakan zai zamo karshen rayuwarsu kenan, a can Kanon shi da ita, to ya fi son haka.
Ya dubi wasu dandazon kiyasai a gefen kafarsa da suke tafiya daga cikin wani tarin ciyayi zuwa jikin wata bishiya, wasu dauke da abinci a bakunansu, wasu kuma ba sa dauke da komai. Kiyasan suna tare da ‘yan uwansu a dunkule, cikin nishadi da annashuwa, shi kuwa ga shi a yau ya bar ‘yan ragowar ‘yan uwansa cikin bakin ciki da kunci.
*****
A hankali a hankali ransa ya ninku sosai a vaci, duk gidan sun san Zuhra ba ta yin doguwar tafiya ba tare da sanin su ba, idan kuma ta tafin ba ta dadewa haka, bare ba ta fada ba. Tun safe ga shi yanzu karfe takwas da minti daya na dare.
Alhaji Masa’ud ya dauke kanshi daga kallon agogon da ke hannunshi, ya goge goshinsa da ke jike da gumi, idanunsa jawur, kadan ya rage ya fitar da hawayen kuka.
‘Sun fita da Abba a mota da safe, Abban ke jan ta.’ Ya maimaita batun da maigadinsa ya fada gare shi. Ya ya ma za a yi haka ta faru. Ya san irin abin da ke tsakanin Abban da Zuhra, na tsanar da ta yi masa, abinda bai tava tunani zai faru ba, Abba ya dauki Zuhra a mota sun fita, lamarin abin mamaki ne da tambaya.
Yanzu ga shi an karade ko ina da nema, an yi cigiya, alamu sun nuna ba sa cikin garin Kano ko kusa, idan suna nan kuwa to ba lafiya.
Sai yanzu ya tuna da abinda ya manta tuntuni da ya ke bilinbituwarsa, wayarsa ya jawo, ya lalubo lambar ‘yar tasa, ya maka kira. Ya taki sa’a, a bugun farko ba sakewa ya riske ta, hakan ya yi daidai da lokacin da ita ma a nata vangare ta ke ta kokarin binciko Baban nata don gaya masa halin da take ciki.
‘Daddy! Daddy!! Abba ne ya dauko ni daga gida…Daddy ya…..’ A gaggauce ta ke maganar, tana gwama numfashi kamar za ta fitar da diyan hanjin cikinta. Abba ne ya warce wayar, ya hadata da bishiyar da kiyasan nan suka kafa sansaninsu don yin taron gaggawa, ta tarwatse.
Gumi ya jike fuskar Alhaji Masa’ud, hawayen da ya rike tsawon lokaci ya ziraro daga cikin ido daya, zuciyarsa kamar za ta faso ta fito ta kirjinsa. Ya kuma buga wayar, a kashe take a yanzu don ta sa wayar ta sanar da shi hakan. Ya kuma bugawa ya fi sau shurin masaki, wanda ya samu tabbacin abinda ya tsorata cewar an kashe ko an karve wayar ne an kasha ta.
Ya razana, gumi da hawaye babu wanda bai wadata a fuskarsa ba, shi za a yiwa haka? Ina Abba ya kai masa ‘ya kenan? Ba shi da amsa, sai karin gumi.
Hajiya Kilishi ta shigo da nata ran a vace, da jan idon da ya sha kuka, ‘ya da suke ji da ita, ana kokarin kawar musu da ita. Lamarin babba ne. Ta shigo a daidai lokacin da Alhajin ya samu kiran abokinsa a aikin ‘yansanda.
Sifiritanda Abdu Ado Rano, don haka ta saurara da fadin abin da ta yi niyyar fada tana shigowa.
‘Ina son ganinka da mutanenka yanzu a gidana. Za ku kama min wata mata ne…Ku yi sauri, ina nan ina jira.’
Hajiya Kilishi ta dube shi, tana son yin magana da tambaya, ta gaza. Shi ne ya yi magana a madadin ta.
‘Umma Maryam za a kama min, na san dole yaron ya dawo min da ‘yata, kuma wallahi sai na sa an kulle shi da wulakanci mai tsanani. Kullewar da zai gwammace bai zo duniya ba.’
Hajiya Kilishi ta ce, ‘Daman ina son yi maka magana akan zamansu a gidan nan tun kafin hakan ta faru, sai ga shi abin da ake hange ya faru din….’
‘Na san abinda ki ke son yin magana a kai, ki yi shiru kawai, karshen lamarin ya zo, daga wannan kamun da za a yi mata, to sai dai ta kare rayuwarta a gidan kaso, ita da gidan nan har abada…’
Ba su dade da yin shiru ba, ayarin su Sifiritanda Abdu Ado Rano suka iso.
‘Alhaji me ya faru?’
‘Na yi zaton kana da labarin vatan ‘yata tun safe?’
Sifiritanda Abdu ya dan yi jim na nazari ‘Ba masaniya, tun da ba ka gaya min ba, sai dai na ji a rediyo da kuma ta dibishin-dibishin, amma ban yi zaton ‘yar gurin ka ba ce, shi ya sa.’
Bayan ajiyar zuciya Alhaji Masa’udu ya ce.
‘To ‘ya ta ce, wani dan iskan yaro da ke gidan nan ya dauke ta a mota, ba a san inda ya kai ta ba, amma mahaifiyarsa tana nan ina son a tafi da ita, na san dole ya fito da Zuhra ko a ina ya kai ta.’
Ya kamata Sifiritanda Abdu ya yi tambayoyi ga Alhaji Masa’udu game da wannan lamari, to amma shi a yanzu aiki Alhaji ke kokarin sa shi ba aikinsa na ‘yan sanda zai yi ba, wannan aiki ne da kayan ‘yansanda.
Alhajin ne ya jagorance su zuwa kofar dakin da Umma Maryam ta ke zaune, gefen ta kuwa Samira ce, dukkanin su suna cikin damuwa, suna da masaniyar abin da ya faru na rasa Abba da Zuhra da aka yi a gidan, duk da ba ta Abba ake yi ba.
Ko ina Samir kuma? Dan soyayya yana can wai shi ya fita neman masoyiyarsa Zuhra. Ana dara, shi yana fadin dare ne ya yi.
‘Ita na ke son ku kama.’ Alhaji Masa’udu ne ya nuna Umma Maryam da nufin abinda ya fada.
A tare Umma Maryam da ‘yarta suka dago da dubansu, ga mutanen da ke kewaye da su, masu bakaken kaya da Alhaji Masa’udu mai koriyar rinanniyar shadda, rinin Sanagal. Gabanta bai fadi ba kamar na yadda Samira ya fadi, ta kalli Alhaji Masa’udu.
‘A kan me za a tafi da ni?’
‘Ke ki ka sani, in kin je can kya gaya musu ba ke ki ka sa dan ki ya sace min ‘ya ba.’
Murmushi ta yi. Murmushin da ke nuna idan akwai tunani gami da aiki da hankali, ta ya ya za a ce Abba ne ya dauki Zuhra a mota ya gudu da ita. Ya kamata a sake tunani.
Ya katse mata tunani.
‘Malama tashi mu je.’ Sifiritanda Abdu Ado ne, ya fada.
Ta yunkura don mikewa, Samira ta kankameta da kuka, ‘Babu inda za ki Umma, sai dai in gidan za mu bari.’
‘Ke, kina bukatar tsamin jiki ne ko kuwa?’ Daya daga cikin ‘yansandan ya yi tsawa gare ta. Ko a jikinta an tsikari kakkausa, ta yi kamkam da mahaifiyarta.
Wanda ya yi maganar, ya kai mata wafta, bai ankara ba sai ya ji mari. Kowa ya yi mamaki har Samirar ma haka, don ba ta yi zaton marin daga uwar tata ba.
‘Duk giggiwar mutum da wulakancinsa ya kare a kaina da sauran mazan, amma ban da wannan ‘yar, don haka ka shiga taitayinka, ka yi aikin da aka sa ka, ba wulakanci ba.’
Ya gaza tavuka komai, shi wanda aka mara din. A cikin su babu wanda ya iya kokarin yin wani abu, musamman don ganin yanayin fuskarta, da yadda take a zuciye.
Da ta ga sun yi cirko-cirko babu mai shirin yin Magana, sai ta ce, ‘Mu je mana.’
Jiki ba kwari, Sifiritanda da mutanensa suka juya don cika aiki. Samira ta so hanawa, Umma Maryam ta kwave ta.
‘Ki kyale su ba ki ga mai umarnin ba ne.’ Tana nufin Alhaji Masa’udu.
Da hanzari tana kuka, Samira ta nufi gaban Alhaji Masa’udu, ta fada kan kafar sa tana kuka, tana rokon sa ya kyale mata mahaifiya, kar a tafi da ita.
‘Don Allah Alhaji ka yi hakuri, ka kyale ta ni a kama ni.’
Haure ta ya yi da kafarsa, har ta tuntsira da baya. Ya wuce abinsa, yana tsaki. Yayin da su Sifiritanda suka yi gaba da Umma Maryam, gurin da suka ajiye motarsu hayis ta aiki. A lokacin Samira ta kuma yunkurin kara yin wani abu a karo na gaba, amma ina zarata biyu masu sanye da bakaken kaya suka hana ta. Tana ji, tana gani aka shiga da uwar tata, aka tafi da ita, ba yadda za ta yi, an fi karfinta.
Shin ina Samir?
Ta tambayi zuciyar ta, bayan ganin motsawar motar da ke dauke da mahaifiyar ta.
Duk wani abu da za ta yi na ban hakuri da kokarin nusarwa ga dukkanin halittar da ke gidan nan, tun daga maigadi har zuwa kan Alhaji Masa’udu babu wanda Samira ba ta yi ba, don nuna mahaifiyarta ba ta da masaniya ko hannu akan batun Zuhra, amma ko kadan babu wanda ya saurareta bare damuwa da abin da take son nunawa.
Ta galavaita a wannan rana, ta kuma rasa abin yi. Daki dai baya tashi ragaya ta zauna, ko Samira ta bar gidan nan da kanta ko kar ta bari, dole ne ma ta bari din. Ba ta san ofishin ‘yansandan da aka tafi da Ummanta ba, sai dai ta lura a jikin motar an rubuta sunan dibishin din, don haka can ta yi tsammanin za a kai ta.
Tsammaninta ya tabbata ne a lokacin da ta je ofishin ‘yansandan, ta yi kicivis da Sifiritanda Audu, sai dai ta je a rashin sa’a, domin wai tuni an kulle Umma Maryam din a sel, kuma Sifiritandan ya ki sauraronta, don haka ta nufi wani dansanda da take ganin zai saurare ta da abin da ya kawo ta, fuskarsa akwai alamun haka. Sai dai ba ta samu hakan ba, ko kusa da hakan ma, kamar yadda ta tsammata.
Da ta kara matsawa ga wani ma abin ba dadi, sai dai ta wani vangaren kuma ba yabo ba fallasa, domin shi ya ba ta shawara, yana cewa da ita.
‘Yarinya da ma kin yi hakuri, da tunanin wai a sako ko a sasanta don fito da wannan matar, wannan case din nata babbane, dama kokari ki ka yi, ki ka je, ki ka samo mata abincin da za ta ci da ruwa.’
Al’amarin ya tsallake tunaninta, shakka babu an shirya wulakanta mata uwa, in ban da haka ya a za a yi daga kawo ta ofishin ‘yansanda sai kawai a kulle ta, kuma a nuna alamun babu batun sauraron wani nata, abin babba ne.
Dolenta, ta hakura da neman taimakon yadda za a yi, daman ana neman taimako ne a inda ake sa ran samu. To babu fuska ga wadannan mutane masu riguna da wanduna gami da huluna da fuskoki bakake, don haka ta sauya tunanin ta zuwa ga nemo abincin, tun da ta san za ta iya samun dama daga gare su, ta baiwa mahaifiyar tata abincin.
Ta fice daga dibishin din, kuka take yi gami da tunanin inda za ta nufa ta samo abin da ta tafi nema din.
A haka ta fita, ‘Yankura ta nufa.
A yanzu kam ta san sun bar gidan Alhaji Masa’udu, ba ta tunanin komawa gidan. Shin ina Samir ya tafi ya bar su a cikin wannan hali? Da gaske ne Abba ne ya dauke Zuhra ya gudu da ita?
Ita kanta ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne, ba za ta tava yarda cewar Abba zai sace Zuhra ba.
A daidai wannan lokacin da Samira ke neman hanyar fitar da mahaifiyarta daga ukubar ban-ji-ba-ban-gani-ba, Umma Maryam din na dakin tuhuma na dibishin din, Sifiritanda Audu da Sufeto mai binciken masu laifi, Sufetor Iro Aliyu na tare da ita, suna ta yi mata tambayoyi irin na raini.
‘Malama ki gaya mana inda ki ka sa danki ya kai ‘yar mutane, in ba haka ba wallahi hukuncin ki mai tsananin ukuba ne.’ In ji Sufeto Iro.
Ta yi murmushi ‘Ai sai ka yi kuma.’
Sufeto Iro ya dubi Sifiritanda Audu, yanzu ya kara tabbatar da abin da ake gaya masa, lallai ya yarda mahaukaciya ce. Anya ba ta duka? Kar fa ta rufe mu da duka? Ya dubeta, duban nutsuwa, sai dai bai ga alamun abin da ya yi tunani a gareta ba, idan ma tana dukan to yana sa ran ba za ta yi galaba a kansa ba. Duk da haka bai ci gaba da zama ba, ya mike tsaye.
‘Wato kin ki amsa laifinki ko? Kin fi aminta da halin kuncin da za ki shiga ke nan. Shi kenan, kin tara kin samu.’ Ya dubi Sifiritanda Abdu, ‘Ina ganin a mayar da ita kawai, Monde a kaita kotu, abin da hukunci ya kama a yi mata.’
Sifiritanda Audu ya girgiza kai.
‘Idan aka yi haka lamarin ya kara tsayi kenan, ai so ake ko ta wane hali a matsa mata ta fito da ‘yar mutane.’
Sufeto Iro ya yi murmushi, ya kama hannun Sifiritanda Audu zuwa kofar ofishin, yana magana a hankali, yana cewa.
‘Amma ka san cewar wannan matar ba ta da hannu akan abin da ake tuhumar ta ko?’
Sifiritanda Audu ya dubeshi ba tare da yin magana ba.
‘Ka amsa min mana.’ Ya bukata.
Sifiritanda Audu ya yi ajiyar zuciya a nutse.
‘Haka ne, amma ai…’
Sufeto Iro ya ce.
‘Amma me? To abin da ya kamata ku yi shi ne, ku lallavata aja kes din, tun da kun shaka. In har ku ka takura ta, ba shakka za a iya haifar da mara ido, domin idan hukunci aka je mahaukaciya ce, idan kuma takura mata da kuma zalunci za ku yi anan, to za ta iya kuskurewa, ku shiga tasku, musamman ace aljanune tare da ita, sai ka ga an yi bawan-bawan…’
Ya yi jim, na lokaci madaidaici yana nazarin kalaman, ya hango abin da yake son fitar dashi a zancensa sannan ya fahimci hatsarin da ke tattare da kes din, to amma fa ba zai bar uwar miyar da Alhaji Masa’udu din zai bashi ba, bare tavin gishirin da ya karva.
‘Kai rabu da ita, mu ma haukace mata za mu yi, idan ita na zagi take yi mu na duka zamu yi mata, idan na duka take yi mu sai mu yi mata na kisa, ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda ko? Kuma ai danta ne ke tare da yarinyar.’
Sufeto Iro ya girgiza kai kawai yana kallonsa.
‘Akwai matsala.’ Ya fada a ransa.
*
Wasa-wasa sai ga Samira ta zama ma’aikaciya ta komai. Kwanaki hudu kenan da kulle mahaifiyar tata, babu wata magana ta nuna za a sake ta. Sannan kuma ita ce mai samo mata abinci da abin sha, ta yin aikatau da suka shafi dako, wankin mota, daukar kasa, debo ruwa, goge gilashin mota da sauransu.
Mutanen da suke ganinta a yayin aiwatar da wannan ayyuka nata suna matukar mamaki, kyakkyawar yarinya mai kamannin salihanci, da alamun mutunci da karimci.
Babban abin da ya fi damun Samira da mahaifiyarta dake kulle a sel, shi ne tabbacin Abba da Zuhra sun vata, duk da a vangaren sawa-ayi ba a damu da vatan Abban ba sai dai Zuhra. To kari akai shi ne, shi ma Samir ya bi sahu, domin tun ranar faruwar al’amarin na farko, shi ma aka neme shi aka rasa.
Ba kulleta a sel bane ke sa ta kuka ba, face yadda lamarin vacewar jininta ke gudana gareta. Na farko mijinta ya vace mata da gani, yadda aka yi masa sharrin garkame shi a kurkuku, to ga Abba ma an yi wani kullin na vatar da shi, sannan ga Samir ma kwanaki hudu, biyar zuwa bakwai babu labarinsa. Ita ma ga ta a sel an voyeta, ba ta san hawa ba bare saukowa, Allah mai iko, me ke shirin faruwa da ita da lamuranta ne?
Ita da ‘yar ta ko yaushe cikin zubar da hawaye suke, babu kakkautawa.
Lokacin, misalin karfe daya ne, rana ta yi zafi karshen zafi, wannan bai dami Samira ba, wacce ke tsakanin jerin gwanon motocin dake titin Ibrahim Taiwo, dauke da robar ruwan omo da tsumman goge gilashin motoci, na kokarinta, na samun abin sanyawa a baki, ita da mahaifiyarta da ke kulle a sel.
Masu motoci na yin mamaki da lamarinta, yanayinta da kyawunta – amma tana yin wannan sana’a, wasu na ganin ko mahaukaciya ce, kai da yawa ma a mahaukaciyar suka dauke ta. To koma dai menene hakan na sa idan ta zo wanke gilashin ake barinta maimakon a hanata, kuma idan ta gama sai ka ga mai motar ya dunkulo kudi ya mika mata. Don haka take samun kudin samarwa mahaifiyarta abinci da na ruwan sha.