Babi Na Hudu
Afilin saukar jirgin sama na Malam Aminu Kano, jirgin KLM ne tsaye, baki daga Ingila suna saukowa sannu a hankali, wasu suna hadawa da kalle-kalle ta yiwu na tsari da yanayin birnin Kanon, wasu suna cikin murmushi a fuskokinsu, wasu kuma a murtuke suke, gajiya ce ko kuma wani hali ne da suke ciki? Oho. Wasu kuwa yanayin nasu ba yabo ba fallasa.
A cikin wadanda yanayin nasu ba yabo bare fallasa kuwa har da Kabir, sai dai yana hadawa da ‘yan kalle-kalle. Bayan tsawon shekaru da Kabir ya kwashe a Ingila yana karatu, yau ne ya dawo gida, saboda ya kammala karatun nasa. Sai dai dawowar tashi, ya riski matsala – Matsalar kuwa ita ce, ta vatan kanwarsa Zuhra.
Tun satin da ya wuce a lokacin yana shirye-shiryen tahowa ya bugo wayar cewa yana nan tahowa, tun a lokacin aka sanar da shi halin da ake ciki na wai kanwarsa ta vata, abin ya dameshi matuka don tun a lokacin ya so tahowa, amma ba dama, sai a yanzu.
Tarihi ko labarin karatun Kabir a Ingila yana da abin mamaki da al’ajabi. Ya dai fara karatun ne tun daga firamare har zuwa digiri da ya yi a fannin ilimin kimiyyar tsirrai (Botany). A Ingilar ya kai shekaru goma sha uku a duniya, lamarin kuwa ya fara faruwa. Maimakon karatu, sai ga Kabir ya zama cikakken fitinanne, wannan kuwa ya faru ne saboda karancin tarbiyya da ya samu da kuma shagwava.
Sata, fitina, rashin ji da jiji da kai da Kabir ke da su, su suka sa har ya tara yara su shida har shi suka zama su bakwai, inda suka kira kansu 7 Street Bad Boys. A cikin su akwai Turawa ‘yan kasa guda biyar, sai kuma shi da wani mai suna Nnayi dan kasar Gambiya a matsayin baki.
A wannan lokaci ne, suka koyi tu’ammali da bindiga, suka iya ta, suka kware da sibaral-na-bayye, suka kware wajen rainin hankali da gagara.
To amma da yake Allah ya so Kabir da yin karatun, da taimakon Allah da taimakon wani bature malaminsu na makarantar gaba da firamare mai suna Shaun Wright, wanda ya sha alwashin kawo karshen su da fitinar su, inda ya sa su a gaba, da nazarinsu da halayensu, har sai da ya shawo kan uku daga cikin su, wanda ya hada har da Kabir. Inda ya tsaya tsayin daka a kansu, har zuwa jami’ar da Kabir din ya gama. Sauran yaran hudu kuwa suka bijire, yanzu da Kabir ya kammala digirin sa, yana girmama malamin nan, to suma ragowar hudun nan, sun zama shaihunan malamai a fannin ta’addanci, har suna ganin su Kabir ajawuna ne.
Duk da haka har yanzu Kabir yana tare da tsantsar zafin kai, dama an ce mai hali baya fasawa. Don haka a lokacin da ya ji wai kanwarsa, ta vata, wai saceta aka yi, sai yake ganin duk fadin Nijeriya ba uban da ya isa ya sace masa kanwa ya kwana lafiya. Idan har ta tabbata haka, to zai dauki mataki da hukunci da kansa. Yanzu da ya iso Nijeriya to aikin sa na farko ke nan, da zai yi kafin abu na gaba. Gani yake, kamar ma ya nemo ta ya gama, sai dai in ba ta raye.
Direban mahaifinsa ya zo daukar sa, mahaifin nasa Alhaji Masa’ud ba zai sami damar zuwa daukar sa ba. Kanwar sa kuwa ba ta nan, bare ta zo ta dauke shi. Yana isa wurin motar, Sa’idu direba ya yi masa barka da dawowa.
‘Yauwa barkan ka da gida.’ Ya sa masa kayansa a bayan motar.
Daga haka Kabir bai kuma cewa komai ba, suka dauki hanya, bi wannan titi, wuce wancan sai ga su a kan titin Ibrahim Taiwo. Danja ce ta tsayar da su, shi kam Kabir a matsayin sa na bako, kalle-kalle ya ke yi, sai dai yana jin sa a takure, to bare kuma an zo cunkoso, ran sa a vace yake, ganin garin ya ke a harbutse.
Idan zai kwatanta da inda ya baro, to garinsa Kano bola ne, garin sa Kano daji ne mai miyagun namun daji. E mana, miyagun namun daji mana, idan aka ce namun daji har aka kara musu da kambawar miyagu, to nan da nan mutum zai kawo a ransa irin su vauna, zaki, damisa, kura, vera, maciji ne da sauransu.
To haka ya ke ga al’ummar Nijeriya, duk akwai fiye da ire-iren wadancan miyagun dajin, akwai muggan verayin da suka fi verayen duk duniya iya sata, akwai muggan azzaluman da suka fi duk wani mugun zaki ko damisa zalunci, mugunta ko, ko mugun dawan dukkanin dazuzzukan duniya albarka.
Kai abubuwan dai ga su nan ba a cewa komai, a iya cewa barkatai, ba adadi dan fulani ya ga shanun azzalumin sarki.
Akwai arziki a kasa an wawashe su, akwai mutane masu ilimi a kasar sun zama dakikai, adalai sun zama azzalumai, malamai sun zama jahilai, sarakuna sun zama zakuna, shugabanni sun maye a matsayin shaidanu.
Dukkanin mintunan da su Kabir suka yi tsaye a danjar suna jiran a ba su damar wucewa, ga yawan cunkoson motocin da ke gurin, yana cike da tunani ne, ransa a vace yake, gani yake ya baro birni, gurin walawa da sakewa, gurin ‘yanci da walwala ya dawo kuntataccen kauye mai tsananin kunci da ukuba, wani daji yake ganin ya shiga mai tarin miyagun namun daji.
Tunanin sa ya katse a daidai lokacin da aka ba su damar wucewa, direban motar ya ja. Sai bayan sun gifta kadan ta kusa da yarinyar sannan ya fuskanci dalilin katsewar tunanin nasa.
Kyakkyawar yarinya ce, tsaye a gefe rike da abin goge gilasan mota, wanda almajirai ke yi, su sai abin sawa a baki. Idan har Kabir ya lura to ya ga lokacin da ta ke goge musu gilashin motarsu, kamar yadda ake yi, sai a goge sannan mai mota ya baiwa mai gogewar din abin da ba a rasa ba, idan ya yi niyya.
Cikin hanzari Kabir ya zura hannu a aljihunsa, ya jawo wasu takardun kudi da bai san nawa ba ne, ya dai tabbatar da cewar daloli ne, ta gilashin motar ya zura hannun sa ya watsa mata su.
Har suka yi nisa, Kabir bai juya ya kalli gaban sa ba, face kallon inda wannan yarinya mai sana’ar goge gilashin mota ta ke, ita kuwa ko a jikinta, an yakushi kakkausa, domin ba ta ma ganshi ba.
Daina ganin komai da tunanin komai ya yi sai na yarinya mai wankin gilashin mota. Tun da ya dawo gida Nijeriya, Kanon dabo, bai tsammanin ya ga wani abu mai kyau, sai a ganin yarinyar nan. Kyau da ya kwanta masa a rai. Ya gamsar da shi.
A zahirin Samira tana da halittun da suka hada kyau, sai dai ko kadan ita ba ta kai kololuwar kyawu ba.
Har lokacin da su Kabir suka isa gida tunanin ta yake yi, sai yanzu ya tabbatar wa kansa ya yi kuskure, kamata ya yi ya tsaya, ya ganta su gaisa, sai yanzu ya tabbatarwa kansa cewar ta shiga ransa ta dalilai biyu zuwa uku, yanayinta da kuma abin da take yi na wankin gilas, da alama ya tausaya mata, ko ta ba shi mamaki. Ya kamata ya san dalilin da ya sa ta yin wannan sana’ar, a saninsa ko a Turai mata ba su yin wannan sana’ar, can da hankali ke kwance bare nan Nijeriya. Ko kuma tsananin ne ya yi yawa, da zai sa ‘yanmata, matasa, masu kamala za su fito kan titi suna irin wannan sana’a?
Sai dai tun da ya zo ita kadai ya gani a duk titin da suka bi zuwa gida.
Sai a lokacin da direba ya iso kofar gidan, Kabir ya kuma farga, direban na kokarin shiga get din gidan ya dakatar da shi.
‘Wait.’ Ya dakatar da direban ‘Kar ka shiga, juya mu koma gurin traffic din nan, mai road jam da muka dade.’
Bai yi musu ba, duk da yana da bukatar sanin dalili, sai dai ba hali, ya juya, don cika umarni. A yanzu hankalin Kabir ya tafi ga son kara ganin yarinya mai wankin gilashin mota.
A nata vangaren Samira, duk abin da ya faru, na kallon da Kabir ke yi mata, har zuwa lokacin da ya watso mata kudin nan sam hankalin ta ba ya gurin, ba ta lura ba.
Lokacin da dalolin da Kabir ya watso mata suka dira a kan kwalta, wani gurgu ne mai cangalawa da sanduna biyu ya kai musu barra, kadan ya rage wani dan acava ya yi tafiyar ruwa da shi, Allah ya auna masa arziki, shi ko a jikinsa, domin lokacin da dan acavar ke hamdalar Allah ya kare shi bai karasa ragowar gawar da ba ta shi ba, to shi ma gurgun a lokacin ya ke hamdalar kwakwasar dalolin guda uku dake neman tashi ta sanadiyyar iska.
Sai dai yana yin gefe, ya nufi gurin da Samira ke tsaye, ya isa, ya kuma mika mata kudin. Ta karva amma tana kallon sa da kuma abin da ya ba ta.
‘Ke aka watsowa ba ki lura ba, motar nan ruwan madara da ki ka wankewa gilas, daga ciki aka watso su.’
Ba ta iya yin magana ba kai tsaye a lokacin sai da ta yi wa kudin kyakkyawan kallo, kana ta ce.
‘Wadannan ai ba kudinmu ba ne na nan.’
Gurgun ya kuma fadin.
‘E mana, ai Wapa za ki je, in ki ka taki sa’a, kudin da yawa fa.’
Ta yi tsaye tana kallon sa da nazarin zancensa.
Da ya ga haka sai ya kuma fadin.
‘To ko zuwa zan yi, in raka ki?’
Ba ta amsa masa ba. To amma a lokacin tana da bukatar ta tsaya, ta kuma cika jakar ta, ta sami abin da zata sayawa mahaifiyarta abinci, da kuma ita kan ta – Sai kuma kudin da take son yin belin mahaifiyarta, kamar yadda wani dan sanda ya sanar da ita cewar ta samo wani abu, shi zai yi cuku-cukun da zai sa a fito da mahaifiyar tata.
‘Ki zo mana in raka ki.’ Gurgun ya katse ta.
Ta dube shi, da ta yi niyyar ta ba shi kyautar kudin ya je can ya karata, sai ta ga idan ta yi masa haka zai ga ko ta wulakanta shi.
‘Mu je, amma yanzu za mu dawo.’
‘To me za mu tsaya yi a can?’
Suka rankaya. A kasa suka nufi kasuwar canjin kudin.
Suna ba da baya motar su Kabir ta iso gurin. Motar na tsayawa, ya fito a kagauce da hanzari yana raba idanu nan da can, tsakanin motocin da suka yi sahu-sahu suna jiran a ba su hannu, da tarin almajirai, da masu saye da sayarwa a jerin gwanon motocin. Babu inda idanun Kabir ba ya sintiri, daga nan zuwa can da can din.
Da ya ga kamar a haka ba zai ganta ba, sai ya yi tattaki zuwa kan wani dan tudu da ya hanga a gefe, ya hau tudun ya kara tsayi, ya ci gaba da hangawa bai hangota ba. Ya baro gurin, ya nufi gurin wani mai sayar da jarida da ya gani a can tsakiyar titi, lokacin da ya je tsallaka titi kadan ya rage wani dan acava ya yi tafiyar ruwa da shi, Allah ya kiyaye, shi ko damuwa bai yi ba, ya isa ga inda ya dosa.
Bayan sallama ya ce da mai jaridar.
‘Don Allah ina wannan yarinyar mai wanke gilas take?’
Mai sayar da jaridar ya dube shi, sannan shi ma ya hanhanga tsakanin mtoci inda ya ke sa ran ganin ta, babu ita bare alamarta, ya kuma dubawa.
‘Dazun nan na hangota, amma kaga yanzu ba ta nan, ko ina ta nufa…?’
Bai sauke maganar sa ba, wani mai sayar da katin waya da ke gefen sa ya cafe.
‘Na ga sun yi nan tare da Isa gurgu…’
Kabir ya kalli inda aka nuna din kamar mai kokarin hangota, sannan ya juya ya koma inda ya baro motarsu. Tunani ya ke yi a yanzu, tunanin yanda ya dawo neman wata yarinya da bai san ta ba, bai tava ganinta ba, wata yarinya, talaka.
Ba yin kansa ba ne, zuciyarsa ce ke son hakan, to me zuciyar tasa take nufi? Ya tambayi kanshi. Kafin ya lalubo amsa daga malaluba tunanin nasa ne ya katse. Ba wani abu ba ne ya sa shi katsewar ba, sai hango wasu ‘yanmata biyu da ya yi sun nufo hanyar da ya ke. Ya bi su da kallo a nutse, karshe ya bi su da tsaki, ‘ashe wasu kucakai ne.’ Haka ya ce a ransa da ya ga ba Samira ba ce.
Lallai akwai abin da zuciyarsa ke shirya masa dangane da budurwa mai wanke gilashin mota da ya gani. Me ya kamata ya yi a yanzu?
‘Ai kawai ka bi hanyar da aka ce sun bi, ko ka dace ka yi kicivis da ita.’ Hakan ya yi, amma kuma bai rabu da tunanin ranshi ba.
Ya bi hanyar bai ganta ba, a can karshen hanyar ya sa direban ya tsaya, da ya tsaya din, ya fito, ya tsallaka tsakiyar titin da ke daf da sakateriyar karamar hukumar Fagge, yana ta hange-hange. Wani saurayi da budurwa da suka taho, suka nufo in da ya ke su suka dauke masa hankali, budurwar ta yi masa kama da wacce ya fito nema, ko da a fizge ne, don haka ya kura mata idanu babu kiftawa.
Saurayin da budurwar sun lura da hakan kuma sun tsargu, ba su ba ma hatta mutanen da ke wuce wa ta kusa da su sun lura da hakan.
‘Malam lafiya?’ Saurayin ya dakawa Kabir tsawa.
Kabir ya yi ajiyar zuciya.
‘Am sorry, sorry. Ku yi hakuri.’
Bai hakura din ba, ya ja tsaki mai tsayi, kana ya wuce suka tafi shi da yarinyar.
Kabir ya tabbatar ba ita ba ce, ya juya babu laka a jiki, ya nufi gurin motarsa, bai yi magana da direba ba, ya bude kofar motar ya shiga.
‘Mu je gida.’ Ya fada a takaice.
Bayan amsawa direban ya ja motar, ya kara gaba.
Lokacin da su Samira suka isa kasuwar canjin kudi ta Wapa, a cike take da mutane sai dai wannan bai dame su ba, suka matsa ga wani da suka ga alamar canjin ya ke yi.
Ba su kuskure ba, domin dan canji ne, irin mai kiran mutanen da ya ga sun nufo gurin – sai dai bai damu da su ba, domin ganin alamun babu mamora a tare da su da ya yi, tamkar verayen masallaci ya gansu.
Har lokacin da suka yi masa magana bai damu da su ba, ya dauka irin masu yin tambaya ne, ko mabarata, shi hankalinsa yana kan wani dan gayen kauye da ya hango ya cakaro, ya dauka akwai wani canji a tare da shi, bai san cewar da zai caje shi, to da Naira goma ce kacal zai tarar a aljihunsa.
‘Ina jin ku.’ Ya ce da su Samira a wulakance.
Isa gurgu ne ya amsa masa ‘Canji muka kawo.’
Ya sake duban su. ‘To Bismillan ku.’ Ya mika musu hannu.
Samira ta mika masa kudin. Yanzu ya tabbatar da lallai canjin suka zo, domin kudin manya ne, ko da zai cuce su ya zalunce su shi kan shi zai sami dubu uku ko uku da dari biyar a kai. To amma ya ya aka yi suka sami wannan kudin? Ya kamata ya tambaye su, ko don tsaftace sana’arsa da kasuwarsa.
‘Ya aka yi ku ka sami dala haka, ko a wajen barar ne?’
Isa ya amsa ‘Kwarai kuwa, wani dan tahaliki ne ya jikanmu.’
Dan canjin nan ya dube su, sannan ya sanar da su cewar yana zuwa. A kan idanunsu ya shige wani shago dake dan nesa da inda suke. Su dai kallon sa kawai suke yi. Jim kadan da shigar sa sai ga shi ya fito, ya mikawa Samira.
‘Kudin naku Naira dubu takwas ne.’
Wani yarr Samira ta ji a ranta, gabanta ya so ya fadi, har ma ya fadi din ta karva da hannu yana rawa. Isa gurgu take kallo da idanun mamaki.
Dan canjin ya lura da hakan.
”Yan mata ai kudin haka yanayinsu yake, guda daya sai ki ji kudi tsababa, ba irin Nijeriya ba ne, da karshen girman kudin sa shi ne Naira dubu daya.’
‘Mun gode.’ Samira ta ce, sannan suka juya tare da Isa gurgu. A hanya ta raba kudin gida biyu ta ba shi rabi, attafau Isa gurgu ya ki karva, yana cewa.
‘Ai ni ladan ganin ido ya kamata ki ba ni, tun da guminki ne.’
Sai da kyar Samira ta amince, ta ba shi Naira dubu biyu a ciki – Suka ci gaba da tafiya zuwa inda ya kamata, gurin sana’arsu. A yayin da suka yi kwanar zuwa gurin danjar, ya yi daidai da komawar Kabir cikin motarsa don komawa gida.
Samira ta dubi Isa gurgu.
‘Ka ga mutumin can da ya jefo kudin nan. Anya ba mantawa ya yi ba, ya dawo karva?’
Gaban Isa gurgu ya fadi, tabbas mutumin ne. Zai iya gane motar nan da nan, saboda shi gwani ne na kirga kyawawan motoci na gani a fada da suka gifta ta wurin, idan za a tambaye shi kalar motoci kyawawa launi kaza da kaza nawa ne suka wuce a ranar Alhamis tsaf zai iya fadar su. Bare kuma ta wannan mutumin da ya jefo wa Samira kudi.
Haka idan aka ce ya bayyana sanfuran su, zai bayyana, ya ce wannan Hummer ce, wancan kia ce, waccan kuma end of discussion ce da sauransu.
Ya yi ajiyar zuciya.
‘Shi ne kuwa, amma ga shi can yana kokarin tafiya.’
‘Mu yi sauri, mu tare shi, mu ba shi kudinshi.’ Cewar Samira.
Isa ya kuma jin yarr a ransa, babu yanda zai yi dole ya biye ta Samira, suka zuba a guje zuwa gurin – sai dai sun makaro, domin har ya shiga motar, sun tafi.