Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Babu mamaki ga yadda Kabir ya kullacewa zuciyarsa, gami da yarda dari bisa dari ga batun mahaifinsa akan batun Umma Maryam, ashe akwai wata banzar mata da ta ke kokarin tarwatsa danginsa, wai kuma yana raye a duniya.

Idan haka ne maganin abin ya zo, domin shi zai yi maganin ta, duk irin tuggunta.

Sai dai kuma zuciyarsa ta fi damuwa gami da tunanin yadda zai nemo yarinyar da ya gani a ranar dawowarsa daga Turai, a bakin danja tana wanke gilasan mota, ana biyanta. Ko banza ana bikin duniya akan yi na kiyama, zai iya tauna taura biyu a baki.

Zai iya maganin matsalar da ke addabar gidansu, danginsa, da kuma samar wa zuciyarsa abin da ta ke kawa-zuci.

Ga shi dai dawowarsa ya riski abubuwa masu yawa na ci gaba na daukaka, arzikin mahaifinsa ya kara havaka, ga irin tanadin da mahaifinsa ya yi masa, sai sam-barka, sai kuma ga shi ya riski wani al’amari na soyayya, to ya dai kamata ya yi ta din, tun da shi bai ma san ta ba, ko da yake wacce ya so sanin shi kansa bai kamata ya kirata da soyayya ba, soyayyar ‘ya’yan Turawa, marasa kunya.

Ya isa gurin motar da mahaifin nasa ya mallaka masa domin zirga-zirga, ya bude ya shiga. Mintunan da ya kwashe tsakanin barin gida da hawa babban titi ba su wuce goma sha biyu ba sai ga shi akan titin Ibrahim Taiwo. Tun daga lokacin ya fara raba idanu don nemo wacce ya zo domin ta.

Wata motar jigilar pure water ce a gaban motarsa, don haka sai ya dan zame kadan gefe da ta shi motar sannan ya ke samun damar hango can gaba, daidai wurin danjar, inda ya ke sa ran ganin yarinyar. Hakansa kuwa ya cimma ruwa, ya hangota tana goge gilashin wata mota kirar honda me ya rage masa? Kawai ya samu ya matsa gare ta, ko ya fita daga cikin cunkoson motocin da ya ke ya yi fakin, ya je gare ta.

Samira ta kammala goge gilashin motar, ta dan yi gefe alamun tsumayi daga mai motar, Allah ya taimake ta ya dauko Naira hamsin, ya mika mata, sauri take ta tafi gurin mahaifiyarta, ta kai mata abinci don haka tana karvar Naira hamsin din a gurguje ta tsallaka daya vangaren titin, ta nufi hanyar da za ta kai ta ofishin ‘yan sandan, gurin mahaifiyarta.

Kabir ya karasa daf da inda ya hango ta, cikin farin cikinsa, sai kuma nan da nan farin cikin nasa ya juya, ya sauyu zuwa takaici saboda rashin ganinta a gurin. Ya yi ta dube-dube tun yana tunanin cewar idanunsa ba gaskiya suke fada masa ba, har ya yarda cewar gaskiya ne bai gan ta din ba, to ko aljana ce? Kai ba aljana ba ce. Hankalin sa ya kara tashi, tunaninsa ya yawaita.

Damunsa da aka yi da hon ya dawo da hankalinsa, ashe tuni an ba su hannu, ya hada cunkoso, bai ma san ashe ya kashe motar ba, da ya rasa abin yi sai ya fito, ya isa ga gaban motar (bonnet) ya bude, wai a zuwan motar ce ta mutu.

Shi kansa ya san da wuya ace dalleliyar mota irin wannan ta mace, sai dai hakan ya rage masa tsangwama daga masu ababen hawa, hatta wasu ‘yan sanda biyu da yalo-fifa da suka nufo gurin sa da zafi, sai kuma suka yi sanyi.

‘Yallavai ashe motar ce ta samu matsala.’ Yalo-fifa ya ce da Kabir.

Kabir ya amsa ‘Kwarai kuwa.’

‘Me ya same ta?’ Dayan ya tambaya.

‘Mutuwa kawai ta yi.’

Wannan ya bai wa Kabir damar ci gaba da hangawa ga wacce ya ke nema, ba tare da takurawa ba, domin idan da bai yi haka ba sai dai ya tafi can nesa ya ajiye motar, sannan ya dawo ya yi duban. Bai hangota ba, ya ga wani gurgu a kusa da shi da ya zo neman Ta Annabi gurin sa.

‘Akwai wata yarinya da ta ke goge gilas din mota a nan gurin, yanzu na hango ta, ina ta nufa?’

Isa gurgu ne. Ya hanga inda Samira ta nufa, ya yi nuni da hannunsa, ga inda ta nufa din.

‘Yanzun nan ta nufi wannan hanyar.’ Ya ce da Kabir.

Kabir ya bi gurin da kallo. Jim kadan ya yi ajiyar zuciya, kana ya zaro dari ya mika masa.

‘Na gode.’ Ya ce da Isa gurgu. Ya raya bin ta a ransa.

Samira ta isa kofar ofishin ‘yansandan, ta yi musu sallama kamar yadda ta saba, wani mai kayan tireda da ke kofar ofishin wanda suna dan gaisawa da ita ya ce.

‘Kin dawo, sannu da zuwa.’

Ta amsa masa, da alama akwai abin da ya ke son gaya mata, sai dai ita ba ta kula ba ta wuce zuwa cikin harabar ofishin. Wani dan sanda mai mukamin kofur ya bi ta da kallo.

Ta isa gurin kanta kamar yadda ta saba, tana kokarin neman uzirin mikawa mahaifiyar tata Umma Maryam abincin da ta kawo mata. Dan sandan da ta fuskanta ya rigata da fadin.

‘Hala ba ki san an fita da mahaifiyarki ba?’

Yanayinta ya sauya, akwai razana a tare da ita, kafin ta kai ga tambayar fita da ita zuwa ina, dan sandan ya ci gaba da bayyana mata.

‘Kin san a ka’ida bai kamata mutum ya dade haka ba tare da an mikashi matsayinsa ba, ko sallama ko kuma zuwa kotu, to an kai su kotu a dazu, ita da sauran wadanda ya kamata a kai kotun sakateriyar Abdu Bako.’

Ta bi shi da kallo galala, daga bisani ta juya, ta fice daga ofishin. A gurguje, zuwa ta yi ta nemi mota, ta shiga, ba jira a gaggauce ta ke amma hakan bai hanata samun vata lokaci ba a gurin motar, da ta shiga, abinka da motar haya. Ta samu dai aka kai su, ta biya kudin motar, ta nufi cikin harabar sakateriyar ta Audu Bako vangaren da kotunan suke. Wannan ya yi daidai da fitowar wata shiga-ba-biya, fita-da-Allah-ya-isa.

Samira ta bi motar da kallo, kamar mai kokarin gano mahaifiyar tata a cikin motar, bayan ta giftata ne ta dauke kai ta ci gaba da tafiya.

Allah sarki, rashin sani ya fi dare duhu, da ace tana ganin cikin bakar motar da ta gano wacce ta zo nema din kuwa, ita kuwa Umma Maryam da ke tsaye a bakin ‘yan kofofin cikin motar wadanda suke taimakawa na cikin motar gano na waje, ya sa ta gano ‘yar tata, ta bi ta da kallo cikin tsananin kunan zuci da tausayi, wani hawaye mai dumi ya ci gaba da biyo kuncinta, kasa jurewa ta yi, sai da ta kwalla kira ga ‘yar tata, amma ita kanta ta san ba za ta jiyo ta ba, ta fadi a cikin motar tana kuka.

Wahalar Samira ta takaita domin a kofar rukunin kotunan ta yi arba da wani dan sanda da ta sha gani a can ofishin da aka kulle mahaifiyar tata, ta yi saurin tambayarsa.

‘Yallavai don Allah wacce kotu a ka kai mahaifiyata.’

Yallavan ya dubeta kafin ya ce.

‘Yanzun nan an tafi da su fursuna ta Gwauron Dutse, ai tuni alkali ya gama yanke musu hukunci …’

Samira ba ta ci gaba da jin batun wannan yallavan ba, kamannin motar nan ne a kwakwalwarta.

*****

Mutumin da ‘yan uwansa ke nema, wato Samir a yanzu idan ka ganshi zai yi wuya ka ganeshi, domin ya kiririce ya susuce ya zamo tamkar mahaukaci. Koda yake halin da ya sa kansa ko ya sami kansa a ciki dole ya zamo kamar mahaukacin.

Shi dai Samir ya fada fagen tsananin soyayyar wacce yake so, wato Zuhra. Son da ya ke yi mata ba ya jin bari bare magani, irin son nan ne da ake kira makaho kuma kurma, wanda ya sa ya ke ganin ya kamata, ya bar mahaifiyarsa da ‘yan uwansa, jininsa ya tafi neman abinda zai kulla alakar soyayyarsa da masoyiyarsa.

Tunanin Samir ya kulle kaf, ba shi da wani tsaftataccen tunani da ya wuce na ya mallaki Zuhra, wannan ya sa yake ji a ransa cewar zai iya yin komai ko ya rabu da kowa, akan son Zuhra. Don haka a karshen tunanin Samir shi ne, babu abinda ya kawo masa matsala irin rashin kudi, don haka ya zavi ya nemi kudi ta dukkanin hanyar da ya ga zai iya. Ya kuwa sami damar shiga cikin rukunin dambe, inda yake sa ran zai sami kudin.

Samir ya komar da zamansa ga sansanin gurin da ake yin damben, wanda hakan ya faru tun da ya gujewa mahaifiyarsa da ‘yan uwansa, inda su ma suka neme shi suka rasa.

Zuwa wannan lokaci, Samir ya kara dambe da abokan karawarsa sau hudu, inda a dukkanin karawar saboda rashin kwarewa da shiri na musamman yake shan kayi, duk kammaninsa sun fara rikida, idan ka ganshi babu maraba da mahaukacin, sai dai duk da lallasa shi din da ake yi, yana samun wasu ‘yan kudade na ka’idar yin damben da kuma na liki ga masoyansa, sai kuma hakan ke sa shi ganin wata rana zai cimma nasara ga burinsa.

Zaune yake jigum kamar wani tsohon biri, a gefen bishiyar da ke kusa da kewayen gurin karawar damben. Mafi akasari gurin zamansa kenan, ba shi da abokin hira, bai cika motsawa da yawa ba, har ya yi nisa, wani lokacin ma a gurin yake kwana.

Abin da ya fi samuwa a tare da shi, shi ne tunani, mafi yawan lokaci yana zaune yana tunani. Mafi abin da ya fi son ci shi ne gyada, sai kuma abin da ya samu daga irin abincin da yara ke kawowa na sayarwa, dan naira ashirin-ashirin, shi bai cika cin irin abincin da ‘yan uwansa ‘yan dambe ke ci ba, abinci mai kyau, mai rai da lafiya. Sai dai ya koyi zukar tabar wiwi, wani lokaci ma idan ka ga hakoran sa a waje yana dariya, to ya ga abar ne.

Sai kuma wani abokinsa, da idan suna hira, mai suna Alu, shima dan dambe ne, kuma shi ne kadai Samir ya baiwa labarin son da yake yi wa Zuhra, Alu ne kadai ke karfafa masa gwiwar cewa ya kwantar da hankalinsa zai sami Zuhra, zai aure ta. Samir yana jin dadin batunsa sosai.

Mutum na biyu da Samir ke yin ‘yar hira da ita mace ce, wata karuwa da ta like masa, ta ke yawan kulashi, shi kuwa ganin ta yake kamar java, duk da tana da kyau, amma a gurin Samir mace daya ce a duniya, sai kuma sauran mataye, wato Zuhra dinsa.

Yana zaunen ya ji maganarta. Ba sai ya daga kai ya duba ba, ya san ko wace ce, Hinde ce, makale-mata, sunan da ya ba ta ke nan.

‘Samiri!’ Ta kira sunan da suke kiran sa. Ba ta jira ya amsa mata ba da yake akwai sanin hali ya sa ta ci gaba da cewa.

‘Jibi ne karonku da Horo ko?’ Tambaya ta yi masa, amma bai amsa mata ba, ta ji a ranta daman ba zai amsa mata din ba. Ta dora da.

‘Da za ka bi ta shawara ta da ka fasa wannan karawar, saboda Horo dai ba shi da imani.’

Samir ya yi murmushi ‘Ki fito kai tsaye, ki fadi abin da ki ke son fada, kina son gaya min cewar ni ba sa’an karon sa ba ne, ya fi ni. To a haka zan yi, kuma ina sa ran kashe shi (cinye shi) sai dai ki mutu.’

Ta yi murmushi mara gamsarwa, a zahiri tausayin sa take ji, kuma ta san dalilin da ya sa Samir ke taron aradu da ka, ga dukkanin dan damben da aka sa karawar da shi, bai wuce neman kudin da hanyar da zai mallaki masoyiyarsa ba, kamar yadda Alu ya shaida mata. Kai tsaye ta yi magana a gare shi.

‘Samir ka aureni mana, zan daina karuwanci.’

Babban abin da ya tsana ke nan ta yi masa maganar so ko aure, to anan ake rigimar, so shu’umi ne, amma Hinde ai tana da kyau irin nata, sai dai shi fa Samir bai gani. Ya amsa mata zancenta.

‘Ba zan aure ki ba.’

Ba ta yi mamaki ba a bayyane, sai dai ranta ya yi kuna, kuma daman ta saba da jin irin wadannan kalaman daga gare shi. Ta ce.

‘Amma kana ba ni mamaki Samir, mutum ya ce yana son ka don Allah da Annabi (SAW) kuma zai aure ka ya daina abin da yake, ai kamata ya yi ka yi masa adalci, ko ba ka son shi ba, ka voye, ka bi da shi ta hanya mafi dacewa. Yanzu ko don in daina, wannan bakar rayuwa ai ya kamata ace ka yi min kyakkyawan zato, da fatan alheri ka rungumi lamurrana, ka tallafi rainin rayuwata, ka dora ni a hanya zahira, mai inganci.’

Ya furta dariyar ban haushi a bakinsa.

‘Kina ba ni mamaki Hinde, ai ni ban san inda ake yin so dole ba, bai kamata ki sani a gaba ba, kina neman yi min dole akan abin da ba na ra’ayi bana bukatar sa. Kamar yadda ki ke so na, don Allah da Annabi (SAW), haka nima na ke kin ki don Allah da Annabi (SAW), kuma tun da Allah ya sa ke da kanki kin san rayuwar da ki ke yi ba ta da kyau, ai abu ya zo da sauki kawai sai ki daina, ki tsamo rayuwar ta ki daga cikin halin da take ciki, nima ki bar ni in tsamo tawa rayuwar daga cikin halin da take ciki…’

Hawaye ne cike da idanunta ‘Gaskiya sai dai ka yi hakuri amma ba zan iya kyale ka ba, kuma na yi alkawarin sai na aure ka, don ban tava sa abu a gaba ba, ban ci nasarar sa ba. Kai ina mai tabbatar maka wadda ka sa a gaban ma ba za ka yi nasara a kanta ba, ba za ka aure ta ba.’

Ta tunzura shi matuka, ta tada masa da tsumin fushi da takaicinsa. Daidai lokacin da ya daga hannu sai kaude ta, ya rabata da rayuwarta, Alu ya iso gurin, Allah ya taimaka ya fahimci abin da ake ciki, don haka cikin sauri ya isa gare shi, ya rike masa hannu.

‘Kar ka kashe musu ‘ya.’

Idanunsa sun yi ja, sun kankance, huci yake ran maza ya vaci, yana kallon abokinsa Alu wanda ya hanashi yin ta’asa.

‘Idan ka aikata hakan akwai matsala, domin na san sai ya hana ka karon ka da Horo, wanda muke sa ran za ka baiwa ‘yan kallo mamaki, domin akwai tabbacin za ka kashe shi, kuma za ka sami kudi fiye da yadda ake zato, za ka sami biyan bukatar ka, za ka ji dadi sosai…’

Maganar Alu ta yiwa Samir dadi, matuka, ta kuma bakantawa Hinde, matukar bakantawa.

*****

Ba tsananin gudu Kabir yake yi a motarsa ba, don haka birkin da ya yi gaggawar takawa bai haddasa masa hatsari ba, ya yi gaggawar yin gefe guda, motocin da ke biye da shi suma suka yi hanzarin taka birki gami da kaucewa, masu zagi na yi, masu tsaki da hantara ma na yi.

Kabir bai damu ba, ya yi saurin kashe motar, idanunsa na kan wacce ya tsaya domin ta, wadda ya gani tana tafe a kasa cikin hali da yanayi na galavaita.

Ba wata ba ce, face yarinya mai wanke gilasan motoci a danjar titin Ibrahim Taiwo, wato Samira.

Halin da ya ganta a ciki ya kara sanyata a cikin ransa, ya ji ta cika masa zuciya fal, ta kame dukkanin jikinsa gaba daya. Da hanzari ya nufi inda ta nufa, ba shi da burin da ya wuce ya kai gare ta, hakan ya sashi manta motar a bude, kuma makullin motar a jiki, bai zare ba.

Lokacin da ya kusa da ita, ya yi daidai da tsallakawar ta titi, ta tsakanin wasu manyan motoci guda biyu da suka yi jerin gwano, kamar mai son su kade ta.

Kabir ya razana da yadda ta tsallaka titin, ya tsorata, yana fadin ‘Inna Lillahi wa Inna ilaihir raji’un.’ Yana tsaye a gurin cikin mutuwar tsaye, ya yi ajiyar zuciya ganin ta tsallake babu abin da ya faru gare ta.

Bayan wucewar motocin hankalin Kabir ya tashi, takaici ya isa gare shi, rashin hangota da ya yi, ya duba dukkanin hagu da dama, gefe da gefe bai hangota ba, ta vace masa. Tunaninsa ya raya masa cewar aljana ce, sai dai zuciyarsa ba ta gamsu da hakan ba.

Ya tsallaka da gudu, kai tsaye ya doshi bayan makarantar koyon sana’o’i ta Kofar Nassarawa, (Government Technical College), cikin sassarfa da gudu-gudu, hanyar da tunaninsa da kwakwalwarsa suka ba shi nan ya ke dosa, wulla can doshi can, zaga can sai ga shi ya karade gurare da dama, gami da doguwar tafiya da ta haddasa masa gajiya, amma bai ganta ba. A yanzu idan ka gan shi za ka iya tunanin sabon hauka ne, babu maraba da wahalalle.

Sai a lokacin da ya gaji tuvus ne, sannan barin mukullin motarsa a jikin motar ya fado masa a rai, ya juya da gudu don komawa inda ya yasar da motar. Gudu yake tukuru, gumi da tsananin halin da ya ke ciki har ba a cewa komai.

Ya sha kwana da gudu, kamar zai tashi sama, kana ya ja ya tsaya kyam kamar wanda yalo-fifa ya tsayar, kiris ya raga ya tunkude ta, tsananin haki yake kamar ransa zai fita, huci yake, kallon yarinyar yake kamar zai hadiye ta. Yarinyar da ya ke nema ce ruwa a jallo, ido bude, wato yarinya mai wankin gilasan motoci ana biyanta, Samira.

Kamar yadda ya tsaya, ya kafa mata idanu haka itama ta zuba masa nata idanun, tana kuka. Sun jima a haka, kafin daga bisani su yi ajiyar zuciya a tare, rasa me ya kamata ya ce da ita ya yi, don haka ya ce.

‘Sannu.’ Ba ta amsa masa ba. Tunani ta ke yi, tunanin inda ta san shi, amma ta rasa saboda halin da take ciki, amma a zahiri ta ji a ranta kamar ta sanshi. Ko me kama da shi.

Shi ma ya kamata a ce ya san ta din, to amma halin da ya ke ciki na sonta, ya mamaye hakan, don haka bai baiwa hakan muhimmanci ba.

‘Ki yi hakuri da halin bin ki da na yi, wannan ya faru ne saboda dalilin da zan gaya miki a yanzu.’

‘Ba na bukatar ji.’ Ta fada masa.

‘Afuwa za ki yi min, ba wani abu ne da za ki ki shi ba. Adalci za ki yi min, ki saurare ni, idan ya so daga bisani sai ki yanke min duk hukuncin da ya kamata, zan yi biyayya ga haka….’

Ta katse shi ‘Ashe ke nan ya zama dole sai na ji abin da za ka fada?’

‘Ba haka nake nufi ba. Nufi na ki yi adalci a gare ni, a matsayin bawan da yake neman samun haka a gare ki.’ Ya dan yi jinkiri, kafin ya dora da bayyana mata dukkanin farkon fara ganin ta zuwa wannan lokacin. Ya so, ya bayyana mata ko shi wane ne, sai ya takaita, saboda ya gujewa kar ta gaji, ta yi tafiyarta.

Bayan ta gama jin shi tsaf, sai ta ce.

‘Wannan duk kai ta shafa, ba ni ba, don haka ka rabu da ni ka fita hanyata.’

Ya fahimci ranta a vace ya ke matuka, dama abin da ke ranta yana matukar damunta, to amma ya kamata, ya shawo kanta a wannan loton ka da ya yi wasa da dama mai kyau ta wuce shi. Sai dai kuma hakansa bai cimma ruwa ba, domin da ya nemi matsa mata sai da ransa ya yi matukar vaci. Kuma ta wuce shi, ta bar shi a tsaye, hawaye a cikin idanunshi.

Ya dade yana kallonta, kafin daga bisani ya yi ajiyar zuciya mai daci, ya fara tafiya don komawa gurin da ya ajiye motarsa. Bai gama sanin dukkanin halin da ya ke ciki ba a yayin tafiyar da ya ke, amma ya san lokacin da ya isa gurin da ya ajiye motar, inda ya tarar babu ita, babu kuma alamar ta, yanzu ne ya tuna tabbatarwa a jikin motar ya bar mukullin, duk da haka bai hana shi shafa dukkanin aljifansa ba, a tunaninsa ko zai ji wani abu mai kama da mukulli, babu.

Ya ji zafi a ransa, don ya tabbatar ya yi asarar motar, an sace ta, amma zafin da ya ke tare da shi na rasa kyakkyawan kalami daga Samira, ya fi damunsa, abin da rai ke so, da ace ya sami kyakkyawan kalami daga Samira, to da zai iya bayar da kyautar ire-iren motar tasa guda biyu.

Hawaye ya kuma zubowa daga idanunsa a karo na biyar. Ya fara takawa a hankali da nufin tafiya gida daga inda yake a tsaye din, ya yi taku a kalla goma sha biyu, kansa a kasa, lokacin da ya ji wani alamu a gabansa, a lokacin ya dago da kanshi.

Gaba daya, kakarataf din jikin sa ne ya ji ya dauki tsuma, yanayinsa ya sauya. Samira ce a gabansa. Sakin baki ya yi, ya kasa magana, har sai da ita din ta ce.

‘Ka yi hakuri da maganganuna, ina cikin wani hali ne na vacin rai. Ka yi min hakuri.’ Daga haka ba ta kuma cewa komai ba, ta wuce, ta bar shi nan. Ya kasa cewa komai, ya kyale kunnuwansa na yi masa maimai din zancenta.

Kafin ya ankara ta vace masa, wannan kuma shi ne kuskuren da ya yi a karo na biyu.

*****

‘Ya kamata ka san wa ka ke son rainawa wayo. Ka san ni din ba kanwar lasa ba ne da za ka rinka zuwar min da duk wata shegantaka da ka ga dama. Idan ban da rainin hankali ya za ka taso da wani waskataccen bakin ka, ka ce wai in ba ka kudi har miliyan takwas. Ina laifin ka ce min maula ka zo, in sa ma maka ko da dari uku ko biyu ko biyar ba…’

Alhaji Masa’udu ya ce da Alhaji Kantafi.

Kantafi ya yi murmushi ‘Lallai kowa ya kalli auran jaki ya san zai yi varnar kara. Kar ka manta cewar a gabanmu ka kulla kasuwancin zalunci, wanda sanin kanka mune ‘yan kamashon sa, muna da namu kason, dole ko an ki ko an so, ko kuma a fasa kasuwancin kowa ya rasa, shin ka manta da hakan?’

Alhaji Masa’udu ya san abin da yake nufi, bai yi magana ba. Kantafi ya dora.

‘Jin dadin ka in rinka zuwa sannu a hankali ina yafita, sai wani lokacin kuma in sake dawowa. To amma idan ka ki, wannan ruwanka ne yiwa kai adalci ko rashin sa, duk wanda ka ga ya kwana lafiya to fa shi ya so, kuma kura ce ta kan ci kura, babu yadda za a yi kare ya ci kura.’

Alhaji Masa’ud ya fusata ‘Lallai a wannan karon karen zai ci kura ya hada da romon vauna, domin na daina yankawa kare ciyawa.’

‘Haka ka ce?’ Cewar Kantafi.

‘E, abin da na fada ke nan.’

‘Ka manta da nadama ko?’

‘Kai ka san ta.’ Fadin Alhaji Masa’ud. Suka kalli juna, ido cikin ido tsawon lokaci, sai murmushin mugunta da suka yiwa juna na karshe.

<< Launin So 5Launin So 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×