Skip to content
Part 8 of 10 in the Series Launin So by Kabiru Yusuf Fagge

Tun kafin hadarin ya hadu guri guda Zuhra da Abba suke tafiya, sun mike hanya, ba su da tabbacin inda suka dosa, sai dai alamun da ke nuna suna tunanin hanyar titi za ta kai su, amma a zahiri daji suka kara nausawa.

Zuhra ce a gaba, Abba a gefe, babu ruwan wani da wani a cikinsu. Yanayin jikinsu, ba a Magana, saboda muni na jigata da shiga halin wahala.

Sannu a hankali yayyafi ya fara sauka, tun yana yi a hankali har ya fara karfi, daga bisani ruwa mai suna ruwa ya fara yawa, ya yi karfi. Allah da ikonsa ruwan sai ya yi karfi da iska mai tsanani, bayin Allahn nan a haka suke tafiya, kowannensu babu tantama yana jin jiki na dukan ruwa da sanyi, ajiyar zuciya suke yi.

Ba su san inda suke nufa ba, wanda hakan ya sa suka kai kansu cikin wani kududdufi, a zahiri tun a farko-farko sun lura da ruwa ya fara lashe kwaurin su, zuwa gwiwa, zuwa cinya amma saboda cushewa da wasu al’amura da zuciyarsu ta yi, ya sa ba su kula ba, har sai da ba su ankara ba ruwa mai karfi ya ribace su da taimakon tavo, ya zurara da su zuwa cikin ainihin kogin, ya yi awon gaba da su.

A lokacin hankalin Abba ya yi kan Zuhra, hankalinsa ya tashi, gabansa ya shiga faduwa, ya yi karfin hali, da kokarin ganin ya fitar da ita daga mugun halin da suke barazanar fadawa.

Tsawon lokaci ruwan na watangaririya da su kafin Allah ya baiwa Abba dama ya fito da su zuwa bakin gava, ya tura ta can gefe gami da kokarin tokare ta da wani reshen bishiya da iska ta vallo, shi ma ya sami gefe ya fadi cikin hali mai muni.

Ruwan saman bai sassauta ba, ya ci gaba da laftar su ba kakkautawa, har na tsawon lokacin da Allah ya debar masa, sannan aka dauke ruwan, sai da aka yi sama da mintuna arba’in sannan Zuhra ta farfado, ta fara raba idanu da wani hali na daban, sannu a hankali tana wartsakewa, tana dan motsawa har idon ta ya kai kan Abba, a gefe guda yake kwance magashiyan, ta kura masa idanu, sannan ta motsa bakinta, ta kawar da kai gefe, wani yanayi ta ji a tare da shi.

Ragowar mintuna biyar da suka biyo baya sun taimaka mata wartsakewa, ta kokarta ta mike zaune da kyar, ta jingina da reshen bishiyar da ke bayanta, ta kurawa Abba idanu, da har yanzu bai farfado ba.

Ta kawar da kanta daga kallonsa, ta dubi yanayin gurin da suke, ta kalli kogin, sannan ta tuna abinda ya faru zuwa zamewarta da tavo, ta tabbatar sun wahala, matuka, ta mayar da kallonta gefen da take, wani kafcecen itace ta gani mai tsini a karshensa, tunani ta yi da ta cake da shi, da nan da nan babu ita, ta mutu. Ta juyo da kallonta gurin Abba, gabanta ne ya fadi saboda hada ido da suka yi.

Ba ta dauke ganinta daga gareshi ba, shi ma haka, suna haka har ya wartsake, ya mike zaune, suka fuskanci juna sosai da sosai, a yanzu yanayin kallonsu ya bambanta da na baya da suka saba yiwa juna.

Zuciyar kowanne cike da wani sakonni na al’amura da yawa. Kallon bai gundire su ba, mamaki ma yake ba su.

‘Ka….ka…ga rayuwa.’ Da rawar baki Zuhra ta yi maganar. Ita kanta ta san sautin maganar ba ya fita, kamar yadda ba ta jin komai sosai a kunnenta na sauti.

Ya kuma dubanta sosai. Suka yi ajiyar zuciya a tare, suka dauke kansu ga duban juna.

‘Zuhra…’ Karon farko kenan a dukkanin rayuwarsa da ya kira sunan ta da irin wannan yanayi.

Ko alamun ji ba ta yi ba, bare ta juyo ta dube shi, ta ji dalilin kiran. Gabansa ya fadi da karfi, abin da ya yi tunani da nazari shi ke shirin faruwa ko ma ya faru din. Idan kuwa Zuhra ta kurumce to lallai ya yi mata babban laifi, ya cuce ta. Haka kawai ya ke jin wani irin yanayi na game da rayuwar Zuhrar a ransa. Yana jin ta a rai, yana jin tausayinta, ya damu da yanayin halin da ta ke ciki, a yanzu ya ke jin ta a ransa a matsayin ‘yar uwarsa, ko me ya sa? Ya lura tun a baya yake cikin wannan hali na tausayawa Zuhrar.

Ya yi wani tunani da ya ba shi tsoro, wanda nan da nan ya kawar da tunanin a ganinshi don kar ya zama gaskiya, ya za a yi ya so Zuhra?

A gare ta kuwa, tun da ya shiga wannan halin tunanin ta ke yi, tunanin me ya sa ta goyi bayan iyayenta suka yiwa Umma Maryam da ‘ya’yanta wulakanci da rashin kirki, cusgunawa da takurawa. Yanzu ta yi nadamar zamowa daya daga ciki, domin ga shi a yanzu yana taimaka wa rayuwarta, ba ta yarda da fadar sa ba cewar so ya ke yi ta yi mutuwar wulakanci ba, domin ai duk kokarin da ta yi na kashe kanta, ai yanayi ne na mutuwar wulakanci, ta dubi inda yake, kana ta kawar da kanta can wani guri.

Abba don ya tabbatar da tunaninsa, sai ya kuma kiran sunanta, shiru, ya sake, babu alamun da suka nuna ta ji. Ya kura mata idanu, sannan ya daga murya da karfi ya kira sunan nata, wanda har sai da dajin ya amsa, amman ga Zuhra ita jin kiran ta yi kamar mai yi mata rada, ta juyo a hankali da nutsuwa ta dube shi.

Ya tabbatar wa kansa abin da ya zata, hawaye ya fara zubowa daga idanun sa, masu zafi da tsantsar tausayawa. Ita ma hawayen ta fara yi.

Da ace kowannen su zai ga zuciyar dan uwansa da sun yardar su ‘yan uwan juna ne na jini, masoyan juna kuma.

Suna zaune a haka cikin yayyafi-yayyafin da ake yi, wanda su bai dame su ba, ba su ankara ba ruwan ya sake varkewa kamar da bakin kwarya, wata iska mai karfi mai kama da guguwa ta mamaye su, ba zato suka afka cikin wani hali mai ban tsoro. Tsawon lokacin da ba su tantance yawan sa ba, suka farfado a lokacin da ruwan ya dauke, a wani guri daban mai fili, gindin wata bishiya a gaban wasu karata su hudu. Da yake Zuhra ce ta fara farfadowa ba ta iya yin komai ba sai bin su da kallo da take yi, tana kuma kallon Abba da ke kwance, a daure.

Shi kuwa Abba da ya farfado ko gama wartsakewa bai yi ba, ya yunkura zai nufi gurin Zuhra da ya ga kartai biyu sun kewaye ta, sai ya ji shi a daure, ya yi kici-kicin wai ko da halin suncewa, ya ji shi daure tamau, kawai sai ya koma kwancen daga bisani ya dago kai ya dubi mutanen da suke kansu, sannan ya dubi Zuhra sosai, kamar yadda take hawaye, haka shi ma ya ke yi, ya kura mata idanu har lokacin da daya daga cikin kartan nan dan kabilar Ibo ya katse shi.

I tell you na him’ (Na gaya maka ita ce) a lokacin yana kallon Zuhra.

Is true, ita ce. Lallai mun samu kudi.’ Wanda ake gayawa din, Bakatafe ne ya amsa. Suka yi dariya gaba daya.

Suna cikin wadanda suka riski sanarwar cigiyar Zuhrar a kafafen watsa labarai, da irin makudan kudaden da aka sanya ga dukkan wanda ya samo inda ta ke. Tun a lokacin suka sha alwashin idan Allah ya sa suka yi kicivis da ita, to fa sai sun ninka, ninki ga kudaden ladan da aka sa ga duk wanda ya ganta din. Musamman da ya ke kwana biyu sana’ar tasu ta fashi babu riba sosai.

To ga shi addu’arsu ta karvu, ya rage gare su da su san hanyar fitowar makudansu. Abba kallon su kawai yake yi, yana nazarin su, da ya nazarci Zuhra kuwa sai ya ji farin ciki ya kama shi, saboda alamun da ya gani na tana ji sosai a yanzu.

*****

Wayarsa da ke ajiye a kan tebur ta yi kara, ya tsani ya ji an kira shi saboda takaici, da kuma halin da yake ciki na vatan ‘yarsa Zuhra. Sannan kuma yana matukar son jin an kira shi don yana sa ran za a ce an ga diyar ta sa, ba don haka ba da ba zai rinka daukar wayar ba, musamman idan ya tuna da yadda Kantafi ke damun sa.

Ya sa hannu a hankali ya dauki wayar, voyayyiyar lamba ya gani, shi kuma ba ya dauka, don haka ya kyale ta, ta yi kararta, ta gama ta katse. Tana katsewa ya ji gabansa ya fadi, me ya sa bai dauka ba? Ya kurawa wayar idanu, ransa a vace, jira yake a kara kira ya daga, kuma ga shi, ba shi da damar kira. Zuwa can kamar an yi fushi, sai ya ji an kira, ya duba, a wannan karon ransa ya kara vaci, ba waccan voyayyiyar lambar ba ce, wannan a rubuce a sunan wanda ya kira an rubuta Masomin Asara, wato Kantafi. Cikin hanzari yana huci ya katse kiran. Yana katsewa da sakan bakwai kira daga voyayyiyar lamba ya kuma shigo wa, duk da haka ya yi zargin Kantafi ne ya kira shi, amma ya dauka a hankan, yana fadin ‘Hello…..wane ne…?’

Daga voyayyiyar lambar aka ce.

‘Ba ka san ko wane ne ba, sauraro ake son ka yi. Daga wadanda suka tsinci ‘yar ka ne…’

Alhaji Masa’ud ya yi zumbur. Bai yi magana ba, ya kara nutsuwa ga sauraro, a can vangaren kuwa ba a tsaya da magana ba.

‘Babu batun doguwar magana, idan kana gidanka, ka fita kofar gida, jikin katangar gidan, akwai sako ajiye a leda ka dauka ka duba, idan kuma ba ka gida, ka yi saurin komawa gidan, domin ‘yarka na cikin ledar.’ Aka katse layin.

Gaban Alhaji Masa’ud ya yi mugun faduwa.

‘Me ake nufi da ‘yata na cikin ledar? An kashe ta ke nan?’ Gumi ya jika shi sharkaf, ashe yana matukar son Zuhra. Wani abu da ya ke ba shi mamaki shi ne, ina Abba yake, tun da wannan ba maganarsa ba ce, ko zuwa ya yi ya hada kai da ‘yan bindiga-dadi haka.

Da sauri ya mike, ya bazamo zuwa kofar gidan nasa kamar yadda aka bukata. Sam, tunaninsa a kulle yake dif, bai yi tunanin yaudara ko kwatankwacin sa ba.

Maigadi yana barka da fitowa Alhaji, amma babu alamun ya ji shi, da kansa ya bude karamar kofar dake jikin babbar kofar gidan, ya fita, yana fita babu abin da ya fara yin ido biyu da shi, sai ledar nan da ke zaune, ajiye a gefe guda, tana tsimayen shi.

Ya raina tudun ta, don haka bai yi zaton ganin ‘yarsa a ciki ba, ya je gare ta, ya mika hannu ya dauka, bude ta ya yi, ya kalli cikinta, takarda ya gani da faifan sidi (CD) a cikin gidansa, ya sa hannu ya dauko takardar, ya karasa warware ta, da zummar karantawa.

Mu ne muka taki sa’ar samun garavasar lashe kyautar da ka yi niyyar yi ga dukkan wanda ya gano inda ‘yarka ta ke. Don haka muke yi maka albishir, hankalinka ya kwanta tamkar tsumma a randa, wahalarka ta yanke a yanzu.

Sai dai kawai farashin da ka ware ga wanda ya kawo maka ita din ya yi mana kadan, domin ko banza muna da yawa da muka tsince ta. Sannan ba ma bukatar ciniki, mun yanke abin da ya kamata ka ba mu, babu yawa miliyan ashirin ne. Ba ma bukatar cece-kuce, mun san yadda ka matsu din nan, za ka fi son ‘yarka fiye da miliyan ashirin din.

Domin karin bayani sai ka kalli faifan sidin da ke tare da takardar nan. Da kuma bayan takardar, inda za ka riski ainihin inda ake bukata a mika a kuma karva, da fatan ka gane….

Bai gama karantawa face gumi ya rufe shi sharkaf, idanu kwala-kwala ya ke kallon takardar da faifan sidin.

Ya bazama zuwa cikin gida, a hanya, a falo ya yi kicivis da Hajiya Kilishi, ta dube shi.

‘Alhaji me ya faru?’

Bai kulata ba, ya isa gaban hadakar kayan kallon falon, ya kunna bidiyo-sidi ya fito da masakin faifan sidi, ya zura sidin da ke hannunsa, ya mayar da shi a gaggauce ya kunna akwati mai hoton, talabijin. ‘Yan sakanni hoton da ake bukata ya bayyana, wanda ya razana Alhaji Masa’udu.

Zuhra ce daddaure, hannu da kafa da baki, cikin wani mummunan yanayi da wahala, jigata da wulakanci, kuka take da hawaye mai kunci.

Hajiya Kilishi da ke tsaye ta fashe da kuka don ganin halin da ‘yarta ke ciki, shi kuwa Alhaji Masa’ud gumi ne ya fi fito masa, akwai kwalla da ta taru a idanun sa.

Hoton bai dade ba, sai gargadi da ya biyo baya da kuma dukkanin tsarin yadda za a kai musu kudin da karvar Zuhrar, sai kuma kwakkwaran jan kunne da suka yi masa.

Alhaji Masa’udu ya kalli faifan nan, vangaren ‘yarsa ya fi a kirga a dan lokacin nan.

‘Me ya kamata a yi ke nan?’ Hajiya ce da wannan batu.

Alhaji Masa’udu ya dago, ya dube ta kawai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce.

‘Kudin zan sa a kai musu, ko in kai musu su ba ni ‘ya ta.’

Suka yi shiru kafin maganar Kabir ta katse musu shirun.

‘Hakan ba zai kawo mafita ba Dadi, domin za su iya mayar da kai hanyar kasuwancinsu, idan suka karvi wannan su kara neman wani kudin fiye da wannan daga gurin ka.’

Uwa da uban suka bi Kabir da kallo, ba su san lokacin da ya iso falon ba, ba su yi magana ba har ya ci gaba.

‘Kamata ya yi a bi abin cikin hikima, ko da za a hada da ‘yansanda a yi dabara a kamasu, domin duk barazanar da suka yi, ai akwai yadda za a bi musu, suma ba za su farga da hakan ba. Sannan Dadi wannan ne batun da nake gaya maka cewar Abban Umma Maryam ba zai iya sace Zuhra ba, to ga zahiri na kokarin fito wa…’

Alhaji Masa’udu ya daka masa tsawa, ‘Ba wannan batu nake son ji ba, kai a takaice ma ba na son ganin ka yanzu a nan, kuma ba na son kara tsoma bakinka, idan har ka ki kuwa to ni da kai ne, za ka gane kurenka.’

Kabir ya yi shiru, yana sauraron mahaifinsa a zahiri yana cikin fushi, matukar fushi.

*****

Bugun kalangun da ke tashi a harabar gidan damben, shi ne abin da ke cika kunnuwan duk wanda ya shiga ciki. Dan kewayen da ake kara dambe zagaye yake da mutane rukuni-rukuni, kowanne vangare da irin rukuninsa, akwai alhazan birni da karuwansu a zazzaune, wasu akan bencina, na gaba-gaba kuwa a kan tabarmi.

Daga wani vangaren kuwa masu abu ne da nasu abin, wato zaratan samari ne tuttuve daga su sai gajerun wanduna ko dogaye, yawancinsu hannayensu daure da zare suna jiran lokaci, duk da sanin su da damben da za a fara ta manya, ran gari ce.

Akwai masu sayar da kayayyaki kamar goro da taba da alewa ko ruwan sanyi da angur da lemon zaki na leda, akwai kuma makada da ke girke a vangaren kudu na filin sai aikin bugun gangunan su suke yi.

Wani figigin maroki ya ratso filin, ya isa gurin da Samir ke tsaye, yana ta kyarma ya shiga yi masa kirari.

Yau ranar mazaje, ‘yanmata a koma da baya, a rufu cikin zani. Ina gwanin wani ga gugan karfe sha kwaramniya yau ga Samir a ranar mazaje, wasu sun ce ba su iya ba, wasu sun ja da baya, kai ka ara ka yafa, ka ji ka gani gagara gasa.’

Da yake yau ce ranar da aka shirya yin wannan gagarumin karon tsakanin Samir, Shagon Dantamalla da Horo mai Gadamurki, kuma ana ganin karon kawai za a yi a ranar, manyan alhazai sun bayyana a gurin don sanya caca da zavar gwarzo. Ita wannan ranar dama Samir ya ke jira, domin ya samu kudin da yake ganin zai nemi auren Zuhra.

Daga nasa vangaren Horo mai Gadamurki, maroka uku ne ke kiraranta shi, daman ya fi samun magoya baya, da wadanda suka zave shi, domin kowa ma ganin taurin kan Samir yake yi da tarar aradu da ka irin nashi, amma Horo ya fi karfin shi nesa ba kusa ba, hakan ne ma ya sa mutane biyu ne kawai suka zave shi suka sa kudi a kansa, suke ganin zai lashe damben. Amma mafi yawa sun san ba za a wuce turmi daya zuwa biyu ba Horo zai gama da lamuran Samir kowa ya huta.

Horon dai horo ne, mai mummunar kama, dakakken kato ne narke guri guda, mai fuska abar tsoro da kwarjini.

Mai gabatarwa, kuma alkalin damben ya fara gabatarwa da baiwa masu dambe izinin shigowa fagen karawa, domin fara dauki ba dadi.

Horo mai Gadamurki ya shiga cikin kasaita. Wuri kam ya rude, yayin da shi ma dai Samir ya shiga filin karon.

Daga shigar su alkali ya bayar da dama aka fara gabzawa, idanu a rufe, maza kan maza, ‘yan kallo suka shiga sowa, makada na aikin kida, maroka na kirari, mazaje a bayan fili na tsuma da karkarwa.

A ka fara turmi na farko, inda shi Horo yana yi ne cikin gwaninta, yana so ya yiwa Samir kisan burgewa, kisan mummuke, kisan da nan gaba ba zai kuma marmarin taren ire-iren sa ba, yayin da shi kuma Samir ya ke nasa kokarin na dalilin dambatawar tasa.

A wannan turmi Horo mai Gadamurki ne ya yi nasarar yi wa Samir mahangurva guda uku, daman ai da ganin kura an san ta ci mutum, aka tafi hutun zagaye na farko, kafin a je ga turmi na biyu.

Wasa-wasa sai ga Samir ya yi taurin rai an je turmi na hudu, Horo bai kashe shi ba, wanda a lokacin wasu daga cikin ‘yan kallo sun fara sowa suna komawa goyon bayansa, suna masa tafi.

Wannan abu sai ya baiwa Horo haushi, ya yi fushi, ya fusata, ya kuma kullace wa ransa ba za a fita daga wannan turmi ba ba tare da ya lashe Samir ba, ai kuwa nan ya rinka kirvar sa, yana yi masa mahangurva da tagwan nausa, kafin wani lokaci Samir ya fara ganin taurari faffaru da jajaye.

Guri ya yi shiru ba ka jin motsi ga kowa face na mutanen Horo, yanzu jira kawai ake yi a ga irin kisan da zai yiwa Samir.

A wannan lokacin, Allah ya yankewa su Umma Maryam, Alhaji Yusuf, Kabir da Samira wahalarsu ta neman Samir, domin an ba su tabbacin ga inda yake wato gidan dambe, kuma sun karaso a lokacin kai tsaye suka shiga gurin, bayan sun biya kudin shiga. Zuwansu daidai gurin ya zo daidai da wani naushi da Horo ya yiwa Samir, ya tafi da baya taga-taga zai fadi, idanunsa da suka kusa rufewa, suka gane masa iyayensa da kanwarsa kamar a mafarki. Mutanen gurin kansu sun yi mamaki da rashin faduwarsa, da yadda yake a tsaye.

Can kamar an tsikare shi, bayan wani dan tunani da ya yi kawai sai gani aka yi ya zabura zuwa ga inda Horo mai mahangurva yake. Ya shiga nausar sa ba kakkautawa, anan a inda Horo yake tsaye mutane sun dauka juriya ce da bajinta irin ta gwanaye, gwarzaye, kawai sai gani suka yi ya fadi ruf-da-ciki rikica.

Ai kuwa guri ya kaure da sowa da tafi, da murna ga masoyan Samir domin nasarar da ya samu ta kisan Horo. Shi ma can gefe ya koma jikin bishiya ya zauna a galavaice, yana kallon inda mahaifinsa ke tsaye.

Umma Maryam da Samira kuka suke yi. Gaba dayansu suka dunguma gareshi, suka isa tare da kewaye shi, babu wanda ya iya magana a cikin su, sai shi Samir din.

‘Umma ina Zuhra….? Umma ya dokeni a kirji….cikina yana min zafi ku taimaka min da magani…’ Duhu-duhu ya ke gani a idanunsa, ba wanda ya ke gani sai mahaifiyarsa, sai kuma hoton Zuhra.

‘Mu yi saurin kai shi asibiti a dubashi, don yana bukatar hakan.’ Kabir ya fada.

Ba su yi musu ba. Kabir din da Alhaji Yusuf suka dauke shi zuwa waje, inda suka ajiye motar Kabir, suna kokarin sanya shi a motar ne abokin Samir din ya kawo musu kudin da ya lashe a damben. Ba su karva ba, sai da kyar Samira ta karva, bayan da ya takura mata.

Suka ja motar, suka tafi. Ba don zuwan su ba da sai dai ko mutuwa zai yi ya mutu a filin damben nan, amma babu wanda zai yi kokarin kai shi asibiti.

Asibitin Nassarawa suka kai shi na gwamnatin jihar Kano. Cikin sa’a Kabir ya hadu da wani abokinsa wanda dalilin haka ya sa suka duba shi da wuri. Tsawon mintuna hamsin da shida, likitan mai suna Jamil ya fito, ya sami su Alhaji Yusuf wadanda suke jiran tsammani. Ya dubi Kabir.

‘Wannan bawan Allah yana cikin mummunan hali. Ba wai bugun da aka yi masa bane babbar matsala ba, yana cikin matukar halin tunani da soyayyar wata yarinya da yake ta ambatar sunanta….’

Samira ta yi saurin cewa ‘Zuhra!’ Dakta Jamil ya gyada kai, ‘Kwarai ita. To amma yanzu cikin ikon Allah mun shawo kan matsalar, mun yi masa allura da duk kulawar da ta kamata. Don haka ku kwantar da hankulanku gami da yin hakuri nan da ‘yan awoyi biyu za ku gan shi ya warware.’ Suka yi gaba da Kabir suna tattaunawa, yana tambayarsa abin da ya kamata su yi.

<< Launin So 7Launin So 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×