Shiru tayi bata tanka ba. A madadin ta tanka ma sai ta ƙara ƙarfin kukanta, daga sharɓen hawaye zuwa shessheƙa. Zuciyarta cunkushe da wani irin baƙin ciki da ɓacin rai mai tsanani.
‘Ta ina za ta iya fita da cikin shege a jikinta? Ta ina za ta fara kallon idanun jama’ar unguwarsu da suke mata kallon nutsattsiyar yarinya a baya, a yanzu kuma duk suna da labarin abinda ta aikata? Baza ta iya ba, baza ta taɓa iyawa ba.
A yadda take jin ƙuna da raɗaɗi a cikin ranta ji take ina ma Allah ya ɗauki rayuwarta a daidai wannan lokaci. Gara ta mutu ta huta da wannan mummunan abun baƙin ciki da ya same ta. Da gaskiyar Mal bahaushe da ya ce duk abinda namiji yayi ado ne, su biyu suka aikata zunubin, a taƙaice ma laifinta bai fi kaso sha biyar cikin ɗari ba. Saboda komai ya faru ne ba da son ranta ba, a bisa tilastawa ne da kuma tsoron rasa abin son zuciyarta. Saboda ya tabbatar mata matuƙar bata amince ba to babu shi babu ita har abada, da wannan barazanar ta amince da shi tana rusa kuka. Amma ga shi a yanzu Lokaci yayi da ita kaɗai take sharɓan romon azaba da baƙin cikin da ke tattare da wannan saɓo da suka aikata su biyu.
Ga babban damuwarta rashin mahaifiyarta da ƴan’uwanta, ko a wane hali suke ciki? Ko suna tunanin ita a wane hali take ciki? Ko suna tausaya ma halin da take ciki? Suna ƙaunarta ko sanadiyyar abinda ta aikata ya sa sun daina son ta da ƙaunarta? Ummanmu ko za ta iya yafe mata? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…’
Da zuwa nan a tunaninta jin zuciyarta na neman tarwatsewa sai ta ɗora hannu biyu a kanta ta fashe da wani irin ƙaƙƙarfan kuka mai tafe da ihu, duk a ƙoƙarinta na a fahimci irin halin da take ciki a tausaya mata.
“Ikon Allah”
Ummee ta faɗa da mamakin Ziyada fal a fuskarta, hannunta dafe da haɓa. Wani ɗan tunani da tayi kuma yasa ta zauna a gefen gadon da Ziyadar take zaune. Da taushin murya ta fara rarrashinta da tausasan kalamai bayan ta sauke mata hannun da ta ɗora akai, zuciyarta cike da tausayin yarinyar.
“Haba mana Ziyada. Don Allah ki kwantar da hankalinki. Ki saurara da wannan kukan ki share hawayenki kar Alhaji ko Yayanku su shigo suyi tsammanin wani abu aka yi miki. Ba dai asibiti bane bakya son zuwa?”
Da saurin gaske ta ɗaga kai, alamar eh!
“To zancen asibiti an barta daga yau. Ko Alhaji ya sake magana zan san abinda zan faɗa mishi mu kore maganar zuwanki asibiti. Shi kenan?”
Nan ma kai ta sake ɗagawa. A hankali take rage ƙarfin kukan, har ta samu nasarar tsayar da kukan gaba ɗaya. Tana ji kaso arba’in da biyar na damuwarta ta ragu. Sai murza idanu take yi, ita dai Hajiya Hauwa tana zaune tana kallonta, har ta gama goge idanun gaba ɗaya.
“Kin ga kukan da kika yi har ya sa idanunki sun kumbura, ga su sunyi jajaye. Ki rage saurin kuka kin ji ko? Nan gaba kaɗan uwa za ki zama, ba ko wane abu bane za ki buɗe mishi baki kina kuka. Abinda nake so ki dinga tunawa shi ne rayuwarmu ba’a hannunmu yake ba. Duk abinda ya faru da mu yana daga cikin ƙaddarar da aka rubuta mana tun kafin a haife mu, cikakken imani kuwa yana tabbatuwa ne idan bawa yayi haƙuri, ya jure, ya rungumi ƙaddarar da za ta afko mishi mai kyau da mare kyau. Kin gane ko?”
Kamar wacce aka ɗinke ma baki. A yanzu ma bata iya cewa komai ba sai ɗaga kai da tayi, alamar ta gane.
“Yauwa ƴar albarka. To yanzu faɗa min, me kike son ci yau da yamma? Ki faɗi duk abinda kike so in dafa miki, komai wahalarsa ni kuma in sha Allah zan samar miki abinda ranki ke so. Faɗa min kin ji yarinyata? Ni yanzu fa ke ce Autata, Khamis tuni na yar da shi can a bola. Faɗa min kin ji Autalli Ziyada?”
Yatsun hannayenta take ta mammatsawa, duk da kalaman rarrashi da nasihar Ummee sun samu matsuguni a cikin zuciyarta ta kasa sakin ranta. Can bayan wasu daƙiƙu ta buɗe baki daƙyar ta ce
“Dambu.”
Sosai Ummee ta ƙara yi mata nasiha da kalamai na kwantar da hankali kafin ta fice daga ɗakin. Izuwa yanzu Allah ya sani tausayi ƙwarai Ziyadan take ba ta. Yarinya ba wata babba ba amma ta bi layin shaiɗaniyar soyayya, a ƙarshe bata tashi da komai ba sai ƙatoton sifili.
Yo ƙaton sifili mana, ko da nan gaba an ɗaura musu aure da Khamis Tarihin baƙin tabon da suka yi ma rayuwarsu bazai taɓa gogewa ba. Duk tsawon zamani da saurin gudu irin na LOKACI dole a cikin jama’a sai an samu masu bayar da wannan shuɗaɗɗen mummunan tarihi. Haka rayuwa take, LOKACI mai zuwa da baƙin al’amura. Shi kuwa tarihi ba shi tausayi komai kayi za’a bayar da labari walau na kirki ko akasin haka. Masu jini a jika ne suke ji kamar babu wanda ya kaisu Izzah, shi yasa suke cin karensu babu babbaka ba tare da tunanin yau da gobe za’a maimaita tarihi ba.
Da zuwa nan a tunaninta bata san sa’adda idanunta suka cicciko da ƙwallah ba, karo na farko a rayuwarta da ta yardar ma kanta lallai fa da sakacinsu a taɓarɓarewar tarbiyar Khamis. Amma daga wannan lokacin in Allah ya yarda za su gyara, sun sha alwashin gyara daga duka ɓangarorin biyu, za suyi ƙwaƙƙwaran tauna ga tsakuwa don aya ta shiga taitayinta.
Da wannan dalilin yasa suka nesanta Khamis da gidan gaba ɗaya, makaranta aka mayar da shi, can garin kanon dabo. Kuma kasancewar Pc na makarantar Aminin Abba ne sai aka saka matakan tsaro da tsanani sosai akan shige da ficen Khamis ɗin. Ko hutu aka yi gidan Pc yake hutu shi da sauran ƴaƴanshi guda biyu maza.
Hankalin Khamis ɗin a tashe yake. Sosai yake cikin takura da wannan tsanani da ake mishi. Amma idan ya tuna Ziyada tana can gidansu ƙarƙashin kulawar iyayensa, da gudan jininsa a jikinta, lokaci kaɗan ya rage ta zama mallakinsa, sai yaji kaso sittin cikin ɗari na damuwarsa ta yaye. Da gaske yake son Ziyada, duk wasu matakai na wahala ko na jin daɗi ko a mugun mafarki ba ya fatan ya rabu da ita. Shi yasa ya shirya matakai daki-daki na hanyoyin da zai bi don cimma ƙudurinsa na aurenta. Alwashi na ƙarshe da yasha ɗauka akan soyayyarsu shi ne
“Ko an raba su da ƙarfi da yaji, an ɗaura mata aure da wani, tabbas duk inda ta shige sai ya lalubo ta ya gudu da ita.”
Sai ga shi tun kafin akai wancan matakin ya fara jiyo ƙamshin zamowarta mallakinsa. Baza ace ɗari bisa ɗari ya mayar da hankali a karatu ba, sittin da biyar bisa ɗari na hankalinsa a dole ya mayar kan karatun ne, tun da ba shi da wani abin yi bayan wannan karatun. Kuma iyayensa sun rantse masa da girman Allah matuƙar bai mayar da hankali ya fita da sakamako na azo a gani ba, in zai shafe shekaru goma yana maimaita aji sai ya maimaita.
Wannan rantsuwa da suka shata kuma yaga tabbacin da gaske suke a fuskokinsu shi ya karya duk wani kuzari da karsashinshi. Ya mayar da hankali don samun kwalin da zai bashi lasisin komawa gida, a aura mishi masoyiyarsa, sa’annan ya cigaba da tsula tsiyatakunsa yadda yake so.
Zancen zuwa asibiti dai dole aka barshi, duk sun fahimci damuwar yarinyar. Amma saboda gudun yin kitso da ƙwarƙwata Hajiya Hauwa dole ta lalubo wata ƙwararriyar Nurse a asibitin Nursing home tana zuwa har gida ta auna Ziyada, ta duba lafiyarta da na abinda ke cikinta.
A haka rayuwar ke tuƙawa da daɗi babu daɗi ana tafiya cikin godiya da ni’imomin Ubangiji har zuwa sadda cikin Ziyada yakai watanni tara. Ba’a taɓa yin hoton cikin ba, amma daga yadda cikin yayi wani irin girma har yana neman rinjayarta shi ne abinda yake ɗaga hankalin Ummee, Abba, Ya Yusuf. Sun tanadi duk abinda za’a buƙata na jarirai biyu, saboda Nurse ta tabbatar musu abin cikin ba ɗaya bane, amma tunda ba’a yi hoto ba baza ta iya cewa ga jinsin jariran ba.
Duk kulawa da tarairayar da Ziyada ke samu hankalinta a tashe yake. Ta rame, ta zabge sai tsinin ciki a gaba. Kullum sai tayi kuka idan ta kalli wannan zungureren cikin ta tuna ba na halali bane. Ga fargaba da tsoro danƙare da zuciyarta na tunanin za ta haihu lafiya ko baza ta haihu lafiya ba? Ga tunanin Ummanmu da kullum sai tayi mafarkinta. Har ƙasa ta duƙa ta roƙi alfarmar Abba yaje ya nemo mata yafiya gurin Ummanmu ko za ta samu sassauci a rayuwarta amma sam Ummanmu ta ƙi saurarensa. Haka ya fito daga gidan jikinsa a sanyaye, gwuiyawunsa a saɓule, zuciyarsa cike taf da matsanancin tausayin Ziyada. Haka ya koma gidan ba tare da wata ƙwaƙƙwaran magana ba.
Daga yadda Ziyada ta ganshi ya shigo falo tasan ba bayani, bata saurari abinda zai ce mata ba don ta san bai wuce nasiha ba da a kullum rana ta Allah tunda cikin ya tsufa sai sunyi mata. Tana tangaɗi ta shige ɗakin da take zaune ta saka kuka.
Zuciyarta cike da tsoro da fargaban kar mutuwa ta ɗauke ta gurin haihuwa ba tare da ta nemi afuwar wacce tayi silar zuwanta duniya ba. Me za ta cewa Allah idan ta mutu a irin wannan halin?
“Ya Rabb! Ya Rabb!! Ya Rabbi ka dubi baiwarka ka kawo min ɗauki. Astagfirullah, wa’atubu ilaik, astagfirullah, wa’atubu ilaik”
Kalaman da take ta maimaitawa kenan cikin kuka da damuwa mai tsanani danƙare a zuciyarta.
*****
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.. Mun shiga uku.! Ziyada? kinyi hauka ne? Ki gyara mana kar ki halaka kanki ki halaka abinda ke cikinki…”
Ummee ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali tana sake riƙe ƙafar Ziyada na hagu da ƙarfin gaske.
Acan ɓangaren Nurse Halima itama riƙe take da ƙafar Ziyada na dama.
Suna ja a ƙoƙarinsu na buɗe ƙafafunta don ba abinda ke cikinta damar samun hanyar fitowa.
Gaba ɗaya su ukun sun haɗa zufa sunyi kashirɓin. Tun ɗazu suke abu ɗaya, sai kan ɗa ya taho zai fito kawai sai Ziyada ta haɗe ƙafafunta cikin magagin azaba, tun suna rarrashinta a dole suka saka mata ƙarfi, hankalinsu a tashe, zukatansu cike da tsoron abinda zai iya faruwa.
A wahalce Ziyada ta ɗago idanu daƙyar ta zuba kan Ummee, laɓɓan bakinta sai rawa suke yi saboda wahala da raɗaɗin ciwon naƙuda.
“Um…mee…”
Ta kira ta daƙyar, da wani irin shessheƙa a muryarta kamar wacce tayi tseren gudu.
“Ummanmu… ku roƙe ta… ta yafe.. min.. idan ba haka ba… Bazan iya… da kaina.. ba…”
Ta faɗi maganganun a rarrabe kamar mai koyon magana. Lokaci ɗaya azababben ciwo ya sake turnuƙeta, sai ta fara jan numfashi mai ƙarfi a fis-fisge, cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka juye, wani irin miyau mai yauƙi da kauri ya fara fita daga bakinta.
A tsorace Ummee ta saki ƙafarta, ta fara matsawa tana ja da baya, idanunta a warwaje. Bayyanannen tashin hankali ƙarara kan fuskarta, kamar wacce a tura sai ta fice daga ɗakin a guje, ta wuce su Abba da Yusuf da ke tsaye hankulansu tashe ta fice daga falon. Ko kafin su cimmata da tambayar lafiya har ta buɗe ƙofar gidan ta fice ba tare da ta duba tsalawar da dare ya fara yi ba. A lokacin ƙarfe sha biyu da rabi na dare.
A daidai wannan lokacin, tana zaune akan darduma. Ta kasa barci sam, tun bayan faruwar al’amarin kusan kullum yini take da tunanin Auta, amma tunanin yau ya fi na kullum. Ga wani irin faɗuwar gaba da take fama da shi tun daga magrib.
Ko da ta sanya haƙarƙarinta akan gado da nufin yin barci a takaice wani gajeren barci ya ɗauke ta mai cike da mugun mafarki. Ziyada ta gani tana rusa kuka, an ɗaga ta sama a daidai wani ƙaton rami da ke ci da wuta gagga gagga. Hannaye biyu take miƙo mata tana ihu da magiyar ta yafe mata, yafiyarta ne kaɗai zai cire ta daga cikin wannan ƙangi na azaba, idan bata yafe mata ba faɗawa cikin wutar za tayi.
Fuskarta a ɗaure sosai take kallon Ziyada. Har ta juya za ta wuce ko da ta waiwaya baya sai taga ashe wutar har ya fara laso ƙafafun Ziyadar, a daidai lokacin ta farka a firgice. Ta haɗa zufa tayi kashirɓin, addu’ar neman tsari daga mugun ji da mugun gani tayi sannan ta sauka zuwa banɗaki domin ta ɗauro alwala. A daidai wannan lokacin aka fara bugun ƙofar gidan a haukace.
Da fari tsai tayi da hankalinta guri ɗaya da tunanin gidan ake bugawa ko ba nan bane? Ko da ta tabbatar sai ta mayar da hankalinta kan agogo, ganin lokaci yasa tayi shiru tana tunanin wa ke buga mata gida a wannan lokacin?
Tana isa falo ta ci karo da su Rukayya sun fito daga ɗakinsu, hankalinsu a tashe, jikinsu sai rawa yake yi suna riƙe da hannun juna. Duk a tsammaninsu ɓarayi ne suka kawo musu farmaki. Kallo ɗaya Ummanmu tayi musu ta nufi ƙofar fita daga falon za ta buɗe, da sauri suka riƙo hannayenta.
“Ummanmu, don Allah kar ki fita. Idan ɓarayi ne suka kawo mana farmaki fa? Ba ma so wani abu ya same ki.”
Kareematu tayi maganar a raunane, idanunta ciccike da hawaye.
“Ku kwantar da hankalinku. Ba buɗewa zanyi ba. Leƙawa zanyi in ga suwa ke ƙwanƙwasa ƙofar. Ba ɓarayi bane in Allah ya yarda.”
Duk da ta faɗa musu haka hankalinsu bai kwanta ba, suna riƙe da ita suka taka a hankali cikin sanɗa zuwa gurin ƙyauren gidan. Kasancewar akwai wutar lantarki ko ina a unguwar, ko da ta leƙa ta wata ƙaramar kafa da ke jikin ƙofar sai ta ga Hajiya Hauwa, tana tsaye tana buga kofar gidan cikin tashin hankali, fuskarta kaca-kaca da hawaye. Ga Yusuf da Alhaji Abubakar tsaye a kusa da ita, a fuskokinsu kawai za’a karanci damuwa ƙarara.
Wani irin faɗuwa gabanta yayi, da saurin gaske ta ƙwace hannayenta daga cikin na ƴaƴan ta zare sakatar ƙofar gidan ta buɗe. Bakinta ɗauke da duk wata irin addu’a da ta zo mata a kusa. Ko kafin ta tambayi lafiya Hajiya Hauwa ta zube a ƙasa gabanta, gwuiwa bibiyu.
Ta haɗe hannayenta guri ɗaya alamar roƙo, tana kallon Ummanmu da wani irin maɗaukakin tashin hankali a fuska da muryarta ta ce
“Ba don mu ba, don darajar Sarkin da ya halicci duniya da abinda ke cikinta… Ba don laifin da Khamis ya aikata ba don ƙaunarki ga Fiyayyen Halitta SAW… Ba don Ziyada da ta kasance mai laifi a gare ki ba don darajar Alƙur’ani mai girma nake roƙon ki yafe mata. A halin da take ciki yanzu, tana cikin tsaka mai wuya, wani irin hali na tsakanin mutuwa da rayuwa, babu abinda ta fi tsananin buƙata a yanzu irin yafiyarki, ko Allah zai dube ta ya sauƙaƙa mata halin da take ciki… Akan gwuiwa take, tun magriba take abu ɗaya, sai haihuwa ta taho da ƙarfi sai komai ya tsaya cak, a yanzu haka na baro ta ne tana cikin hali na tsinkau… tsinkau…”
Ta ƙarasa maganar haɗe da fashewa da wani irin ƙaƙƙarfan kuka mai bayyana tsoro da raunin da zuciyarta yayi.