Skip to content
Part 13 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Ya tafi da sauri da niyyar zubewa a ƙasa gabanta ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu.

“Zauna kan kujera, kar ka zauna a ƙasa.”
Ta faɗa a dake, kamar bata fahimci abinda yake niyyar yi ba.Jikinsa a sanyaye ya nemi guri kan kujera ya zauna, zuciyarsa cunkushe da tunani da saƙe-saƙe. Iyayensa sun tabbatar masa Ummanmu ta yafe masa, amma daga irin kallon da take masa na yanzu babu abinda ya canza daga na baya. Kallo mai bayyana tsana ƙarara, mai ɗauke da saƙon jin haushi da tarayya dashi a dolen-dole domin an rasa yadda za’ayi da shi.

“Khamis barka da dawowa. Ya makaranta? Ina fatan an kammala lafiya?”

Ta katse mishi tunani da waɗannan tambayoyin.Ɗan muskutawa yayi ya gyara zama, ya ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa. Daƙyar ya buɗe baki ya amsa da,

“Lafiya ƙalau Alhamdulillahi Ummanmu. Da fatan mun same ku lafiya?”

“Lafiya ƙalau.” Shammatarta yayi ya zube ƙasa kamar yadda yayi niyya tun da farko.

“Ummanmu, na sani laifukana masu yawa ne a gare ki. Duk da na samu kyakkyawan labarin kin furta kalmar yafiya a kan laifukan da nayi miki. Amma zuciyata ta kasa nutsuwa, zan so ji da kunne na cewar kin yafe min, don girman Allah ba don halina ba ki yafe min…”

“Me yasa kake tantama kan yafiyar da na ce nayi maka a baya?”

Ta jefa mishi tambayar bayan ta tsattsare shi da idanu.

“Laifukana masu yawa ne. Furta kalmar yafiya a lokaci ɗaya abu ne da ban taɓa tsammanin samu anan kusa ba. Don darajar Fiyayyen halitta SAW…” “Na yafe maka Khamis. Da gaske nake na yafe maka, don Allah da Manzonsa SAW. Amma kuma ina so ka sani, tarayya da kai tun a karon fari abu ne da ko kaɗan bai kwanta min a zuciya ba, wataƙila dai zuwa can gaba, idan ka baibaiye ni da kyawawan halayenka da ni sam ban hange su ba. Ka riƙe Ziyada irin nagartaccen riƙon da sam ban hangi za ta samu a tattare da kai ba, tabbas idan abubuwa biyunnan suka faru zan ƙaunaceka Khamis, zanyi alfaharin kasancewarka suriki a gare ni. Amma a yanzu, ina mai baka haƙurin jure ko wani kalar kallo daga gare ni.”

“Na gode Ummanmu. Na gode ƙwarai. Jin kalmar yafiya daga bakinki ba ƙaramin faranta mini rai yayi ba. Kuma in sha Allahu zan ba maraɗa kunya, cikin ƙanƙanin lokaci da yaddar Allah zan share duk wani tantama daga zuciyarki. A daure a saka mana albarka…”

“Allah yayi muku albarka.”

Ta faɗa tun kafin ya ƙarasa faɗin abinda yayi niyya. Duk da jin kalaman da suka fito a bakinsa sun ɗan samar mata da nutsuwa har lokacin bata saki fuskarta ba, ba yabo ba fallasa.

Umarni ta sake yi mishi kan ya koma kan kujera ya zauna. Amma sai ya gyara zama a ƙasa ya bata haƙuri, ya tabbatar mata nan ɗin ya fi masa. Taɓe baki tayi ta kawar da kallonta daga gare shi. Ta ɗaga waya ta kira lambar ƙanwarta ta bada umarnin a shigo da Ziyada. Mintuna uku tsakani aka shigo da Ziyada cikin falon, wani irin tattausan ƙamshi da take bazawa duk yadda Khamis yaso riƙe kanshi ya kasa, sai da ya ɗaga idanu a bayyane ya bita da kallo.

‘Tsarki ya tabbata a gareka ya mahaliccin wannan kyakkyawar yarinya.’

Ya faɗa a zuciyarsa. Lumshe idanu yayi ya buɗe hanci sosai ya shaƙi daddaɗan ƙamshin da jikinta ke fitarwa a daidai lokacin da aka zaunar da ita kusa da shi.

Duk da abubuwan da suka faru a baya. Ba tare da kunya ko tunanin me mutane za su ce ba, gaggarumin taron biki Ummanmu ta haɗa bayan an sanya ranar tarewar Ziyada a gidan Khamis. Iyayensa sun ba maraɗa kunya, duk wasu abubuwa da ake yi na al’ada ba suyi ƙasa a gwuiwa ba wajen gabatarwa. Kayan lefe masu tsananin kyau da tsada suka haɗa mata na gani a faɗa. Bayan fargaba da tsoron da ya cika zuciyar Khamis ya hana shi yin ido biyu da Ummanmu tun bayan dawowarsa, yau ita da kanta ta ce ma Ummee ta tura mata shi. Ba don komai ba sai don ta damƙa mishi amanar Ziyada.

Ko da Aunty Lami ta zaunar da Ziyada kusa da Khamis ficewa tayi daga falon. Duk su biyun kansu na ƙasa, babu abinda ke tashi a falon sai shessheƙan kukan Ziyada da yake fita a hankali.

“Ziyada? kukan me kike yi?”

Ummanmu ta tambayeta, da ɗan taƙaitaccen murmushi a fuskarta. Kallon ƴar tata take yi, a zuciyarta take yaba yadda tayi kyau sosai a cikin leshin da aka yi mata ɗinkin doguwar riga. Rigar ta zauna a jikinta cif-cif, kamar ba ɗinkin telolinmu na gida ba. Ɗan yalolon mayafi kalar leshin jikinta aka rufa mata a kanta. Sassauƙar kwalliya aka yi ma farar fuskarta da aka shafe sati biyu ana goge ta da kayayyakin gyaran jiki, kwalliyar sai ya ƙara fitar da ƙuruciyarta a fili. Babu mai kallonta a ce ta taɓa ɗaukar ciki balle haihuwa, balle kuma har ayi tunanin shayarwa take yi a wannan lokacin.

“Ummanmu, ina sake neman afuwarki, don Allah, ki yafe min.” Ziyada tayi maganar cikin shessheƙar kuka, gwanin ban tausayi.

A dabarance Khamis da yake jin kukanta na sauka a zuciyarsa kamar ana zuba mishi tafasasshen ruwa ya miƙa hannunsa ya lalubo nata guda ɗaya ya riƙe. Ya fara matsawa a hankali alamar rarrashi. Duk abinda yake yi kan idanun Ummanmu. Girgiza kai tayi, ta ɗan cije gefen baki ta ƙara faɗaɗa murmushinta.

“Na yafe miki tuntuni Ziyada. Na faɗa a bayan idanunki, a gaban idanunki ma na maimaita ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Daga yau na soke neman yafiya akan wannan al’amarin da ya daɗe da shuɗewa, ina fatan kun fahimce ni?

A tare suka ɗaga kai, alamar sun fahimta.

“Madallah! Khamis ga Ziyada. Ziyada ga Khamis. A yanzu kun wuce ƙaramin mataki irinna saurayi da budurwa, kun taka babban matsayi ne na ma’aurata. Ni kam ba ni da wata doguwar nasiha da zan yi muku a wannan lokaci.

Abu ɗaya da zan tunasar da ku shi ne, ku kuka ga junanku kuka ce kuna so, kuka bi duk wasu matakai da hanyoyi da kuke so har Allah ya tabbatar da aure a tsakaninku. Don haka kuyi haƙuri da junanku, da daɗi babu daɗi ku gudu tare ku tsira tare. Rayuwar auren gaba ɗaya haƙuri ce, yi ma juna uzuri, da kuma kawar da kai kan ƙananun abubuwan da basu taka kara sun karya ba. Ziyada, ki riƙe mijinki da hannu bibiyu, daga ranar da aka ɗaura muku aure ya fi kowa matsayi a gurinki, idan na ce kowa ina nufin har ni, don haka, in dai ba kalmar saki ce ta ratsa a tsakaninku ba don Allah kar ki kuskura ki nufo ni da wata matsala dangane da rayuwar gidan aurenki.”

Da sauri idanu warwaje fuska kaca-kaca da hawaye Ziyada ta ɗaga idanu tana kallon Ummanmu. “Ƙwarai kuwa.”

Ummanmu ta tabbatar mata.

“Duk maganar da kika ji na faɗa miki iya zallar gaskiyar magana kenan Ziyada. Ga Hajiya Hauwa nan, ki riƙe ta a matsayin uwa ba uwar miji ba, ina da kyakkyawan zato na za su share miki hawaye fiye da yadda ni zan share miki. Ina muku fatan alkhairi, Allah yayi muku albarka ya kawar da duk wani ƙalubale da tashin-tashina da za ku fuskanta a zamantakewarku.”

“Ameen ya Allah” Khamis ya amsa a fili. Ita kuma Ziyada ta amsa a zuciya. Hankalinta a tashe da jin irin kalaman da suka fito daga bakin Ummammu.

Alƙur’ani mai girma izufi sittin Ummanmu ta ɗauka a gefenta, ta miƙe a nutse ta ƙarasa inda suke zaune ta damƙa ma Ziyada a hannunta. “Ki riƙe da hannu bibiyu, aduk sa’adda wani abu ya taso ki gaba ki nemi waraka daga cikinsa. Allah ya bada zaman lafiya.”

Anan ma dai Khamis ɗin ne ya amsa, ita kuwa Ziyada sai ƙara ƙarfin kukanta tayi. Ummanmu ta juya za ta koma mazauninta da sauri ta riƙe ƙafafun uwar tana rusa kuka. A bazata wasu hawaye suka cicciko mata idanu, da sauri ta mayar da su, ta haɗiye wani kakkauran miyau da yai mata karan tsaye a maƙoshi saboda damuwa da damuwar Autarta. Juyawa tayi a hankali tasa hannu ta ɗaga Ziyadar tsaye, sannan ta rungumeta, bayanta take bugawa a hankali alamar rarrashi. A hankali ƙarfin kukan nata ke raguwa har ta koma sauke ajiyar zuciya.

Shigowar Aunty Lami karo na biyu da tunasar da su lokaci ya tafi yasa aka ɓamɓare Ziyada daga jikin Ummanmu ba don duk su biyun ransu yana so ba. A wannan daren za’a kai amarya gidan mijinta, kuma ba’a cikin unguwar bane. Can sabon kawo Alhaji Abubakar ya sai ma Khamis wani ɗan madaidaicin gida mai ban sha’awa. Duk yadda Ummee tai ta surutun me yasa baza’a nemi gida nan kusa da su ko zagayen cikin unguwar rimi a saya mishi ba kunnen uwar shegu yayi da ita. Sai da cinikin gida ya kammala sannan ya zaunar da ita ya karanta mata dalilinsa na nesanta Khamis da unguwar.

“Rayuwar Nauwara nake dubawa, duk da samuwarta ya zo ne a bisa ƙaddara ba kowa ne zai dubi haka ba. Ke kin san halin mutanenmu, abun alkhairi ne ake iya mantawa da shi har abada, na sharri duk tsawon zamani lokaci bayan lokaci za’a dinga taso da zancen shuɗaɗɗen al’amarin. Ki dubi yanayin yarinyar mana, nan gaba kaɗan za’a yaye ta, azo batun saka ta a makarantar boko da islamiya. A yanzu wani zamani ne muke ciki da duk munin al’amari iyaye basa kunyar magana a gaban ƴaƴansu, cuɗanyar Nauwara da yaran da suka san asalinta zai sa a dinga goranta mata.

A ganina duk da zancen duniya ba ya ɓuya, nesantata da unguwarnan zai sauƙaƙa matsi da gorin da za ta iya fuskanta daga gurin yara ƴan’uwanta da manyan da basa iya gani suyi shiru. Ki bari ya gina rayuwarshi acan inda bai san kowa ba shi ma ba’a sanshi ba. Mu taya su da addu’ar Allah ya kaɗe fitina ya basu zaman lafiya.” “Ameen.”

Ta amsa jikinta a sanyaye. Ta gamsu da bayananshi ɗari bisa ɗari, lokaci ɗaya burinta na riƙe Nauwara a gurinta daga yaye nan take yabi ruwa. Kamar ƙaramar yarinya sai ta fara matsar ƙwallah, zuciyarta cike da damuwar mummunar ƙaddarar da kaso tamanin cikin ɗari na faruwarta ya afka ne kan tsarkakakkiyar ruhin da bata san hawa ba balle sauka.*****Shekara kwana, haka zalika yau da gobe bata bar komai ba. Kwanci tashi ba wuya a gurin Ubangiji. Kamar jiya ne Ziyada da Khamis da ƴar jaririyarsu suka tare a sabon gidansu. Zama ne suke yi na farin ciki da ƙaunar juna, soyayya da yarda haɗe da tausayi sun samu gurin zama sosai a zamantakewarsu.

Sam-sam karatu ba shi a tsarin Khamis, duk yadda Abba yaso ya cigaba da karatu ya ƙi. Don haka da takardunsa na sakandire aka yi amfani wajen samar masa aiki a hukumar Alhazai. Da albashin da yake samu duk wata da kuma ɗan ihsanin da iyayen da Yayanshi Yusuf ke mishi suke tafiyar da rayuwarsu cikin wadata na rufin asiri.

Nauwara na da shekara ɗaya da wata uku aka cire ta a bakin nono, a lokacin Ziyada na ɗauke da cikin wata uku, su kansu iyayen basu sani ba sai zuwan Ummee gidan ta faɗa a gaban Khamis. Wannan dalilin yasa Ummee bata bar gidan ba sai da Nauwara da kayanta, sanadin ɗauke ta a bakin nono kenan. Duniya ba gidan zama ba, idan ajali yayi kira ko da ciwo ko babu dole a amsa kiran Ubangijin sammai da ƙassai. A wata ranar litinin da magrib Abba ya shiga cikin ɗaki da nufin cire babbar rigar jikinshi, ba tare da sanin dalili ba sai salatinshi Ummee ta jiyo da ƙarfi, ko da ta shiga a guje don ganin abinda yake faruwa ganinshi tayi kwance a ƙasa yana gwaranci, a lokacin har an karya mishi harshe.

Hankali tashe ta ɗaga waya ta kira Yusuf, ashe ba nisa yayi ba. Yana daf da shigowa cikin gidan. Tun kafin ya shigo ya ɗaga waya ya kira Dr. Nura ya sanar da shi halin da ake ciki. Yana shiga ya tarar da Ummee ta tasa Abba a gaba tana rusa kuka gwanin ban tausayi, hannayenta na riƙe a cikin nashi. Idanunshi buɗe tar a kanta, Gwarancin magana yake yi sam ba ta jin abinda yake cewa.

Yana ganin Yusuf ya sake hannun Ummee ya damƙo shi yana wani irin maganganun da shi ma sam ba ya fahimtar abinda yake cewa. Suna a haka likita ya shigo gidan, daƙyar da jiɓin goshi suka samu nasarar ɗaga shi daga ƙasa zuwa kan gado, wani irin nauyi jikin Abba yayi kamar ba shi ba. Kamar jiran su mayar da shi gado ake yi, nan take jikin ya ƙara rikicewa, gwarancin ya cigaba da yi wanda bayan sun saurara sosai sun ji dai ya faɗi sunan Khamis, sai kuma suka ji ya cigaba da jan kalmar shahada, har zuwa sa’adda mala’ikan mutuwa ya zare ransa. Faɗin irin tashin hankalin da wannan ahali suka shiga ɓata baki ne. Sai dai fatan Allah ya jiƙan waɗanda suka rigayemu gidan gaskiya. Tun daga wannan lokacin, Ummee bata sake lafiya ba. A haka aka kwashe kwanaki arba’in yau fari gobe tsumma. Lamarin da ya ƙara jefa ƴaƴan cikin damuwa da tashin hankali.

Saboda a kwantar mata da hankali Khamis da Ziyada gidan suka koma da zama, amma duk da haka dai sai godiyar Allah. A wannan lokacin ne kuma wani abin gagarumin tashin hankalin ya sake ɓullowa ta ɓangaren Khamis. Wata yarinya ce ƴar gidan masu kuɗi a unguwar dosa ta maƙale ita shi take so. Sunanta Rufaida, babban abin damuwa da tashin hankalin kuma shi ne a wannan lokacin bai fi saura watanni uku a ɗaura mata aure da saurayinta da suka shafe shekaru biyar suna soyayya ba.

Sun haɗu da Khamis ne lokacin da suke zirga-zirga a hukumar Alhazai, al’adar mahaifin yarinyar ne duk ƴar da zai aurar sai ya biya mata kujera ta je ɗakin Allah tayi ɗawafi. A wannan lokacin ne Allah ya haɗa ta da Khamis, da farko shi ne ya maƙale mata, saboda kyakkyawa ce ta gaban kwatance, ga yanga da magana cikin shagwaɓa irin yadda yake so a jikin mace. A tsarin zubi na halittar jiki Khamis ba wani kyakkyawa ne na azo a gani ba. Amma fa ɗan gaye ne na ƙarshe, ga iya ɗaukar wanka, idan yayi wani shigar ya shiga inda ba’a sanshi ba sai ayi tsammanin ɗan gidan minista ne. Idan aka zo ɓangaren lafuzza da iya tsara mace kam babu dama ne, tun sa’adda yake yaro a firamari abokansa har hayansa suke yi yana tsara musu ƴanmatansu irin soyayyar nan ta ƙuruciya.

Tun da Khamis ya samu lambar Rufaida ya tasa ta gaba da kira, wani irin kulawa da tarairaya yake mata a waya wanda ko kaɗan saurayinta Ibrahim bai gwada mata irinsa. Ko da ta tafi saudiya duk tsadar kuɗin kira tsakanin ƙasar nigeria da sa’udiyya ba tare da damuwar komai haka yake loda kuɗi su shafe lokuta masu tsayi yana tsara ta, da kwarzanta zubin halittar da Allah yayi mata. Ita kanta baza ta ce ga takamaimai lokacin da zuciyarta ta faɗa a soyayyarsa ba, kawai ta wayi gari ne tana yima saurayinta Ibrahim wani irin gaggarumin tsana, daɗai wata kalma ta soyayya bata taɓa shiga tsakaninsu ba.

<< Lokaci 12Lokaci 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×