“Wannan shi ne yaron da kika ce kina masifar so?”
Alhaji Abdurrashid ya tambayeta yana sake ƙure hoton Khamis da kallo, hoton da ya mamaye gaba ɗaya fuskar wayar Rufaida.
Shagwaɓe fuska tayi kamar za ta fashe da kuka, ta ƙara tura baki gaba, kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta buɗe baki a shagwaɓe ta ce
“Daddy dan Allah…”
“Saurara Mamana.”
Ya katse ta cikin tsawa-tsawa da muryarsa a fusace, wani abu da shi kanshi bazai tuna lokaci na ƙarshe da yayi mata ba.
Lumshe idanu yayi, yaja nannauyan numfashi ya sauke, ya nemi gefen kujera ya zauna yana kallonta. Ƙoƙarin sassauta muryarsa yayi ganin har ta fara jan shessheƙar kuka.
“Haba Mamana. Kar ki rusa daɗaɗɗen ginin da muka ɗauki tsawon shekara da shekaru muna yi miki mana. Shi yaron ɗan gidan Uban waye a jihar nan? Mecece sana’arsa? Me ya tara na kadarori? Gidajen mai nawa ya mallaka a faɗin nigeria?”
“Hmmm! My dear da za ka ji ta tawa da ka daina ɓata lokacinka akan yarinyar nan. Shi yaron fa ba ɗan kowa bane, infact ma ba shi ma da wani hali na arziki. Ƙaramin yaro ne sosai da babu abinda ya tasa a gaba sai yaudarar ƴanmata. Matarsa ɗaya da tsohon ciki, sai shegiyar ƴar da suka haifa kafin aure…”
A tare Rufaida da Mahaifinta suka ɗaga idanu suna kallon Hajiya Balkisu da maɗaukakin mamaki a fuskarsu.
“Ƙwarai kuwa! Kuna mamaki ko? Nima haka nayi mamaki sa’adda waɗanda na ba kwangilar bincike suka kawo min cikakkun bayanan. Idrees Moha ne da ƴan tawagarsa, kun san dai baza su taɓa kawo min zancen da ba haka ba. Don haka zancen wannan ɗan iskan yaron na soke ta a gidannan, daga yau, daga yanzu. Kuma aure tsakaninki da Ibrahim kamar anyi an gama…”
“Dadddyyyyyy”
Rufaida ta ƙwalla kiran sunan uban muryarta tafe da wani ihun kuka mai ƙarfin gaske, sanin halin uwar na rashin ɗaukar wargi yasa ta miƙe tsaye a zabure ta afka jikin mahaifin ta ruƙunƙumeshi tana rusa kuka.
Hankalinta a tashe, aure tsakaninta da Ibrahim ko baza’a aura mata Khamis ba abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Balle ma tunda ta ji inda maganganun Mamee suka dire ta san sharri kawai ake ma Khamis ɗin ta. An ƙagi shiryayyen labarin ne domin a dakusar da ƙarfin soyayyarsa a zuciyarta. In dai ita ce anyi a banza, baza ta taɓa daina son Khamis ba, wanda ake son ta aura ɗin baza ta aure shi ba.
Da wani irin bala’in fushi Hajiya Bilkisu ta taho za ta janyota a jikin uban yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.
“Yi haƙuri My dear, Allah ya huci zuciyarki. Ƙyaleni da Mamana, zan shawo kan al’amarin da gaggawa in Allah ya yarda.”
Fuuuu kamar kububuwa ta fice daga falon cikin fushi ta nufi ɓangarenta. Tana shiga ta ɗauki wayarta ta dannawa Ibrahim kira, daƙiƙu biyar da fara ringing ɗin wayar aka ɗaga daga can ɓangaren.
“Ibbu kana ina ne?”
Ta tambaya da muryarta a zafafe ba tare da ta bi takan gaisuwar da yake jera mata a ladabce ba.
“Mum, me yake faruwa? Ga ni a filin jirgi zan tafi Abuja…”
“Ka soke tafiyar nan yanzunnan. Duk abinda kake yi ka nemi Moha ya baka cikakken bayani kan tsinannen yaron nan kasa a kamo shi ku canja mishi kamanni. Wataƙila ɗan gayun da yake yi ne yake jan hankalin Rufaida zuwa gare shi, ku canja mishi kamanni sosai yadda ko uwar da ta haife shi ba lallai ta shaida kamanninshi ba. Ku kora mishi ƙwaƙƙwaran kashaidi, sannan ku titsiye shi ya kira Rufaida a gabanku ya ce baya son ta, bazai taɓa aurenta ba. Idan hakan ya faru nasan tabbas za ta dawo cikin hayyacinta…”
Shigowar Daddy cikin ɗakin yasa ta sauke wayar daga kunnenta ba tare da ta aje numfashin maganarta daidai ba, biye a bayanshi Rufaida ce, sai raɓewa take yi a bayan Uban saboda tsoron uwar.
Ko da suka shiga ɗakinshi hankalin Alhajin ya kasa kwanciya. Fushi a fuskar Hajiya ba abu bane da yake ƙaunar gani, don haka ya taso Rufaida a gaba da cewar suzo su bata haƙuri. A kunnensu duk sun ji irin maganganun da take yi, amma sai suka nuna kamar basu ji komai ba.
“Ammee, don Allah kiyi haƙuri ki yafe min. Bazan sake yi miki musu ba in Allah ya yarda.”
Rufaida ta faɗa a raunane, har lokacin bata fito fili sunyi ido biyu da uwar ba.
Harara ta watsa musu su biyun. Kamar ƙaramar yarinya sai ta tura baki gaba, ta kawar da kanta gefe ɗaya, ta zauna a gefen katifa tana karkaɗa ƙafafu.
“Haba Hajiyar Alhaji Abdurrasheed. Haba sarauniyar zuciyar ɗan similmilinta Abdurrasheed. Shalelenki ce fa, kuma Autarki, ashe za ki iya fushi mai tsawo da ita har ya shafi ni Hubbinki da kike kirarin hasken zuciyarki?”
Ya faɗa da wani irin taushin murya, haɗe da shagwargwaɓe fuska kamar matashi sabon jini a gaban budurwar da yake bala’in so.
Duk yadda takai ga son cigaba da ɗaure fuska ta kasa, a dole ta saki lallausan murmushi tana kallon cikin idanun Alhajin. Da gaskiyar Mal bahaushe da ya ce soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, musayar kallo suke yi a tsakaninsu suna aika ma junansu saƙonnin da ke bayyana asirin zuciyarsu.
Ita dai Rufaida ganin zancen na neman canza salo a hankali ta saɓe daga bayan uban ta fice daga ɗakin, jikinta babu inda baya rawa. A guje ta faɗa ɗakin Daddy ta ɗauki wayarta, tana shiga ɗakinta ta mayar da ƙofa ta rufe haɗe da murza ɗan makulli.
Safa da marwa ta fara yi a tsakar ɗakinta bayan ta danna kira ma Khamis, sai da tayi mishi kira uku bai ɗauka ba, izuwa lokacin ta haɗa zufa tayi kashirɓin, kasancewarta mai saurin kuka har ta fara hawaye, zuciyarta cike da tunanin rashin imani da tausayin Ibbu idan abu ya biyo ta kanta ko kuma soyayyar da yake mata.
Sai a kira na biyar ya ɗaga wayar, da magagin barci a muryarsa ya fara jera mata kirari kamar yadda ya saba.
“Dakata don Allah Lolly, kana ina ne yanzu haka?”
Ta katse shi da sauri, muryarta na bayyana tashin hankali ƙarara.
“Lafiya? Me yake faruwa? Ina family house ɗinmu yanzu haka, kin san Mum ɗina ba lafiya…”
“Ka gudu Khamis”
Ta katse shi da sauri.
“In gudu fa kika ce? Ban fahimce ki ba…”
“Eh! In dai kana son ka tsira da ranka da lafiyarka kayi gaggawar guduwa daga gidanku yanzunnan. Ammee na ta bada umarnin duk inda kake a neme ka ayi maka mugun dukan da za’a kusa hallaka ka, kuma waɗanda ta turo su dake ka ko kaɗan ba su da imani da tausayi, Wallahi za su iya kashe ka ma, kuma babu abinda zai faru don sun kashe ka…”
Ƙit wayar ta katse daga can ɓangarenshi.
******
Ba tare da tausayi ko duba girma da yanayin rashin lafiyar da take ciki ba suka janyo ta ƙiiii a wulaƙance daga cikin uwarɗakinta zuwa falo. Kamar kayan wanki haka suka yasar da ita, kanta ya bugu ƙum da jikin kujera. Wani marayan ihu ta saki a galabaice.
Jikin Yusuf babu inda ba ya rawa ya sake yunƙurawa da dukkan ƙarfinsa don ƙwacewa daga mugun riƙon da suka yi masa amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ya kasa yi. Duk abinda yake yi Ibbu yana hankalce da shi, a zafafe ya ɗaga hannu ya zabga ma Yusuf ƙaƙƙarfan marin da yasa jin shi ɗaukewa na wucin gadi.
Hankali tashe Ummee ta runtse idanu da ƙarfin gaske haɗe da fashewa da kuka.
“Ke tsohuwa, na rantse da wanda raina ke hannunsa idan baki rufe mana baki ba yanzunnan zan ɗirka ma wannan yaron naki Alburushi. Ina Yaronki Khamis ya shiga? gurinsa muka zo…”
“Baya nan”
Ta katse shi cikin kuka da rawar murya. Kafin ya amsa ta ƙara da cewa
“Na rantse da Allah ba ya nan. Don Allah kuyi haƙuri, ko me yayi muku kuyi mana aikin gafara, don Allah, don Annabi kar ku taɓa rayukan da basu ji ba basu gani ba…”
“Yi mana shiru! munafuka kawai.”
Ya katse ta cikin tsawa mai bala’in ƙarfi. Da yanayinsa na ƙaƙƙarfan saurayi mai jini a jika ya ƙarasa inda take yashe ya take yatsun ƙafafunta na hagu ya murje da ƙarfin gaske, ta buɗe baki za tayi ihu ya nuna mata hancin bindiga.
“Kina buɗe wannan ruɓaɓɓen bakin naki mai kama da masai ni kuma zan fasa ƙwaƙwalwarki kanki da bindiga. Kin san me ya kawo mu wannan akulkin gidan naki a daidai wannan lokacin?”
A galabaice ta girgiza kai, alamar bata sani ba. Jikinta sai rawa yake yi saboda azaban zafi da raɗaɗin da ƙafarta da ya taka take yi.
“Kwanakin baya, Hajiya Bilkisu mahaifiyar yarinyar da nake mutuwar so ta aiko da kashaidin ɗan iskan yaronki Khamis ya fita daga harkar Babyna, saboda tun da daɗewa maganar aure ke tsakanina da ita. Amma saboda shi yaronki shaiɗani ne ya saba yaudarar ƴanmata har yanzu bai fita daga harkar matata ba, a maimakon yaja baya da ita ma sai ya ƙara dagewa kullum ba shi da aikin yi sai hure mata kunne, yana ƙara rura wutar tsana da muguwar ƙiyayya tsakanina da ita. Hmmm!”
Yayi wani dogon ƙwafa ya cije leɓensa na ƙasa, ƙanƙance idanunsa yayi yana kallonta da ɗaurarriyar fuska ya cigaba da cewa.
“Kin san me na taho da niyyar yi masa?”
Anan ma dai kai ta iya girgizawa a wahalce.
Kan kujeran da ke kusa da ita ya zauna ya cigaba da magana a nutse, a fuskarsa za’a fahimci zallar gaskiyar magana yake faɗa, maganganun fitowa suke daga can ƙarƙashin zuciyarsa.
“Tahowa nayi da niyyar in ɗauke shi, in ɓoye shi a inda har abada baza ku sake jin ɓurɓushin labarinsa ba. Wata sassaiɓar azaba nayi masa tanadi, ta yadda a hankali ransa zai dinga fita daga jikinsa har zuwa sa’adda zan shafe babinsa gaba ɗaya a doron ƙasa, kin ga ko ba komai an rage mugun iri. Wulaƙantattun ƴaƴa mayaudara, masu shiga tsakanin soyayyar gaskiya da aka gina ta tun da daɗewa.
Amma tunda ban same shi ba, wannan zuwan da nayi bazai zama a banza ba, zan tafi da wannan ɗan’uwan nasa a madadinsa, na san duk inda yake idan yaji labarin yayansa na hannuna zai miƙo kanshi a sauƙaƙe…”
“A’a! wayyo!! Dan Allah na shiga uku!!! Don Annabi SAW kar kai haka, ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka ka bar min ɗana. Na yarda ku nemi Khamis duk inda yake a faɗin duniyar nan, kuyi masa duk abinda kuka so kuyi masa, amma shi wannan babu ruwansa. Yaro ne mai tsananin ladabi da biyayya, babu komai tsakanina da shi sai sam barka, tunda na haife shi daɗai bai taɓa jefa ni a cikin wani gagarumin ɓacin rai ba. Don darajar fiyayyen halitta SAW kayi haƙuri. Na tuba, na bi Allah na bi ku!!!”
Wani matsanancin tausayin tsohuwar ne ya lulluɓe zuciyar Moha, ganin yadda take magiya tana rusa kuka da dukkan ɗan ragowar ƙarfinta take roƙon Ibbu ya ƙyale mata yaronta. Shi kuwa Ibbu da alamun ko gezau baiyi ba, duk yadda take magiyar ko saurarenta baya yi, sai umarni da yake ba matasan da suke riƙe da Yusuf kan su gaggauta yi masa mugun ɗauri irin na huhun goro.
Aka ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Duk yadda Yusuf yake ƙoƙarin ƙwatar kansa zuwa ga mahaifiyarsa ya kasa, izuwa wannan lokacinma ya galabaita gaba ɗaya saboda bugun da suke kai mishi ta ko wane ɓangare.
“Ibbu, ka ƙyale shi Pls, kamar yadda mahaifiyar yaron ta faɗa shi wannan bai san komai ba. Infact ma yana baƙin ciki sosai da abinda ɗan’uwansa yake aikatawa. Ka ƙyale shi, na yi maka alƙawarin in sha Allah duk inda Khamis ya shiga in dai yana cikin garinnan kafin safiya zan damƙa shi a hannunka, in Allah ya yarda.”
Ibbu shiru yayi na tsawon daƙiƙu talatin yana tunani, kamar bazai amince ba. Amma da ya tuna wanene Moha da kuma sanin muhimmancinsa a gurin Hajiya Bilkisu sai ya bada umarnin a ƙyale Yusuf, babu ɓata lokaci suka fice daga gidan.
Duk da halin galabaitar da yake ciki haka ya rarrafa a wahalce zuwa gurin mahaifiyarsa.
“Ummee? Ummee? Ummee? sannu Ummee, kiyi haƙuri, ki yafe min don Allah, na kasa ceto ki a hannun waɗannan azzaluman…”
Ya rungumeta a jikinsa ya fashe da kuka, hankalinsa a tashe, ganin yadda take jan numfashi a wahalce shi ne abinda yake ƙara ɗaga masa hankali.
******
“Ban… gane ba? Me kake nufi Ƙalb…? Idan ba jikin Ummee bane ya tashi me zai sa ka nemi tafiya da ni a gaggauce haka?”
Ta jefa mishi tambayoyin cikin rashin fahimta.
A maimakon ya amsa mata sai yaja ɗan ƙaramin tsaki, hannunta ɗaya ya damƙa ya fara jan ta da nufin su fice daga gidan.
Turjewa ta fara yi, fuskarta da damuwa ƙarara. Magana take so suyi da mahaifiyarta shi kuma yana neman katse mata hanzari. Ganin da gaske ƙoƙarin ficewa da ita yake yi yasa ta ce,
“Wai miye haka kake yi?ina za ka kai…”
“Ziya, don Allah ki rufe min baki. Tunda na tabbatar miki ba jikin Ummee bane ya tashi ai kin san dai bazan tafi da ke don in cutar da ke ba ko? Muje don Allah, kina saka ni ƙara ɓata lokaci…”
“To na ji, ka ga ban daɗe da shigowa gurin Ummanmu ba, bari in mata sallama, in ɗakko Nauwara da take barci.”
Ta faɗa cikin rawar murya tana waige-waige, hankalinta a tashe. Daga yadda ta ganshi kwatsam a yammacinnan ta rasa dalilin da yasa hankalinta ya kasa kwanciya. Kuma a maimakon ya shiga gidan nasu kai tsaye kamar yadda ya saba a kwanakin kiranta yayi a waya ta fito da cewar za ta karɓi saƙo.
“Manta da su kawai. Ba lokaci, duk minti ɗaya da zan sake ɓatawa anan gurin rayuwata ke ƙara shiga cikin haɗari. Muje, zanyi miki bayani a hanya.”
Taimakon da Allah yayi mata shi ne babban hijabi ne a jikinta saboda tsohon cikin da take ɗauke da shi. Haka ta bi bayanshi ba don ranta na so ba suka fice daga gidan Ummanmu. A zatonta gidansu Ummee za su shiga, sai taga ko kallon gidan baiyi ba ya ƙara fincikar hannunta da sauri suka wuce gidan.
Lamarin nashi ya daina bata mamaki sai dai tsoro, kamar wacce aka ɗinkewa baki. Bata ƙara tambayarshi inda za su je ba har ya tare musu keke napep suka shiga su biyun.
“Malam tashar kawo za ka kaimu.”
Jin abinda ya faɗa yasa ta kallon fuskarsa, aka yi arashi shi ɗin ma ita yake kallo. Na wasu daƙiƙu suka yi musayar kallo a tsakaninsu da mabanbantan saƙonni a cikin idanuwansu. Shi ya fara kawar da kai zuwa gefen hanya, ita kuwa ƙasa ta duƙar da kanta tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙara hauhawa.