Skip to content
Part 16 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Yakai gwauro ya kai mari a tsakar ɗakin, hankalinsa a ɗugunzume, a ƙarshe dai gefen katifar ya zube daɓas. Hannu biyu yasa ya riƙe kanshi da yake ji yana mishi wani irin ciwo kamar zai rabe gida biyu.

“Yaro, ka kwantar da hankalinka. Za’ayi aikin shashatau, ɓangaren daɗin aikin shi ne tabbas za’a manta da al’amarin kamar bai taɓa faruwa ba. Sannan za ka yi rayuwa irin wacce ka daɗe kana mafarkin yi, ba tare da wata gagarumar matsala ta sake rutsawa da kai ba. Za ka shiga haɗarurruka, amma duk haɗarin da za ka shiga tabbas za ka samu hanya mai ɓullewa a cikinta.

Ɓangaren rashin daɗin aikin kuma shi ne za’a rasa rayuka biyu, da na wanda kake yiwa matsanancin so, da na wanda kake yiwa soyayya tsaka-tsakiya. A bayan waɗannan rayukan babu wata rai da za’a sake rasawa sai dai idan kai ne kaso hakan. Zaɓi ya rage naka, ayi aikin yau ko kuma kana buƙatar lokaci don yin shawara da zuciyarka?”

Ga tsammanin Duwan da Hadi a take Khamis zai bayar da damar ayi aikin, saboda yadda ya nuna musu yana cikin matuƙar damuwa da tashin hankali kan wannan al’amari. Sai ya shayar da su mamaki ta hanyar cewa a bashi lokaci yayi shawara.

“To kana da daren yau kawai, domin na hangi wani gaggarumin tashin hankali ɗauke da balbalin bala’i yana tunkaro ka. A cikin wannan tashin hankali kana iya rasa ranka, iyalinka za ta iya rasa ranta, gudan jininka za ta iya rasa ranta, mahaifiyarka za ta iya rasa ranta, wanda zai sha a cikin makusanta daga ahalinka kawai wani dogon yaro ne ga shi can a tsaye.”

Nan take malamin ya fara lissafa kamannin yayanshi Yusuf.

Da waɗannan munanan maganganun da basa ɗauke da komai sai zallar firgitarwa da tashin hankali suka baro gurin Malam. A cikin mota a hanyarsu ta komawa gida kallo ɗaya za’a mishi a gane a birkice yake, yayi da na sanin amincewa maganganun Duwan da Hadi ya fi sau ɗari. Yayi da na sanin warware musu irin halin da yake ciki a yanzu, da bai faɗa musu ba da yanzu yana zaune lafiya ƙalau ba tare da ya jiyo waɗancan maganganun da suke neman tarwatsa shi ba.

Duk yadda suka so sake birkita mishi lissafi ta hanyar ƙara kwaɗaitar da shi irin samun arzikin da ke cikin harkarsu ya ƙi saurarensu. A ƙarshe da yaga za su hana shi tunani sai ya kalle su ranshi a ɓace ya ce
“Don Allah ku sauke ni anan, zan nemi mai mashin ya ƙarasa da ni gida.”

Da yake lallaɓashi suke yi duk su biyun sai suka hau bashi haƙuri hankalinsu a tashe, daga bisani suka yi shiru, zukatansu cike da addu’ar Allah yasa ya amince ma duk abinda Malam ya sanar da shi.

Khamis ɗin yayi daidai da irin tsarin matashin da Oga ya daɗe yana nema a cikin harkarsu. Ƙungiya ce gare su babba, da ta tara matasa masu jini a jika da yawan gaske, amma ire-irensu Khamis waɗanda tun tale-tale da baiwarsu suke tafe suna da ƙaranci a cikin ƙungiyar. Shiyasa ko kusa ba sa fatan ya janye ma tayin da suka mishi, wanda a karon farko ya nuna amincewarsa ɗari bisa ɗari jin irin samun da ke cikin harkar.

Zaman ƙuda ne ya gudana a tsakaninsu har suka ƙarasa farkon layin gidan Alhaji Bashir suka sauke shi, duk zukatansu babu daɗi ko kaɗan, kamar waɗanda aka yi ma gagarumin mutuwa.

In da Allah ya taimaki Khamis magrib tayi, daman kafin su tafi gurin Malamin sai da ya kawo saƙon man fetur ɗin da aka bashi sannan ya sake fita, bayan yayi ma Hajiya da Ziyada ƙaryar zai shiga kasuwa ya siyo takalmi.

Sukuku ya ƙarasa daren kamar mare lafiya, yana idar da sallar isha’i ko abinci bai ci ba ya shige ɗakinsa, bayan ya faɗa musu kanshi na ciwo.

Kamar mai naƙuda, idan yayi gabas yayi yamma sai ya juya kudu da arewa, daga ƙarshe kuma sai ya ɓuge da zaman ƴan bori a tsakar ɗakin ko kuma bakin katifarsa. Haka yai ta safa da marwa har zuwa ƙarfe biyu na dare bai yanke matsaya guda ɗaya ba tsakanin yin aikin Malam da barin aikin.

Idan yayi kamar zai amince sai ya tuna an ce za’a rasa rai na mutum biyu? Rayukan su wanene waɗannan guda biyun? Idan ya mayar da zuciyarsa ɓangaren rashin amincewa sai ya tuna balbalin bala’in da aka ce yana tunkarosa, har ma zai iya rasa ransa da duk wani da ya kusancesa.

Da ya rasa waƙar farawa sai ya janyo wayar da Duwan ya mallaka masa da cewar duk shawarar da ya yanke ya kira ya sanar mishi, shi kuma sai ya kira Malam ya faɗa mishi halin da ake ciki.

Lambar Duwan ɗin ya lalubo ya danna masa kira, daga can ɓangaren kamar dama zaman jiran yake yi, tana fara ringin ya ɗauka.
“Khamis? Baka yi barci ba? Ya ake ciki? Allah dai yasa ba kira kayi ka sanar da ni baka amince da buƙatar da muka tunkareta da ita ba. Khamis ko baka amince da aikin Malam ba babu matsala, za mu iya roƙonsa yayi aikin da zai dakushe ƙarfin bala’in da yace yana tunkararka, in yaso sai ka cigaba da rayuwarka anan Kano, ba sai ka koma Kaduna ba balle har ka haɗu da iyayen wancan yarinyar da suke neman hallaka ka. Cikin ƙanƙanin lokaci in dai kana yin abinda ake so za ka mallaki tamfatsetsen gida irin wacce baka taɓa mafarkin mallaka ba a rayuwarka, za ka mallaki mota mai tsada, sutura sai irin wacce kake so za ka dinga sanyawa…”

Da wani irin gajiya da kasala sosai a muryarsa ya katse shi da cewa
“Duwan, don Allah ka saurare ni. Ni Sam ba na sha’awar yin dauwamammiyar rayuwa a Kano. Kaduna zan koma, don haka ka faɗa ma Malam na amince ayi aikin da zai sa iyayen Rufaida su manta da al’amarina gaba ɗaya a rayuwarsu.”

Acan ɓangaren Duwan da wayarsa take a amsa kuwwa idanu suka haɗa shi da Hadi suka yi murmushin cin nasara. A muryarsa kawai za’a fahimci yana cikin farin ciki.
“Angama Khamis, zan sanar da Malam yanzunnan. Ka kwantar da hankalinka don Allah. Komai zai tafi daidai kamar yadda na faɗa maka.”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin yadda a maimakon ya samu sauƙin fargaba da tsoron da yake ciki tunda ya amince ayi aikin sai wani sabon ƙunci da ɓacin rai ne ya lulluɓeshi. Yaja shessheƙa sau biyu, kamar bazai sake cewa komai ba sai kuma ya ce.
“Gobe misalin 11 zan fito mu haɗu, ku kaini gurin Ogan naku. Na amince zanyi harka da ƙungiyarku, amma sam bazan bi hanyar da kuke bi ba.”

Katse wayar da yayi daidai yake tafe da wani ƙaƙƙarfan bugawa daga zuciyarsa. Lumshe idanu yayi, sai kuma ya tafi a hankali ya kwanta akan katifarsa, jin da yayi bugawar zuciyarsa ta ƙi sassautawa yasa shi sa hannu bibiyu ya dafe saitin zuciyar, a haka wani nannauyan barci mai tafe da muggan mafarkai yayi awon gaba da shi.

******

“Mmmmmme ka ce? Allah yayi me?”
Alhaji Bashir ya tambaya bakinsa na rawa, a zuciyarsa yake ƙaryata abinda kunnensa yaji a wayar.

Daga can ɓangaren Yusuf shessheƙa yaja cikin kuka, tsawon daƙiƙu talatin yana kuka kamar bazai yi magana ba, sai kuma ya buɗe baki daƙyar ya maimaita abinda ya ce da farko.
“A faɗa ma Khamis… Yanzunnan… Allah yayi ma Ummee rasuwa…”

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!! Hajiya Hauwa’u ta rasu? Laahaula walaa ƙuwwata illah billah…”
Wayar da ta suɓuce a hannunshi zuwa ƙasa ya hana shi ƙarasa abinda yake cewa. Bai bi ta kan wayar ba, sai ficewa da sassarfa zuwa kicin inda Hajiya take hada-hadar haɗa abincin rana Ziyada na taimaka mata da miƙa ƙananun abubuwa.

“Hajiya, Hajiya, Hajiya.”
Haka ya dinga ƙwalla kiran sunanta a ruɗe kamar ƙaramin da ke neman mahaifiyarsa. Ya kusa isa kicin ɗin ta fito da sassarfa suka haɗe a tsakiyar falo.
“Alhaji lafiya k…?”

“Kin ji abinda yake faruwa a kaduna? Hajiya Hauwa’u mahaifiyar Khamis ce Allah ya karɓi rayuwarta…”

“Laa’ilaha illallahu Muhammadur-rasulillahi…”

Ƙaƙƙarfan ihun Ziyada da suka jiyo daga kicin shi ya ankarar da su wanzuwarta a gurin. Rige-rigen isa kicin ɗin aka yi tsakanin Hajiya da Alhaji. Ko da suka isa sai suka tarar da ita tsaye guri ɗaya, jikinta babu inda ba ya rawa, ta haɗa zufa tayi kashirɓin, hannayenta duk biyu dafe da mararta da take jin yana mata wani irin murɗawa a haukace kamar mai jin gudawa. Laɓɓan bakinta sai rawa yake yi.

“Ziyada? Lafiya kuwa?”
Suka haɗa baki gurin tambayarta, hankalinsu a tashe, ƙur suke kallonta suna kallo da karantar halin da take ciki. Kamar ma dai sun manta Hajiya Hauwa’u da aka faɗi ta rasu sarkuwarta ce.

“Umm…meee…”
Ta yago maganar daƙyar, har lokacin bata saki cikinta da ta tallabe ba, kuma jikinta bai daina rawar da yake yi ba.
“Ttttaaaaa rasu…? Wayyoooo Allah bayana zai ɓalle Hajiya…”

Sai a lokacin suka ankara da abinda ke faruwa. Da saurin gaske Hajiya ta ƙarasa ta riƙeta tana jera mata kalaman rarrashi domin kwantar mata da hankali.

Sai dai kuma jin rasuwar Ummee farat ɗaya ya tasar ma Ziyada zazzafan naƙuda, lokaci ɗaya azabar ciwo yasa ta kusa rinjayar Hajiya su zube a tsakar kicin ɗin, da sauri Alhaji ya riƙo hannayenta. Bisa babin lalura a dole ya kamata da taimakon Hajiya suka fice da ita sannu a hankali zuwa gurin mota.

Khamis baya nan, tun goma na safe ya fice a gidan. Don haka duk wainar da ake toyawa ba shi da labari.

Ko da suka isa asibiti daƙyar aka karɓeta saboda ba’a asibitin take awo ba. Sai da Alhaji Bashir ya tabbatar musu ƴarsa ce baƙuwa tana aure a kaduna, ziyara ta kawo musu naƙuda ya risketa ba tare da sanin ita kanta lokacin haihuwar yayi ba.

A wannan karon kuma sai Allah ya dube ta, daman ko wace haihuwa da yadda take zuwa, gajeriyar naƙuda tayi. Bayan awa ɗaya da zuwansu Allah ya sauketa lafiya, ta sunkuto ƴarta ƙatuwa, jajur da ita, Tubarakallah ma sha Allah.

Kafin ta haihu anyi ma Alhaji list na duk abubuwan da za’a buƙata, don haka ta haihu komai da za’a buƙata yana ajiye a kusa. Da maijego da jaririya duk lafiya ƙalau suke, cikin ƙanƙanin lokaci aka gama shirya su, aka miƙa Ziyada ɗakin hutu, wacce take ta matsar ƙwallah tana jero addu’o’in neman gafara da samun rahama ga Ummee. Baiwar Allah da baza ta taɓa mantawa da ita ba saboda irin ƙaunar da take gwada mata ita da Nauwara.

Gaba ɗaya hankalinta ya tattara ya koma gida, ji take kamar tayi tsuntsuwa ko kuma ta rufe idanu ta buɗe ta ganta a Kaduna. Hajiya da Alhaji Bashir ma hankalinsu a ɗugunzume yake, minti ɗaya biyu sai su ɗaga idanu su kalli agogo, ƙarfe uku da kwata na rana. Babu Khamis babu alamunsa, bayan sun bar ma Maigadi sallahun lallai yana dawowa a faɗa mishi sun tafi da Ziyada asibiti, da sunan asibitin da za su kai ta.

Rashin ganinsa shi ya basu tabbacin bai koma gida ba har wannan lokacin, gashi kuma babu waya a hannunsa balle su kira su sanar da shi abinda yake faruwa.

Har bayan Magrib da likita ya sake duba Mai jego da Baby ya tabbatar da lafiyarsu Khamis bai je asibitin ba. Haka Alhaji ya sake kwasarsu zuwa gida, hankalinsa a ɗugunzume sosai yana tunanin inda Khamis ya shiga a tsawon yinin, izuwa lokacin ya fara addu’ar Allah yasa dai ba wani mummunan abu ne ya same shi ba.

******

Mutuwa yankan ƙauna. Mutuwar Ummee da Abba ga Yusuf rashi ne da ba ya jin har gaban abada zai iya mantawa da su. Ya tabbata maraya gaba da baya, ko da ake cewa mutuwa tana kunyar ɗa da mahaifi shi dai kam bata ji kunyarsa ba. Akan idanunsa Abba ya rasu, haka zalika Ummee tana riƙe da hannayensa bayan ta gama jaddada mishi wasiyyar lallai ya riƙe amanar ƙaninsa, duk juyin juya hali irinna rayuwa da duk irin rikicin da Khamis zai ɗakko kar ya taɓa juya mishi baya.
“Wannan roƙo ne da kuma Umarni Yusuf.”
Ta kira sunanshi, abinda bata cika yi ba a matsayinshi na ɗan fari.

Daga nan kuma sai wani irin tari mai haɗe da shaƙuwa ya sarƙeta, daƙyar tarin ya lafa bayan ya jera mata sannu sau ba adadi, hankalinsa a tashe, hawaye wasu na korar wasu a idanunsa kamar ba namiji ba. Har ta buɗe baki za tayi magana sai kuma tayi shiru, ta ƙura mishi idanu, itama hawaye ke gangara a gefe da gefen idanunta.

Ƙarara yake kallon rauni da sarewa a rayuwar duniya tattare da ita. Tayi tari sau biyu, a fisge ta fara jera kalmar shahada cike da ƙarfin hali, lokaci ɗaya yake ganin yadda idanunta suke ƙaƙƙafewa sannu a hankali, har zuwa sa’adda mala’ikan mutuwa ya zare ran mahaifiyarsa ba tare da jin kunyar shi ɗanta da yake riƙe da hannayenta ba. Izuwa wannan lokacin, saboda kukan da yake rusawa jikinsa har wani irin jijjiga yake yi, daga ƙarshe ma kifa kansa yayi akan ƙirjinta ya cigaba da kuka, ba tare da tunanin me ya kamata ya aikata a daidai wannan lokacin ba.

Kasancewar asibitin kuɗi ne ba na gwamnati ba, ɗakin da aka kwantar da Ummee gado biyu, tun jiya da yamma aka sallami maƙwafciyarta da take ɗaya gadon, ƙanwar Ummee da take jinyarta kuma yana zuwa da safe ta tafi gida da niyyar yin wanka ta ɗebo kayan sakawa, domin sun tashi a safiyar ranar jikin da sauƙi, ba tare da saninsu ba sauƙin tafiya ne.

Maraici, abu ne da idan ba wanda ya shiga cikinsa ba babu wanda zai bayar da labarin yadda yanayin yake. Ji yake duniyar gaba ɗaya ba ta yi masa daɗi, ya tsani kowa da komai, hatta kansa ya tsana, babu abinda yake so a daidai wannan lokacin da yake kuka sai mutuwa ta ɗauki ranshi kanshi yana jikin Ummee.

A daidai wannan lokacin, Ummanmu ta sanyo kai cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Ruƙayya na biye da ita, hannunta riƙe da kwandon abinci.

Ganin halin da Yusuf ke ciki yasa Ummanmu jan salati da ƙarfin gaske, a ɗimauce ta saki jakar hannunta ta ƙarasa gefen gadon da sassarfa, har lokacin bakinta bai daina ambaton Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ba.

Cikin minti ɗaya ta gama fahimtar abinda ya faru. Jikinta na rawa tana hawaye ta ɗaga kan Yusuf daga jikin gawar ta jingina da kujerar da yake zaune, ta riƙe hannunsa ɗaya tana rarrashinshi da kalamai na kwantar da hankali, sannan ta umarceshi da yayi ta maimaita
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allahumma ajirnee fi musibatee, wa akhlifnee khairan minha.”

Tun yana jan shessheƙa yana sauke ajiyar zuciya irinna wanda ya daɗe yana kuka, har taji ya fara maimaita kalmomin da ta umarce shi, cikin matsanancin tausayin yaron ta kama gefen mayafinta ta goge hawayen da ya ɓata mata fuska.

Hankalinta ta mayar bakin ƙofa, sai taga Ruƙayya duƙe a ƙasa ta rufe fuska da hijabin jikinta tana kuka. Don haka da kanta ta fice ta sanar da likita halin da ake ciki. Ko da likitoci suka shigo, umarni suka yi musu kan su fita waje za su duba gawar don tabbatar da ta rasu ko da sauran numfashi.

Daƙyar Yusuf ya iya miƙewa tsaye yana layi ya fice daga ɗakin, nan bakin ƙofar ɗakin ya zauna a ƙasa, ba tare da damuwar asibiti bane, zai iya kwasar wasu ƙwayoyin cutar.

<< Lokaci 15Lokaci 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×