"Ko da muka yi sallama ya tafi ni kuma na shiga gida a gaggauce na shige can ƙuryar ɗakina. Na lalubo lambar Malam da tun a waje na adanata na danna mishi kira.
"Assalamu alaikum wa rah-matullahi ta'ala wa barakatuh."
Malamin yayi sallama daga can ɓangarensa da wata irin murya mai bayyana girma da kwarjinin malunta.
Lokaci ɗaya na ƙara nutsuwa, na gaishe shi a ladabce. Bayan ya amsa gaisuwar a nutse na kora mishi bayanin duk halin da nake ciki.
Ya fahimceni ƙwarai, ya kuma tausaya min. Malamin yayi min ƴan nasihohi kan muhimmancin bin umarnin iyaye. . .
Ma Sha Allah