Skip to content
Part 22 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Sannu! Sannu Imam!! Yi haƙuri, yi shiru ka ji ɗan Baba? Sannu! Rufe bakin, yi shiru kar tazo ta ƙara maka. Zan siya maka alawa ka ji ko?”

Ire-iren tausasan kalaman da Uban yake ta furtawa ɗan kenan hankalinsa a tashe, Fuskarsa cike da matsananciyar tausayin ɗan ƙaramin yaron.

Nan tsakar gidan ya zauna yana ta rarrashin yaron da kalamai na kwantar da hankali. Amma har lokacin Imam rusa ihu yake yi kamar ba ya jin yaren hausa da uban ke magana da shi.

Ko kallo basu ishi Mama Ladidi da take ta safa da marwa tsakanin kicin zuwa ɗaki tana ƙoƙarin kammala aikin awarar da take sayarwa da rana. Zuciyarta baƙi-ƙirin, sosai taji zafin marin da babbar ƴar tata tayi ma Autarta, amma ba ta da ikon tsawatarwa. Ta sani ko ta buɗe baki da zummar faɗa sai dai su raba hali a tsakar gidan kamar yadda suka saba ita da uban da shi ke ɗaure ma Samira tana aikata duk mulkin da taga dama a cikin gidan.

“Wai miye haka? Menene haka ake min a cikin gidannan? Saboda Allah da Annabi barcin safen ma baza’a barni inyi a mutunce cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba?”
Samira ta faɗi haka cikin faɗa da masifa bayan ta yaye labulen ɗakinta tana kallon cikin gidan, kamar ita ce Uban shi ne ɗan cikin sauri yasa hannuwa biyu ya damƙe bakin Imam, ya zama ƙaran kukan baya fita sai dai gurnani.

“Imam na rantse da Allah idan ka bari nazo gurinnan sai na ci ubanka. Don uwarka me yasa baka je makaranta yau ba?”

Ta sake faɗa cikin tsawa sosai.

“Kiyi haƙuri Gimbiya, ya tashi da zazzaɓi ne a jikinsa shi yasa Ladidi ta ce ya zauna yau gobe sai ya tafi. Amma sauran ƴan’uwansa tuni sun daɗe da isa makaranta.”

Uban ya amsa mata da sanyin murya.

Tinƙis-tinƙis ta tako daga cikin ɗakinta har zuwa inda suke zaune akan dandaryar siminti. Jin da tayi yaron ba lafiya sai ta ji a ranta bata kyauta ba da tayi saurin ɗora hannu a kanshi.

Tana isa gurinsu ɗan tsugunawa tayi kaɗan ta taɓa gefen wuyan yaron, zafi rau taji a hannunta. Hankali tashe ta ɗauke hannunta ta janyo yaron zuwa jikinta. Da tsawa-tsawa ta ce,

“Baba sakar mishi baki mana, kai baka ji yadda jikinshi yayi zafi sosai bane?”

“Yi haƙuri Gimbiya. Na ji, ai wai don kar kukan nashi ya cigaba da damunki ne.”

A takaice ta harari uban, sannan ta mayarda hankalinta kan fuskar Imam ɗin tana kallon yadda sashin hannunta ya fito raɗau a kumatunsa. Da tausayi sosai a fuskarta ta sake rungume shi,

“Yi haƙuri ɗan Ƙanina, ban san baka da lafiya ba shi yasa na mare ka. Yi shiru, zan siya maka Rufaida anjima idan na fita. Ka ji ko?”

A galabaice yaron ya gyaɗa kai, sai kuma a hankali ya fara rage ƙarfin kukan da yake yi har yayi shiru, sai sauke ajiyar zuciya akai-akai da yake yi.

“Mama an kaishi Kemis?”

Ta tambayi uwar a daidai lokacin da tazo giftawa ta gefensu zuwa gurin wanke-wanke.

Ko kallon banza bata samu daga uwar ba balle tasa ran za ta amsa mata.

Cikin faɗa ya taso ma uwar kamar zai cinye ta ɗanye.

“Miye haka kike yi Ladidi? Baki ji Gimbiya na tambayarki ba…?”

“Ban ji ba. Ban san wata Gimbiya ba, kai da ka ji kuma ka santa ai sai ka amsa mata.”

Ta amsa shi da murya a cushe.

Da sauri ya yunƙura ya miƙe tsaye a zafafe zai fara sauke mata ruwan bala’i Samira ta dakatar da shi.

“Baba don Allah kar ku saka min ciwon kai. Riƙe shi, bari in ɗakko kuɗi ka kaishi asibiti. Jikinsa yayi zafi sosai.”

“To Gimbiya. Allah dai yayi miki albarka. Allah ya ƙara buɗi.”

Jikinsa na tsuma ya karɓi ɗan daga hannunta ita kuma ta miƙe tsaye. Sosa ƙeya ya fara yi da murmushi a fuskarsa ya sake cewa,

“Ummm Gimbiya na ce ba? Idan alƙawarinnan nawa ya samu a haɗo min da shi. Kin san Alhaji Idin ba alƙawari ke gare shi ba. Jin da yayi kwana biyu shiru yana iya sayar da Napep ɗin.”

“Baba ca nake saura cikon ɗari da hamsin ne?”

“Ɗari biyu dai, daure ki bani ɗari biyu Gimbiyar Babanta. Kin san dole sai na sallami dillalai da ƴan kanzagi da masu cin la’ada, ko a nan arba’in da bakwai nayi lissafi.

Canjin dubu ukun da su zan saka mai in fara aiki da Napep ɗin.”

Daƙiƙu sittin ta ɓata tana kallonshi shi kuma sai washe haƙora yake yi yana sosa ƙeya alamun rashin gaskiya ƙarara. Sai kuma ta juya ta nufi cikin ɗakinta, zuciyarta cike da takaicin halin mahaifinta na rashin gaskiya da almubazzaranci da kuɗi.

Har ta shige cikin ɗakinta kirari yake jera mata kamar gimbiyar gaske da bafadenta. Zuciyarsa cike da addu’ar Allah yasa dai ta fito mishi da dubu ɗari biyun, lallai kam yau da ya fantama iya fantamawa.

Mintuna sha biyar ta ɓata a cikin ɗaki kafin ta fito, a lokacin har Imam ya fara barci a jikin Baban. Dubu ashirin ta fara miƙa masa, ta ƙara da cewa,

“Ka kai Imam asibiti. Baba ka tabbatar anyi mishi duk abinda ya kamata, kar kuma ka kira ni da ƙorafin dubu ashirin ya gaza in dai ba kwantar da shi aka yi ba. Ga wannan kuma”

Ta sake miƙa mishi bandir ɗin dubu dubu guda biyu.

“Baba ga kuɗin da ka buƙata, ina lissafe da abinda na baka a cikin satinnan ɗari biyar kenan. Ina zuba ido anjima kazo da keke napep ɗin da ka siya, kuma kar ka kuskura kazo min da zancen an damfareka irinna lokutan baya. Idan hakan ya faru na rantse da Allah zan yanke baka ko sisin kwabo…”

“Bama za’ayi haka ba in Allah ya yarda Gimbiya. Maƙiya da mahassada ai sai suyi mana dariya.”

Ya ƙarasa maganar yana aika ma da Mama harara a fakaice.

“Oho! Ni dai na faɗa maka.”

Daga haka bata sake cewa komai ba ta nufi ɗakinta, har ta kusa shigewa ta waigo tana kallon yadda yake cusa kuɗaɗen a aljihunshi jikinshi na tsuma.

Ƙasa-ƙasa taja tsaki ta sake cewa.

“Duk yadda ake ciki a asibitin ka kira ka sanar min. Kuma kar ka kuskura kadawo ka barshi acan, ko da wani uzurin ya taso maka ka sanar min in san yadda za’ayi.

“Angama Gimbiya. Ai ni kin gama da ni tunda kika bani kuɗinnan. Allah yayi miki albarka…”

“Uhmmm! Allah ya kyauta irin wannan rayuwa. Tirrr! Kuyanga ta haifi Uwargijiyarta. Allah wadaran naka ya lalace!”

Mama ta sake yada ma Ƴa da uban habaici a daidai lokacin da ta sake giftawa ta gefensu.

A fusace uban ya buɗe baki da niyyar balbaleta da bala’i da saurin gaske Samira ta katse shi ta hanyar kiran sunanshi da ƙarfi.

Idanunshi ya mayar kanta yana jiran umarninta. Shi kam da gasken gaske Samira ta isa da shi, tunda ta kasance mai yawan faranta mishi da magance duk matsalolin da suka taso mishi. In ba don ita ba, a cikin wannan matsanancin talauci da halin ƙaƙanikayi da yake ciki ya zaiyi da rayuwarsa? A saboda ita yanzu ba ya wata gagarumar wahala, kashi tamanin da biyar cikin ɗari na hidimarshi da ƙannenta huɗu duk ita ke ɗaukewa. Don ma Allah ya haɗa shi da mace mai taurin kai na tsiya, har yau ta ƙi gamsuwa da sahihancin aikin da Sameera ta ce musu ta samu, ai da romon arzikin da za su dinga sharɓa ya ninninka haka…

“Baba, lokaci yana sake ƙurewa. Ka ɗauki Imam ku tafi asibiti, ina sauraren wayarka.”
Da saurin gaske ta bankaɗe labulen ɗakin ta shige tun kafin uwar ta sake yaɓo mata wata mai zafin.

Uban ma da sauri ya kinkimi Imam ya saɓa a kafaɗa, da sassarfa ya fice daga gidan.

Ko da ta shiga ɗakinta ta kasa komawa barci, zama tayi a gefen faffaɗan gadonta ta ɗauki wayarta tana latsawa a hankali. Zuciyarta cunkushe da damuwa, ko kaɗan ba ta gane inda take shige da fice a wayar. Babban damuwarta shi ne yadda rashin fahimta kullum ƙara ta’azzara yake tsakaninta da Mamanta. Bayan kuma ada ba haka bane, duk cikinsu ita ce kamar ƙawa aminiyar shawara ga Mama.

Ta zaci fara samun kuɗinta da ɗaukar nauyin gidan zai ƙara siyo mata soyayya ce ta ko wane ɓangare, eh to bata ce bata samu ba. Ta samu a gurin mahaifinsu da a baya sam bai damu da damuwarsu ba. A gurin Mama kuma maimakon a samu cigaba soyayyar ce take rikiɗewa a hankali zuwa ƙiyayya, har ya zama ko ƙanƙani ba ta ganin ɗigo na son ta a idanun Mama. A aikace kuma tana nuna mata ba ta son ta ba ta ƙaunarta. Kuma duk yadda maman za tayi tana yi don guje ma cin abin hannunta. A fili take faɗa mata baza ta taɓa cin dukiyar hannunta ba tunda har yau ta kasa faɗa mata takamaimai hanyar da take samun kuɗi.

A ɗakinta akwai duk abinda za ta buƙata, tana fara samun kuɗi ta kira masu gini suka rusa ɗakinta, da yake tsakar gidan akwai fili kuma mallakin mahaifinsu ne sai tasa suka ƙara faɗaɗa ɗakin, aka fitar mata da bayi, da kicin, aka ƙara faɗin ɗakin. Da yake akwai kuɗi a ƙasa cikin ƙanƙanin lokaci suka gama. Funitures masu tsada ta zuba kamar mai shirin zama na har abada ba tare da aure ba.

Ganin tunani bazai kai ta ko ina ba yasa ta miƙe a gurguje ta faɗa wanka. Ta san duk inda Rahma take a yanzu tana hanyar zuwa gidan, jiya ta kira Khamis bai ɗaga ba kuma bai biyo kiranta ba, shi yasa ta yanke shawarar fita nemanshi duk inda yake ayau ɗin.

******

“Uwar ruwa tawa ni na Allah. Kwana biyu? ko da yake ni wallahi fushi ma nake da ke, shi yasa jiya ina ganin kiranki naki ɗagawa. Wato ke yanzu kin wuce ajinmu shi yasa ko an neme ki bakya amsa tayi sai sa’adda kikayi niyya ko? To kar dai a manta baya, duk wata ɗaukaka mu ne tsanin da aka fara takawa wajen cimmawa…”

“Kai fa babban matsalata da kai kenan Kham! Ka cika habaici da tsugudidi kamar wani mace. Yawan zama da Big Aunty gaba ɗaya ta lalataka da tsegumi. Yanzu ba ga ni da kaina na nemeka ba? Ni har na isa in ce zan manta Ubana na bariki? Ai ƙarya nake yi wallahi. Ko ka manta kai ne ka janyo hannun Samira idanunta na rufe ka buɗe, sabuwar hanyar da babu wanda ya taɓa bi kabi a sukwane kayi yadda kake so har sai da ka tabbatar ka gamsu sannan ka buɗe ƙofar ga wasu tsamaye suka fara dangwalar ruwan kankanar da ka raɗa mata suna?”

A tare ita da shi suka kwashe da mahaukaciyar dariya. Ba tare da jin kunyar idanun Rahama da take sanye da zumbulelen hijabi ba suka tafa kamar abokai.

“To ya? ita kuma wannan fa? Namu namu ne ko kuwa can ga su gada ne?”
Ya tambayeta idanunshi na kan Rahama sannan ya kashe mata ido ɗaya.

“Wai wannan? Na kawo ta ne ka saka mata albarka. Ka san fa gaba ɗayanmu munyi ittifaki kayan da ka fara saka ma hannu ba ƙaramin albarka da ɗaukaka yake samu ba. Shi yasa na nace lallai kafin fara komai sai mun nemi Babbar harka ya saka tabarraki, wata ƙila ma idan da rabo bayan jin irin kayan ka haɗa ta da wani ƙusa da zai yi mata yayyafin ita da talauci haihata – haihata.”

Wani irin dariya yayi irinta bosawa yana ƙure Rahama da kallo irinta ƙurullah, duk da a cikin zumbulelen hijabi take, mayun idanunsa tuni sun hango mishi abubuwan da yake buƙatar ganinsu. Can kuma sai ya kawar da kai ya ɗan taɓe baki
“Na gani, babu laifi, amma fa yau ba ranar sa’a bace. Ranar laraba da misalin ƙarfe tara na dare ki shirya min ita tsaf ki aje ta a bakin teku.”

A marairaice Rahama ta kalli Samira, idanunta ciccike da hawaye ta buɗe baki da tattausan muryarta mai tsayuwa a zuciyar mai saurare ta ce,

“Kin ji sai laraba ya ce, izuwa lokacin aikin gama ya gama. Gobe litinin da sassafe suka ce in kai kuɗaɗennan idan ba haka ba duk abinda ya faru kar inyi kuka da su…”
Sai ga hawaye sharrrr wasu na korar wasu a idanunta. Da rawar murya sosai mai bayyana tashin hankali da kasancewa cikin ƙololuwar damuwa ta cigaba da cewa
“Ki faɗa mishi ya taimaka min, don girman Allah. Dubu ɗari biyu da hamsin ɗinnan da zan kai musu ran mahaifiyata zan ceta da su. Yau nake so ayi komai a gama gobe in kai musu kuɗin, don Allah…”

Ta cire hijabin jikinta tayi hurgi da shi gefe ɗaya. Doguwar rigar atamfar jikinta da ta fara shan ruwa ta fara kici-kicin cirewa tana cigaba da cewa

“Bari ka gani, ina da komai cikakke da za’a gani ayi sha’awa. Samira ta faɗa min a haɗuwa biyu ma zan iya samun fiye da abinda nake nema, don Allah ka taimaka min, gobe kawai nake da…”

“Ki ce mata kar ta cire rigarta anan, yau ba ranar sa’a bace. Dole sai jibin dai. Amma tunda kuɗaɗen da take buƙata babu yawa sosai Uwar ruwa ki ara mata mana?”

Tun kafin ya rufe baki Samira ta haɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk!
“Ba na son wulaƙanci Kham! Da ace ina da kuɗin da zan iya ranta mata za ka ganmu anan ne? Ba ni da kuɗi. Kai me zai hana ka ranta mata? Daga baya duk hanyar da za ka fanshe kuɗinka ka sani.”

Ta ƙarasa maganar da murguɗa baki.

“Any way! Shi kenan”

Ya ɗage kafaɗunsa alamun rashin damuwa.

“Ni zan bata kuɗin.”

Yana kallon Rahama yaga ta ɗaga hannunta sama tana godiya ga Allah a fili jin abinda ya ce. Wani abu da bai saba ji kan matan bariki bane ya ɗarsu a zuciyarsa, abin ba komai bane face tausayi. A tausashe ya ce

“Ke dai ki riƙe min alƙawari, kar kiga na baki kuɗi kiyi tunanin janyewa daga harƙalla tsakanina da ke. Kin ganni ba ni da kyau, ki tambayi Uwar ruwa za ta faɗa miki wanene Khamis.”

“Na gode, na gode Yaya Khamis! Allah ya saka maka da alkhairi. Yadda ka taimaka min ina roƙon Allah ya taimakeka. In Allah ya yarda za ka same ni mai cika alƙawari.”

“Allah yasa haka. Yanzu ya za’ayi da biyan kuɗin? Babu cash a hannuna. Za muje asibitin ne in biya ko za ki bani acc number?”
“Idan bazan takura muku ba sai muje asibitin ka biya kuɗin. Acc ɗina yana da matsala…”

“Haba Rahama, gatar ai ya miki yawa. Kina dai ganin irin yawon da muka yi kafin na samu nasarar ganin Khamis, ɗan man motar da nasha duk ya gama ƙonewa… Yanzu kuma so kike ki ce in sake kai ki wani asibiti…”

“Kin shiga uku Uwar ruwa. In dai damuwarki ta man mota ce muje, zanyi miki full tank.”
Khamis ya faɗa yana hararar Samira, zuciyarsa cike sosai da tausayin Rahama. A sanyaye yaji muryarta tana cewa,

“Na gode dukanku. Allah ya biya ku da alkhairinsa.”

<< Lokaci 21Lokaci 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×