Skip to content
Part 24 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Da murya mai baiyana tsananin jin daɗi da farin ciki Ogan ya amsa da,

“Da kyau Khamis! Dakyau Yaron kirki, na sani, in dai kana nan baza mu taɓa neman abu mu rasa a jihar kaduna ba.”

“Wannan gaskiya ne Oga.”

Ya amsa da salon kwarzanta kansa, fuskarsa na bayyana jin daɗin yadda Ogan ya yabe shi.

“Madallah! Yanzu zan aiko maka da adireshin gidan hutun da suke so su sauka, da kuma ƴan canjin da za’a sai musu duk abinda zai daɗaɗa musu da na shan man zirga-zirga. Sauran bayanin kuma idan sun zo zaka ji daga bakunansu. Ina fatan mun fahimci juna?”

Gyaɗa kai yayi kamar Ogan na ganinshi, sannan ya amsa da,

“Ƙwarai kuwa Oga, Na gode Allah ya ƙara girma.”

Suna gama wayar ya hau kiraye-kirayen waya ga waɗanda suka dace ga aikin da aka saka shi. Kafin ya gama har Oga ya tura mishi adireshin da kuma maƙudan kuɗaɗen da yayi alkawari. Tsabar murna da ganin yawan kuɗin yasa Khamis ƙwalla ihun murna haɗe da yin alkafira akan gado.

Tsam yayi yana ƙara tunanin yadda zai gudanar da komai cikin ƙwarewa da gwanancewa fiye da yadda Ogan ya buƙata. Tun daga sunan wajen da za su sauka, da kuma kudin da ya gani wai na abinci kawai da zirga-zirga yasan cewa da gaske Oga yake wannan babbar tawaga ce.

Da wuri yayi shirin kwanciya bayan ya gama harhaɗa duk wayoyin da ya tabbatar gobe da safe za su bashi kyakkyawar sakamako na abinda yake buƙata. Tun da ya shige cikin ɗakin ya kulle bai buɗe ƙofa ba, bai ma yi yunƙurin fita ba don ya ji gidan tsit, alamun yaran da uwar gidan duk sun kwanta.

Can wajen sha biyu da rabi na dare yaji cikinshi ya matsa mishi da kukan yunwa, a dole ya tashi ya buɗe ƙofar ya fita falo, daga nan ya wuce kicin.

Ɗan ragowar farfesun naman rago da Ziyada ta bari a cikin microwave ya ɗauka ya zauna a kicin ɗin yana ci, a rayuwarshi yana matuƙar son farfesun naman rago yayi ruwa-ruwa sosai, shi yasa yake ci cikin shauƙi yana kurɓar romon naman.

Yana shan farfesun ya ɗaga wayarsa ya kira Yasmin wacce yake kira da Lolly, tun ɗazu da yake waya da ƴan shilolin da zai ɗora kan aikin gobe take ta kiranshi, katsewa yai ta yi ita kuma tana sake kira, daƙyar ta haƙura bayan ya tura mata saƙon yana cikin muhimmin uzuri ne zai kira ta idan ya gama.

Kamar daman zaman jiranshi take yi, ringin ɗaya, biyu da ɗaga wayar da sauri. Tun kafin ya ce komai ta sakar mishi kukan shagwaɓa tana ƙorafin yanzu ya daina yayinta.

“Daman an faɗa min, duk sa’adda kake ɗokin mace za ka ɗaga darajarta ne fiye da yadda ake tsammani. Idan kuma ka daina yi da ita to za ka yadda ƙwallon mangwaro ne kawai ka huta da ƙuda…”

“Haba Ƴanmatana, haba Lolly pop ɗina. Ni na isa in ce zan daina yayinki? Idan na rabu da ke ta ina zan samu wacce za ta maye min gurbinki? Yanzu dai kiyi haƙuri, na karɓi laifina. Gobe da yamma irin biyar ɗinnan kiyi min wani zazzafan shiri, zan zo in ɗauke ki ki raka ni Birthday ɗin Bobby. Ko da wannan rakiyar ya isa ya tabbatar miki ke ce tauraruwa mafi tsananin haske a zuciyata.”

A can ɓangarenta saboda tsananin murna bata san sa’adda ta saki lallausan dariya mai tafe da shessheƙa na jan hankali ba. Nan ta buɗe baki cikin zazzaƙar muryarta ta fara faɗa mishi irin matsanancin son da take mishi shi ma yana amsa mata da kulawa, tsawon mintuna fiye da ashirin kafin yayi mata sallama bayan ya gilla mata ƙaryar ako wane lokaci wayarsa za ta iya mutuwa saboda rashin caji.

A inda ya gama cin naman nan ya bar kayan ya tashi zuwa cikin falon, har zai wuce ta ƙofar ɗan ƙaramin ɗakin baƙin da Ziyada ta mayar da shi ɗakin barcinta sai ya fasa. Ya tura kofar ɗakin a hankali ya leƙa, sai ya hangeta kan ƴar madaidaiciyar katifar ɗakin har tayi barci. Mayar da ƙofar ɗakin yayi ya rufe a hankali sannan ya wuce ɗaki ya kwanta, da burin gobe da wuri zai bar gidan.

Washe gari kuwa tunda sassafe zakara ya bashi sa’a ya shirya, domin tun da ya dawo sallar asubah bai koma barci ba. Wanka ya shiga, bayan gama ƙalailaita da shiri a nutse ya fito tsaf-tsaf da shi, babu wanda zai kalle shi ya ce shi ne mahaifin Mannira balle Nauwara da ta tasamma zama budurwa.

Lokacin da zai fita yaran ƙananu ko tashi basu yi ba, Ziyada ya samu a kicin tana kokarin haɗa musu abin kari ita da Nauwara da Mannira.

Da fuskar ƙauna da tausayi yake kallonta, sosai yaso ya ɗauko mata mai aiki saboda ta dinga rage mata wasu abubuwan tun ma kafin lamarin zaman auren nasu ya taɓarɓare kamar haka, amma tayi tsalle ta dire ta ce ba ta buƙata. Ta gwammace tayi komai na aikin gidanta da kanta.

Ya tsaya daga bakin ƙofar kicin ɗin yana gyara maɓallan links ɗin rigarshi lokaci ɗaya kuma yana amsa gaisuwar Nauwara da Mannira.

“Ziya zan fita yanzu, akwai wani muhimmin aiki dake gabana yau, don haka idan ba sa’a ba ma zan yini ne a waje. Kila sai yamma sosai ko dare zan dawo, yadda dai ta kaya min. Ayi min addu’a don Allah.”

A kaikaice ta juya tana kallonshi, sai kuma ta mele baki gefe ɗaya. Ciki-ciki can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Allah Ya bada sa’a”

A zatonta ma bai ji ba sai da ya amsa da

“Amin”

Nauwara da Mannira suka bi shi da addu’ar Allah kiyaye. Duka ya amsa musu da fara’a kafin ya fita yana lalubar makullin motarshi a aljihu.

Kai tsaye yana fita daga gida masaukin da bakin za su sauka ya fara zuwa. Sai da ya tabbatar da komai ya tsaru yadda yake so, ya biya kuɗaɗe masu kauri na duk wani abu da za su buƙata na ci ko sha har zuwa sadda za su bar garin sannan ya bar masaukin.

Daga nan kai tsaye mahaɗar da ya ce ko wacce yarinya ta jira shi ya nufa, kallo ɗaya yayi ma shirin da suka yi ya ji gamsuwa sosai a zuciyarsa. Sun haɗe sosai cikin irin shigar da ya bayyana yarintarsu da gogewa a barikanci, irin yadda suka fito shar fiye da yadda ya zata, daman ya san su ba dama ne.

Da irin wannan dirin jikin da shigar da suka yi babu wani ɗan hannu a harkar da zai kalle su bai ji miyaun bakinshi ya tsinke ba. Ko shi ɗin daurewa yayi ya kawar da kai don kar ya tsaya kwantar da ƙwalamarshi ya janyo ma kanshi mishkila wajen caskar maƙudan kuɗaɗen da yake hangen zai samu.

Zuwa lokacin da ya koma masaukin baƙin, motarshi ɗauke take zuƙa-zuƙan yanmatan guda huɗu.

Shi yayi musu jagora zuwa ɗaya daga cikin ɗakunan da aka kama ma tawagar. Zama yayi a tsakiyarsu kamar mace ya sake tunasar da su irin salo-salo na ƙololuwar iskanci da za su tafi da baƙin, ya kuma tabbatar sun gamsu, sannan ya raba su zuwa ɗakuna huɗu da ya kama ma baƙin.

Lambar wayar da Oga ya bashi ya kira, bayan gabatar da kanshi a mai masaukinsu ya ƙara da tabbatar musu komai ya kammalu yadda ake so, suma suka bashi tabbacin suna gaf da isowa gidan baƙin, sannan ya kashe wayar, zuciyarshi cike da addu’ar Allah yasa har a gama wannan harka baza’a sami matsala ba ko kaɗan.

Motarshi ya buɗe ya shiga ya zauna yana jiran ƙarasowarsu.

Yana nan zaune sai ga wasu jibga-jibgan Land Cruiser da Land Rovers suna shigowa wajen, motocin Hillux biyu cike da security kuma suna take musu baya.

Jiki na rawa ya bude motar ya fita. Wanda yake zaton shine chief security ya nufa, ya mishi bayanin ko wanene shi, bayan gama caje-caje da dube-duben jikinshi kamar wanda zai gana da shugaban ƙasa sannan suka ƙarasa tare wajen baƙin.

Saboda tsananin ruɗewa da kwarjininsu Khamis durƙusawa yayi a gabansu yana musu sannu da zuwa. Suka amsa gaisuwarsa a ƙasaice. Bayan sun gaisa, da rawar jiki ya musu jagora zuwa inda aka tanadar musu, har lokacin a zuciyarsa bai tsagaita da addu’ar Allah yasa kar ƴanmatan su bashi kunya ba.

Yana gama nuna musu ɗakunan da ya kama aka mika mishi ambulan cike da kudi da sunan na shan mai a mota. Irin nauyin da yaji ambulan ɗin yayi ya tabbatar ba ƙananun kuɗaɗe bane a ciki. Godiya ya dinga yi kamar bakinshi zai faɗo ƙasa sannan ya ƙara gaba.

Yana shiga motarshi ya kasa haƙurin jira ya fita daga harabar gurin, yage ambulan ɗin yayi don ganin nawa ke ciki?. Hannuwa ya kai ya rufe bakinshi da sauri saboda wani ƙaƙƙarfan ihun murna da ya nemi suɓuce mishi, ambulan ɗin cike take da dalolin Amurka.

Ƴar ƙaramar ihu ya sake a karo na biyu yana dukan sitiyarin motar bakinshi har kunne. Ko kaɗan bai damu da masu wucewa suna kallonshi da mamaki a fuskokinsu ba, dariya yake ta ɓaɓɓakawa, zuciyarshi cike da jinjina al’amarin. Lallai komarshi tayi nasarar kama babban kifi ƙato, luntsumeme irin wanda bai taɓa samun nasarar kamawa ba.

Ya kasa haƙurin yamma tayi kamar yadda suka tsara zai je ya ɗauki Lolly ta raka shi bikin birthday ɗin abokinshi, wayarshi ya fiddo ya kira Kankana, irin wannan maƙudan kuɗaɗe dole ya nemi ƴar sharholiya ta taya shi holewa, amma har ya ƙaraci ringing bata ɗaga ba. Kira uku yayi mata ta ƙi ɗaukar wayar, tsaki yaja ƙasa-ƙasa kafin ya lalubo lambar Ƴar madara.

Yana da lambobin ƴanmata tsoffin hannu da sabbin hannu sun fi ɗari biyar a wayarshi, amma ako wane mataki na harkokinshi yana neman wacce ta dace da gurin ne. Kankana ita ce ƴar sharholiyar da za tayi daidai da cin dukiyar nan, tunda ta ƙi ɗagawa arziki ya wuce ta, shi yasa ya lalubo Ƴar madara, a rashin uwa akan yi uwar ɗaki, ba laifi ita ma za’a je da ita.

Wayar bai daɗe yana ringing ba ta ɗaga da zumuɗi, domin ba kasafai ya cika kiranta ba, ita ce take nacin bibiyarsa. A taƙaice ma sai su shafe wata guda cur in dai ba buƙatarsa ce ta kai da kai ta taso ba bai taɓa kiranta. A hakan dai kuma take bala’in so da kishin shi.

“Ƴar madarata kina ina yanzu?”

Ya jefa mata tambayar a ƙagauce.

“Gani a makaranta Derling, lafiya dai ko…?”

“Ki jira ni a bakin Get, ga ni nan zuwa in ɗauke ki.”

Ya katse ta da faɗin haka sannan ya katse wayar.

A gaggauce ta miƙe daga cikin ajin da bai fi saura minti biyar ba lecturer ya shigo, ƴan ƙananun komatsanta take tattarawa tana turawa cikin jaka. Kham ya tsani jira, shi yasa take sauri-sauri ta isa bakin get tun kafin ya ƙaraso ya fara bala’in ta shanya shi. Ko kuma ma yayi wucewarsa ya bata hutu na wata biyu kamar yadda yai mata kwanakin baya. Sai da tai ta kiranshi tana bibiyar duk inda tasan za ta same shi da kukanta tana bashi haƙuri. Daƙyar Big Aunty ta samu nasarar sasanta su, tun daga wannan lokacin take kaffa-kaffa tare da ƙara riƙe al’amarinsa da muhimmanci.

“Khadija? ina za ki ne haka naga kina tattara kayayyaki?”

Ƙawarta Aliya ta tambayeta da mamaki a fuskarta.

Ɗaure fuska tayi tamau, ta ɗan harari ƙawar kafin ta da,

“Khamis zan gani anan bakin get, yanzu zan dawo…”

“Amma dai kina sane yanzu Dr. Nuhu zai shigo ko? Kuma idan ya shigo babu wata ɗaliba ko ɗalibin da yake bari ya shigo mishi class…”

“Na sani Aliyah! Don Allah ki ƙyale ni. Idan ban samu lecture yau ba ai gobe da jibi ma ranaku ne ko? Ni kinga tafiyata, sai gobe idan mun haɗu.”

Da sauri ta rataya jakarta a kafaɗa ta fice daga cikin ajin ta nufi bakin get, kamar yadda Khamis ya umarceta.

Cikin abinda bai gaza minti talatin ba ya karasa makarantar KASU inda Ƴar madara take karatu. A bakin gate ya hangota sai waige-waigen neman ta inda zai ɓullo take yi, bisa ga dukkan alamu ta daɗe tsaye a gurin.

Yayi fakin a gabanta, da saurin gaske ta bude gefen mai zaman banza ta shiga tana jifanshi da murmushi cike da kissa da salon ɗaukar hankali.

Ainihin sunanta Khadija. Irin yarannnan ne da suka tashi cikin tsananin gata da kulawa da kaunar iyaye. Mahaifinta mai kudi ne sosai, kuma bai cika zama a gari ba. Yayin da mahaifiyarta ta kasance yar bani-na-iya. Ita dai duk abinda ɗanta yake so, to shi take so. Musamman da yaran nata suka kasance su uku kacal duka mata, Khadijar ce kuma karama a cikinsu.

Tunda Allah Ya ɗaura idon Khamis a kanta shekaru biyu da suka wuce, shikenan. Ya dinga bibiyarta har sai da ta amince mishi. Tana matuƙar son shi kamar tayi hauka, kuma tsakaninta da Allah aurenshi take so tayi. Shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yana juyata yadda yake so kamar waina a tandar mai shi. A kullum yana gilla mata ƙaryar shi zai aureta, tunda kuwa shi zai aure ta babu aibu don yayi yadda yake so da kayan da ya rage ƙiris ya zama mallakinsa.

Darussan da bata samu halarta ba kenan, domin ɗaukarta yayi suka shiga gari wajajen shaƙatawa da cin abinci. Daga ƙarshe dai suka dangana da wani gidan gonar abokinshi suka yada zango anan. Yini guda cur suna tare suna sheƙe ayarsu yadda suke so. Sai gaf da magriba sannan ya maidata gida, nan ma sun daɗe suna hira da ita a cikin motarshi, da ƙyar suka rabu tana zuba mishi shagwaɓar bata son su ya tafi, shi kuma ya rarrashe ta da cewa tayi hakuri, nan da ɗan lokaci kaɗan za ta tare a gidanshi ma gabaɗaya su huta da wannan tamɓele.

Maganar da ta faranta mata rai kenan suka rabu tana ta wage baki.

Bayan sun rabu ya ɗauki hanyar komawa gida. Tukinshi yake cikin nishadi da annashuwa, yana kallon yadda Lolly ke ta kiranshi amma ya ƙi ɗagawa, daga ƙarshe ma ya danna wayar a silent yaba banza ajiyarta.

Yinin yau yayi shi cikin farin ciki da annashuwa ƙwarai da gaske, lokaci bayan lokaci yana saka hannu ya buɗe aljihun gaban motar ya kalli envelop ɗin dalolin nan. Ga kuma yadda Ƴar Madara ta yini tana tarairayar da salo-salo na soyayya iri daban-daban, ko sisi bai bata ba, don ita ba kuɗinshi bane a gabanta. A mafiyawancin lokuta ma ita ke kashe mishi maƙudan kuɗaɗe.

Kamar an ce ya kalli fuskar wayarsa, wani mummunar bugawa ƙirjinshi yayi, lokaci ɗaya zuciyarsa ta ɗugunzuma, hankalinsa ya tashi, cike da tsoro da fargaba yake ƙara gwalalo idanu yana kallon sunan Yaya Yusuf da yake yawo a fuskar wayar.

<< Lokaci 23Lokaci 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×