A fusace ta miƙe tsaye daga zaunen da take tana cewa,
“Ƙarya kike yi wallahi kawata! Sai dai in baza ki faɗa min ba. Amma taya za’ayi haka kawai rana ɗaya kiyi irin wannan magagan arzikin bayan ba ruwan kuɗi ake yi daga sama ba? Sannan kuma ba tsintarsu ake yi a ƙasa ba?
Amma tunda haka kika ce, na kula akwai zamba cikin aminci a tsakaninmu. Talaucin da yayi min rumfa yasa kin fara guduna, kina so ki nuna min yanzu kin daina yi da ni. Ba komai, ni ce har zan nemi wani abu a wajenki ki kasa yi min, na gode.”
Tayi narai-narai da fuska alamun gaf take da fashewa da kuka. Murya a sanyaye ta cigaba da cewa,
“Sai yanzu kuma na ƙara fahimtar abinda ƙawancenmu take nufi a wajenki”
Gefen hijabin jikinta ta kama ta goge ƴan ƙananun ƙwallar da suka cika mata idanu. Rai ɓace ta juya za ta fita daga sabon ɗakin da aka gyarawa Samirar.
Da saurin gaske ita kuma ta kamo hannunta ta zaunar da ita a gefen faffaɗan gado ɗan Italiya da aka saka a ɗakin. Da muryar rarrashi ta fara magana fuskarta cike taf da murmushi.
“Haba ƙawata, daɗina da ke saurin harzuƙa bayan kin san ni da ke bata ɓaci. Kwantar da hankalinki ki saurareni da kyau, yau dai zan fayyace miki gaskiyar zare da abawa”
Tiryan-tiryan ta bata labarin irin harkar da take yi ba tare da ta ɓoye mata komi ba, da irin samun da take yi a harkar, wanda shi ne ma har yayi sanadiyar arzikinta lokaci guda bayan Allah Ya haɗata da wani dan majalisa yana kashe mata kuɗi kamar bai san zafinsu ba.
Bata kuma tsaya wata kwana-kwana ba ta yiwa Rahma tayin ta shiga harkar itama, cikin hikima da salon iya magana ta dinga kwaɗaita mata irin arzikin da zata yi cikin ƙanƙanin lokaci, za ta taka duk jihar da take so a faɗin nigeria da ƙasashen ƙetare.
Rahma shiru tayi ta kasa magana, baki da hanci buɗe take kallon Samira. Zuciyarta cike da saƙe-saƙe da mamakin irin aikin da ƙawar tata ke yi. Amma da ta ƙara zurfafa tunani ta wani ɓangaren bata yi mamaki ba, don kuwa dama can Samira mayyar kuɗi ce, kuma kwaɗayayyiya ce ta bugawa a jarida.
Tun suna yara ƙanana ta sha kamata a shagon Isiya mai provition na unguwarsu suna abinda ba dai-dai ba yana sallamarta, kawar da ido kawai tayi ta rufe bakinta tunda ita ma tana ɗan lasa mata cikin abubuwan da yake bata.
A lokacin da suke makarantar sakandire kuma an sha yaɗa zargin cewa Samirar yar Lesbian ce. Amma bata taɓa yarda ba tunda ita dai bata taɓa nuna mata wani alamu da zai tabbatar mata ga abinda take aikatawa ba.
Sai a yanzu da Samirar ta faɗa mata da bakinta bayan harkar bin maza har matan ma suna ɗan taɓa raƙashewarsu. Jikinta ne yayi sanyi ƙalau, sai kallon Samirar take yi ita kuwa ko a jikinta.
Haka suka rabu ba tare da ta bata wani gamsasshiyar amsa kan za ta bi layin da take bi ko kuma za ta ci gaba da juyi cikin talauci da ƙangin rayuwa? Tsawon kwanaki bakwai ta kwashe cikin tunani a ƙarshe dai ta yanke ma kanta shawarar baza ta zubar da mutuncinta kan wani abin duniya fararre ƙararre ba. Daga baya ta watsar da tunanin komai ta cigaba da harkokinta. Tunda ba laifi itama tana ɗan samu ta hannun Samirar, tana taimaka mata da ƴan ƙananun abubuwa, tsaffin suturu waɗanda a gurin Rahma sabbi ne kar da abinci na kwaɗayi wanda Allah ya tsaga da rabonta duk tana bata, wani lokacin har ma da ƴan kudade musamnan idan jarinta ya karye saboda rashin lafiyar da Iyallu take fama da shi.
Ita ma Samirar bata takura mata ba, amma dai ta ci gaba da mata rijiya ta bayan fage. Duk sa’adda suka zauna a fakaice take nuna arziki fa ya fi talauci, kuma a wannan marrar babu wata sassauƙar hanya da za tabi tayi arziki lokaci ɗaya illah wannan hanya da take kai.
Abinda ya jefa Rahma cikin wannan mawuyacin halin a yanzu shi ne da rashin lafiyar Iyallu ta tsananta aka kaita asibiti, inda kai tsaye suka ce ƙodarta ce ta samu matsala. Suka kuma bukaci zunzurutun kudi har naira dubu dari biyu da hamsin, ita kuma bata da su bata da hanyar samunsu. Gidansu ma da suke zaune wani akurkin wajene da aka bar musu gado, bata tunanin ko sayar da shi zasu yi zai kai kuɗin da ake buƙata.
Daga farko so tayi Samira ta ranta mata, ita kuwa a lokacin ta shafawa idonta toka tace mata bata da su.
A tunanin Samirar, ta yaya za ayi kura ta sha bugu gardi ya kwashe romon? Ita taje ta sayar da jikinta ta samu kuɗi, ita kuma da ta killace nata jikin ta kwashe romon kuɗin? Ai ba zai yiwu ba.
Ɗaure fuska tayi tamau ta fito ƙarara ta nuna mata kawai ta bada kai bori ya hau in dai tana son biyan kuɗin maganin mahaifiyarta.
“Ki saurare ni dakyau Rahma. Ranar wanka ba’a ɓoyon cibi. Nima fa kuɗaɗennan da kika ga ina wadaƙa da su ba bani ake yi a kyauta. Saɓatta juyatta ake yi kwatankwacin bani gishiri in baka manda. Don haka a wannan gaɓar ina mai baki haƙuri wajen sanar da ke bani da wani taimako da zan iya miki. Idan za ki nemi kuɗi da jikinki sai inyi miki hanya sassauƙa a fita biyu ko uku za ki iya samun fiye da abinda kike nema.”
Ta ɓata lokaci sosai tana hure mata kunne tare da tsoratata da cewar idan kuma gawar Iyallu take buƙatar gani to ta tsaya sanya har kwaɗo yayi mata ƙafa.
Daga karshe dai ganin ba ta da yadda za tayi a dole ta amince akan zata shiga harkar. Mafarin haɗuwarta da Khamis kenan har yayi mata taimakon da ya mata akan sharaɗin ranar laraba zasu je ta fara biyanshi kuɗaɗen da ya kashe mata. Tun da aka yi aikin Iyallu cikin nasara da wannan taraddadin take kwana tana tashi.
Hankalinta a tashe yake sosai. Ita dai duk talaucinta bata taɓa aikata wani aiki makamancin wannan ba. Allah ya sani lamarin ko sha’awa bai bata. Amma yadda Samira ta dinga kwaɗaita mata da kuma shirin da ta dinga mata cikin ƴan kwanakin da magunguna iri-iri yasa lokaci bayan lokaci take ɗokin itama ta ƙunduma ciki ko za ta ɗanɗani irin lagwadar da Samirar ke faɗin bayan samun kuɗi akwai a cikin harkar.’
Lokacin da taga kiran wayar Khamis ya shigo mata, sai da taji ana ta mata wani luguden daka a kirjinta. Ji take kamar tayi gina a ƙasa ta shige ciki, ko kuma ta shige bayan Iyallu da barci ya fara ɗaukarta ta ɓuya, ko Allah zaisa Khamis ya hakura ya ƙyale ta.
Lokaci ɗaya zafafan hawaye suka ɓalle mata, tayi gabas tayi yamma sai ta tsaya cak a tsakar ɗakin tana shatatar hawaye.
Ta sani, kowa yaci ladan kuturu dole yayi masa aski. Sannan kuma Samira ta ɓata lokaci tana feɗe mata wanene Khamis da irin halayensa na taƙadaranci, idan har abinda Samira take faɗa mata gaskiyane, ko ƙasa ta bakwai za ta shiga ta ɓuya sai ya bita ya zaƙulota.
Ƙarfin hali ta ƙarasa kusa da Iyallu ta tashe ta, sama-sama ta fada mata za ta koma gida, kuma acan zata kwana saboda sana’arta, amma ta biya wata nas za ta dinga kewayawa tana dubata tunda babu wanda zai tsaya tare da ita.
“Kiyi haƙuri Iyallu, kuɗin hannuna sun ƙare tas! Dole in ɗanyi sana’a ko ta gobe ce kawai don mu samu na ɓatarwa. Ko kina buƙatar wani abu kafin in tafi?”
Da saurin gaske uwar ta girgiza kai alamar a’a. Ta ƙara da yi mata godiya da sanya albarka, har tana jaddada mata lallai ta kulle ƙofar ɗakinsu da wuri tunda ita kaɗai ce za ta kwana a gidan. Haka ta fita daga ɗakin jiki a sanyaye bayan ta amsa da to.
A bakin asibitin ta samu Khamis cikin motarshi yana jiranta. Ta buɗe gefen mai zaman banza ta shiga tana gaidashi, muryarta ƙasa-ƙasa.
Wani shegen kallon ƙurilla yake jefa mata kamar wani tsohon maye. Riga da siket ne a jikinta waɗanda suka ɗan kamata, ire-iren shigar da Samira tace tayi kenan a ranar. Duk da cewa ba mayafi bane a jikinta, amma da yake hijabinta roba ce, ta bi jikinta ta lafe, ana ganin duk wani abu na jikinta.
Wani kakkauran miyau ya haɗiya muƙut. A fili ya dinga yabon halittarta, don kuwa ba ta da wata makusa ta kowane ɓangare. Wai ma don a hakan bata gama sanin darajar jikin nata ba da kuma yadda zata yi amfani da jikin nata ta samu abinda take so.
Ire-iren maganganu da kamalan yabo da yake watsa mata sune suka ɗan kwantar mata da hankali har suka ƙarasa masaukinsu.
Wani gida a can cikin GRA da bata taba ganin kwatankwacinshi ba a tsayin rayuwarta.
Tun daga gate ɗin gidanma kaɗai za’a san cewa ba ƙananun Naira aka narka ba wajen gini da ƙayata gidan, kai hatta da abin ban ruwan fulawoyin da aka yiwa kofar gidan kwawanya dasu na zamani, bata taɓa ganin irinsu ba.
Bata ƙara tsinkewa da kyawun gidan ba sai da suka shiga farfajiyar gidan. Taga wasu danƙara-danƙaran motoci BMW da sports car Audi da bikes da wasu abubuwan ma da bata san amfaninsu ba, sai taji ta kara tsinkewa da lamarin waɗannan mutane.
Sun ɗan jima a cikin motar yana ƙara koya mata dabaru da kisisina kamar wata mace.
“Nutsuwa fa zaki yi sosai kin gane? Ki saki jikinki. Shi gayenne ya faɗa min ya fi son sabon shiga a harkar shi yasa na kawo ki. Idan kika saki jikinki ta haka ne kawai zaki samu abinda kike so cikin lokaci ƙanƙani. Idan yaga kina ɗari-ɗari sosai duk da ke sabon shiga ne tuni zai sallama ki ba tare da wani abin arziki ba. Kin gane abinda nake nufi?”
Ta gyada kai a tsorace.
Yayi ɗan murmushi,
“Yauwa Baby, haka nake son ji! Idan kin shiga, kiyi saurin cire wannan hijabin, saboda ina so ya ga lallai fa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, ki rikita mana shi da kyau ya zamana ya kasa gane gabas balle yamma… Wannan ƙirar taki ni idan ni ne ke sai dai Allah Ya kiyaye ɓarna, amma wallahi ba ƙaramin haɗa kashi zannyi ba. Ta ko wane ɓangare kin haɗu ne ƴanmata! Zubinki da tsarinki ai irin na matan manyane! Nan gaba kaɗan ai sai kinfi ƙarfin waɗannan ƙananun ƙwarin, ina faɗa miki sai dai Sarakai da gwamnoni!!”
Da irin wannan hilar ya samu ya ƙara fasa mata kai. Ƴar shakka da tsoron da take ji tuni ta sauka daga kanta, ta saki jikinta sosai tana ɗaukar duk irin karatun da yake biya mata.
Waya ya kira ya sanar da cewa sun iso, bata san me aka ce ba, kawai dai taji yana amsa da,
“To.”
Yana katse wayar ya juya ya sanar da ita ta fita su ƙarasa. Shi da kanshi ya kai ta har cikin gidan, ya damƙata a hannun wani kyakkyawan matashi da yake zaune suna shan shisha shi da abokanshi sannan ya fita daga falon.
*******
Washegari ƙarfe sha biyun rana ya koma zai ɗaukota, daman kwana ɗaya za tayi a gurin. An biya shi kuɗin sallamarsa tun kafin ma ya kaita gidan. Sannu a hankali ya gangara kan motarshi zuwa farfajiyar gidan. Wayarshi ya ɗauka ya kira Rahma ya sanar da ita yana jiranta a waje.
Ta amsa mishi ga ta nan zuwa. Amma wani abin mamaki shi ne shiru-shiru yana zaman jiranta fiye da mintuna talatin, har ya fara gajiya, ya ja tsaki a karo na kusan biyar tare da janyo wayarshi da niyar ya sake kiranta, sai yaga an buɗe ƙofar an fito.
Rahma ce, gefenta kuma wani kyakkyawan matashi ne saɓanin wanda ya damƙa ta a hannunsa jiya, yana maƙale da ita. Bai yi mamaki ba da ya ga matashin yaro ne sosai, watakila ma idan aka bibiya da kaɗan ya girmi Rahama. A harka irin tashi ba ya tunanin akwai wani abu da zai gani wanda zai girgiza shi nan kusa.
Da ganin fuskar yaron ya fahimci ɗan gidan kuɗi ne, jinjina kai yayi. A zuciyarsa yake ayyana lallai Rahma ta shigo da ƙafar dama, yasan ba ƙaramin samu za ta yi ba, yara irin waɗannan kashe kuɗi a banza kawai suka iya domin basu san zafin neman ba, an riga an tara musu.
Yana kallonsu sai da saurayin ya gama rirriƙeta yana aika mata da sumbata ta ko wane ɓangare kafin ta ɓamɓare jikinta daƙyar, shi kuma matashin ya damƙa mata wata ƙaramar jaka kamar irin wadda ake rabawa souvenir a wajen biki, ko bai duba ba yasan ko menene a cikin jakar.
Daƙyar suka rabu ta fara takowa sannu a hankali tana cije leɓe har ta ƙaraso kusa da motarsa, shi kuma cike da zumuɗi ya buɗe mata ƙofar motar ta shiga ta zauna, ya ja suka tafi ba tare da ya tsaya jan dogon zance ba ko nuna mata ɓacin ran shanya shi da tayi wajen jiran fitowarta ba.
Yana tuƙi yana satar kallonta yana karantar yanayin da take ciki. Akwai alamun gajiya da wahala a tare da ita sosai, amma kuma duk da haka murmushin yaƙe ne shimfiɗe akan fuskarta tana ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki.
“Akwai zafi ko? Ko in kaiki asibiti likita ya duba ki?”
Ya tambayeta da kulawa a fuska da muryarsa.
Narai-narai tayi da idanu sannan ta amsa da,
“A’a! Likita ya duba ni acan, kuma an bani magunguna. Kawai dai rashin sabo ne, zafin kaɗan ya rage.”
Ganin haka yasa ya fara tsokanarta da magana,
“a’ah! Kaga manyan mata Hajiya Rahama da kanta! Wannan wage baki haka da fara’a? Da alama dai ta samu da yawa ko?”
Ita kuwa ta saki baki tana wangala dariya tare da warware mishi duk wani abu daya wakana.
“… don Allah fa? Da gaske yanzu yaronnan dan gidan Alhaji Kanta ne?”
Ta gyada kai cikin wani irin farin ciki da rawar kai, “wallahi kuwa! Ni kaina nayi mamaki sosai. Ba a nan kasar yake zaune ba shi yasa, a Moscow yake. Yanzun ma hutu ne yazo yi. Amma yace kafin ya tafi zamu dinga haduwa. Kaga har lambar wayarshi ya bani!”
Kai kawai yake jinjinawa cikin mamaki, “maganar gaskiya Rahma kin shigo cikin harkar nan da kafar dama wallahi. Ni dama naji a jikina, ai na fada miki ranar laraba ranar sa’a ce da nasara.”
Itama ta gyada kai tana murmushi.
Yace, “wannan yaron kiyi kokari ki rikeshi da kyau wallahi. Idan Allah Ya tarfawa garinki nono, sai kiga kafin ya koma kin kama gidan kanki da mota!”
Idanu ta zare har da dafe kirji, “don girman Allah fa Yaya Khamis?”
Yayi dariya cike da duniyanci, “ina fada miki. Ke irin wadannan mutanen fa ba na wasa bane. Harka dasu mugun daga darajar mutum take yi!”