Skip to content
Part 27 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Wayyo Allah naaa… Allah na gode maka.”

Ta faɗa da dariya da wani irin murya mai bayyana ta kai ƙololuwar jin daɗin maganganunsa a zuciyarta. Sai ɗan jujjuya kai take yi dama da hagu irin daɗi ya mata yawa, idanunta a lumshe. Babu abinda take hange ƙarara a cikin idanunta sai ga ta cikin lokaci kaɗan ta zama big girl, har ma fiye da Samira. Ta mallaki ƙatoton gida na gani a faɗa, tana hawa manyan motoci tana taka duk ƙasar da take so a lokacin da take so.

Tuni duk wani danshin da-na sani da take ji a zuciyarta ya kama gabansa. Duk wani ciwo da take ji a jikinta na farin shiga tuni ta neme shi ta rasa. Shaiɗan ya samu gurin zama rashe-rashe a zuciyarta, babu abinda take hange sai daula da ɗaukakar da wannan harka zai janyo mata.

Tana wannan tunane-tunanen fuskarta cike da murmushi har bata san sa’adda Khamis ya ƙarasa unguwarsu ba.

Can nesa sosai da gidansu ya samu waje yayi fakin ɗin motar inda babu gilmawar mutane sosai. Ba tare da fargaba ko shakkar komai ba yasa tafin hannunsa ya shafo gefen fuskarta don dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.

“Hey.. Mun zo fa. Tunanin me kike yi haka tun ɗazu sai murmushi kike yi?”

“Uhmmm! Kai dai bari Yaya Khamis! Ka san halin zuciya da jaye-jaye, hango ni nake a cikin kwanaki ƙalilan na mallaki wasu maƙudan kuɗaɗe da ko a mafarki ban taɓa tunanin samunsu ba.”

A tare su biyun suka ƙyalƙyale da dariya. Cike da duniyanci ya miƙa mata hannu suka tafa kamar wasu ƙawaye.

“In dai za ki dinga ɗagawa dakyau ana bugawa za ki mallaki abinda baki taɓa tsammani ba. Bariki ce fa, alalen gero nake faɗa miki idan kin iya ta miki dakyau idan baki iya ba ta kwaɓe miki cikin ƙanƙanin lokaci.”

Dariyar suka sake yi. Jakar da aka bata ya ɗakko ya zazzage kuɗaɗen ciki a jikinta. Ko da suka ƙirga dubu ɗai-ɗaya har dubu ɗari biyar cass ke cikin jakar.

Wani irin ƙaƙƙarfan ihun murna Rahma ta saki saboda farin cikin da ya sake lulluɓeta. Cikin kwana ɗaya kacal aka yi mata wannan kyautar bayan uban ciye-ciye da shaye-shayen kayan daɗi masu bala’in tsada da tayi ina ga ta kwana uku? Kenan idan tayi sati ɗaya lissafin kuɗaɗen da da za’a bata bazai yiwu a yini ɗaya ba.

Ta buɗe baki za ta sake sakin ihu da saurin gaske Khamis yasa hannu ya toshe mata bakin, duk da gilasan motar tasa masu duhu ne kuma a rufe suke sai waigawa yake yi kar azo ihunta na farko ya janyo hankalin mutane kan motar ayi musu wani tunani na daban.

“Ke! Miye haka kike yi? Kina so ki janyo min duka a gurin ƴan unguwa ne?”

Ya faɗa hankalinsa a ɗan tashe, har lokacin bai daina waige ba.

Sai a lokacin ta dawo cikin hankalinta ta tuna a ina suke? Daƙyar ta iya daidaita kanta amma har lokacin fara’a bai bar kan fuskarta ba.

“Yi haƙuri Yayana. Ka san abinka da ba-saban-ba. Wallahi ban taɓa riƙe dubu hamsin tawa ta kaina a lokaci guda ba, yau kam na riƙe dubu ɗari biyar dumus tawa ta kaina ai dole inyi ihu. Da wata mai ƙaramar ƙwaƙwalwarce ma ai zarewa za tayi.”

“Ke na faɗa miki waɗannan kuɗaɗen fa ba’a bakin komai suke ba. Nan da lokaci kaɗan in dai kin iya takunki za ki mallaki ninkin ba ninkin ɗin su. Don haka ki koyi nutsuwa da ganin manyan kuɗaɗe, kar ki kuskura ki dinga nuna ƙauyanci da maitar son kuɗinki a fili, ko da kuwa a gaban Samira ne da ta san wacece ke a baya. Kin gane?”

“Na gane.”

Ta amsa tana jinjina kai alamar gamsuwa.

“Good girl. Once again ina ƙara taya ki murnar shigowa da ƙafar dama. Ba kowa ke taka irin sa’ar da kika yi ba.”

“Na gode Yayana. Bazan manta da kai ba. Allah yabar zumunci a tsakaninmu.”

“Ameen”

Ya amsa fuskarsa yalwace da murmushi.

Idanunta ta mayar kan kuɗaɗen da suke zube a cinyarta, a nutse ta ƙirga kuɗaɗen da ya bata aro ta miƙa mishi, sannan ta ƙara da dubu hamsin daban ta miƙa mishi.

“Ga wannan Yaya Khamis, kuɗin da ka ara min ne. Wannan kuma dubu hamsin ne, kayi haƙuri da shi, ka ga kuɗaɗen da suka rage babu yawa.”

Ta ƙarasa maganar a marairaice tana shagwaɓe fuska. Samira ta faɗa mata tayi hankali da Khamis, mutum ne mai bala’in wayau, zai iya karɓe kaso casa’in na kuɗaɗen ya barta da kaso goma, shi yasa tun kafin ya kawo wani ƙabli da ba’adi tayi saurin miƙa masa dubu hamsin bayan biyan bashinsa.

Amma ga mamakin da ya shayar da ita ya barta da buɗewar baki na tsawon wasu daƙiƙu shi ne cewa da yayi ta bar kuɗaɗen gaba ɗaya. Kuɗin asibiti kyauta ya bata, kuma bazai karɓi ko sisi a cikin abinda ta bashi ba.

“Ni dai kawai abinda nake so shi ne, a cikin kwanaki bakwai da zan baki hutu nan gaba kiyi ƙoƙarin siyan mai da duk wasu kaya na gyaran jiki ki gyara fatarki ta sake fitowa tas, jikinki ya ƙara laushi da sulɓi, ki kuma sayi suturu masu kyau da ɗaukar hankali, ki dinga cin kayan kwaɗayi masu gina jiki waɗanda zai sa a cikin ƙanƙanin lokaci ki amsa sunan Babbar yarinya. Kin gane abinda nake nufi?”

Har lokacin mamakinsa bai gama sakinta ba. Don haka ta kasa magana, sai kai da ta ɗaga masa kamar wata wawuya. alamun ta gane abinda yake nufi.

Yadda ta saki bakin tana bin shi da kallo ne ya saka shi ƙyalƙyalewa da dariya. Ya san me take tunani, ya kuma san mamakin da take yi. Shi da Samira kar ta san kar ne, ya san duk wasu munanan maganganu da za ta iya faɗa ma Rahma a game da shi, shi yasa yayi wannan takun don goge duk wani baƙi da Kankana za ta goga mishi a gurin Rahma. Kuma ya tabbata daga wannan taku da yayi haƙarshi ya cimma ruwa…

Cikin nutsuwa ya tattara mata kuɗaɗen gaba ɗaya ya mayar cikin jakar, ya gyara mata zaman siririn gyalen kanta da ya zame zuwa kafaɗunta.

“Kije ki huta Beby. Sai munyi magana.”

Har ta kama ƙofar motar za ta buɗe sai ya dakatar da ita ta hanyar cewa

“In baki wata shawara?”

Nan ma dai kai ta ɗaga mishi.

“Kar ki kuskura ko da wasa ki faɗa ma Kankana yawan kuɗaɗen da aka baki. Ki rage yawan kuɗin sosai, ki ce mata basu ma isa ki biya ni bashi na ba shi yasa kika roƙi alfarmar in ɗaga miki ƙafa zuwa gaba. Kin gane?”

“Eh”

Ta amsa da bakinta.

“Kin san me yasa nace miki haka?”

Ya tambayeta.

“A’a”

“A irin wannan harkar tamu babu amana. Ko ciki ɗaya kuka fito da mace kar ki kuskura ki bata amana, idan ba haka ba za kiyi kuka da idanunki.”

Kai ta gyaɗa mishi. Ta ƙara da cewa

“Na gane! Tabbas na gane!!”

A karo na biyu suka sake yin sallama, ta fita daga motar ta nufi hanyar gidansu. A ƙasan ranta take ƙara warware bayanin da yayi mata filla-filla, tana jin gamsuwa da maganganunsa ɗari bisa ɗari fiye da ma Samira da ta kasance aminiyarta tun na yarinta.

Sama-sama ta dinga amsa gaisuwar masu mata ya mai jiki? a haka har ta ƙarasa cikin ɗan akurkin gidansu, ta yiwa kudinnan wawan ɓoye da ko an shiga gidan baza’a taɓa tsammanin akwai maƙudan kuɗi a ajiye ba, Dubu hamsin ta cire kawai.

Wanka ta sake yi ta gasa jikinta sosai sannan ta shirya tsaf ta yiwa gidansu Samira tsinke. Tayi sa’a gidan babu kowa, don haka suka shige can kuryar ɗaki suna maida yadda aka yi.

Bayan ta gama maida mata yadda aka yi, ta gilla mata ƙaryar dubu ɗari biyu kacal aka bata, ta ba Khamis dubu Hamsin kyauta. Ta sake gyara zama, ta kalleta fuska ɗauke da alamun damuwa tace

“Ni yanzu babbar damuwata ita ce me zan cewa Iyallu? Kin san dai idan ta ganni da kuɗaɗe rana ɗaya ina harkokina dole za ta ɗiga min alamar tambaya. Ni kuwa har ga Allah yadda na fara jin dumus ɗin nan, ba na jin akwai wani abu da zai saka ni yin rivas daga hanyar da kika ɗora ni. Sannan yadda na ɗanɗani zafin talauci ba zan iya ɓoye-ɓoye wajen kashe kuɗi ba gaskiya, burina nima in fara fantamawa kamar yadda kike yi.”

Samira ta kwashe da dariya ta bata hannu suka tafa

“Shgiyata ƙawata! Wato sai yanzu ne kika gane karatun da na shafe tsawon shekaru ina biya miki. Talauci fa bala’i ne daga shi sai kafirci. Amma dai ki kwantar da hankalinki. Wannan ai duk ba wata matsala bace da zai hana ki chilling.

Kinga, Kawai ki ce mata wannan mutumin da ya taimaka mata ya biya kuɗin aikinta shi ya miki hanya kika samu bashin gwamnati kika kafa jari, ko kuma kice mata shi ya ara miki kawai ki fara babbar sana’a”

Rahma shiru tayi tana tunani, sai kuma ta hau gyaɗa kanta tana murmushi
“Kwarai wannan shawara taki tayi, kuma haka za ayi. Amma zan dai ce mata bashin gwamnati na samu kawai, kin san irin abun nan sai mutum ya iya taku, a faɗi abinda duk yadda za’aje azo baza’a kwana a ciki ba. Kin dai gane ai?”

Ta ƙarasa maganar haɗe da kashe mata ido ɗaya. Dariya suka yi haɗe da tafawa.

“Yauwa! To yanzu dai tunda kin bada kai bori ya hau, zan gabatar dake a wajen uwar ƙungiyarmu.”

Cike da alamun tambaya Rahma take kallonta, da mamaki sosai a fuskarta ta ce,

“Uwar ƙungiya? Wacece kuma uwar kungiya?”

“Kar ki damu, wannan kungiyar ita zata baki cover ki dinga duk abinda kike so kuma kika ga dama ba tare da wani ya zargeki ba. Kinga ke zaki iya fakewa da sana’ar kayan gwanjo ko wani abu haka dai, ki tafi kije kiyi neman kuɗinki cikin salama. In yaso idan kin dawo ki kwashi kayan gwanjonki ki dawo gida kice sarin kaya kika je. Kinga kin ƙara samun lulluɓi babu wanda zai zargi abinda kike yi ta ƙarƙashin ƙasa ko?”

Rahma ta gyada kai,

“Gaskiya kawata wannan shawarar taki tayi! Na kuma gode miki sosai da sosai, Allah Ya ƙara mana danƙon zumunci.”

Fari da idanu tayi kafin ta amsa da

“Ameen dai Ƙawata”

Kuɗin da ta je da su gidan ta ɗauko a cikin jaka, ta zare dubu goma a ciki ta miƙawa Samira Arba’in ɗin tace,

“Ga wannan ƙawata, kiyi haƙuri ba yawa. Ko mai kya zuba a mota.

Babu kunya ta amsa tana mata godiya, fuskarta yalwace da fara’a take cewa,

“Banda abinki ƙawata har da wata hidima ta daban bayan wadda ke gabanki?”

“Kin ji ki da wata magana, Idan da ba don ke ɗin ba ma ta yaya zan samu waɗannan kuɗaɗen? Ai ni dai tsakaninmu sai godiya da fatan alkhairi.”

“Ba komai Rahma. Yanzu dai bari in shirya a gurguje muje gurin Iyallu daga can kuma sai mu je ki ga uwar Ƙungiya!”

Cikin mintuna sha biyar ta gama shiryawa, suka ɗunguma a motar Samira suka tafi asibitin. Ko kaɗan ba ta cikin damuwa da barin asibitin tun jiya, ta biya wadatattun kuɗin da za’a kula da uwar. Har zuwa wannan lokacin da ake daf da kiran sallar la’asar wancan nurse ɗin da ta ba kuɗi bata tafi gida ba, ita da ya kamata ace tun safe ta koma gida amma saboda kuɗin da aka bata tana asibitin tana kula da Iyallu. Shi yasa hankalinta kwance yake kamar tsumma a randa.

Sai da suka tsaya a shago ta yiwa Iyallu sayayyar kayan buƙata, kayan shayi, lemuka da tarkacen abubuwan da ba lallai ta ci ko tasha ba.

Suka tsaya a wani gidan abinci ta sai mata naman kai da ya dahu ruguf da sakwara miyar egusi kafin suka yiwa asibitin tsinke.

Iyallu rikicewa tayi da ganin ganimar da aka loda a gabanta. Ta sanya naman nan a gaba da sakwara duk uban yawanshi sai da ta cinye tas ta suɗe robobin take away.

Ta karbi kwalbar lemun pulp mai sanyi da Rahma ta mika mata shima ta kwankwaɗe tas, ta saki wata doguwar gyatsa kamar wadda ta tada ƙaton rago.

Sai lokacin take tambayar su Rahma inda suka samu kuɗin wannan uban hidima da suka lodo mata.

Nan Rahma ta karkace kai ta dinga kora mata bayanin yadda aka yi wanda ya taimakesu ya tausayawa halin da take ciki, shi ne ya mata hanya aka bata bashin gwamnati domin tayi jarin sana’a na kanta ba rance ba.

“Ai shi yasa kika ga tun safe ban samu zuwa ba. Tun da sassafe muna can tare da Samira sai yanzu aka gama ciccike takardu aka damƙa min kuɗin. Bayan komawarmu gida wanka kawai muka yi muka taho nan.”

Daɗi ya yiwa Iyallu yawa, ba kuma tare da tsaurara bincike ba ko tambaya ba, ta hau sambaɗawa Alhaji Hamisu albarka, da Samira wacce ko da yaushe ba ta gajiya wajen ɗawainiya da Rahma.

A fili take ta jero addu’o’i kan Allah yasa ma sana’ar Rahma albarka, ita ma ta bata jarin kanta kuma tayi kokari ta canza musu gidan zama daga ƙuntatacce zuwa wadatacce.

*******

“Wawww! Yarinya tayi Meerah. A ina kika samo wannan daƙwalwar?”

Wata ƙatuwar mata da Samirah ta ce ita ce uwar ƙungiya Hajiya Ladidi ta faɗa, tana kallon Rahma sama da ƙasa, wani irin kallo da yasa ita kanta Rahma ta fara tsorata da yanayin matar. Duba da yadda take ta gwalalo idanu tana haɗiye miyau akai-akai.

Dariya Samira tayi, suka haɗa idanu da Rahma ta ƙyafta mata idanu, tayi mata alamun ta saki jikinta. Sannan ta mayar da hankalinta kan Hajiya Ladidi wacce duk suke kira Uwar ƙungiya ta ce,

“Hajjaju ita ce fa ƙawarnan tawa da lokaci bayan lokaci nake baku labarinta. Babban kai ne da ita, tuntuni nake kiranta bata amsa ba sai yanzu Allah yayi. Shi yasa na kawo ta ayi mata register da ƙungiya, amma fa sabon shiga ce. A bi ta sannu-sannu ba takura har ta ga komai ga-da-ga a yadda abubuwan suke.”

Wani irin dariya Uwar ƙungiya ta saki wanda ya ƙara fito da siffarta na gogaggun ƴan duniya. Ta matsa kusa da Rahma ta ɗora hannunta guda kan cinyarta tana ɗan latsawa sannu a hankali.

“Ba matsala. Wannan ai ba komai bane Meerah. Amma fa bazan ɓoye miki ba ta tafi da ni ɗari bisa ɗari. Bari in ɗan shafa in ji akwai mai?”

A bazata kawai Rahma ta ji hannun matar saman ƙirjinta. Daman duk a tsorace take da matsa cinyarta da take yi tana lashe baki kamar tsohuwar mayya, don haka tayi saurin miƙewa tsaye idanunta warwaje taja da baya.

<< Lokaci 26Lokaci 28 >>

1 thought on “Lokaci 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×