Duk mazauna gurin sai suka mayar da hankulansu kan Khamis, ana jiran aji ta bakinsa, ko kuma ya ƙaryata Fiddausi kamar yadda ta ce.
Amma sai ya ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa sosai, ya kasa cewa uffan!
“Hmmm! Kun gani ko? Ai bazai iya musawa ba. Saboda ya san ba shi da gaskiya.”
Ta faɗi haka idanunta na kanshi, zuciyarta cike da takaicinsa, ji take kamar ta tashi ta shaƙe shi a gurin har sai ya daina numfashi.
“Khamis”
Alhaji Yusuf ya kira sunansa a hankali. Bai jira ya amsa kiran ba ya cigaba da cewa.
“Da gaske ne abinda wannan yarinyar ta faɗa?”
A nan ma dai shiru yayi, ya kasa amsawa. Zuciyarsa cike da matsananciyar kunya da tausayin Yayansa.
“Kai don ubanka ba tambayarka ake yi ba?”
Ɗaya daga cikin jami’an tsaron ya daka mishi wani gigitaccen tsawo tare da janyo wani ƙaton sanda zai buga mishi a baya.
“Wayyo Allah don Allah kuyi haƙuri. Da gaske ne, wallahi da gaske ne duk abinda ta faɗa. Don girman Allah kuyi haƙuri ku yafe min.”
Ya faɗa a ruɗe, jikinsa sai rawa yake yi saboda tsoro. Lokaci ɗaya hawaye suka ɓalle mishi.
Mahaifin Firdausi mai suna Alhaji Lukman kalli Alhaji Yusuf ya ce.
“Ka ga Malam, ba wani abu yasa muka kawo wannan ƙanin naka nan gurin ba sai don dalilai guda uku.
Bazan ce mishi Allah ya isa lalatar da yayi min a cikin iyalina ba. Amma kan tafe kan isa LOKACI na tafiya da yaddar Allah sai ya girbi abinda ya shuka da hannayensa.
Ya cutar da ni. Khamis ka cutar da ni, amma ka yiwa kanka ne. Na kai ƙararka gurin wanda yayi ni yayi ka kuma ya haramta zalunci a tsakaninmu.
Abinda nake so da hukuma su tilasta wannan yaro ya aikata abu uku ne.
Na farko ya je ya karya asirin da yayi ma Nana.
Na biyu ya biya ta duk irin kuɗaɗen da ta kashe gurin neman magani.
Na uku ya kawo komai da ake buƙata na neman aure a ɗaura musu aure da gaggawa. Wannan shi ne kawai abinda nake so hukuma ta tilasta shi ya aikata…”
Da wani irin matsanancin ɓacin rai da takaicin kalaman da mahaifin Firdausi ya gama furtawa Khamis ya katse shi da cewa.
“Kayi haƙuri Alhaji, Allah ya sani wallahi ko mata sun ƙare a duniya bazan taɓa iya auren Firdausi ba…”
Kafin Khamis ya rufe baki cikin wani irin mahaukacin fushi da zafin nama Alhaji Yusuf ya sauke mishi wasu tagwayen maruka a kuncinsa dama da hagu.
Wuta ne ya ɗauke mishi na wucin gadi, babu abinda yake gani suna gilmawa ta cikin idanuwansa sai wasu taurari masu tsananin haske da ƙyalƙyali.
Jijiyoyin sadar da saƙonni a cikin ƙwaƙwalwar kansa suka tsaya cak!! Tun kafin iyayensu su rasu bazai iya tuna lokaci na ƙarshe da Yayan ya mare shi ba.
Balle kuma bayan rasuwarsu da Yayan ya ninka kulawa da lallaɓawar da yake masa. Duk irin iskancin da yake tsulawa haƙuri yake yi yana cigaba da yi mishi nasiha akai-akai.
Ya dawo cikin hayyacinsa ne yaga Yayansa durƙushe gwuiyawu a ƙasa gaban Alhaji Lukhman. Hankalinsa a tashe yake cewa.
“Kayi haƙuri Alhaji. Na san an cutar da kai, an dasa maka wani mummunan tsiro a cikin ahalinka, wanda in ba wani iko na Allah ba duk saurin tafiya irin na LOKACI ko ya wuce da al’amarin a idanun al’umma bazai taɓa wucewa da lamarin a zukatanku matsayinku na iyayen wannan yarinya ba.
Bazan roƙeka ka yafe ma Khamis ba. Sa’annan bazan roƙi ka sassauta a ɗaya daga cikin hukunci ukun nan da kake son yi akan shi ba. Amma zan roƙi alfarma don girman Allah SWT da darajar fiyayyen halitta SAW ka janye ƙarar nan daga gaban hukuma mu sulhunta a gida.
Ina rantse maka da girman Allah zan tilasta shi ko yana so ko baya so babu ɗaya daga cikin hukuncinka da ya isa ya tsallake. Amma ina roƙon a janye maganar nan daga gaban hukuma.
Saboda shi Khamis ɗin yana da iyali, da ƙananan ƴaƴa har guda biyar…”
“Kan ubancan kayyasa”
Firdausi ta lailayo wani ashar ta maka fuskarta na bayyana matsanancin firgicin da ta shiga da jin maganar Alhaji Yusuf ta ƙarshe. Kafin kowa ya ce wani abu ta miƙa tsaye hannunta riƙe da ƙugu tana cewa.
“Khamis ɗin ne yake da mata har ma da yara biyar?”
Tayi tambayar tana tsattsare Alhaji Yusuf da wani irin kallo mai kama da bata yarda da abinda ya ce ba.
Kafin ya amsa mata tambayarta ɗaya daga cikin jami’an tsaron ya sake cewa, shi ma da fuska mai bayyana matsananciyar mamaki.
“Wai wannan ɗan ƙaramin yaro matashin da a ido muke mishi kallon bai wuce talatin ba shi ne da iyali masu yawa haka?”
“Hmmm! Ƙwarai kuwa.”
Ya basu tabbacin maganarsa. Ya ƙara da cewa.
“Da girmana da mutuncina ko ku yarda ko kar ku yarda bazan taɓa yin ƙarya domin kawai in kuɓutar da ƙanina ba.”
Wayarsa ya sake ɗaukowa a karo na biyu ya lalubo hoton Khamis da matarsa da ƴaƴansa ya nuna musu.
Hoto ne da aka ɗauka na ahali mai bayyana farin ciki da kwanciyar hankalin da yake ciki. Khamis ya riƙe ƙugun wata kyakkyawar matashiya, irin riƙon da idan ba matarsa bace babu ta yadda za’ayi yayi mata wannan riƙo.
Ga ƴaƴansu mata huɗu da ɗa namiji ɗaya tsaitsaye a gefensu suna kallon iyayen da dariya da yanayin mamaki a fuskokinsu. Biyu daga cikin yaran har ɗan rufe baki sukai suna dariya.
Ya sake buɗo wanj hoton ya miƙa musu duk suka gani. Gamsuwar da ya gani a fuskokinsu yasa shi cewa
“Shekarun Khamis talatin da biyar ne ni kuma shekaruna arba’in da biyu. Khamis yayi aure tun yana da shekaru ashirin da biyu a duniya, a cikin ƴaƴansa baku ga akwai wacce ta tasarma zama budurwa ba?”
“Amma dai kai kam kayi asara Khamis! Saboda Allah da Annabi kana zagaye da wannan albarkar ƴaƴan a tare da kai, da kyakkyawar mace son kowa ƙin wanda ya rasa matsayin matarka a gefenka kake tsula irin wannan iskancin da ko ni saurayi bazan iya aikatawa ba?”
“Ubanwa ya ce ka kai idanunka kan matata?”
Khamis ya tambayeshi cikin zafin murya da idanu mai bayyana bala’in kishin matarsa da yake yi.
Da zafin rai shima Yayan Firdausi ya amsa da.
“Ubanka ne yakai idanuna kanta. Au!!! Ashe babu daɗi? Kake lalata wasu ƴaƴan masu tarbiya amma kai ko magana ba ka so ayi kan matarka?
Idan kuma Allah ya juyo maka da abinda kake aikatawa kan ƴaƴa ko matarka fa…?”
“Allah ma bazai sa ba. Mugu ɗan masara mai baƙar aniya, aniyarka ta bi ka. Bakinka ya sari ɗanyen kashi.”
Khamis ya katse shi da faɗin haka fuskarsa na bayyana matsanancin ɓacin rai, zuciyarsa sai tafarfasa take yi saboda muguwar fatan da aka yi kan iyalinsa.
“Baza ka rufe ma mutane baki ba ko?”
Alhaji Yusuf ya faɗi haka cikin ɓacin rai tare da miƙewa tsaye a fusace yana niyyar kai mishi mangari.
Cikin nutsuwa Alhaji Lukhman ya riƙo hannunsa.
“Ƙyale shi, barshi kawai. Rawa sosai kansa yake yi, ba na jin ƙananun marukan da kake masa zai sa kanshi ya tsaya guri ɗaya. Bari hukuma su ɗan ɗunɗuma shi ko na minti goma ne don yasan ba wasa ko mayar da magana ya tara mu anan ba.”
Yana rufe baki a fusace masu fushi da fushin wani suka ɗaga Khamis cak tare da yin ciki da shi. Mintuna biyu tsakani duk girman gurin ba’a jin komai sai sautin muryarshi yana kwarma ihu da surutai cikin matsanancin azaba da ficewa a hayyaci.
“Na amince, wallahi tallahi na amince, zan aure ta. Don Allah kuyi haƙuri kar ku kashe ni, wayyo Allah hannuna, wayyo bayana, wayyo kaina… wayyo, wayyo, wayyo kun karya min ƙafa…”
A hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa, ya lumshe idanunsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa sauri-sauri saboda muryar ƙaninsa da yake jiyowa cikin mawuyacin hali.
Duk ihu ɗaya idan Khamis ɗin yayi ji yake kamar ana zuba mishi tafasasshen ruwa a zuciyarsa.
Babu abinda yake tunawa a daidai wannan lokacin sai wasiyyar da mahaifiyarsu ta bar masa game da ƙaninsa. A lokacin bai fi saura minti goma ba Allah ya karɓi rayuwarta.
Duk kunyar da take nuna mishi matsayinshi na ɗan fari a gareta hannayensa biyu ta riƙe a cikin nata. Ta kalle shi fuskarta na bayyana rauni irin na sarewa da cigaba da rayuwar duniya.
“Alhaji, wannan ciwo nawa ni na san ba na tashi bane. Wasiyya ɗaya zan bar maka…”
Sai tari ya sarƙe ta, sannu ya dinga jera mata hankalinsa a tashe. Ko da ya miƙa mata kofin ruwa kawar da kai tayi, har sai da tarin ya lafa mata.
“Alhaji, ga amanar ƙaninka, na barshi a hannun Allah na barshi a hannunka. Ka kula min da shi, don Allah, fiye da yadda za ka kula da ƴaƴan cikinka.
Na san kana haƙuri da shi, don Allah ka ƙara, ka sake ninka haƙurinka akansa da munanan halayensa.
Zai daina, wata rana zai daina in Allah ya yarda. Zai shiryu, har ma wata-rana ya zama kamar bai yi waɗannan rashin jin ba. Allah yayi muku albarka.”
Daga waɗannan kalaman kalmar shahada ne ya zama maganarta na ƙarshe a duniya.
‘ Allah ya sani yana iyakar ƙoƙarinsa kan Khamis, a wannan matakin da ya zura idanu ana dukansa ba shi da yadda zaiyi ne, ba shi yasa a daki Khamis ba balle yasa a dakatar da dukan da ake mishi.
A wannan lamari idan akwai abinda zai iya yi neman alfarma ne kawai da bayar da haƙuri, kan haka kuma yayi iyakar ƙoƙarinsa.
Khamis ɗin shi yaja ma kanshi da ya shiga gonar waɗannan bayin Allah.
Da bai je ya lalata ƴarsu ba ta ina za su sanshi balle har su saka ayi mishi irin wannan dukan?
Bai ga laifinsu ba, ko kaɗan bai ji haushinsu ba. Idan shi ne aka yi ma ƴarshi abinda aka yi ma ɗiyar wannan bawan Allah zai iya aikata fiye da haka ma.’
Minti goma na cika suka dawo da shi gurin. Yaraf, suka zuba shi kan kujera kamar kayan wanki. Ko da Alhaji Yusuf ya ɗaga idanu ya kalle shi bai san sa’adda wasu zafafan ƙwalla suka taru a idanunsa ba.
Gaba ɗaya sun canza mishi kamanni, kamar ba shi ne suka shige da shi yana a matsayin kyakkyawan matashi ɗan ƙwalisa ba. Yanzu kam da ƴanmatansa za su ganshi a kyauta baza su ɗauke shi ba.
“Da kyau! Kila yanzu kaifin harshe da rashin kunyar zai ragu. Idrees a maimaita mishi sharuɗɗan da na gindaya muji zai amince ko har yanzu da sauranshi?”
Alhaji Lukhman ya faɗa idanunshi na kan ɗaya daga cikin yayyin Firdausi. A fuskarsa ko kaɗan babu alhini ko tausayin yadda aka ji ma Khamis ɗin.
“Za ka karya asirin da kayi ma Fiddausi. Za ka biyata duk kuɗaɗen da ta kashe gurin neman maganin karya asirin da kayi mata. Sannan za ka aure ta da gaggawa.
Ka amince…”
“Na amince! Wallahi tallahi na amince! Zan aikata duk abinda kuke so. Don Allah kuyi haƙuri ku yafe min.”
Ya faɗa bakinsa na rawa, jikinsa ko ina amsawa yake da bala’in ciwo. Wani irin duka ne suka yi masa na rubdugu kamar wanda yayi karo da babbar mota, kusan ko ina na jikinsa ya samu kasonsa.
A halin yanzu babu abinda yake so irin su fice daga nan gurin, shi yasa ya yanke ma kansa shawarar amincewa duk abinda suke so.
“Wayyo Allah”
Firdausi da kanta yake kan waya tana daddanawa ta faɗi haka a zabure, kamar wacce wani abu ya tsunguleta.
Hankalin mazauna gurin duk sai ya koma kanta, aka fara jera mata tambayar lafiya? Me yake damunta?
Bata sami sararin amsawa ba ta miƙe tsaye da saurin gaske, ita kaɗai ta fara runtse idanu tana ciccije baki haɗe da matse ƙaƙafu, kamar wacce fitsari ya matseta.
“Feedy lafiya? Me yake damunki…?”
“Yaya, Yaya, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Abba, Abba Ka gani ko? Yayan Khamis ka ga irinta ko? Asirin ne ya motsa min wallahi.”
Da saurin gaske ta duƙe zuwa ƙasa tana dafe da mararta. A hankali kuma ta saki wani marayan kuka gwanin ban tausayi tana cigaba da maganganu.
“Taya ake tunanin bazan cigaba da tsinema wannan gayen ba? Ku dubi irin mummunan halin tambaɗewar da ya jefa rayuwata a ciki, tsawon shekara ɗaya da wani abu, ya gama lalata min rayuwata… Khamis Allah ya isa tsakanina da kai.”
Jin da tayi lamarin yana ƙara tsananta yasa ta miƙe tsaye a haukace, ɗan yalolon mayafin da ta yafa a kanta tuni yayi gefe ɗaya.
Da saurin gaske ta ƙwace a hannun Yayunta da suke rirriƙeta ta kaima Khamis wata wawuyar runguma.
“Ya zanyi? ya zanyi da kai Khamis ya zanyi da rayuwata? Tashi muje kawai inda muka saba zuwa ka bani maganin da ka saba bani ko zan dawo cikin nutsuwata…”
Da ƙyar da jiɓin goshi ƴan’uwanta suka ɓamɓareta a jikinsa. Ta bala’in ba wa kowa tausayi a gurin.
Alhaji Yusuf kuwa sunkwui da kanshi ƙasa yayi yana share ƙwallar tausayin wannan yarinya da ɗan’uwansa ya gurɓata ma rayuwa.
Ya ɗaga idanu ya sake kallonta, irin yadda take tumami tana ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun ƴan’uwanta zuwa gurin Khamis ta ruƙunƙume shi shi ne abinda ke ƙara ɗaga masa hankali.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!! Ga doki har doki amma ƙafar na sakaina. Wannan wace irin gurɓatacciyar duniya ce muke rayuwa a cikinta?
Yanzu fa duk zamannan da suke yi kan case ɗin mummanan alfasha ne tsakanin matasa biyu da basuyi aure ba. Ɓangaren yarinya mahaifinta da Yayunta duk ga su zaune a gurin, sun san tuni wani ya daɗe da ratsa gonar ɗiyarsu, lamarin da ya faru ba sau ɗaya ba sau biyu ba, babu iyaka.
Kuma akan wannan lamarin ne har suka sami ƙwarin gwuiwar kai zancen ga hukuma, ba tare da tsoro ko fargabar irin kallon da za’a yi musu da ita kanta yarinyar ba?
A ɓangaren wanda ya aikata ta’asar kuma ga shi zaune babu ruwansa. An faɗa yayi bai musa ba, ya kuma ƙara tabbatarwa ya aikata. Har ga shi ma zaune yana ƙoƙarin kare ƙaninsa da kowa a gurin yake yiwa kallon mazinaci, ba tare da shi ɗin yana jin kunya ba.
Wannan wace irin duniya ce muke ciki da kunya tayi ƙaranci a idanun mutane? Lallai Alƙiyama ta kusa tsayawa. Faɗe ne na fiyayyen halitta SAW idan alƙiyama ta kusanto za’a ɗauke kunya daga idanun mutane.’
A ƙarshe dai dole aka fice da Firdausi tana kuka tana turjewa. Cikin mota suka tura ta, ƴan’uwanta biyu suka tare ta a baya ɗayan kuma yaja mota a guje suka bar harabar gurin.
Alhaji Lukhman tunda ya saukar da kanshi ƙasa har ƴaƴan nasa suka bar gurin bai iya ɗaga kansa ba.
Ko da Alhaji Yusuf ya kalle shi da kyau, sai ya hangi ɗigar ƙwallah ɗis ɗis a dakekiyar shaddar da ke jikinsa.
“Lahaula walaaƙuwwata illa billah.”
Alhaji Yusuf ya faɗa a sanyaye cikin yanayi na rauni da sakankancewa ga Allah, da neman agajinsa.
Sai ya mayar da hankalinsa kan jami’an tsaro ya ce,
“Ranka ya daɗe, akwai inda za’a iya ciro min kuɗi anan gurin?”
Yayi tambayar idanunshi na kan wanda ya fahimci shi ne babba a cikinsu.