Skip to content
Part 30 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

A wajen da iyayensu za su kafa ma Nauwara doka, anan take tashi ta kakkaɓe siket ɗinta da dokar ta ƙara gaba. Amma fa ko kaɗan baza ta taɓa nuna musu baza ta bi abinda suka ce ba saboda tsananin iya takunta.

A bayan idanunsu abinda take so shi take yi, tuni take ma mantawa da wani kashaidi da jan kunnen da ake yawan yi musu a gida. Kuma duk tsananin sa idonsu basu gano ga abinda take aikatawa a waje ba, kullum cikin yabonta Uban yake yi. Kafatanin ƴan gidansu babu wanda yasan ciki da waje na halayen Nauwara sai Mannira, wacce suke kwana waje ɗaya suna tashi. Ita kuma duk rashin jituwar da suke yi tana tsananin ƙaunar ƴar’uwarta, ba za ta taɓa iya tona mata asiri a gaban iyayensu ba.

Kuma wani abun ikon Allah, sai ya zamana gaba ɗaya iyayen sun fi son Nauwara sosai da sosai, ko don ta kasance ɗiyarsu ta fari ce da aka samu cikinta a wani yanayi bayan gudanar da zazzafar soyayya? Sau tari daga Mummy har Daddy ba sa iya ɓoye tsananin son da suke mata. Kuma sun fifita lamarinta akan sauran ‘ya’yan.

Nannauyar ajiyar zuciya Mannira ta sauke, a karo na biyu ta sake hararar Nauwara sannan ta ce
“To tunda dai ba tsoronsu kike ji ba su biyun, me zai hana ki daina wani ɓoye-ɓoye da fuska biyun da kike yi? Kawai ki fito fili ki faɗa musu ke fa makarantar nan musamman ta islamiya da Hadda bakya son su kuma bakya ƙaunar zuwa? Kin ga shi kenan kowa sai ya huta. Daddy ya daina asarar maƙudan kuɗaɗen da yake biya miki na makaranta, shi kuma Mu’allim ya daina damuwa idan baki zo makaranta ba. Idan kuma baza ki iya ba ni zan sauƙaƙe miki sai in faɗa musu da kaina ga halin da kike ciki”

Ganin Mannira ta fara ɗaukar abun da zafi yasa Nauwara ta sassauta. Tayi murmushi tana dafa kafaɗarta, a tausashe ta ce
“Haba shalelen ƙanwata! Ke ma kin san ba ma ƴar haka da ke! Kuma ma ni Wallahi tsokanarki nake yi, ni har na isa da gaske in ce ba na tsoron Daddy da Mu’allim? Amma don Allah kiyi min uzuri ƙanwas, ya kike so inyi? Wani masifaffen sabon lakcara ne wallahi ya taso mu gaba, kusan duk lokacin lectures ɗin shi baya yi sai yace muje da yamma, kin ji dalili kenan.

Kuma dai kin san halin Daddy, idan na mishi bayani ba lallai ya amince ta sauƙi ba, zai iya cewa in haƙura da lakcar, ko kuma ya ce shi zai kai ni da kanshi, salon yasa ɗalibai suyi ta zunɗena ni kuma in kasa sakewa inyi abinda ya kamata. Kin ga na ma manta, musamman fa nayo miki tsaraba don farin cikinki ƴar ƙanwata, cakuletin dairy milk na sayo miki, kuma ma har kati zan sanya miki yanzu da mun koma gida.”

Da yake ita ma Mannirah da waya a hannunta, Nauwara ta gama sanin lagonta bai wuce na katin waya da kayan zaƙi ba. Tunda Daddynsu baya sanya mata katin waya akai-akai sai dai Data, a cewarshi wa za ta kira? Itama wayar kawai ya siya mata ne saboda makaranta. Ita kuwa Nauwara saboda ƴar lele ce a cewarshi ita ta fara girma ba kamar Mannira ba har account na musamman ya buɗe mata, duk wata yake sanya mata kuɗaɗen kashewa da na amfanin makaranta. A cewarsa barin ƴanmata da ƙananun buƙatunsu shi ke sa su fara kwaɗayin abin hannun samari.

Ɗan murmushi kawai Mannira tayi mata, wannan murmushin kuwa alamu ne na komai ya wuce. Hannu ta miƙa ta karɓi ledar cakulet ɗin da Nauwara take miƙa mata. Cikin su biyun babu wacce ta sake magana suka cigaba da tafiya har suka ƙarasa gida.

A kicin suka samu Momy tana ƙoƙarin kammala girkin abincin dare. Sannu da gida suka yi mata, suna shiga ɗakinsu suka cire kayan makaranta, Nauwara ta bi lafiyar gado ta kwanta da cewa ta gaji hutawa zata yi kafin lokacin sallar magrib. Ita kuwa Mannira ta fita zuwa kicin ta fara kamawa Mommynsu aikin da take yi, jefi-jefi suna hira tana bata labarin Makarantarsu.

Bata koma ɗaki ba sai da suka gama komai, tayi alwala a bayin falo ta shige ɗakinsu. Ko da ta ɗauki wayarta da niyar jona caji sai taga Nauwara ta tura mata katin dubu biyu, idanunta ta mayar kan Nauwara da tayi ɗai-ɗai kan gado tana sharɓan barci, sai tayi ɗan murmushi kawai, zuciyarta cike da farin cikin katin wayar.

Cin abinci ba tare da Daddy ba abu ne da tun a baya suka saba da shi, balle yanzu da likkafa ta cigaba. Harkokinshi sun ƙara faɗaɗa sosai, a mafiyawancin lokuta in dai yana garin kaduna rana ɗai-ɗai kwanciyar barci kawai ke mayar da shi gidan.

Alaƙar iyayen zuwa yanzu babu komai a ciki sai ƙarin taɓarɓarewa, wani irin zama suke yi kamar na dolen-dole, kuma an rasa yadda za’ayi da juna. Igiya ɗaya ta rage a tsakaninsu saboda yawan tashe-tashen hankulan da suke samu tsakani, kuma har yanzu sun kasa samun maslaha da sasanci a tsakaninsu. Ziyada ta ƙi haƙura ta kawar da kai kan abubuwan da yake yi, shi kuma ya ƙi canza halaye, ba ma shi da niyyar canjawa.

Suna gama cin abinci daƙyar Nauwara ta kwashe kayan zuwa kicin bayan Mummy ta yi mata kaca-kaca kan son jiki da lalacin da take da shi, daga can ta wuce ɗakinsu don ma kar a sake sakata wani aikin.

Ita kuwa Mannira da aiki bai damunta tas ta gyara gurin da suka ɓata, ta goge ko ina ƙal. Sannan ta shige kicin tayi wanke-wanke ta ƙarasa gyara komai, gurin yayi fes kamar basuyi aikin abinci ba.

Ko da ta koma falon duk yadda Mommy tayi nacin ta zauna ta huta saboda tun da ta dawo makaranta bata huta ba murmushi kawai tayi, ƙannen ta umarta suka kwaso ƙur’anansu ta karɓa musu hadda, kowa a cikinsu ta ƙara mata daidai yadda za ta iya, sannan tayi ma Mummy sai da safe ta nufi ɗakinsu, zuciyarta cike da jin daɗin kyawawan addu’o’i da sanya albarka da Mummy take ta mata har ta shige ɗakinsu.

Tana shiga cikin ɗaki jikinta har rawa yake yi lokacin da ta cire wayarta daga jikin caji, ta lelleƙa Nauwara dakyau ta ga tuni tayi nisa a barci. Da saurin gaske ta shige banɗakinsu ta kulle ƙofar ta ciki, ta jingina da jikin sink tare da latso sunan wanda take cike da azarɓaɓin son jin muryarsa.

Daga can ɓangarensa kamar daman abinda yake jira kenan. Wayar tana shiga ya ɗaga. Abu na farko da ya fara yi shi ne sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya.

Cike da wani irin sassanyar salo na soyayya da rauni ya sakar mata kuka a hankali, a raunane ya ce
“Qurratul-Ayn”
Ya kira ta da sunan da shi kaɗai ne yake faɗa mata, muryarsa tafe da wani irin shessheƙa mai tsuma zuciya.

Wani irin yam-yam jikinta ya fara yi kamar ana mata tafiyar tsutsa a gadon baya, wani shauƙi da jiri-jiri da ya nemi kwasarta ya yar ba shiri ta ƙara bin jikin sink ɗin ta lafe tana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri
“Qalb! Afuwan! Afuwan don girman Allah! Allah ya huci zuciyarka Qalbina. Yi haƙuri plsssss! Daina kukan muyi magana, ka ji?”
Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe, har tana ɗan bubbuga ƙafa a hankali kamar tana gabansa.

Daƙyar ta samu yayi shiru bayan ta ɓata lokaci tana rarrashinsa da zaƙaƙan kalamai masu kwantar da hankalin masoyi.
“Fatan ka yini lafiya Qalb?”

Daga ɓangarenshi ajiyar zuciya ya sake saukewa, da sanyin murya sosai kamar mara lafiya ya ce
“Ina fa lafiya Qurratul Ayn”

Da sauri ta zabura hannu dafe da kirji hankalinta a tashe ta ce
“Subhanallahi! Qalb ba ka da lafiya? Me yake damunka? Ka sha magani? Ina yake maka ciwo?”
Ta jera mishi duka tambayoyin a rikice, zuciyarta har wata katantanwa take yi saboda jin ba shi da lafiya.

Shiru yayi yana ta sassauke mata numfashi a kunne, bai amsa mata ba sai da ya gama tayar mata da hankali sosai kafin ya ce
“Ni ba inda ke min ciwo. Ba ke ce kika wani manta da ni ba yau gaba-ɗaya, ko tunanin ki kira ni ba kya yi bayan kuma ni kin hanani in kiraki ko in turo miki da saƙo. Don Allah ya kike so inyi da raina ne Qurratul Ayn? Kina so soyayyarki tayi ajalina ne? Wallahi-Wallahi yau ko abinci na kasa ci saboda rashin jin muryarki. Don Allah ki dinga tausayawa min, Qurratul-Ayn soyayyarki ta yi min yawa, amma kar ki manta ba ni na ɗora ma kaina ba… Ki dinga tausaya min… Don Allah…”

Tsabar yadda kalamansa suke tsumamata bata san sadda ta duƙe ƙasa a bayin ba, idanunta a lumshe, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta da take ji yana bugawa da sauri-sauri. Da bala’in gudu take jin yadda soyayyarshi ke ƙara cike duk wani lungu da saƙo na zuciyarta.

Ta sani tana tsananin son Qalb, amma ko rantsuwa tayi babu kaffara soyayyar da yake mata ya ninninka wanda take mishi. Tana son shi sosai, amma son da yake mata ya wuce a misalta.

“Baza ki amsa ni ba ko?”
Ya katse mata tunani ta hanyar sake faɗa a marairaice, bayan sun shafe mintuna uku shiru, kuɗin wayar kawai ke tafiya a iska.

“Allah ya huci zuciyarka Qalb! Wallahi har ka bani tsoro! Na yi zaton rashin lafiya kake yi da gaske har na ji nima rashin lafiyar na niman kama ni”

“Rashin ci da sha na a wajenki ba komi bane ba ko Baby? Kuma gani kike yi don ban ji muryarki na yini guda ba, hakan ba komai bane a gurinki ko?”

A sanyaye ta sake cewa
“Ka yi hakuri rabin raina, kasan ba da niyya na faɗi hakan ba. Kai kanka shaida ne kan yadda na damu da kai da lamuranka sosai. Ni sai na ji ma gaba-ɗaya na tsani kaina da na iya zama na cika cikina da abinci, bayan kuma kai kana nan baka ci komai ba…”

Da sauri ya katse ta da cewa
“Gwara da kika ci Qurra, idan baki ci komai ba zafin sai yayi min yawa. Dama can rashin jin muryarki da ban yi ba ne yasa na kasa cin komai, domin duk tunanina ba lafiya kike ba. Amma yanzu Alhamdulillahi, kuzarina ya dawo, muna gama waya zan nemi abinci in ci”

“Yauwa Qalbina, don Allah ka ci da yawa fa sosai, ka ji ko?”
Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe.

“To! Na ji! Yanzu dai ki hau whatsapp! Ina cin abinci muna hira, sai in ci da yawa ma don zan ji kamar kina kusa da ni.”

Cike da ɗoki ta amsa da to, suka yi musayar kalmar ina son ki ina son ka nima sannan suka katse wayar a tare.

Layin waya guda biyu ke gareta ba tare da sanin iyayen ba. Da ɓoyayyen layin ta bude facebook da Whatsapp da wani suna na daban, wanda take sa ran duk daɗewa ba za a taɓa gane ita ce ba.

Doka ta farko da ake kafa musu a gidan idan an basu waya ita ce babu chatting ko wani iri ne, babu zancen kiran abokai ko musayar saƙonni. Kawai amfanin wayar su dinga browsing kan abubuwan makaranta, sai kuma communication a tsakanin su ƴan gidan kawai.

Ba ta mancewa lokacin da Nauwara tana ss2 Daddynsu ya kamata tana WhatsApp da wata yar ajinsu, irin faɗa da tashin hankalin da suka gani a lokacin ba kaɗan bane. Wai ma don Allah ya sa ko da ya ƙwace wayar, lambar ƙawar kaɗai ya gani a gurin Chat.

Kuma da gaske yaga tana mata ƙarin haske ne akan wani assignment da aka basu. Amma duk da hakan ba ƙaramin faɗa da fushi yayi ba, har wayar ya ƙwace gabaɗaya ya kulleta. Sai da ƙyar da magiya sannan ya bata, bayan ya canza mata wayar gabaɗaya da sabon layi. Shi yasa su biyun suke taka-tsan-tsan ƙwarai da gaske.

Data ta buɗe, ta watsa ruwa a gurguje ta murɗa abin floshing ruwa ya zubo sha, kamar dai duk daɗewar da tayi a cikin bayin tana gabatar da uzuri ne. Wayarta ta duƙunƙune a cikin kaya ta fice daga banɗakin.

Idanunta kan Nauwara, sai taga har lokacin tana sharar barci. Taƙaitaccen murmushi tayi ta shafa mai sama-sama ta saka kayan barci ta bi lafiyar gadon. Can nesa da Nauwara ta kwanta ta juya ta yadda ko da ta farka baza taga abinda take yi ba.

Kai tsaye whatsapp ta shiga, sai ta ganshi yana online. Har ya tura mata hoton abincin da zai ci yana mata bismillah ta taya shi ci. Nan ta biye mishi suna ta musayar kalaman ƙauna har ya gama cin abincin, ya kwanta suka ɗora daga nan.

Sai can wajen ƙarfe sha biyu da rabi sannan suka yi sallama daƙyar, ba don su biyun suna so ba, yana ta maimaita mata yana sonta kamar fitar numfashi itama tana maida mishi da martani.

Ranta fari ƙal ta lumshe idanu tayi shiru, ita kaɗai take sakin murmushi, wayarta na ɗore a ƙirjinta. Ita da kanta baza ta ce ga lokacin da tayi nutso a kogin ƙauna da soyayya mai tsanani haka ba, wani abin mamakin kuma shi ne kaf ƴan gidansu babu wanda yasan tana cikin wannan halin.

Muhsin sunan saurayin da take tsananin so da ƙauna. Yayan wata ƴar ajinsu ce Fadila, sun haɗu da shi ne lokaci na farko da yaje kai Fadila makaranta, saboda rashin lafiyar direbansu.

Mannira yarinya ce mai tsananin ƙoƙari, shi yasa ɗalibai sa’anninta ke shisshige mata don suyi ƙawance. Da salon cusa kai ta janyo Mannira wai tazo su gaisa da Yayanta, da farko kamar baza ta je ba, amma aka ce ƙaddara ta riga fata.

Rabon ayi, duk da kasancewarta yarinya mai tsananin kunya da bata cika kallon mutane cikin ido ba kamar maganaɗisu haka ta ƙure Muhsin da kallo. Kyakkyawan matashi ajin farko, fari sol ga dirin jiki kamar jarumin fina-finan indiya Hritik Roshan.

Soyayya daga kallon farko shi ne abinda ya samu Mannira. Shi ma cikin ikon Allah kamar haɗin baki, daga kallon farkon ya ji ta kwanta mishi arai, ya kamu da sonta mai tsanani, a yadda ya bayyana ma ƙanwarsa.

Ta hanyar Fadila ya sanar mata da saƙonshi da ƙoƙon bararshi, bata wani tsaya jan aji ba ta amince kai tsaye, tunda faɗuwa tazo dai-dai da zama.

Tun suna musayar takarda saboda rashin wayarta a lokacin, watarana kuma suyi waya a wayar Fadila idan taje makaranta da ita, har dai suka koma ta wayarta bayan an saya mata. Itama a nan ɓangaren duk ƙwaƙwa da sanya idon iyayenta basu gano abinda take ciki ba har yanzu.

Shekararsu fiye da ɗaya da haɗuwa, kullum soyayyarsu ƙara zurfi take yi. Ta kai matakin da take jin cewa ba ma zata iya rayuwa ba tare da Muhsin ba. Tuni ta gama yankewa ranta cewa tana gama makarantar sakandare kawai za ta faɗa ma iyayenta ita aure aure take so. A kaita gidan mijinta Muhsin su ci karensu babu babbaka da hujja.

<< Lokaci 29Lokaci 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.