“Kin fara cin kai ne ko?”
Khamis ya jefa mata tambayar yana aika mata da wani irin kallo da ta rasa gane in da ya dosa. Kafin ta amsa ya ƙara da cewa,
“Kina sane dai Salim Kanta har yanzu saurayin Aminiyarki Rahma ne. Ko kin zaci sun rabu ne…?”
“Ina sane basu rabu ba.”
Ta katse shi da sauri tana galla mishi harara, zuciyarta cike fal da takaicin maganganunsa. Daman tun da taga yai shiru, ya afka a zuzzurfar tunani ta san wani ƙabli da ba’adi zai kawo mata. Zai kuma yi ya gama, akan wannan maganar tana nan akan bakanta, babu gudu babu ja da baya. Wannan burin daɗaɗɗen abu ne da ya daɗe kwance can cikin zuciyarta. Kawai dai bata taɓa furta mishi bane sai yanzu da take ganin lokacin ya sani ya yi.
Muskutawa tayi ta gyara zama, ta cigaba da magana muryarta na fita zafi-zafi.
“Sai me don har yanzu yana saurayinta? Akwai wani zane ne a jikin Rahma wanda ni ba ni da shi? Mace nake cikakkiya kamar yadda take mace, menene za ta gwada min? Zan yi mishi fiye da abinda take mishi, kai ma shaida ne na fi Rahma ƙwarewa da sanin makamar aiki. Yarinyar da take cikin duhu dunɗum sai da na kama hannunta na fito da ita sarari, ita kanta ta san ni uwarta ce a bariki.”
Tayi fari da idanunta sannan ta ɗan sassauta murya ta ci gaba da cewa
“Kuma in ban da kai da abinka Kham, wannan harkar ta mu ai kowa tasa ta fisshe shi ne. So so ne amma son kai ya fi ko?”
Tsawon daƙiƙu ya ɓata yana kallonta, zuciyarsa cike fal da mamakin ƙarfin halinta. Duk da sanin da yayi ba sa shiri yanzu da Rahma abu ne da bai taɓa tsammani ba fitowar irin waɗannan maganganun daga bakinta. Ɗaure fuska yayi tamau don ta tabbatar duk abinda zai faɗa mata a yanzu iya gaskiyar maganar kenan.
“Na san so so ne amma son kai ya fi. Amma gaskiya kin ba ni mamaki, a yadda Rahma take faɗa min irin amincin da ke tsakaninku ban tsammaci jin irin maganganunnan daga bakinki ba.
Abu ɗaya da nake so ki sani ba ni a cikin wannan maganar. Rahma yarinyar kirki ce, ni kam tsakanina da ita babu ƴar haka, ko a bariki akwai sanin halacci. Ba zan taɓa ba ki goyon baya ba a wannan maganar ba. Don yanzu haka zancen da nake miki ana gab da ɗaura auren Salim Kanta da Rahma. Maganar aure ta daɗe da yin nisa a tsakaninsu, ƴan kwanaki kaɗan suka rage…”
Wata irin zabura da tayi ta miƙe a haukace ya hana Khamis ajiye numfashin maganarsa daidai. Idanu ya zuba mata, yana kallon yadda tsabar rikicewa yasa sai da tayi adungure sau biyu kafin ta iya sauka daga kan gadon.
Da rarrafe ta ƙarasa gabanshi, murya na rawa bakinta na ɓar-ɓar, hankalinta a bala’in tashe ta ce,
“Don Allah, idan tsokanata kake yi ka daina. Da gaske kake yi ko da wasa?”
Shiru yayi yana kallonta, kamar bazai amsa mata ba. Sai kuma ya gyaɗa kai, alamun tabbas da gaske yake yi. Don share mata tantama sai ya ƙara da cewa
“Wallahi da gaske nake miki.”
Tsabar tashin hankali da baƙin ciki yasa ta ɗora hannu biyu akai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, kamar wacce aka faɗa mata mutuwar iyayenta. Fuskarta na nuna tsantsar hassada da baƙin ciki da kishi mai tsanani.
Ta tafasa sauke Khamis bai ce mata ba, sai ma taɓe baki da yayi ya matsa daga kusa da ita yana ci gaba da tattara komatsan shi.
Ta ɗauki tsawon lokaci tana rusa kuka, sai juye-juye take yi a tsakar ɗakin kamar mai naƙuda. Can kuma sai ta ɗauke kukan ɗif, kamar ɗaukewar ruwan sama. Ta miƙe tsaye zumbur! Ta fara da zagaye a cikin kamar mai yin safa da marwa, har lokacin bata sauke hannuwanta akai ba.
Idan Khamis ya kalle ta, sai yayi kamar zai fashe da dariya sai kuma ya fuske. Lalle da gaske ne ƴa mace lokacinta taƙaitacce ne ba kamar na ɗa namiji ba, kamar dai ba Kankanar da ya sani shekarun baya ba, halittun jikinta da suka kasance suna jan hankalin maza zuwa gare ta duk sun fara la’asar.
“Bazai yiwu ba. Ka san Allah? Ba zata saɓu ba bindiga a ruwa. Duka-duka yaushe Rahma ta shigo fagen bariki da za tayi wannan kyakkyawan ƙarshen? Wannan labarin naka ƙanzon kurege ne kawai, Na rantse da Allah ba zai taba yiwuwa ba!! Rahama da auren Salim? Inaaa, wasa kenan!! Ai yadda na ɗauki shekaru maza suna gare-gare da ni sai ta ɗauki fiye da shekarun da na ɗauka. A zuciyata ka san irin mummunar tanadin da nake yiwa Rahma kuwa?”
A haukace ta ƙarasa kusa da shi ta tsaya a gabansa, sai zazzare idanu take yi kamar wacce ta sha kayan maye.
“Shekaru masu yawa na ɗauka ina ƙoƙarin janyo Rahma a harkar bariki, ban samu nasarar dulmiyar da ita ba sai a lokacin da na fara fitar da tsammani. Don haka nake so tayi mummunan ƙarko irin na Magajiyar gidan karuwar, ƙarshen ƙanjamau da sana’ar goro da taba. Ni zanyi aure ba ita ba, tabbas ni zan auri Salim Kanta ba ita ba, kuma ka rubuta ka ajiye, ka zuba ido ka gani, za ka ce na faɗa maka!”
Aka ce wanda yayi nisa ba ya jin kira, daga irin kallon da yake mata ya gane ta fara ficewa daga hayyacinta. Don haka ya saki murmushi a tausashe.
“To Hajiya Samira. Tunda ke ce me ikon sakawa da hanawa Allah ya bada sa’a, fatan alkhairi Kankana!”
Harara ta watsa mishi mai zafi kamar idanunta za su zazzago ƙasa, ita kanta ta san gatse yayi mata, ko kuma ta ce jirwaye me da kamar wanka.
“Ka yi ka gama, na lura abin naka ya koma munafunci. Idan ba munafurci da cin amana ba ni da Rahma wa ka fara sani? Ba damuwa, duk ku biyun za ku gane shayi ruwa ne.
Wallahi ko sama da ƙasa za su haɗu auren nan ba za a ɗaura shi ba. Haba! Haba!! Idan na bari Auren ya ɗauru na zama shegiya kenan, Ni banyi aure ba ace wai Rahma za ta yi? Auren ma ba wulaƙantaccen aure ba sai gidan wanda ake gani a matsayin gwamnan Kaduna na gobe? Ai ba ma zai yiwu ba sam!”
Khamis dai ya fahimci duk abinda zai faɗa mata baza ta taɓa fahimtarshi ba, sai ya matsa gaban madubi ya ɗauki makullin motarshi da wayarshi ya nufi ƙofa zai fita, sai da ya kama hannun ƙofar ya buɗe sannan ya waiga inda taka tsaye kamar mutum mutumi
“Samira, shawara ɗaya da zan iya baki ita ce, ki manta da zancen baƙin ciki da hassada a zuciyarki. Domin ita Rahma ko kaɗan ba ki a gabanta, idan ta buɗe baki za ta yi magana a kanki kullum alkhairinki take faɗa. Da wannan dalilin yasa baza ki taɓa samun galaba a kanta ba, da za ki ji ta tawa, ki yada kai a gaban Rahma ki kwashi garar arziki. Kika sani ma ko ta miki hanya ke ma kiga ta dalilinta kin dace da samun mijin ko cikin abokan Salim? Idan kuwa kika tsaya ‘kyashi da hassada ke za ki kwana a ciki Wallahi, don ita hassada ga mai rabo taki ce. Shawara ce kyauta na ba ki, idan kin ga dama ki ɗauka, idan kuma kin ƙi, matsalarki ce. Sadda kwaɓarki za ta ƙarasa tsinkewa tsululu kar ki sake ki neme ni. Ni kin ga tafiyata.”
Da saurin gaske ya ƙarasa ficewa daga ɗakin, sama-sama yake jin muryarta tana watsa mishi ruwan ashariya da tsinuwa.
Ko bayan fitarsa, ta kasa tsinana komai, bakin gado ta koma ta zauna hannu dafe da ƙunci tana ta saka da warwarar ta yadda zata ɓullowa al’amarin. Duk sadda ta tuna wai Rahma zata yi aure, ita ta barta tana yawon ta zubar yayinda ita take killace a gidan aure. Gidan auren ma gidan matsayi da ɗaukaka, sai ta ji duk ranta ya ƙara ɗugunzuma, hankalinta ya tashi, zafafan hawaye su gangaro daga idanunta.
Ba ita ta motsa daga inda take zaune ba sai da masu gyaran ɗaki ma’aikatan hotel ɗin suka ƙwanƙwasa ƙofa suna mata tunin kuɗinta da ta biya ya ƙare.
Haka nan ba don ranta ya so ba ta fara mayar da kayan jikinta, a sanyaye take komao kamar wacce aka lakaɗawa duka. Tana fita daga ɗakin hotel ɗin, ta tari adaidaita sahu ta shiga. Har ta ce ya kai ta gida, sun ɗauki hanya sai kuma ta canza shawara.
Ta ce ya kai ta gidan wata ƙawarta Ramlatu, a sanin da tayi ma Ramlatu ƙwararriya ce a wajen bin malaman tsibbu. Kuma ittifaƙan duk ƙawayensu sun yarda in dai Ramlatu tayi niyyar taimaka miki, to kamar yankar wuƙa haka za ta kai ki gurin boka ya miki zazzafan aikin da za’a share hawayenki.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, a zuciyarta take jin kamar ma buƙatarta ya biya. Shaf ta mance da Ramlatu, da me zai kaita neman Khamis balle har ya caccaɓa mata baƙaƙen maganganun da ya yaɓa mata? Ƙasa-ƙasa ta ja tsaki, zuciyarta cike da takaici da baƙin cikin Khamis.
Wani babban rashin sa’a da ta buga shi ne ko da suka isa gidan su Ramlatu bata same ta ba, inda Allah ya taimake ta shi ne tana sauka daga kan keken ta hangi ƙanwar Ramlatu ta fito daga gidan, ita ta faɗa mata kwana uku kenan ba ta a gida.
“Ina ta tafi?”
Ta tambaya fuskarta na bayyana damuwa ƙarara.
“Mu ma bamu sani ba, amma dai na ji Inna ta ce jibi za ta dawo.”
Tana niyyar tambayar lambarta yarinyar ta falla a guje. Har za ta shiga gidan, sai kuma ta fasa shiga ta koma cikin keken, ta faɗa mishi layinsu.
‘Gara kawai in wuce gida, jibin sai in sake dawowa.’
Ta ayyana hakan a zuciyarta.
*****
“Ya maganar da muka yi da ke rannan?”
Umma ta jefa mata tambayar daf da za ta shige cikin ɗakinta. A kasalance ta waiwayo ta kalle ta, ƙirjinta ne ya buga daram! Ganin wani bala’in ɗaure fuska da Umma tayi tamau, kamar bata taɓa sanin wani abu wai shi dariya ba.
Jikinta a sanyaye ta saukar da fuskarta ƙasa. Daman ga kwantaccen ɓacin ran da Khamis ya cusa mata, sai zafin ya haɗe mata biyu, a yadda take ji kamar ta ɗaga hannuwa biyu tai ta rusa ihu ko za ta ji dama-dama.
“Ummmaaa…”
Ta ja sunan a raunane, sai kuma hawaye suka ɓalle mata wasu na korar wasu, kamar an buɗe famfo.
A bazata wani jiri da ya nemi maka ta da saurin gaske ta dafe bango, sai kuma ta silale zuwa ƙasa tana cigaba da sharɓan kuka.
Daga kallon fuskan Umma za’a gane ko misƙala zarrah babu tausayin Samira a zuciyarta. A maimakon ta rarrashe ta da tausasan kalamai ma wani gigitaccen tsawa ta daka mata, babu shiri ta haɗiye kukan kamar ɗaukewar ruwan sama.
“Samira kina wasa da ni ko?”
Umma ta jefa mata tambayar cikin tsawa.
A gigice ta ɗaga kanta tana kallon uwar, bakinta na rawa ta amsa da
“Bab-bab-ba haka bane Umma. Kik… kikk… kiyi haƙuri… Har yanzu ina lalubawa ne…”
“Dakata Samira!”
Ta sake katse ta haɗe da kiran sunanta cikin tsawa. Sunan da ba kasafai ta cika kira kai tsaye ba saboda kasancewarta ƴar farko.
“Kin san Allah? Bari in sake rantse miki a karo na biyu. Na rantse da girman Allah matuƙar kika cike watanni ukun da na ɗiba miki ba tare da kin fito da mijin aure ba sadakar ki zan bayar ga Inusa. Ba dai yanzu kin ci watanni biyu a cikin ukun ba? Allah ya kaimu ƙarshen watan gobe ki gani, zan nuna miki har gobe ruwa na maganin dauɗa.”
Fuuuu ta wuce daga gurin a fusace.
Ta bar Samira cikin mawuyacin hali ita ba sumammiya ba ita ba ido biyu ba. Da jin sunan Inusa a matsayin wanda Umma ke shirin aura mata idan bata fito da mijin aure ba, duk wasu jijiyoyi da suke sadar da saƙonni na cikin kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta suka tsaya cak!!
‘Inusa, wani tuzuru ne da ya daɗe yana nacin son ta a nan unguwarsu. Ya daɗe bayyi aure ba, domin a kaɗan ne shekarunsa basu kai hamsin ba, kuma har lokacin bayyi auren farko ba. Iyayenshi da ƴan unguwa tun suna ganin abin na lafiya ne har sun fara tunanin aljana ce ta aure shi. Domin fau-fau yake gudun batun aure.
Bayan Samira da yake nacin so tana wulaƙanta shi bai taɓa gigin neman wata budurwar ba. Ko zaɓo mishi iyaye da ƴan’uwa suka yi ba ya taɓa kulawa, haka nan za’a gaji a shiriritar da maganar.
“In dai ana so inyi aure to a bani Samira. Idan ba ita ba har in koma ga Allah bazan taɓa yin aure ba. An halicci Inusa don Samira ne.”
Amsar da yake bayarwa kenan a duk lokacin da aka tsokano shi da zancen ya ƙi aure.
Ita kuwa a ɓangaren Samira a duniya babu saurayin da ta tsana kamar shi. Duk yadda yake nacin son ta ko sau ɗaya bata taɓa ba shi dama ba balle har ta saurare shi. Duk inda ta samu dama wulaƙanci take karta mishi, amma har gobe bai daina nacin son ta ba.’
Bata dawo hayyacinta ba, sai da ta ji hayaniyar ƙannenta sun dawo Makarantar islamiya. Duk yadda suke nacin faɗin Aunty Samira sannu da gida ko kallonsu bata yi ba ta shige cikin ɗakinta ta banko ƙofar da ƙarfi.
Kan gadonta ta zube, ta ƙura ma saman ɗakin idanu tana tsiyayar da hawaye masu zafi.
“Baba, ina ka shige Baba?”
Tayi maganar a raunane, hawaye na ƙara ƙarfin gudu a idanunta.
“Baba don Allah ka dawo. Umma tana so ta kassara rayuwata. Baaabaaaaa?”
Ta ƙwalla kiran sunan da ƙarfi haɗe da ƙara fashewa da wani mahaukacin kuka.
‘Tun da mahaifinsu yayi ɓatan dabo, shekaru uku kenan har yau ko labarin inda yake basu ji ba. Labarin da suka samu dai daga bakin shaƙiƙan abokan cacarsa shi ne, an cinye shi daga wata gagarumin caca ne da ya buga shi da wasu baƙin attajirai. Takaicin maƙudan dalolin da yana ji yana gani yayi asararsu yasa shi son yin zamba cikin aminci, ta hanyar kwashe kuɗaɗen ya danna layar zana ya ɓace. Abinda bai sani ba sun fi shi hatsabibanci, kuma a gurin duk wani ɗan caca babban zunubi ne ƙoƙarin yin zamba cikin aminci. Sai da ya kwashe kuɗaɗen tas yana niyyar danna layar zananshi ya ɓace suka yi ram da shi, a gaban kowa suka lakaɗa mishi tsinannen duka kamar za su kashe shi. Hankali tashe abokan Baban suka kira ƴan sanda amma kafin isowar hukuma suka jefa shi a cikin motarsu suka bar gurin, ba kuma tare da sun faɗi in da za su kai shi ba.
Har yau ba amo ba labarinsa.’
Tun bayan ɓacewarsa da yadda Umma take matsa mata lamba bata taɓa kukan rashin Baban nasu kamar yadda tayi yau ba. Ta san da yana nan, Umma bata isa tayi mata wannan hukuncin na mulkin mulaka’u ba. Wani abu da ya ƙara mata baƙin ciki da takaici shi ne duk yadda take ihu tana kiran sunan Baban ƙanninta da mahaifiyarta babu wanda ya bi ta kanta balle har ya rarrashe ta. Tana ihun kukan wani nannauyan barci ya saɗaɗo yayi awon gaba da ita.
Good