Skip to content
Part 37 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Yayuna maza biyu da nake bi kin san ba’a ƙasar nan suke karatu ba. Suna zuwa ne kawai idan sun samu dogon hutu. Sauran biyun kuma babban Yayanmu da mai bi masa Ƴan sanda ne, su kuma aiki ba ya barinsu zama, yau suna nan gobe suna can. Shi yasa kika ga ina abinda naga dama son raina, babu mai sa min ido!”

Nauwara ta sake yin jim cikin tunani kafin tace,

“To me zai hana ko gidan yayunki ki dinga zuwa? Ko kuma kiyi ƙaura can gaba-ɗaya? Saboda zama kai kaɗai a gida ai ba daɗi ƙawata. Ni gaskiya na saba da jin hayaniyar ƙannena da Mummy, ɗan zaman nan da nayi shiru sai naji duk na takura. To ina ga ke da tsawob lokaci kike irin wannan rayuwar?”

Wata irin dariya Aminar ta saki, ta juyo gaba ɗaya tana kallon Nauwara ta ce,

“Tabɗijam! To su dukansu ai babu mai aure, kowa kika gani a cikin su aiki tuƙuru yasa a gaba. Kin san tun tale-tale akan wannan tsarin iyayenmu suka raine mu. Maza sai sunyi digiri da masters ɗaya ko biyu sannan zasu yi aure, ni kuma sai nayi degree kafin in kawo wanda zan aura in ƙarasa masters a ɗakin mijina. To su manyan ma da suka gama karatu suka kama aiki har yanzu babu batun aure a tsarinsu.”

Kame haɓa Nauwara tayi zuciyarta cike da matsanancin mamakin wannan tsari na ahalin Amina. Da yake basu taɓa zurfafa hiran family irin haka ba, shi yasa bata taɓa sani ba. Ashe ita ma Amina iyayenta masu tsattsauran ra’ayin nan ne na sai yaransu sunyi karatun boko mai zurfi kafin suyi aure? Taɓɗijan! Wannan ai a sauƙaƙe ba ma yara lasisin lalacewa ne. Wannan shine ƙaƙa-tsara-ƙaƙa, gaba kura baya siyaki.

Muryar Aminar ce ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.

“Shi yasa kika ganni nan ba ruwana da wani tsari da ra’ayinsu. Na shafawa kaina lafiya na nemi hanyar da za ta ɓulle da ni tun da wur-wuri. To ma su masters ɗin ma basu yi auren ba ina ga ni autarsu da har gobe suke min kallon ban wuce ayi min tsarkin kashi ba? A idanunsu karatu nake yi tuƙuru amma tsuntsu biyu nake jifa da dutse ɗaya. Ko ya kika ce Ƙawalli?”

Ta ƙarasa maganar haɗe da kashe ma Nauwara ido ɗaya.

Murmushin yaƙe kawai Nauwara ta iya jefa mata. A zuciyarta take ji sam tsarin bai mata ba. Ko da wasa bata taɓa tunanin haka rayuwar Amina take ba, ita tana ganin ana mata tsauri da takurawa tana buƙatar ƴanci, ashe gata ake mata kuma hakan ba komi bane akan yadda aka saki rayuwar Amina sakaka ba kwaɓa ba tsangwaɓa? Ragamar rayuwarta gaba-ɗaya aka saki ba kula ba hantara take yin duk abinda taga dama, Allah ya kyauta.

Bata ja maganar da nisa ba, don ba huruminta bane. Tsarinsu ne, suyi duk abinda suke so, rayuwarsu ne. Allah dai ya kyauta mummunan da na sani lokacin da komai ya daɗe da ƙarasa taɓarɓarewa. Kamar ta samu allon talabijin haka take bin Aminar da kallo har zuwa sadda ta gama shiryawa.

Wata shegiyar doguwar riga ta sanya, matsattsiyar doguwar riga ƴar kanti da ta bi jikinta ta lafe gaba-ɗaya kamar wata babyn roba. Irin yadda rigar ta ɗame ta sai kace babu sutura a jikinta.

Bayan ta gama shiryawar kuma, maimakon ko ɗan siririn gyale ne ta sanya ya sakko kafaɗunta a’a, sai kawai tayi wani irin ɗaurin ɗankwali da wani yalolon mayafi wanda da shi gara babu, ta saukar da gashinta da aka yiwa kitso da gashin doki ya sauka har gadon bayanta.

Ta ɗakko wani takalmi mai shegen tsini ta saka a ƙafafunta. Ta cewa Nauwara ta tashi su tafi bayan ta ɗauki wata mitsitsiyar jaka ta maƙala kafaɗarta.

Har sun kai bakin ƙofar fita daga ɗakin sai taja ta tsaya, ta juya tana kallon Nauwara sama da ƙasa kafin ta ce,

“Amma dai ina fatan ba a haka zaki bi ni ba ko?”

Da mamaki take kallon Aminar, sai kuma ta kalli jikinta a tsarge tana neman inda ta kwafsa, rashin ganin illar shigarta yasa ta ce,

“Kamar ya fa? Ban gane me kike nufi ba.”

“Haba Nauwara. Daɗina da ke har yanzu a duhu kike, saboda Allah da wannan zumbulelen hijabin na jikinki sai ka ce matar Liman? Ai sai ki sa mutane suyi mana dariya. Kuma da wannan hijabin ta ina za’a gane cikar gaba da baya balle har a ƙyasa?”

Ƙirjinta ne ya buga daram! Ita har yanzu a iskancin nata bata kai matakin da take iya yawo gayarta babu ko ɗan ƙaramin hijabi a jikinta ba. Gara ma a mafiyawancin lokuta idan ta fita takan canja babban hijabin jikinta ta saka ƙarami, ko gyale bata cika yafawa ba.
“Amina idan na cire hijabin ban san me zan sanya ba, sauri yasa ban ɗakko ɗan ƙaramin hijabin da nake canjawa idan na fita ba!”

“Ok! Matso ki ga.”

Da yake Arabian Gown ce a jikin Nauwara, sai Amina ta sanya ta cire hijabin ta ninke ta cusa a cikin jakarta. Hoda ta sake goga mata a fuskarta, ta gyara mata gira ya kwanta sosai ta goga mata janbaki sama-sama da man laɓɓa, nan da nan sai ga ta ta ƙara fitowa a kyakkyawarta. Gyalen rigar da yake ba wani mai girma ta naɗa mata a kanta, ga rabin gashinta da ba’a kitse ba duk a waje. Sai ta fito ta ƙara kyau sosai kamar balarabiya.

Saboda basaja da yadda Nauwarar take ta mitar kar wanda ta sani ya ganta a faɗawa Daddy sai Aminar ta ba ta face mask ta sanya.

Ita kuwa da ba damuwa tayi da kowa ba, wani makeken baƙin gilashi na Armani ta ɗauka ta sanya a idanunta suka fice daga ɗakin.

Masu aiki na musu a dawo lafiya ko kallonsu Amina bata yi ba. A bakin gate suka ci karo da wata galleliyar mota hummer jeep tana jiransu, Amina ta shige gidan gaba, ita kuma Nauwara ta shige gidan baya.

Tun daga gaisuwar da suka yi da haɗaɗɗen gayen da yaje ɗaukarsu Nauwara ta ji ta ƙara sarewa lamarin Amina gaba-ɗaya. Duk rashin kunyarta ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta iya kiran saurayi ya je har gidan iyayenta ya ɗauke ta ba.

Hannu bi-biyu ta buga tagumi tana kallon hanya, tafi-tafi suna zuga gudu a kan titi har suka shiga wata unguwa, sai ga su a ƙofar wani rantsattsen gida a Ƴan majalisu unguwar dosa.

A ƙofar gate ɗin gidan yayi fakin, Cikin yanga Amina tace mishi.

“Thanks! Idan mun gama zan kira ka.”

Ba tare da kunyar komai ba ya matsa da fuskarsa kusa da tata ya sumbaceta a laɓɓa, kafin ya amsa da.

“Ok!”

Amina na fita Nauwara ma ta buɗe ƙofa ta fita, kafaɗa da kafaɗa suke tafe har zuwa ƙofar ƙaton get ɗin gidan. Wata ƴar madanna Amina ta taɓa, babu jimawa sai ga sautin murya ana tambayarsu.

“Wa ye?”

Amina tayi ƙasa da muryarta tace,

“Sweet baby!”

Babu ɓata lokaci gate ɗin ya buɗe da kansa, ta shige ciki kanta tsaye, Nauwara ta bi bayanta zuciya na ɗar-ɗar kamar a ce kyat ta zura da gudu.

Motocine manya-manya har guda biyar a jere a farfajiyar gidan, motoci na alfarma, a ido kawai idan aka kalle su za’a gane ba ƙananun motoci bane. Tsoro da fargabar da zuciyarta ke ciki ya hana ta nutsuwa ta ƙarewa tsakar gidan kallo. Amina na tafe tana bin ta a baya har zuwa cikin wani haɗaɗɗe kuma tanƙamemen falo, da ya sha set din royal furnitures har biyu masu tsananin kyau.

Duk girman falon ƴanmata biyu suka tarar zaune akan doguwar kujera, da kallon ƴan matan za’a gane yara ne ƙananu, don a ido kamar baza su wuce sa’annin Manneera ba. Wani abu da ya ƙara ɗaga hankalin Nauwara shi ne ganin joint ɗin Shisha a gabansu suna zuƙa cike da gwanancewa. Jikinta ne ya ƙara sanyi ƙalau kamar an tsamo ta a ruwan sanyi.

A kasalance ta samu waje ta lafe akan kujera bayan Amina tayi mata umarnin zama. Amina kuwa ko a jikinta, da alamun ganin hakan ba baƙo bane a duniyarta. Kuma akwai sanayya a tsakaninta da ƴanmata don har sunayensu ta ambata, ta ƙara da tambayar ko kwanansu nawa a gidan?

Ɗaya a cikinsu ta ce mata uku, ɗaya ta ce mata huɗu. A cikin hirar da suke yi ne ta fahimci ƴar farar yarinyar mai suna Zully daga Kano take, ita kuma ƴar baƙar sunanta Molly daga zariya take.

Waya Amina ta ɗaga ta kira matar gidan ta sanar da ita isowarsu. Sannan ta maida hankali kan ƴanmatan suka cigaba da hirarrakinsu har zuwa lokacin da wata hamshaƙiyar mace ta fito.

Baki da hanci Nauwara ta saki tana kallon haɗuwa, matar duk da ta fara manyanta gaskiya ta haɗu ne ba ƙarya. Sanye take da doguwar rigar leshi wacce aka yiwa zaunannen ɗinki na manyan mata wanda ya ƙara fito da kyakkyawar tsarin jikinta. Hannuwanta da kunnuwa da wuya shaƙe da kayan ado na gwal, har da wata siririyar sarƙar gwal a ƙafarta. Fara ce sol kamar ka taɓa jini ya fito, ga ta da ƙiba wadda Nauwara bata taɓa ganin ƙatuwar mace irinta wacce ƙiba yayi mata kyau sosai kamarta ba.

Kujeran da ke fuskantar su ta zauna, ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗora tana ɗan karkaɗawa exactly zama irinna ƙasaitattun mata kafin ta mayar da hankalinta kan ƴanmatannan biyu.

“Zully ki tashi ki shirya, appointment ɗin ki karfe uku na rana za’a zo ɗaukar ki. Ke kuma Molly ki shirya za’a zo a fita dake yanzun nan.”

“To Mummy.”

Suka amsa a tare. Kafin suka miƙe zuwa cikin wani ɗaki da sai da a lokacin Nauwara ta lura da shi.

Hankalinta ta mayar kan su Nauwara, idanunta akan Amina da ɗan murmushi ta ce
“Sweet baby manya! Idon ki kenan? Kwana biyu kin yi wuyar gani.”

“Haba Mommy! Ke ma kin san in dai kuna nan mu ba komai bane! Da bazar da kuka riƙa mana muke taka rawa. Ke ce hanyar ko wane irin babban harka, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana Mummynmu.”

Cikin jin daɗin kirari da addu’ar da tayi mata ta amsa da.

“Amin Sweet baby.”

Sai ta mayar da idanunta kan Nauwara na ƴan wasu daƙiƙu kafin ta ce.

“Wannan fa? Ko ita ce wacce kika yi min maganarta?”

“Eh! Ita ce Mummy. Sabuwar shiga ce ba sabuwar shiga ba a harkar. Babbar matsalar dai iyayenta ne ke da tsauri da sa ido na masifa. Shi yasa har yanzu ta kasa wayewa a harkar. Sannan kuma ita ɗin ɗaliba ce, na san dai a cikin dabarbarunki tsaurin iyayenta da karatunta bazai bada matsala ba Mummy. Ya kike ganin za’ayi?”

“Don wannan ba matsala. Za’a ɗauke mata zuwa mahaɗa saboda tsagaita zirga-zirgarta. Zai zama duk sadda aka samu babban connenction da ya dace da ita ne za’a taɓo ta. Ko tana gida ko makaranta sai a tsara mata dabarar da za tayi ta samu amsa gayyata. Ina fatan dai kin faɗa mata duk tsare-tsare na? Kaso na da za a dinga ware min duk lokacin ta amsa gayyata. Sannan kuma monthly check up da zata dinga kawo min. Kuma sharuɗɗan da muka kafa su zamana an riƙe su gam! Ba gulma, ba munafunci, ba cin dunduniya, ba amsa gayyata a ɓoye ba tare da an sallami Mummy ba. Ƴan mata duk kin amince da sharuɗɗanmu?”

A tare Amina da Nauwara suka gyaɗa kai. Nauwara dai ta ɗaga kan ne ba don ta gamsu ko ta gane wasu sharuɗɗa ake magana akai ba. Kawai dai ta amsa ne saboda tun kafin shigowarsu Amina ta gargaɗe ta duk abinda aka ce ta ce ta amince.

Amina ce ta ƙara da cewa,

“Mommy kin san hakan duk ba matsala ba ce. Kawai dai mu connection muke so, irin manyan connection ɗinnan. payment ma kamar nawa zai kasance komai a hannunki yake, kawai dai idan an baki sai ki wari naki ki bamu sauran. Na san tsakaninmu ba cuta Mummy!”

Gyaɗa kai tayi tana murmushi kanta yana ƙara fasuwa, daɗin harka da ƙananun yara kenan. Da kai da kaya duk mallakar wuya ne sai abinda ta ga damar ba su.
“Ba ku da matsala. Yanzu de bari in yiwa likitanmu magana yazo ya auna mana ita don gane irin gyaran da za’a yi mata. Yadda take ɗanya shataf ɗinnan so nake ya gyara mana ita tsaf ta zamo sabuwa dal a leda. Ina fata dai tana shan magungunan hana ɗaukar abin? Kin san babban ganganci ne mace tai ta ɗauka tana zubarwa ko ɗan yaya ne dole gurin ya samu canji.”

Da sauri Amina ta ce,

“Sosai ma take sha Mummy. Kin san fa harkarnan dole sai ana taka-tsan-tsan! Tun da daɗewa naja kunnenta duk holewar da za’ayi ya zamo bayan amfani da kariya ne.”

Tana dariya ta amsa da

“Haka ne Sweet baby.”

Nauwara take ƙarewa kallo na tsawon mintuna biyu.

Ita dai kanta a ƙasa, duk a tsarge take. Ta bala’in ƙosawa su fice daga gidan saboda yadda take jin ta kamar akan ƙaya. Wani hausa mai kama da zaurance da matar da Amina suke yi duk ba ganewa take yi ba.

“Amina ƙawar nan ta ki ta haɗu gaskiya. Idan tayi saurin sakin jikinta ba ƙaramin daloli zamu samu da ita ba. Akwai manya da na sani sosai dake buƙatar irin ta. Sai ki cigaba da jan hankalinta kina nuna mata yadda abubuwan suke!”

Amina tayi wani murmushi na gogaggun ƴan duniya.

“Don wannan ba ki da matsala Mummy. Za ta bada mamaki cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda.”

“Uhmmm! Allah ya yarda.”

Ta amsa hankalinta na kan wayarta tana daddanawa. Minti ɗaya tsakani ta kara wayar a kunnenta, da alamun lamba ta lalubo ta danna kira.

Sai da aka ɗaga daga can ɓangaren aka fara magana sai suka fahimci da likita take waya.

Hankali tashe Nauwara take sauraren Mummyn da take umartar likitan maza ya katse duk abinda yake yi yazo da kayan aiki. Ga wata ɗanyar yarinya tana so a mata kankara a ɗinke ta dawo ɗanya shataf, sabuwar budurwa dal a leda.

A tsorace ta lalubi hannun Amina da take zaune kusa da ita ta ɗan matsa da ƙarfi, idanunta sunyi ƙwal-ƙwal kamar za ta saka ihu. Ta kasa magana, saboda ganin idanun Mummy a kansu yake.

“Hey! Menene? Ki kwantar da hankalinki. Babu zafin komai fa, allura suke yi a kashe zafin gurin, nima sai da suka yi min. Har aka gama ban san me ake ciki ba.”

Amina ta faɗa mata maganganun don kwantar mata da hankali.

<< Lokaci 36Lokaci 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×