Skip to content
Part 41 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Cikin jimami da damuwa sosai a fuskarta ta ce,

“To amma Malam, ta yaya zan samo waɗannan abubuwa da ka lissafa a matsayin mahaɗin aikin? Musamman ma dai gashin kan gawar da kace.”

Ya taɓe baki kafin ya ce,

“Wannan kuma ya rage na ki Yarinya. Idan kuma kin ga baza ki iya samo kayan aikin da kanki ba, za ki iya biya sai mu sanya waɗanda suka saba yi mana irin waɗannan ayyukan sai su samo mana da kansu. Ke sai ki kawo mana gashin kan Rahma, na san dai wannan bazai gagareki ba.”

Wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Tun da ta ji batun biyan kuɗi, ta san maƙudai zai buƙata waɗanda ba ta da su a halin yanzu. A ziyarar radio da ta dinga yiwa sauran Malamai da bokaye da ƴan tsibbu, duk anan kuɗaɗe da manyan kadarorin da ta mallaka suka ɗaiɗaice. Wani abin takaici kuma shi ne har yanzu babu wani ci gaba ko alamun samun nasara. Ranar auren Salim da Rahma sai ƙara matsowa yake yi.

“Malam, kamar nawa ake buƙata?”

Ta jefa mishi tambayar muryarta na rawa.

Ya sake ɓata lokaci yana lissafe-lissafe a jikin fai-fai, kafin ya ɗaga kai ya hau kora mata bayani. A taƙaice kusan tsabar kuɗaɗe har dubu ɗari takwas ya buƙata, kuma idan an kammala aiki zata bashi dubu ɗari biyar, ladan aikinshi. Don shi a tsarin aikinshi ba ya karɓan ko sisi sai buƙata ta biya.

Shiru tayi cikin ɗimauta da zuzzurfan tunani, bata san ta inda rabin kuɗaɗen za su fito ba ballantana gaba ɗaya kuɗaɗen. Kuma a maimakon zuciyarta ta nabba’a guri ɗaya, a’a! Sai ƙara kwaɗaita mata irin lagwada da uban dukiyar da za ta tara idan buƙata ta biya take yi.

A yanzu ba ta da wani buri a duniya da ya wuce a lalata zancen auren Salim da Rahma. Kishinta da hassada sun cika mata idanu da zuciya, gani take kamar ba za ta iya cigaba da rayuwa ba matuƙar bata rabasu ba. Ita dai kawai ta ga Rahma ta koma matsayin da take a da, tunda dai an ce ai ta inda aka hau ta nan ake sauka, ko kuma ma ita ta maye gurbin da Rahmar take kai a yanzu.

Da wannan dalilin yasa tayi shiru, ta zurfafa tunanin ina za ta samo maƙudan kuɗaɗen da ake buƙata kuma cikin gaggawa? Kwatsam! Allah yasa ta tuno da wata tsohuwar ajiyar sarƙar zinare da ta taɓa yi a cikin wani ɗan ƙaramin akwati can ƙarƙashin gadonta.

Ita kanta sarƙar asali ba mallakinta bane. Satar sarƙar tayi a gidan wani tsohon ɗan siyasa da ya taɓa kuskuren kai ta cikin gidanshi, in da yake rayuwa da matarsa ta sunna. A lokacin ita matar ba ta nan ta tafi Umrah. Ba tare da saninsa ba ta siɗaɗa har ɗakin matarshi ta dinga bincike kamar wacce tayi ajiya har Allah yasa ta ci karo da akwatin sarƙar, bata yi wata-wata ba kuwa ta ɗauke akwatin.

Gudun kar a cafkota sanye da sarƙar a wuyanta yasa fiye shekaru biyu bata taɓa gigin amfani da sarƙar ba. Ita kuma bata siyar ba, a taƙaice ta ma manta da sarƙar. Lallai da gaskiyar Mal Bahaushe da ya ce ajiya maganin wata rana.

Zuciyarta ne yayi mata wasai, lokaci ɗaya fuskarta ya faɗaɗa da murmushi. Tunawa da irin girma da ƙayatuwan zanen sarƙar, ta san zata iya samun fiye da kuɗin da Malam yake buƙata.

Tunawa da karin maganar a rashin tayi ake barin arha, yasa tayi kasa da murya cike da ladabi ta ce
“Malam don Allah a taimaka ayi min ragi. Wallahi ba ni da kuɗi, kuma ka ga zuwana na farko kenan, don Allah a sassauta a rangwanta min. Don Allah ba don ni ba.”
Ta ƙarasa maganar fuskarta a damalmale kamar za ta fashe da kuka.

Da farko kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ja, ta sake dagewa da magiya da roƙo, a ƙarshe dai da ƙyar ya ɗauke mata dubu ɗari a cikin maƙudan kuɗaɗen.

“Matsiyaci!”

Ta faɗi hakan a zuciyarta.

A fili kuwa ta duƙufa tana ta. mishi godiya da addu’o’i kamar wanda ya ɗauke mata biyan kuɗaɗen gaba ɗaya.

Suka rabu bayan ta alƙarwarta mishi a gobe-gobe za ta kai mishi kuɗin, jibi kuma za ta sake komawa ta kai mishi abubuwan Rahma da ya buƙata na mahaɗin aikinta.

Sun fito daga cikin yar bukkar tashi dake can tsakiyar wani jeji a can garin Kaciya, wanda kafin ma su je wajen sun kwashe fiye da mintuna arba’in suna tafiya a ƙafa kuma cikin rairayi, har kuma zuwa lokacin basu ga wata halitta ta gitta ta wajen ba.

Abinda ya ƙara tsuma Samira game da shi har ta sakankance tabbas aikinta kamar anyi an gama shi ne, lokacin da suka shiga cikin bukkar basu ga kowa ba.

Amma kuma da suka yi magana sai suka ji ana ta doka musu gyaran murya. Sai Lovina ta mata alamar da su dakata. Bayan kamar mintuna biyar kawai sai ganin mutum suka yi ya bayyana a sama, a zaune a kan iska kamar wanda yake zaune akan kujera. Hankalinshi kwance da carbi a hannunshi yana ja, haka yake zauna ɗas akan shimfidar wani baƙin buzu har ya ƙarasa ƙasa ya zauna.

Kafin suyi magana ya hau kora musu bayanan ko wanene su, da abinda ke tafe da su. Kai har ɗan ƙaramin hatsarin da ya kusa gitta musu lokacin da motarsu ta kusa yin karo da wata ƙatuwar mota sai da ya faɗa musu.

“Duk wanda ya kamo hanyar zuwa neman taimako guri na, tun daga gida ina ankare da halin da yake ciki. Ba don na tura an kawar da babbar motar daga kusa da motarku ba da yanzu sai dai wasu ba ku ba.”

Da waɗannan kalamai da abubuwa ya gama kame zuciyar Samira kam, ta ji a ranta ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, lallai zai iya yi mata wannan gaggarumin aiki da yake gabanta.

Har sun fara yin nisa da bukkar, Lovina ta dafe kirji tace,

“Kash! Ji wani ragon azanci irin nawa. Kinga na manta da makullin motata a bukkar Malam. Na san kin gaji, don baki saba irin wannan doguwar tafiyar ba. Kin ga zauna kan dutsen can, bari in juya da sassarfa in ɗakko.”

“To shi kenan. Allah Ya taimakemu ma kin tuna da wuri, da yanzu sai mun fita har can bakin titi kafin ki tuna ai da mun shiga uku!”

“Bari ke dai.”

Ta juya da saurin gaske.

Ita kuma Samira ta zauna kan dutsen da Lovina ta nuna mata zuciyarta cike da lissafin yadda rayuwarta za ta canza da irin wulaƙancin da za ta shata in dai har Salim ya aureta.

“Ai Wallahi Najeriya ma tayi min kaɗan, ƙasashen ƙetare kawai zan koma da zama, acan zan cigaba da rayuwa. Ni da Nigeria sai jefi-jefi.”

Ita kaɗai take ta sakin murmushi tana ayyana yadda komai na rayuwarta da ya fara taɓarɓarewa zai saitu sannu a hankali.

Ita kuwa Lovina tana komawa cikin bukkar ita da Malamin tsubbun suka kwashe da dariya har da tafa hannu kamar wasu abokai.

“Shege Idris. Ni yanzu naga sai ƙara ƙwarewa kake yi a harkar nan kamar dai dama can aikinka ne! Ka kuwa ga yadda ka zurma mutuniyar? Yadda ta yarda da abinda kace wallahi ko wuta kace ta shiga babu zafi, afkawa ciki zata yi a guje.”

Ƙaƙƙarfan dariya ya saki irinta bosawa ya ce
“Ke harkar nan ai na faɗa miki ba sauƙi, dole ne sai muna yin yadda za su ƙara yarda da mu ɗari bisa ɗari. Ba gashi yanzu ta yarda za ta saki bakin jaka ba?”

“Ƙwarai kuwa! Ni dai yanzu alƙawarinmu kada ka manta da shi, ka raba su biyu cass ka aiko min da rabona ta cikin account. Ina jin daɗin harka da kai, saboda ba ka yin irin na sauran yan iskan malaman bogi, kai tsaye kake turowa da mutum kason shi babu hauma-hauma, shi yasa kaga ina kawo maka waɗanda nasan zasu buɗe mana jaka mu yi bushasha!”

“To ai adalcin kenan mutuniyar. Wacce tayi maka sanadin arziki kar ka manta da ita wurin sharɓan romom demokraɗiyya. Allah dai ya ƙaro mana kasuwa.!”

Dariya suka sake yi a karo na biyu sannan ta fice da sauri gudun kada Samira ta zargi wani abu, hannunta riƙe da makullin motarta.

Suna tafiya tana ta ƙara yiwa Samira rijiya, ita kuwa sakarar ta dage sai washe baki take jin an ce tana gab da shiga sahun manyan mata da ake ji da su a faɗin jihar kaduna.

*****

Sai yamma liƙis suka shiga Kaduna, duk da tsananin gajiyar da tayi, hakan bai sa tayi ƙasa a gwiwa ba, da zafi-zafi ake bugun ƙarfe. Don haka daga gidansu Lovina ko da ta tare adaidaita maimakon ta nufi gida a’a, gidansu Rahma ta nufa kai tsaye.

Ko da mai keke ya sauke ta ta sallame shi ta fita tsayuwa tayi tana ƙarewa danƙareren kofar get ɗin gidan kallo, ranta fal kishi da baƙin ciki.
“Yanzu ace wai Rahma ce take rayuwa a wannan daular? Rahmar da ni nayi mata sanadin wannan tagomashin, ni na zame mata tsanin da ta taka har ta kai ga wannan matsayin da take ciki, amma shi ne ita da ta hau sai ta kasa taimaka min domin ni ma inyi sama ƙololuwa fiye da ita?”
Taja ƙaƙƙarfan tsaki, sannan tayi ƙwafa zuciyarta a ƙuntace. Daƙyar ta iya dannar zuciyarta ta ƙarasa zuwa gidan.

Gida ne lafiyayye mai kyau kuma na ƴan gayu, tun daga waje zuwa ciki ya sha kayan ado na zamani da kerawa sa’a. Hawa ɗaya ne gidan bene, ga ma’aikata iri-iri suna ta karakaina. Ko da ta shiga ciki babbar sa’ar da tayi ita ce da ta samu Rahma bata nan, sai Iyallu kaɗaii a gidan.

Iyallu ta tare ta da murna da farincikin ganinta, har ga Allah ta ji daɗin zuwanta, don kuwa tunda buɗi ya fara samuwa ga Rahma sai ta ɗauke musu kafa. Ta sa aka cika gaban Samira da kayan ciye-ciye da na lashe-lashe, soyayyen nama, tun daga kan na sa da karamar dabba da kaza, ga dambun nama, ga lemuka, ga su cake, su doughnut.

Dama ba ƙaramar yunwa ta kwaso ba, don haka ta miƙe ƙafa ta dinga naɗar abubuwan nan sai da ta kusa cinye abubuwan da aka kai mata.

A cikin hirar da suke yi ne ta dinga bugar cikin Iyallu tana kwasar labarai. Ta cewa Iyallun zuwa tayi dama taji an ce Rahma ta kusa aure, ta zo ne ta taya ta da wasu hidindimun bikin nata a matsayinta na babbar ƙawarta.

Ita kuwa Iyallu tana ta sanya mata albarka da nuna jin daɗinta. A cikin hirar tasu take faɗa mata ai Salim ya sanya Rahmar a makarantar jami’a, yanzu haka ma tana can saboda jarabawa suke yi, to kuma daga can makaranta za su je wajen yin hoton pre-wedding da ake yayi, shi yasa bata dawo ba har yanzu. Tana ta jaddada mata irin matsanancin son da Salim yake yiwa Rahma, da yadda Allah ya tarfawa garinsu nono, yanzu gashi sun tashi daga sahun marasa shi sun koma mawadata. Har alkawarin da Salim ya yiwa Rahma na fitar da ita ƙasar waje idan ta gama karatunta domin ta ƙaro wani karatun akan hakkin dan Adam sai da ta faɗa ma Samira.

Ita dai tana ta saurarenta tana ɗan yamutsa baki fuskarta ɗauke da murmushin yaƙe, a can ƙasan ranta tsinuwa take saukewa Iyallu da Rahmar gaba-ɗaya, zuciyarta ɗauke da mugun fata kala daban-daban.

Da aka yi magriba tace sallah zata yi, kai tsaye Iyallu tace ta shiga ɗakin Rahma tayi sallar a can kafin ta dawo. Dama abinda take so kenan. Don haka da saurinta ta shiga ɗakin, cikin tsananin sa’a, ta tsamo tsilin gashin Rahma a jikin matajin kanta, kamar kuma don ita sai ta tsinci faratun Rahmar a jikin sink ɗin banɗakin dake maƙale da ɗakinta, da alama yankan farce tayi kafin ta fita. Tsabar murna sai da ta tsaya ta cashe sosai ta girgije, kafin ta fiddo dan kyalle daga cikin Jakarta, ta dauki tsilin farce da gashi ta naɗe. Burinta ya cika.

Ta koma cikin ɗakin tana ƙarewa kayan alatun da aka zuba a ɗakin Rahmar kamar wata matar sarki. Ta dinga ƙwafa ita kaɗai tana masifa tana jan tsaki.

Fita tayi ta samu Iyallu a falo itama ta idar da sallah, ita kwata-kwata ta ma manta sallah ta shiga yi. Yini suka yi shige da fici ita da Lovina, ko Azzuhur da la’asar ma bata yi ba.

Ta gilla ma Iyallu ƙaryar Mamanta take kiranta ta ce tayi sauri kiran gaggawa ne.
“A ba Rahma haƙuri Iyallu, zan dawo ko gobe ko jibi. Na gode ƙwarai, Allah ya sanya alkhairi.”

Iyallu ita ma tana ta godiya, har da ɗaukar dubu biyar ta bata tace ta hau mota. Ta sanya hannu ta karɓe tana ƙara godiya.

Tana fita daga gate ɗin gidan ta juya ta watsawa gidan harara tare da ƙwafa
“Hmmn! Duk za ku ci ƙaniyarku. Ko yaushe tayi wani kuɗin bani don tsabar rainin wayau wai har da cewa inyi kudin mota? Ko da yake, raba mugu da makami dama ai ibada! Ni duk ranar da tazo wajena ma babu sisin kwabo da zan bata daga ita har wannan tsohuwar kilakin diyar tata!”
Ta sake jan tsaki sannan ta ƙara gaba da sauri don kar tsautsayi yasa Rahma ta iske ta a gurin.

Acaɓa ta tara ta hau ya kaita har kofar gidansu.
Kamar ɓarauniya haka ta saci jiki ta shiga gidan. Tsoronta ɗaya shi ne kada Allah sa suyi arangama da Mamanta.

Da Allah Ya taimaketa ta samu tana yin sallar isha’i, sai ta saɗaɗa ta fada ɗakinta ta ɓame. Babu wanda ya kula da shigarta balle ace tana gidan ma.

Washegari ma tunda sassafe zakara ya bata sa’a ta fita. Bayan ta gama yawace-yawacenta, ta dire a kasuwa wajen saida gwala-gwalai. A ba a yi mata cinikin kirki ba ma, miliyan ɗaya da rabi aka bata. Tayi murna kamar me.

Saboda tsabar ɗoki da jindadi kasa daurewa tayi, ta kira Lovina tace taje ta rakata ta kai ma Malam kuɗin aikin, sai tace mata bata gari, amma tunda za ta iya gane hanya, taje kawai ta kai mishi.

Ta kuwa ɗauki hanya ta kai mishi kudin da kuma gashin da farce. Shi kuma yayi mata alkawarin nan da kwana biyu idan ta koma, zai bata kwalli wanda zata yi tozali dashi, suna hada idanu da Salim, shikenan zance ya kare! Zai rabu da Rahma a take, kuma a cikin satin zai aureta.

Da wannan ta koma gida cikin tsananin doki da murna, tana jiran kwana biyu ya cika ta koma ta amso abinda zai farraka masoya.

<< Lokaci 40Lokaci 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×