Skip to content
Part 44 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Kuma…”

Bata san sadda ta ɗaga ɗan yatsarta manuniya ta ɗora akan laɓɓansa ba. Ta riga ta fahimci matsanancin son da yake yi ma yarinyar tun daga labarin farkon haɗuwarsu da ya bata. Don haka a yanzu babu amfanin yayi ta jaddada mata irin son da yake mata, wanda hakan ba ƙaramin luguden daka yake saka ƙirjinta yi ba.

‘So tsuntsu ne. Yana tashi daga wannan bishiyar zuwa wancan.’
A yanzu ne ta ƙara yarda da gaskiyar azancin maganar nan ta Malam bahaushe.

Katse shi da tayi ta hanyar ɗora yatsarta a laɓɓansa yasa shi dakatawa daga faɗin abinda ke zuciyarsa. Tsawon wasu daƙiƙu, idanunsa na kanta, kallonta yake yi, yana ƙoƙarin karantar yanayinta. Amma ya kasa fahimtar komai, saboda ninkakken yanayi ne a fuskarta.

Lura da irin kallon da yake bin ta da shi yasa Ziyada lumshe idanu.
‘Allahumma ajirnee fi-musibati, wa-aklifnee khairan minha.’
Ta maimaita sau uku a zuciyarta kafin tayi ƙarfin halin buɗe idanunta ta ɗora a kanshi.

Hannuwansa biyu ta kamo ta riƙe a cikin nata, duk yadda ta so ɗora ma fuskarta dariya ko ta yaƙe abin ya gagareta, don haka ta watsar ta fara magana tsakanin sanyin murya da zafin murya.
“Abban Nauwara, tun da ka bani labarin soyayyarku na fahimci matsanancin son da kake yi ma Bilkisu. Yanzu abinda nake so in fahimta, menene amfanin ɗauko/sato musu yarinya da kayi? Kar dai ka ce min matsanancin son da kake mata har ya rufe maka idanu ka kasa gane daidai da rashin daidai? Yarinya ƴar gidan Babban malami, wani irin baƙin fenti kake ƙoƙarin gogawa a zuri’arsu? Me yasa…”

“Umman Nauwara don Allah ki dakata da irin waɗannan zantukan naki da suke ƙoƙarin tarwatsa min zuciya. Ki fahimce ni, nayi iyaka ƙoƙarina gurin neman auren yarinyar nan a mutunce ba tare da na ƙetare iyaka ba. Amma ido da ido mahaifinta ya ce bazai ba ni aurenta ba, ya kike so inyi? Ba ni da wata mafita da ta rage min face wannan…”

“Tir!!! da wannan mummunar mafita taka Khamis! In dai mafitar da kake nufi ita ce ka ɗauko nutsattsiyar yarinya ka lalata ta, a ƙarshe ciki ya ɓulla a jikinta, iyayenta su aura maka ita ko suna so ko ba sa so, tir da wannan mafita… Wai tsaya ma in tambaye ka? Bayan matsanancin cakwakiyar da ka fuskanta lokacin da ka nuna kana son aure na, a karo na biyu ka sake fuskantar matsananciyar tsana da kyara lokacin da ka nemi auren Rufaida marigayiya, yanzu a karo na uku ƙeƙe da ƙeƙe mahaifinta ya faɗa maka bazai ba ka aurenta ba. Kai a karan kanka ka taɓa tsayawa ka yi tunanin wani naƙasu ne ke tattare da halayenka da duk sadda ka nemi aure bayan bincike ake cewa baza’a aura maka ba…?!”

Da wani irin tsawa da matsanancin ɓacin rai a fuska da muryarsa ya katse ta da cewa
“Dakata Ziyada…!!”

“Bazan dakata ba Khamis!!!”
Ita ma ta katse shi a tsawace.

Izuwa wannan lokacin, tuni sun saki hannayen juna. Sun miƙe tsaye suna kallon juna a zafafe kamar zakarun da ke shirin dambatuwa.

“Yau gaskiya mai ɗacin da baka so a faɗa maka ita ce zan sake faɗa maka. Wani nagartaccen uba ne zai ɗauki yarinyarsa ya aura ma Namijin da ba shi da aiki sai aikata Zina da ƴanmata kala-daban daban? Wani nagartaccen uba ne zai ɗauki ƴarsa ya aura ma mutumin da bashi da wata ƙwaƙƙwaran sana’a sai kawalci? Ka zama babban jakada na haɗa Zinace-zinace tsakanin al’umma. Yawan ƴaƴa mata da Allah ya baka bai sa ka hankalta ka daina aikata miyagun ayyukan da ka gina rayuwarka akansu ba.

Ko an faɗa maka ana yima Allah wayau ne?”

Tayi wani dariya mai ciwo idanunta ciccike da hawaye kafin ta cigaba da cewa.
“Ka ci ƙarya ka kwana da yunwa Khamis. Wai kai a tunaninka duk munanan ayyukan da kake aikatawa a ɓoye mutane basu sani bane? To bari kaji, tuntuni an daɗe da daina kiwon dabba, mutum ake kiwo.

Duk wani guje-guje da kake yi kana ganin kana ci da buguzum mutane suna kallonka. Allah SWT talala yayi maka. Ina jiye maka tsoron yin da-na sani a lokacin da bai da amfani, idan baka tuba taubatun nasuha ba, da sannu Allah zai kama ka kamu mai tsanani, a lokacin da damar tuba ya ƙure maka.

Wallahi ba wannan yarinyar Bilkisu da iyayenta suka kasance malamai ba, ko ni ce iyayena suke raye kuma kake wannan halin da mummunar sana’ar idan soyayyarka zai yi ajalina baza su taɓa aura maka ni ba…”

“Au! Haka kika ce?”
Ya tambayeta yana wani irin murmushi da kallo ɗaya za’a mishi a fahimci irin murmushin nan ne mai ciwo.

“Ƙwarai… kuwa!!!”
Ta amsa muryarta na rawa, haɗe da saukar wasu zafafan hawaye daga idanunta.

Taku ɗaya, biyu, uku yayi ya ƙarasa inda take tsaye, fuskarsa a murtuke.

Duk da tsoratar da tayi a tunaninta marinta zaiyi, ko gezau bata yi daga inda take tsaye ba. Har lokacin idanunta sun kasa daina tsiyayar da zafafan hawaye, laɓɓanta sai rawa yake yi.

Kallon cikin ido suka yi na tsawan daƙiƙu talatin, fuskarshi na bayyana matsanancin ɓacin rai da takaicin ɗacin da munanan kalamanta suka jefa zuciyarsa a ciki.

A yayinda nata fuskar ke bayyana rauni, ƙunci, damuwa, raɗaɗin tono baƙin al’amarin da tuntuni yake danƙare a zuciyarta.

“Ziyada, idan na fahimci kalamanki dakyau, a iya tsawon shekarun da muka kwashe muna zaman aure kamar babu wani abu na alfahari da kika tsinta a tarayyarki da ni mijinki uban ƴaƴanki. Ayau ke ce har kika iya tsayawa a gabana kina faɗa min da iyayenki na raye baza su taɓa aura min ke a matsayin mata ba, da kika fahimci haka, kuma kika san munanan halaye na da mummunar sana’ar da nake yi, meyasa baki taɓa neman maraba tsakanina da ke ba…?”

“Darajar ƴaƴana kake ci Khamis”
Ta amsa kai tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba.

Hannu biyu tasa ta fara goge hawayen idanunta amma sun gagara tsayawa, tana goge wasu suna sake sakkowa a guje kamar an buɗe famfo. Da ta fahimci hawayen ba masu tsayawa bane, sai ta sauke hannayenta ta daina goge hawayen ta cigaba da magana muryarta na rawa. Ayau ba sai gobe ba, za ta zazzagewa Khamis duk wasu alfarmomi da take mishi darajar ƴaƴansu yake ci.

In da Allah ya taimaketa shi ne tana daga cikin mutanen da duk matsanancin kukan da suke yi magana ba ya gagararsu.
“Na rantse da Allah… ba don ƴaƴan da ke tsakanina da kai ba kuma huɗu a cikin biyar ɗin mata ne da tuni na daɗe da ficewa daga cikin rayuwarka Khamis. Ko da kuwa son da nake maka zai sa in ƙare rayuwata ba tare da auren wani namijin a kaina ba. Yo Ina ma ƙudan yake balle romonsa? Matsanancin soyayyar da nake maka tuni ka daɗe da tsiyayar da shi saboda baƙin cikin munanan halayenka da mummunar ɗabi’ar da ka riƙa a matsayin sana’arka. Ko a addinance idan na nemi rabuwa da kai da gudu alƙali zai tilastaka ka sake ni, domin babu komai a cikin zama da kai face halaka!! Amma ban taɓa yunƙurin yin haka ba, ba don komai ba kuwa sai don darajar ƴaƴana…”

“Na sake ki Ziyada!!!”

A bazata, kalmar ta dira a kunnuwanta.

Wani abin mamaki shi ne da shi da ya furta kalmar sakin, da ita da ya furtawa kalmar, idanunsu a warwaje suke kallon juna.

Kamar dai ba kalmar sakin yayi niyyar furtawa ba, amma magana zarar bunu… Sai kuma bakinsa yayi masa wani irin nauyi sosai, ya kasa buɗe baki ya soke kalmar sakin ko kuma ya ƙara jaddada kalmar.

Har sai da ita da kanta ta ce
“Ka sake ni Khamis??”
Ta tambaye shi da wani irin rauni sosai a muryarta tana nuna kanta da yatsarta manuniya, idanunta a kanshi tana girgiza mishi kai, kamar dai tana son jin abinda zai furta na gaba ya kasance ya ƙaryata kalmar sakin ne.

“In dai zama da igiyar aure na halaka ne a gare ki Ziyada, darajar ƴaƴa kawai nake ci, na sake ki saki ɗaya Ziyada. Banyi lalacewar da zan zauna da matar da take ganin zaman aure na da ita alfarma take min ba. Ki je, ki bar min ƴaƴana domin ba da su na auro ki ba. Zan bi duk hanyar da zan bi in auri Nana Bilkisu, za ta riƙe min ƴaƴana bisa amana. Kuma ko rantsuwa nayi babu kaffara na tabbata baza ta taɓa goranta min kan halina da sana’ar da nake yi ba, a matsayinta na mai ilimin addini, na tabbata za ta dage da yimin addu’a mai tsanani har zuwa lokacin da Allah zai raba ni da waɗannan munanan halaye nawa.”
Yana gama faɗin haka, bai jira cewarta ba yaja ƙafafunsa da sassarfa ya shige cikin ɗakinsa.

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!”
A bazata ta ji bakinta ya janyo kalmar a fili. Kamar wacce aka yi ma umarni sai ta cigaba da maimaitawa da sauri-sauri. Hakan, shi ya taimaka mata ƙwarai gurin samun gaggarumin sauƙi daga cikin ɗimuwar da sakin ke neman jefata a ciki.

Ta ɗauki tsawon mintuna uku tana maimaitawa kafin ta iya ɗaga ƙafafunta da suka yi sanyi ƙalau ta wuce zuwa ɗakinta. Ko da ta shiga ciki, tsaye tayi a tsakar ɗakin ta ma rasa me za ta aikata?

Karaf! Idanunta ya faɗa kan babban hijabin sallarta da yake ninke ajiye akan dadduma a durowar gefen gadonta. Hijabin ta ɗauka ta zumbula a jikinta, ba tare da damuwa da yadda hijabin yake jan ƙasa ba, har ta nufi ƙofa za ta fita sai ta koma cikin ɗakin ta ɗauki wayarta da yake ajiye a gefen gado, jakarta da take zuba kuɗi da Atm card ɗin ta na banki. Ta fice daga cikin ɗakin da sauri, har ta kai tsakiyar falon sai ta koma ta janyo ƙofar ɗakinta ta murza makulli ta rufe, ta zare key ɗin ta jefa a jaka. Ta fice daga cikin falon ba tare da waiwaye ba.

******

“Sauda? Kin ga kalle ni nan! Nutsu kiyi min bayani, kika ce me ya samu Nana Bilkisu?”
Sheik Abulfatahi ya sake maimaita mata maganar da tambayar a tausashe. A fuska idan aka kalle shi, baza’a taɓa fahimtar tashin hankali da matsanancin fargabar da zuciyarsa ke ciki ba. Amma fa da ana iya tona zuciyarsa a gani… Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un!

“Baaba…”
Saudah taja sunan da duk yaran gidan ke kiran Malam ɗin cikin kuka, sai jan numfarfashi take yi kamar za ta sume.

“Za ki faɗi abinda kika sani ko sai na daka ki anan gurin?”
Mahaifinta yayi maganar cikin tsawa yana waige-waigen neman abinda zai mata rubdugun duka da shi.

Da matsanancin tsoro taja mazaunanta da sauri ta muskuta kusa da Malam ɗin. Domin a fuskokin duk mazauna falon, a fuskarsa ne kawai take hango ɗan dama-dama na sassauci da nutsuwar zai iya fahimtarta.
“Baaba.. Wallahi Allah ba ni da hannu ko masaniya a ɗauke Bilkisu da aka yi. Ban san komai ba, na rantse da Allah. Abinda na sani kawai…”
Cikin kuka ta bada labarin yadda saurayinta Falalu ya uzzura mata akan duk sa’adda Nana Bilkisu ta fito daga gida ta faɗa mishi, akwai saƙon da zai ba ta.

“Ban zafafa ya faɗa min wani saƙo bane saboda ban taɓa tsammanin niyyar cutar da ita yake yi ba. Kawai abinda na sani na kira na faɗa mishi ina tare da Bilkisu a gidansu Farida. Ba’a daɗe ba ya kira ni ga shi a ƙofar gidan, inyi mata dabara mu fita tare. Ko da muka fita bayan gaisuwa sai na lura kamar maganar sirri yake so yayi da ita, don haka na raɗa mata a kunne tayi haƙuri ta jira ni fitsari ya matse ni… Tun daga nan, bayan shiga ta cikin gidan da fitowata ban ɗauki minti biyar ba, ko da na fita, ba Falalu ba Bilkisu, hankali tashe na fara kiranshi a waya baya ɗagawa, daga bisani kuma ya kashe wayarsa… Shi ne, shi ne, sai na tafi gida ban koma gidansu Farida ba… da na kasa nutsuwa sai na faɗa ma Hajiyarmu abinda ya faru ba tare da sanin Alhajinmu na gidan ba…”
Tana zuwa nan a maganarta ta sake fashewa da ƙaƙƙarfan kuka kamar za ta shiɗe.

Shiru ne ya ratsa falon na tsawon wasu daƙiƙu, ba abinda ke tashi sai sautin kukan Sauda, hankalinta a tashe, a tsorace take sosai, domin mahaifinta ya rantse mata da Allah idan ba’a ga Bilkisu ba da hannunsa zai damƙa ta hannun ƴan sanda, ko kashe ta za suyi babu abinda ya dame shi. Tunda dai har da ita ne za’a haɗa baki a cuci aminiyarta.

“Ina lambar wayar Falalun? Ɗan gidan waye a garinnan?”
Babban yayansu Bilkisu Alhaji Idris ya tambayi Sauda.

Jikinta na rawa ta lalubo lambar Falalu a wayarta, saboda ɗimuwa ta kasa karanta lambar, sai kawai ta miƙa masa wayar gaba ɗaya.

“Ɗan gidan Alhaji Ibrahim mai Alawayya ne na can ƙofar Kuyan Bana.”
Mahaifinta ya bada cikakken sunan mahaifin Falalu.
“Kayi haƙuri Malam. Ɗan yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba. Kamar yadda kuka ji daga bakin Saudatu, ban san komai akan wannan lamarin ba, ko jin da nayi Allah ne ya ƙaddara domin da ta san ina gidan baza ta taɓa faɗawa uwarta ga halin da ake ciki ba. Yanzu ga ta nan, ni zan koma gida, duk yadda za kuyi da ita kuyi har zuwa sadda Bilkisu za ta bayyana, tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa zai doka…”

“Alhaji Ibrahim mai Alawayyo, ba shi ne abokin Baban yaronnan Hamisu da sukai ta zuwa gidannan nema ma yaron aurenta ba?”
Malam yayi tambayar idanunsa na kan Alhaji Idris, ba tare da ya bi ta kan maganganun Alhaji Nura mahaifin Sauda ba.

“Shi ne Malam. Ƙwarai kuwa shi ne.”
Ƴan’uwan Bilkisu biyu suka haɗa baki gurin amsawa.

Ko da akayi ta kiran Falalu wayarsa a kashe sai Malam ya bada lambar mahaifinsa aka kira, cikin sa’a kuma kai tsaye wayar ta shiga.

Hankalin Alhaji Ibrahim ba ƙaramin tashi yayi ba bayan gama sauraren bayanin abinda yake faruwa daga bakin Sheik Abulfatahi. Salati da sallallami yake ja yana ƙara maimaitawa, hankalinsa a tashe yake koro duk wasu bayanai da za su wanke shi a idanun Sheik don tabbatar mishi bai da masaniya ta kusa ko ta nesa kan abinda yake faruwa…

<< Lokaci 43Lokaci 45 >>

1 thought on “Lokaci 44”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.