Akan idanunta Fadila ta taɓe baki, sai kuma ta ce,
“Oho! Wallahi rabona da shi tun jiya da safe da ya kawo ni makaranta.”
Duk da yadda hankalinta ya ƙara ɗugunzuma sai tayi ƙoƙarin dannewa
“Ke da Yayanki Fadila? kuma babu ta yadda za ayi a san halin da yake ciki? Kin san bai da lafiya fa… kuma nayi ta kiran layinsa wayar ba ta shiga. Ya jikin nashi? Ya ji sauƙi?”
“Toh! Ya ji sauƙin kenan. Tunda lafiya ai ita ke ɓuya.”
Fadila ta amsa da rashin damuwa. Mannirah ta buɗe baki za ta sake magana Fadila tayi saurin katse ta da cewa.
“Kin ga bari in je, Mummy na jira na a gida. Idan mun haɗu zan ce mishi kina nemanshi. Bye…”
Bata jira Mannirah ta sake cewa wani abu ba tayi wuf ta faɗa mota direba ya ja suka tafi, suka bar Mannirah tsaye tana raba idanu zuciyarta cike da tunani.
Daƙyar ta iya jan jiki ta shiga keke napep, Har suka ƙarasa gida kuwa bata san sun isa ba tana ta aikin saƙa da warwara. Ta ja ƙafafu kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta shiga gida.
Hannunta har rawa yake yi lokacin da ta janyo wayarta daga kan cikin kayanta taga kiran da aka rasa har uku na Muhsin, mintuna talatin da biyu da suka wuce. Jikinta babu inda ba ya rawa ta bi bayan kiran, a fili take addu’ar Allah yasa ya shiga, kuma ya ɗauka, ta ji halin da yake ciki ko hankalinta zai kwanta.
Bisa ga tsananin sa’a kuwa sai ga wayar ta shiga. Ta saki wata irin wawiyar ajiyar zuciya, saboda tsabar sanyin da jikinta yayi na jin daɗi, sai da taji gwiwoyinta sun sage sun kasa ɗaukarta, ta koma gefen gado ta zube yaraf kamar wata marar laka.
Tayi kasaƙe tana sauraren ƙaran shigar kiran, duk bugawa ɗaya tana jin zuciyarta na tsalle da katantanwa a cikin ƙirjinta.
Sai can har ya kusa tsinkewa zuciyarta cike da taraddadin watakila ba za a ɗaga ba, sai kuma ya ɗaga daga can ɓangaren. Murya can ƙasa sosai kamar wanda yake tsoron magana ya ce
“Hhhe…llowww….!!”
Ya ƙarƙare kalmar yana ƙara jan ta da karan madda shida.
Bugun zuciyarta ta ƙara ninkuwa, muryar ta na rawa da karkarwa ta ce,
“Mmmee… ya ke damunka Hayatiy? Jikin naka ne ya matsa? Ina cikin tashin hankali fiye da tunaninka Wallahi. Don Allah ka faɗa min kana lafiya?”
Ta ƙarasa maganar a raunane kamar za ta fasa ihun kuka.
Muryarshi ta kara yin ƙasa sosai ya amsa da
“No… nothing baby… Babu kkkoo… mi… Kawai dai zazzaɓin ne bai sauka ba har yanzu, ga ciwon jiki… Ina tunanin ko ulcer ta ce ta motsa!”
Nan da nan sai ta ƙara shiga cikin damuwa, hawaye ya ɓalle mata kamar an buɗe famfo, bai ankara ba sai shessheƙarta yaji alamun kuka take yi, kafin yayi magana tace
“Kamar ya ba wani abu bane Ƙalb? Bayan ka taɓa faɗa min idan ulcer ɗin ka ta tashi tana baka wahala sosai da sosai? Na shiga uku…”
“It’s ok Baby… Kar ki damu kanki don Allah balle har ki ƙara min ciwo. Babu wata wahala da zan sha in Allah ya yarda, Though dai gani nan bana iya ko motsin kirki… Amma dai an sa min drip kuma anyi mun allurai, so I’ll be fine. Ki kwantar da hankalinki pls Sweetheart.”
Ta gyaɗa kai a sanyaye kamar yana kallonta, har lokacin hawayen bai tsaya mata ba amma ta rage ƙarfin shessheƙar da take yi.
“Shi kenan Ƙalb, Allah ya ƙara sauƙi. Don Allah ka dinga shan magungunanka akan lokaci, na san baka son shan magani, kaji Habeebee?”
Ƴar dariya ya saki ta ƙarfin hali, daga jin sautin dariyar ma ba ƙaramin jin jiki yake yi ba,
“Na yi alƙawari, zan yi duk abinda kika ce Baby. Amma dai da zan samu in ganki a halin da nake ciki… a sukwane zan ji na warware… Amma de… kar ki damu kanki… Ba komai… Na gode da kulawarki Love…”
“Ka san hakan ba zai yiwu ba Ƙalb, kayi haƙuri. Ni dai kayi ƙoƙarin shan magani domin ka warke da wuri. Then sai ka zo da kanka ka ganni in ganka hankulanmu su kwanta gaba ɗaya!”
A sanyaye ya ce
“To shikenan babyna, na gode sosai da sosai”
Da haka suka yi sallama bakinta bai gajiya ba gurin jera mishi addu’o’in samun sauƙi a gaggauce har ya katse wayar.
Wannan wayar da suka yi ya ɗan kwantar mata da hankali, har ta iya cire kayan jikinta ta canza da na gida tayi sallah.
Ta fita zuwa kicin ta ɗora abincin rana duk da bata san lokacin da Nawwara za ta dawo ba.
Sauƙaƙaƙƙen abinci tayi ta gama cikin ƙanƙanin lokaci, don ma Allah Yasa Mommynsu ta saba musu da ɗabi’ar haɗa miya da sauran side dishes da suke ajiyewa a freezer saboda idan girkin gaggawa ya faɗo musu ko baƙi kai tsaye suyi amfani da shi. Don haka ko a yanzu da Mummy ba ta nan itama Mannirah idan ta samu lokaci ta kan ɗan yi abinda zata iya ta ajiye.
Tana gamawa, ta zuba wanda zata iya ci a plate, ta jera na Daddy a kuloli ta jera a basket, a niyyarta idan ta gama cin abinci a gaggauce za ta kai musu abinci asibiti daga can ta wuce islamiya.
Sai gab da magriba ta koma gida, bata yi wani mamaki ba da taga har lokacin Nauwara bata dawo ba. Domin ta faɗa mata duk ranar da taga ta daɗe to ta shiga hostel ne gurin ƙawayenta suyi karatu saboda jarabawar da yake tunkaro su.
“Kin san bitar karatu cikin mutane ya fi daɗi, in da baki iya ba za’a tunasar da ke kema za ki tunasar da wasu inda basu iya ba ke kin iya.”
Ta tuno maganganun Nauwara kamar a lokacin take faɗa mata.
Kayan jikinta ta canja, ko da ta duba abincin da suke da shi a cikin kula sai taga zai ishe su a wadace ita da Nauwara. Ba buƙatar sai ta sake wani girki, daman Daddy ya faɗa musu ba dole ne sai sun kai musu abinci safe, rana, yamma ba, duk sadda suka samu sararin dafawa kawai a zuba mishi.
A falo ta zauna tana jiran a kira sallar magrib, sai kuma ta miƙe tsaye ta cire wayarta da ke jikin caji ta danna kiran lambar Muhsin, kiran ya shiga, amma har ta gama ringin ba a ɗaga ba. Haƙura tayi ba don ranta ya so ba, zuciyarta cike da addu’ar Allah ya bashi lafiya da gaggawa ta mayar da wayar a caji ta shige banɗaki don ɗauro alwalar sallar magrib da taji an fara kira a wasu masallatai.
Tana idar da sallah, Nauwara ta faɗo cikin falon riƙe da ledoji da jakarta a hannu. Fuskar nan ta sha uban makeup kamar wacce ta fito daga gidan biki, a yangace take taunar cingam tana ƙas-ƙas sannu a hankali.
“Hi Sis! Afuwan! Na barki ke ɗaya ko?”
Nauwara ta faɗa idanunta akan Mannira da take zaune kan dadduma. Sai kuma ta ajiye ledojin a tsakar falon da sassarfa ta ƙarasa kusa da ƙanwar tata tana taɓa goshinta.
“Ya jikinki? Hope dai zazzaɓin bai sake tashi miki ba?”
“Alhamdulillah! Jiki da sauƙi. Sannu da dawowa.”
Mannira ta faɗa idanunta na kan manyan ledojin da Nauwara ta shigo da su. Sai kuma ta mayar da kallonta ga Nauwara ta sake cewa
“Biki kika je ne?”
Wani dariya mai kama da na basarwa Nauwara tayi, kamar baza ta amsa ta ba, sai da ta cire hijabin jikinta ta ninke ta aje a hannun kujera kafin ta amsa da
“Me kika gani?”
“Irin wannan uban kwalliya da kika yi a fuskarki baiyi kama da wacce ta dawo daga makaranta ba. Ga kuma manyan ledojin da kika shigo da su kamar na gudummuwar biki…”
“Uhmmm! Mannirah kenan! Kin san tarayya da masu arziki daɗi ne da shi, sai ki ci arziki ki barshi inda yake. Bayan mun gama karatu ƙawata Amina taja ni muka je Ostrich bakery tayi min waɗannan siye-siyen, ni kuwa tunda ba roƙonta nayi ba hannu bibiyu nasa na karɓa nayi godiya.”
Mannirah ta buɗe baki za ta sake magana tayi saurin katse ta da cewa,
“Wallahi a gajiye nake sosai Sis, ki buɗe ledojin ki ɗebi duk abinda kike so ki bar min ragowar. Bari in watsa ruwa.”
Ko kafin Mannirah ta ce wani abu har ta wuce zuwa ɗakinsu, zuciyarta cike da tunanin Alhaji Nura ɗingishin kuɗi da ta wuni a gurinshi suna sheƙe aya. Lallausan murmushi ta saki tana tunanin yadda ya iya soyayya da ririta mace kamar ba dattijo ba. Babu yadda baiyi da ita ba ta kwana a gurinshi, har ƴan ƙananun ƙwallah yayu mata amma ta ƙeƙashe ƙasa ta baɗawa idanunta toka ta sake jaddada mishi a tsarin yawon barikin da take yi babu kwana a waje.
Dole yayi haƙuri ba don ranshi na so ba, ya barta ta fito daƙyar bayan tayi mishi alƙawarin gobe ƙarfe takwas da rabi na safiya a otal ɗin za tayi mata.
“Nauwara dai likkafa ta ci gaba. Tuni Alhazawan birni da manyan mutanen da Mummy take haɗa ta da su suka ƙarasa buɗe mata idanu tas! A cikin kwamakin ta ƙara wata irin wayewa mai muni da ƙazanta, amma a sirrance take takunta.
Rashin Mummynsu a gida da kuma zaman Daddy a asibiti ya ƙara taimaka mata ƙwarai gurin cin karenta babu babbaka. Duk da dai tun ranar farko ta faɗa ma Mummy duk wanda za’a haɗa ta da shi a faɗa mishi baza ta dinga kwana ba.
Ka’idarta shi ne duk inda take kuma ko da wa take tare ƙarfe shida na yamma za ta bar Otal ɗin, bakwai na dare yayi mata a gida.
Ba tare da wani ja’inja ba Mummy ta amince da haka. Domin a cikin ƴanmatan da suke ƙarƙashinta har da masu barin Otal ƙarfe huɗu na yamma. Ya danganta da yanayin ƴancin da yarinya take da shi a gidansu, ita dai babban burinta ko ɗan yaya ne ya kasance yarinya tana sama mata kuɗaɗen shiga.
Dubu hamsin da a baya idan Daddy ya bata take ganin kamar wata babbar haja ce a wajenta, yanzu ta zame mata kamar ƴan canjin da basu wuce tayi sadakarsu ba. Ƙazamen kuɗaɗe take samu mallakinta halak malak ba tare da ta san takamaimai abunda za tayi da su ba. Daloli sun zame mata kamar naira.
Amina babbar Aminiyarta ta ƙud da ƙud hatsabibiyar yarinya ce wadda ta ƙware a harkar basaja da manipulation. Ita take ƙara tsarawa Nauwara yadda take gudanar da rayuwarta ba tare da ƴan gidansu sun ramfo jirginta ba. Da wannan dalilin yasa mafiyawan kuɗaɗen da take samu Aminar ce take ajiye mata. Shi yasa hankalinta a kwance yake kamar tsumma a randa.
Wayoyi biyu take riƙewa a hannunta, ɗaya wadda Daddy ya saya mata, da ita take amfani a gida, ɗayar kuwa latest iPhone ce wadda ake yayi, wannan ta fafa ce idan an fita waje wadda kuma da ita take amfani wajen gudanar da harkokinta a ɓoye.’
Bayan shigewarta cikin ɗaki, Mannira ta daɗe tana kallon ledojin zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Sannu a hankali take kula da sauye-sauyen da Nauwara ta samu a cikin kwanakin, yadda take kashe kuɗi kamar wacce take kwasosu a ƙasa.
Ba wannan ne karon farko da ta fara komawa gidan da kayan ƙwalam da maƙulashe ba. Wani lokacin idan ta dawo gidan haka zata je musu da tulin ice cream da cakuleti da kayan tanɗe-tanɗe. Yanzu ko ɗakinsu idan aka duba danƙare yake da kayan ciye-ciye mabanbanta kuma masu tsadan gaske.
Wannan hidima da kuɗin kashewa da take ba ta da katin waya da take yawan saka mata kafin wannan ya ƙare ta sake loda mata wasu ya sa bata cika sanya ma Yayar tata idanu ba.
Sannu a hankali ta miƙe tsaye ta fara fitar da kayan cikin ledojin, leda ɗaya dangin kayan shafa ne masu kyau da tsada na gyaran jiki da fata tayi fes! designers kaya waɗanda daga ganinsu ba ƙaramin kuɗi suka lamushe wajen siyarsu ba. Sauran ledojin kuma duk kayan ciye-ciye ne dangin snacks da burger da drinks kala daban-daban.
Kaɗan ta ɗibi, ta kwashi sauran ledojin ta shigar ma Nauwara ɗaki. Sai ta tarar da ita ta fito daga banɗaki tana shiryawa cikin wata sassauƙar doguwar riga.
“Kin ɗibi abinda kike so?”
Ta tambayi Mannirah idanunta na kan turaren da take fesawa a jikinta.
“Eh! Na gode.”
Ta amsa da sanyin murya. Wayarta ta ɗauka ta fice daga ɗakin.
Ko bayan da ta gama shiryawa bata fita zuwa falo ba, ledojin ta ja zuwa gabanta ta ciro Glazed cupcakes da doughnuts ta fara ci tana korawa da lemun exotic na pineapple and coconut.
Abinda ta tsira kenan a ƴan kwanakin, in dai ta fita makaranta tayi yamma sosai, ba kasafai ta cika cin abincin gida da daddare ba.
Tana ɗofana mazaunanta kan kujera kiran Muhsin ya shigo cikin wayarta. Idanu ta bubbuɗe sai kuma ta waiga gefe da gefe jikinta babu inda ba ya rawa, sai kuma a sukwane ta faɗa banɗakin da ke cikin falon ta maida kofar ta rufe har da murza makulli.
Wayar na gaf da tsinkewa ta ɗaga kiran, da sauri kuma cikin rawar murya ta ce
“Ƙalb? Ya kake? Ya jikinka?”
Maimakon ta ji muryar Muhsin, sai taji muryar wani daban yana amsa mata mai jiki da sauƙi.
Jikinta ne yayi wani irin sanyi, hankalinta ya ɗugunzuma nan take, ta kasa ma iya buɗe baki ta tambayeshi ina mai wayar?
Sai shi ne daga can ɓangaren ya sake ce mata
“Muhsin ɗin yana barci ne, ni babban abokinshi ne. Na kira ki ne don in sanar da ke yanzu muka dawo daga asibiti, jikin nashi dai sai a hankali…”
Da rawar murya ta katse shi tana jera mishi tambayoyi a ruɗe
“Asibiti kuma? Wani irin sai a hankali? Me yake faruwa? Don Allah kar ka ɓoye min komai na halin da yake ciki…”
“Kin ga, don Allah ki kwantar da hankalinki ki saurare ni. Na kira ki da amincewarsa ne, amma bai ce in buɗa miki asalin halin da yake ciki ba. Ni kuma dubawa nayi irin matsanancib son da yake tsakaninku da yadda kike ta kiranshi kina nuna damuwarki kan rashin lafiyar bai kamata a ɓoye miki halin da yake ciki ba.
Jikin nashi ne a ɗazu ya ƙara rikicewa fiye da ko wane lokaci shi yasa muka tafi asibiti afujajan. Bayan kulawar manyan likitoci da ya samu yanzu jikin nashi da ɗan sauƙi, kin ganshi yanzu haka ma barci yake yi.
Amma zancen gaskiya yanzu haka ana tunanin kila a fita da shi ƙasar waje, saboda har yanzu likitocin nan basu faɗi takamaiman abinda ke damunshi ba.
Gobe zuwa jibi Daddynshi zai gama duk wasu shirye-shirye zai fita da shi ƙasar Egypt. Kuma I’m afraid idan suka tafi ba zai dawo nan kusa ba. Domin da kunne na naji Daddy ɗin yana cewa karatunshi ma zai jona a can idan ya samu sauƙi…”
Tashin hankali wanda ba’a saka mishi rana… gaba-ɗaya Mannirah sai taji wani jiri ya kwashe ta, ta tafi luuu kamar za ta kifa da sauri ta dafa jikin sink tana jin kanta na juyawa. Ta kasa fahimtar ko kalma ɗaya daga cikin kalaman kwantar da hankali da abokin Muhsin ɗin yake furta mata, a taƙaice ma dai baza ta ce ga lokacin da ya gama maganganunsa ya katse wayar ba don tsananin tashin hankalin da ta shiga.
Ta daɗe tsaye a cikin bayin ba tare da sanin tunanin da take yi ba kafin ta ja ƙafafunta a sanyaye ta fice daga bayin zuwa falo, kan kafet ta zube ba tare da ta kalli ɗaya daga cikin kujerun falon ba.
A wannan dare, haka ta shafe fiye da rabinsa tana saƙe-saƙe. Ashe da gaske ne da ake cewa wani abin baƙin ciki da tashin hankali ya fi gaban kuka. Ko ɗis bata zubar da hawayenta ba a wannan dare. Sai wani irin caji da kanta ya ɗauka kamar wacce ta afa miyagun ƙwayoyi, kafin gari ya waye, ta gama yanke shawarar da take ganin zata fissheta!
Ikon Allah
Me ke Fatima haka kuma? Kar wani abin ya sami Mannira dai