Tun da Asubahi da ta tashi da wani matsanancin ciwon kai ta lallaɓa tayi sallah bata koma barci ba. Duk da dama barcin rabi da rabi tayi saboda rashin sukuni da tarin damuwa da ya dabaibaye zuciyarta.
A gefe guda kuma na zucitarta wani irin matsanancin tsoro da fargaba ne yake taso mata tana yunƙurin dannewa tun sa’adda ta gama yanke shawarar abunda zai fisshe ta. Amma saboda tsabar ƙi faɗi sai ta danganta tsoron na rashin lafiyar Muhsin ce fargabar kuma ta tafiyar da za’a yi da shi ƙasar waje ne har ake zancen idan ya tafi zai daɗe bai dawo ba.
Ta lallaɓa da ƙyar ta shiga kicin, ta ɗora ruwan zafi da kayan ƙamshi bayan ya tadasa ta zuba a flask. Duk aikin da take yi tana yi ne zuciyarta cike da was-wasi. Tsananin damuwa da yayi mata yawa yau ko azkar ɗin da ya zame mata jiki bata samu zarafin yi ba.
Wani faɗuwar gaba na baga-tatan da ya yanko mata yasa ta runtse idanu da ƙarfi hannunta dafe da ƙirji take jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
“Muhsin”
Ta kira sunanshi a fili.
Sai kuma ta janyo wayarta a hanzarce ta fara kiran lambarsa. Tana jin ƙarar shigar kiran sai ta jingina da bango zuciyarta a ƙagauce da a ɗaga kiran, bakinta da addu’ar Allah yasa a ɗauka.
Yau ma har ta fara cire rai da za a ɗaga wayar, sai kuma ta ji an ɗaga lokacin wayar tana daf da tsinkewa. A yanzu ma dai Aminu abokin Muhsin da ya ɗaga wayar jiya da dare ya kora mata bayanin kan Muhsin shi ne ya ɗauka.
A tsaitsaye ta gaishe shi muryarta na bayyana rashin nutsuwa
“Ina Muhsin?”
Shi ne tambayar da ta jefa mishi bayan ya amsa gaisuwarta.
Da nutsuwa sosai ya ɗanyi gyaran murya, kamar bazai amsa ba sai kuma ya ce
“Muhsin ga shi nan a kwance, barci yake yi amma jikin nashi dai babu wani sauƙi sai na musulunci… Da ƙyar ma fa ya samu barcin don sai da likita ya mishi allurar barci. Jiya likitoci biyu ne suka kwana a kanshi…”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…!!!”
Ta faɗa a gigice tare da sulalewa zuwa ƙasa tayi zaman dirshan a kan dandaryar tile ɗin da aka shimfiɗa a ƙasan kicin ɗin.
“Na shiga uku!”
Ta sake faɗa cikin rawar murya hawaye wasu na korar wasu daga kwarmin idanunta.
“Don Allah.. ka turo min adireshin asibitin da yake kwance, zan zo da safennan.”
Ɗan jim yayi kamar bazai amsa ba sai kuma ya ce
“A yanzu haka muna gida, saboda shirin fitar da shi da ake yi shi yasa Dad ya ce gara mu koma gida tunda asibitin ba sauƙi. Family doctors ɗin su ne suke duba shi a gida kafin shirin tafiyar ya kammala…”
“Ok! Na san gidan. Gidansu Fadila ko?”
Ta katse shi da faɗin haka.
Da sauri ya ce
“A’ah, main house ɗin su ne.”
Babu dogon tunani ko neman ƙarin bayani ta ce mishi ya tura mata da adireshin Main house ɗin za ta zo nan ba da jimawa ba.
A gurguje ta cigaba da aikin haɗa musu abin kari, a zuciyarta take ayyana in banda za’a kai ma Daddy abin kari asibiti babu abinda zai sa ta ɓata lokaci gurin haɗa abin karyawa. Toasting ɗin biredi tayi ta soya ƙwai mai ɗan dama. Tana cikin suyan ƙwan aka fara ƙwanƙwasa ƙofar gidan daga can waje.
Katse komai tayi ta kashe wutan ta je ta zura hijabi kan kayan barcin jikinta kafin ta ƙarasa ta buɗe ƙofar gidan. Uncle Jamilu ne, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe shi a ladabce.
“Ina Nauwara?”
Ya tambayeta bayan ya amsa gaisuwar tare da tambayarta ƙarfin jikinta da yadda take ji a yanzu.
“Da sauƙi sosai. Tana ciki tana shiryawa.”
Ta amsa a ladabce, ba don tana da tabbacin Nauwaran tana shiryawar ko akasin haka ba.
“Ki faɗa mata idan kun gama shiryawa ta kira ni, zan kai ku makaranta daga can zan wuce wajen Daddynku. Yau likita ya ce za’a kwance ɗaurin hannunsa. In dai yayi kyau sosai in sha Allah yau za su sallamoshi ya dawo gida.”
“To Uncle. Mun gode Allah ya ƙara girma.”
Ko da ta koma ciki, kai tsaye ta shiga ɗakinsu ta tashi Nauwara haɗi da sanar da ita saƙon Uncle Jamilu, sannan ta koma kicin da sauri ta ƙarasa suyan ƙwan da take yi. Ta shirya kayan karin Khamis a cikin basket su kuma nasu ta kai kan teburin cin abinci.
Ko da ta koma ɗaki, ta tarar da Nauwara har tayi wanka, tana tsaye gaban madubi tana shafa mai, don haka ita ma bata ɓata lokaci ba ta faɗa wanka. Ko da ta fito Nauwara har ta gama shiryawa ta fice falo, don haka itama ta shirya ta sanya kayan makarantarta sannan ta fita falo, har lokacin bata daina jin ƙirjinta yana bugawa lokaci bayan lokaci ba.
Bata jima da fita ba suka gama karyawa a gurguje. Kamar haɗin baki, daga ita har Nauwara tsakurar komai suka yi suka miƙe alamun sun ƙoshi. Gyara komai tayi ta aje inda bazai lalace ba ita kuma Nauwara ta zaro wayarta ta kira Uncle Jamilu.
Da alamun daman su ɗin yake jira, tazarar mintuna biyu tsakani suka ji horn ɗin motarsa a ƙofar gida.
Mannira ta miƙa hannu za ta ɗauki basket ɗin abincin Daddy Nauwara ta riga ta ɗauka, ta sakar mata lallausan murmushi.
“Bari in ɗauka Ƙanwata. Duk ayyukan gidan fa ke kaɗai kika yi yau, Allah dai ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Luvly Sis.”
A taƙaice ta mayar mata da martanin murmushinta, murya ƙasa-ƙasa ta amsa addu’ar da tayi mata kafin suka jera har zuwa ƙofar gida, bayan sun kulle ko ina.
Kamar motar Daddynsu, Nauwara ce ta zauna a gaba, Mannirah tana zaune a baya. Lokaci bayan lokaci Uncle Jamilu yake musu nasiha mai ratsa jiki akan rayuwa da irin abinda ke faruwa a wannan zamanin da muke ciki da yadda za su kiyaye wasu abubuwan har zuwa lokacin da suka isa makarantar su Mannirah. Da za ta fita daga motar, ya zaro naira dubu ɗaya ya miƙa mata, tare da mata jaddada mata
“Ana tashinku fa kada ki tsaya shiririta kina ji na? Ki tari keke da sauri ya mayar da ke gida. In sha Allah zan yiwa Daddynku magana tunda har yanzu direbanku bai dawo daga jinyar mahaifiyar tasa ba ya kamata ya nemi wani ya dinga jigilar kai ku da ɗauko ku a nutse. Bai kamata ku cigaba da gararamba a mashin da keke napep ba.”
“To Uncle. In sha Allah bazan tsaya ba. A gaida Daddy, mun gode Allah ya ƙara girma.”
Ta amsa muryarta na fita a sanyaye. Da idanu ta bi motar da ɗan murmushi a fuskarta ganin yadda Nauwara ke ɗaga hannu tana mata bye bye har zuwa sadda motar ya ɓace a idanunta. Zuciyarta cike da ƙaunar Uncle Jamilu da ƙara ganin kimarsa.
Tun bayan kwantar da Daddyn su a asibiti, yana matukar ƙoƙari wajen ganin ya kula da su ta hanyoyi da dama. Lokuta da dama ya kan zaunar da su yana tambayarsu menene matsalarsu? Idan akwai su faɗa, idan babu su faɗa. Tun suna ƙanana sun daɗe da fahimtar shi ɗin Amini ne na gaskiya ga mahaifinsu.
Kasancewwr ya san duk abinda ya faru da dalilin tafiyar Mummynsu, yana matuƙar ƙoƙarin kwantar musu da hankali da tausasan kalamai na ƙarfafa musu gwuiwa.
Idan ta zauna ta zurfafa tunani har yanzu ta kasa fahimtar dalilin Mommy na tafiya ta barsu, ta kuma kwashi wasu daga cikin yaran su kuma ta barsu anan. Hakan yana nufin bata damu da su bane? ko kuwa dai don su sun kasance manya ne? Idan haka ne, to menene makomar karatun ƙannensu da Mummyn ta datse musu? Kuma yaushe take da niyar dawowa? Ita a ganinta idan ma saboda case din Bilkisu ne, ai ya riga da ya wuce.
Tun da dai yanzu ko sunanta bata ji Daddynsu yana ambata balle a kai ga zuwa inda take. Kuma ma tunda dai ba a kama shi da laifin da aka zargeshi da aikatawa ba, ai tana ga hakan bai isa dalilin da zai sa tai tafiyarta ba (Kasancewar abinda Khamis ya faɗa musu na dalilin tafiyar Mummyn kenan.)
Duk da a wasu lokutan tana ji a jikinta kamar wannan matsalar ta Bilkisu ba shi ne kaɗai dalilin da zai sa Mummy ta tafi ba.
Wani abu da ke ƙara ɗaure mata kai da jefa ta a cikin damuwa shi ne yadda sama ko ƙasa aka nemi Mummyn aka rasa, domin kullum sai sun yi waya da Aunty Kareema da Aunty Rukayya suna tambayarsu wai har yanzu babu labarin Mummy? Aunty Rukayya da ta kasance mai faɗa sosai har rantsuwa tayi ma Mannirah kan cewa wata guda ta ba Khamis matuƙar bai nemo inda Ziyada ta shiga ba tabbas kotu ce za ta raba su.
Minti uku ta ɓata tana wannan tunanin, kafin cikin sauri taja jiki ta bar gurin don kar ɗaya daga cikin malamai ya fito a tarar da ita tsaye a gurin. Da saurin gaske ta ƙara gaba ta tari adaidaita sahu ta hau, ta ciro wayarta daga inda ta maƙaleta cikin aljihun wando ta faɗa mishi kwatancen inda zai kai ta.
Sannan ta lalubo lambar Muhsin domin sanar da abokinsa tana tafe, amma bata san unguwar ba. Ya zauna kusa da waya saboda idan sun kusa za ta bashi ɗan sahun yayi masa cikakken kwatance.
***
Bayan dogon kwatance da shan dogon tafiya kamar za a bar gari aka sauke ta a ƙofar wani tangamemen gida dake can cikin wata unguwa da bata taɓa sanin da wanzuwarta ba a cikin Kaduna, ba don komai ba kuwa sai don saboda tsabar juyewar da kanta yayi. Dama ita dai ba wani yawace-yawace take yi ba, wannan dalilin yasa da taga suna ta tafiya kamar ba za a ƙare ba, ta fara tambayar direban napep ɗin
‘Malam anya kuwa cikin garin Kaduna muke?”
Yayi dariya kafin ya amsa mata da
“Ƙwarai kuwa. Sai dai mun fita daga inda kika sani mun shigo cikin sabbin unguwannin da basu fi shekaru biyu da gama gine-gine ba.”
“Ikon Allah”
Ta faɗa a fili, a cikin ranta kuwa addu’a take ta zabgawa da fatan Allah dai yasa ba sayar da ita mai keken zai yi ba.
Ta fita daga cikin adaidaitan tana jin ƙafafunta har suna ƙoƙarin lanƙwashewa saboda gajiyar zama. Sai da tayi miƙa sannan ta fara tambayarshi nawa za ta bashi?
Dubu biyu yace, ba kuma tare da tambayar ba’asi ko ragi ba ta dauko kuɗin ta ba shi. Ya tayar da adaidaitan ya tafi yana murna tunda ya yi tunanin za ta nemi ragi kuma bata nema ba.
Ta taka zuwa gaban gate ɗin tamfatsetsen gidan da mai keken ya tabbatar mata nan ne aka faɗa mishi kuma ga lambar gidan nan ma, ƙirjinta dai sai luguden daka yake yi kamar ana buga ganga. A saiɓance ta juya ta sake kallon irin gine-ginen da suke cikin unguwar. Unguwa ce ta masu kuɗi sosai ko daga irin haɗaɗɗun gidajen da ta gani, ba hayaniya ko misƙala zarrah.
Ta dawo da idanunta kan ƙofar gate ɗin da take tsaye, ta ɗaga hannu ta fara bugawa sannu a hankali, tun tana yi ƙasa-ƙasa har ta fara bugawa da ɗan ƙarfi, amma sai taji shiru, babu alamar za’a zo a buɗe.
Kusan mintuna biyu tana bugun ƙofa shiru, ga unguwar tayi tsit, ba a ganin giccin ko ɗan tsuntsu balle ɗan mutum. Don haka ta ciro waya ta sake kiran lambar Muhsin wanda Aminu ne yake ɗagawa tun jiya.
“Ga ni a ƙofar gidan. Tun ɗazu ina ta ƙwanƙwasawa ba’a buɗe ba. Ko dai na saɓa lamba ne?”
Ƙorafin da ta fara mishi kenan bayan ya ɗaga kiran.
“Allah sarki Matarmu. Yi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki. Mai gadin ba ya nan, amma ki turo ƙaramin ƙofar gate ɗin ki shigo, a buɗe yake.”
Ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ƙofar ta shiga kamar yadda ya umarce ta. Sai kuma tayi turus bayan ta shiga harabar gidan, sai raba idanu take yi ganin parts parts sun kai kusan guda biyar, cikin rashin sanin inda za ta dosa ta sake ɗaga waya da nufin sake kiran Muhsin.
Kafin kiran ya shiga, ta ga an buɗe part ɗin can ƙarshe an fito ana ɗago mata hannu.
Ta taka a hankali har lokacin zuciyarta cike da ɗar-ɗar ta nufi wajen, sai a lokacin ta fara jin dalmi-dalmin da-na sani bata je ba…
Amma ko da ta ƙarasa kusa da Aminu, da sanyin jiki ya hau faɗa mata yadda Muhsin yake matuƙar jin jiki sai taji duk wannan da na sani da fargaban sun bi iska. Babu abinda take burin gani a wannan lokacin sai masoyinta.
Bayanshi ta bi zuwa cikin falon idanunta cike da hawaye, a fakaice ta ƙarewa falon kallo, babba ne sosai da aka shimfiɗa chinese carpet mai kwalliyar baƙi da ash a jikinsa. Ga kuma wasu narka-narkan manyan kujeru leather seats bakake, acan gefe da dinning table babba sai fridge a gefensa, ga kuma babbar TV da aka lika a jikin bango da sauran kayan tarkacen kallo a haɗe. Abubuwan dake falon kenan, babu wani tarkace, amma yayi kyau sosai.
“Saki jikinki Matarmu, bari in leƙa in yiwa Muhsin ɗin magana. Mommyn shi ma tana ciki da babbar Antynsu, bari in musu magana ku gaisa.”
Bai jira cewarta ba ya buɗe wata ƙofa, ya leƙa ciki ba tare da ya shiga ba.
Daga inda take zaune, ta ji sautin maganganu na tashi sama-sama, amma ba ta fahimtar me ake cewa. Ta dai ga ya maida ƙofar ya rufe, ya juyo da idanunsa kanta yana ƴar dariya
“Aunty ce take min masifa wai na barki zaune ban gabatar miki da ruwa kafin fitowarsu ba.”
“Ayya… Ba komai. Ni ba na ma jin ƙishi.”
Ta faɗa da zallar gaskiyarta.
Bai saurareta ba ya nufi fridge da ke ajiye a gefen dining ya bude ya zaro robar ruwan faro da ta lemon Orange Pulp babba. Sai ya ɗauki ƙaramin kofi na tangaran a kan firidge ɗin ya ajiye a gabanta yana ɗan murmushi
“Ki sha ruwa don Allah Mannirah. Yanzu su Mummy za su fito ku gaisa…”
Ta girgiza kai da sauri ta ce
“Da gaske ba na jin ƙishi. Sauri nake in duba shi in koma makaranta…”
“Haba dai, ko ruwa ai kya ɗan sha kafin a fito da shi. Muhsin ɗin ne sam babu karfi a jikinshi, in ban da ma ke ce sam ba’a fito da shi sai da ƙwaƙƙwaran dalili, shi ne Anty tace bari ta ɗan sa mishi kaya masu nauyi sai ta taya shi ya fito. Mommy ma ta ce ki sha ruwa ga ta nan fitowa”
Ganin yadda ya matsa, yasa ta bincire murfin ruwan ta ɗan tsiyaya kaɗan a kofi ta kurɓa ba don tana jin ƙishin ba. Suka zauna ita da shi jigum-jigum fiye da mintuna uku, har ruwan da ta tsiyaya a kofi ta shanye sannu a hankali, amma ba Muhsin ba labarinsa.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Me ke shirin faruwa ne oh oh