Minti ɗaya biyu uwar da ƴaƴan suke haɗa baki gurin cewa, fuskokinsu ɗauke da zallar tausayi da ƙaunarsa.
"Sannu Daddy. Allah ya yaye maka, muna roƙon Ubangiji ya baka lafiya da gaugawa."
A sannu cikin kulawa da tarairaya suka ɗaga shi a hankali cikin lallaɓawa kamar wani ƙwai, cikin ɗaki suka shigar da shi.
Kan kujera mazaunin mutum uku suka kwantar da shi, Khamis an samu abinda ake so, sai ƙara narkewa yake yi yana langwaɓewa.
Cikin zafin nama Mummy ta surka ruwa mai zafi-zafi ta kai banɗaki.
Ta taimaka mishi yayi wanka. . .