Mannira ta ɗaga kanta da ƙyar da ta ji ya fara mata wani gin-girim kamar an ɗora mata dutse da niyar ta tambaye shi ya aka yi har yanzu basu fito ba? Sai taga gaba ɗaya Aminun ya rarrabe mata gida huɗu. Idanunta suka fara lumshewa a karan kansu, duk yadda taso tayi karfin halin buɗe su ta gagara. Sai kuma ta fara jin wani irin sauti yana mata amsa kuwwa a kunnenta zuwa ƙwaƙwalwarta, a jikinta take ji kamar an ɗauke ta an jefa a cikin ruwa. Bata san lokacin da ta langaɓar da wuya ta kwanta akan kujerar da take zaune ba…
*****
Ƙarfe huɗu na yamma, Khamis ya sake buɗe ƙofar falon gidan ya shiga a karo na kusan biyar, ya fara ƙwalawa Mannira da Nawwara kira amma shiru babu amsa, alamun dai har lokacin babu kowa a gidan.
Hankalinsa ne ya ƙara ɗugunzuma, ihu ne kawai bai ƙwala ba, a karo na barkatai ya sake kiran lambar Mannira a kashe, ko da ya sake kiran Nauwara sai ta sake ce mishi har yanzu basu gama lectures ba.
“Daddy kayi haƙuri, yanzu mun fito sallah ne za mu shiga lecture na ƙarshe, idan mun fito da wuri 5:30 a gida za tayi min. Bye…”
Tayi saurin katse wayar ba tare da ta saurari ƙorafin da yake shirin yi mata kan rashin dawowar Mannira gida har wannan lokacin ba.
‘Ƙarfe sha biyu da rabi aka sallamo shi daga asibiti. Kasancewar tun kafin likita ya basu sallama Sani ƙanin Jamilu da yake jinyarsu duk ya gama tattara kayansu guri ɗaya shi yasa basu ɓata lokaci a cikin asibitin ba. Suna hanyar dawowa ya roƙi alfarmar Jamilu kan cewa su biya su ɗauko Mannira a makaranta, domin lokacin tashinsu yayi. Amma wani abin mamaki shi ne a gabansu aka buga ƙararrawar tashi a makarantar, ɗalibai suka fara fitowa, sai dai wani abun ɗaure kai da ban mamaki shi ne har ɗaliban suka gama fitowa ba Mannirah babu mai kama da ita.
Don haka ya shiga makarantar da kanshi har Ofishin Principal ya tambayi inda take. Da aka duba log ɗin makarantar na ranar sai aka tabbatar mishi da cewa bata ma je makaranta ba. Mamaki ne ya kama shi, da wannan mamakin ya koma gurin Jamilu ya sanar da shi abinda yake faruwa.
“Ka san shekaran jiya ta yi zazzaɓi da ciwon kai. Wata-ƙila jikin ne ya motsa bayan mun sauke ta ta yanke shawarar komawa gida. Daman dai tun safe naga yanayinta sai a hankali.”
Da wannan amsar yasa hankalinshi ya ɗan kwanta, har ya ƙara da
“Habawa! Ko da na ji. Mannirah bata da lalaci ko kaɗan, musamman a fagen karatu. Ko cuta take yi haka nan take tafiya, sai dai idan taga cutar tafi karfinta ne take zama a gida.”
Sun koma gidan cike da fata da burin Allah dai yasa dai cutar ce tasa ta koma gida. Sai dai wayam! Haka suka samu gidan a kulle, alamun babu kowa.
Hankalinshi ne ya ƙara tashi. Amma sai bai nuna ba suka yi sallama da Jamilu kan cewa duk yadda ake ciki zai taɓo shi, lafiya ce in sha Allah. Kila maƙwafta ta shiga, zaman kaɗaici ya isheta.
Ƙarfe biyu, biyu da rabi, uku saura, izuwa lokacin ya kira lambarta fiye da sau talatin Swich off! Kuma har waje ya fita duk maƙwafta da yasan suna abin arziki da Ziyadah sai da ya aika ko Mannira tana nan? Aka tabbatar mishi ba ta nan.
Ƙarfe uku ya figi makullin mota ya bazama gidajen yan’uwa da yasan za ta iya zuwa, amma duk inda yaje labarin ɗaya ne, ba ta nan.
Izuwa lokacin ne ya fara shan jinin jikinshi, ya tabbatarwa da kansa lallai ba lafiya ba. Zuciya da wasu kalolin saƙe-saƙe sai ta fara saƙa mishi ko dai Mannirah guduwa tayi kuwa ta bi bayan Ziyada? Ko kuwa dai wani mummunan abu ne ya faru da ita? Idan ya zo nan a tunaninsa sai yaji ƙirjinsa yayi wani wawan bugawa.
Jikinsa a saiɓance ya cigaba da jan motar zuwa gida, yana shiga cikin layinsu aka ƙwalla kiran sallar la’asar. A maimakon ya ƙarasa gida yayi alwala, tsoron me zai tarar na farin ciki ko akasinsa yasa shi fakawa a gefen masallacin yayi alwala, ya shiga ciki yayi sallah. Ya daɗe yana addu’a kafin ya miƙe ya fice daga cikin masallacin, kallo ɗaya za’ayi masa a gane yana cikin matsananciyar damuwa.
Duk da ya ga ƙofar gidan a kulle yadda ya bari da zai fita, yana shiga ciki ya fara ƙwalla ma Nauwara da Mannirah kira, amma babu wacce ta amsa shi. Ko da ya kira Nauwara da jin amsar da ta bashi na cewar aji za ta shiga sai kawai ya zube jaɓar akan kujera. Hannayensa bibiyu dafe da kansa da yake ji yana mishi wani matsanancin bugawa.
Masu garkuwa da mutane suka sace Mannirah shi ne tunani na ƙarshe da baya son zuciyarsa tana kitsa mishi. To amma ya zaiyi? Muna cikin wani irin mummunan yanayi ne da kwanciyar hankali yayi ƙaranci ga bayin Allah, har gida ana bin mutum a ɗauke shi balle kuma wacce ta fita waje?
To ko dai gurin ƴan sanda zai nufa ya kai musu report na ɓacewarta? Ƙwarin gwuiwar da yaji ya ɗan samu sanadiyyar wannan tunanin yasa shi miƙewa tsaye, kwatsam! Sai ya ji wayarshi ta ɗauki ƙaran kira.
A zabure ya zaro wayar daga aljihu yana kallon sunan mai kiran, sai yaga baƙuwar lamba. A karo na barkatai ƙirjinshi yayi kwance-kwance ya buga daram! Ya ɗaga wayar a tsorace tare da kara ta a kunnensa, cikin rawar murya ya ce
“Hell…loooo…!!”
******
“Umma…”
Da sauri Umman ta katse ta da cewa
“Yau ne bikin Rahma ko?”
A mamakance ta ɗago idanunta farare tas ta kalli Umman, ta kasa cewa komai. Domin abinda take niyyar faɗa ne uwar ta faɗa.
Martanin lallausan murmushi uwar ta mayar mata kafin ta zauna a gefenta.
“Na sani. Na san yau auren Rahma. Kuma fitar da kika ga nayi ɗazu na je can gidan ne nayi musu Allah ya sanya alkhairi. Na ba Iyallu gudummuwar abinda ya samu da gaggawa na dawo gida don kar in barki ke ɗaya…”
“Amma Umma yau bikin Rahma… babu ke babu ni. Abun dai ya yi wani bambaraƙwai…”
Ta sake faɗa a sanyaye, tana jin ba daɗi sosai a zuciyarta. Yadda abubuwa suka juye mata zuwa yadda bata taɓa zato ko tsammani ba a cikin ƴan kwanakin abu ne da ko a mugun mafarki bata taɓa hasashen zai faru ba.
Ko bayan barowarta gidansu Rahma a wancan ranar, har ta nuna mata nadamar ƙarya. Ko kaɗan bata yi niyyar zubar da makaman yaƙinta na niyyar raba Rahma da Salim ba, a yadda take ji ma kamar sai a ranar ta fara son shi. Domin bata taɓa tsayawa ta yi mishi kallon ƙurullah irinna wannan ranar ba.
“Ashe Salim ɗin kyakkyawan gaye ne na gasken gaske bayan ji da kuɗi da ƙuruciya? Lallai idan ta bari Rahma ta aure shi ita ta cigaba da gararamba a titi ta zama ƙatotuwar wawuya.”
A yadda ta tsara, washe gari sammakon komawa gidan Uwar ƙungiya za tayi duk da ta daɗe da nuna mata ita fa ta daina yayinta. Za ta kwantar da kai, tayi ladabin kunama irinna gogaggiyar karuwa har zuwa sadda uwar Ƙungiya za ta aminta da ita tayi mata hanyar zuwa gurin ƙwararren malaminta ɗaya tamkar da miliyan acan ƙasar Nijar. Ta san can ɗin ne kawai za ta je buƙatarta ta biya cikin ƙanƙanin lokaci.
Kwatsam! Sai abubuwan suka juye mata a yadda bata tsammata ba. Bayan fara bata ruwan rubutu mai ɗauke da magani a ciki, da kausasan maganganun da Umma tayi mata. Kwanaki na tafiya sannu a hankali jikinta na yin wani irin sanyi, lamuran rayuwar duniyar duk sun fara fice mata a rai. Babu abinda take so da ƙauna a yanzu irin tayi abinda zai faranta ma Umma rai, shi yasa ko Umman ta fice ta barta a gida ita kaɗai ba ta iya ficewa kamar wacce aka ɗaure da sarƙa. Duk da a wasu lokutan har kuka take yi kan yadda take son fita ta cigaba da munanan harkokinta yadda ta saba.
Ummanta buɗaɗɗiyar macece da bata iya rufa-rufa ba. Ta faɗa ta nanata mata wannan zaman da take yi a gida zaman istibra’i take yi. Kuma ta sake jaddada mata bayan gama istibra’inta da sati biyu ɗaurin aurenta da Isiya zai biyo baya.
“Isiya kuma Umma? saboda Allah kina da tabbacin shi har yanzu yana ƙauna ta?”
Ta tambaya idanunta a ƙasa, da murya mai karkarwa, alamun gaf take da fashewa da kuka.
“Ƙwarai da gaske. Kafin in ƙarfafa zancen aurenki da shi sai da na tuntuɓe shi ya tabbatar min har gaban abada idan akwai bazai daina ƙaunarki ba. Kuma saboda gudun yin kitso da ƙwarƙwata ni da Alhassan (Ƙanin mahaifinsu Samirar) da Uzairu (Ƙanin Umma) muka je har gidansu Isiya muka gana da iyayensa akan maganar auren.
Zubar da mutuncin kanki da kika ɗauki shekaru kina yi ba ɓoyayyen abu bane a gurin kowa na unguwar nan da cikin garinnan. Don haka muka sake musu tishi akan munanan halayenki ba tare da wani ɓoye-ɓoye ba. Da kuma fata da tabbacin da muke da shi kan cewa a yanzu Allah ya shirye ki. Muka roƙe su alfarmar shin sun amince ɗan su Isiya ya auri ke Samira duk da irin abubuwan da kika aikata a baya?”
“Roƙon alfarma kuma Umma?”
Ta faɗa a haukace bayan ta ja wani ƙaƙƙarfan nishi mai tafe da mahaukacin kuka. Jaɓar! Ta zube a ƙasa tayi zaman ƴan bori tana rusa kuka kamar za ta haɗiyi zuciya ta bar duniyar.
Duk tunaninta shi ne, kamar ita Samira? Babbar yarinyar da maza suke rububi? Wacce saboda tsananin ni’imarta suke yiwa laƙabi da Kankana, ita ce dai wai yau ake roƙon alfarma a kanta wulaƙantaccen mutum kamar Isiya wanda bai wuce mai wankin motarta ba ya fito ya aure ta? Wane irin faɗuwar baƙar tasa tayi haka a rayuwarta na duniya? Ashe haka rayuwa take? Ashe da gaske ne kirarin da ake yiwa duniya rawar ƴanmata na gaba ya koma baya? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!!
A wannan rana, Samira bata taɓa tsammanin za ta kai dare ba tare da mala’ikan mutuwa ya zare ranta ba. Har addu’a ta dinga yi a fili kan Allah ya ɗauki rayuwarta, ita kam da ta cigaba da ganin irin wannan munanan kwanakin da suka fara biyowa jere a jere cikin rayuwarta gara kawai alƙiyamarta ta tsaya… Ta san mutuwa tayi ba ta duniyar.
Haka ta kai tsakiyar dare tana sharɓan kuka ba tare da ko zazzaɓi ta yi ba, sai mugun ciwon kai da ya lulluɓeta. Yinin ranar ranka ta kaf ko abinci bata nema ba, ita kuwa Umma ta kawo na mujiya ta zuba mata uffan bata ce mata ba balle har kalaman rarrashi ya shiga tsakaninsu.
Babu abinda ke tada ita sai sallah da lokaci na yi Umma za ta aika ƙannenta kan lallai ta tashi tayi sallah idan ba haka ba ta shigo ɗakin za tayi mugu-mugun saɓa mata.
Umma bata waiwaye ta ba sai washe gari, bayan sun idar da sallar asubah.
“Samira, a tunaninki rashin ƙauna da soyayya ce tasa na karya alkadarinki nayi ma mutum kamar Isiya tayin aurenki ko?”
Bata iya cewa komai ba, sai idanu da ta ɗaga tayi ma Umma kallo ɗaya ta sake sauke su ƙasa a hankali.
Ba tare da damuwar rashin amsawarta ba Umma ta zauna a gefenta ta cigaba da magana.
“Bari ki ji Samira. Ita ƴa mace Ubangiji Allah yana halittarta ne da darajarta. Amma daga lokacin da ta watsar da daraja da kimar da Allah yayi mata to lallai fa za ta ga abu ba auki. Ko kin ƙi ko kin so babu wata hanya da ta kai ta Allah Subhanahu wa ta’ala da Fiyayyen Halitta Sallallahu alaihi wa sallam. Kin taɓa ganin inda akai ɓari aka kwashe tas? Haba Samira! Shi fa mutunci madara ne idan ya zube ba ya taɓa kwasuwa.
Tsammaninki Yadda kika daɗe kina cin karenki ba babbaka ta hanyar saɓa ma Allah za ki kwashi abinda kike so ne nan gaba? Ai Allah ma yayi miki da kyau da kika samu nagartaccen mutum mai ilimin addini kamar Isiya ya ce zai aure ki.
Wai ke me ke cikin ƙwaƙwalwarki ne? Halan baki lura da yadda karuwancin ya fara juya miki baya bane? Ki zauna kiyi tunani da kyau, yadda maza ke son ki da rububinki a baya har yanzu haka suke yi? Sun gama cin moriyar ganga to mi za suyi da kwauronta? In dai ba so kike ki cigaba da wulaƙantar da kanki har zuwa sadda za ki zama magajiya a gidan karuwai ta hanyar sayar da goro da taba ba to aure a daidai wannan lokacin shi ne mutuncin ki.
Zan sake maimaita miki abinda kunnuwanki ba sa son ji. Durƙusawa mukai har ƙasa muka roƙi iyayen Isiya ko za su amince nutsattsen ɗansu da ko a unguwa ya samu shaidar arziki ya aure ki? Sai kuma muka ci sa’a su ɗin dattijan arziki ne, sun amince da buƙatarmu amma bisa sharaɗin idan likita ya auna ki ciki da bai ya tabbatar ba kya ɗauke da cuta ko guda ɗaya a jikinki. Kuma fa bamu ga laifinsu ba, sun ma yi namijin ƙoƙari da suka iya amince mana kan buƙatar da muka je da ita. Da wannan dalilin yasa muka sake duƙawa har ƙasa muka yi godiya, domin tabbas! sun yi mana alfarma da karamcin da ba ko wasu iyaye za su iya yi ba. Har mun kama hanyar fitowa daga gidan mahaifinsa da yake malami ne ya tunasar da mu zancen kiyi Istibra’i kamar yadda addininmu yayi umarni.”
Umma tana zuwa nan a maganganunta sai tayi shiru… Shirun da ya wanzu a tsakaninsu har na tsawon mintuna biyu, kafin daga bisani Umma ta rufe maganganunta da cewa.
“Ba komai yasa nayi duk waɗannan abubuwan ba sai don sauke nauyin da ke kaina a matsayina na mahaifiya, wanda ba tun yanzu ba, Allah shi ne shaida ta akan tun da daɗewa na so in ɗauki irin wannan ƙwaƙƙwaran matakin mahaifinki ya danƙwafe ni.
Yanzu kam zaɓi ya rage gare ki Samira. Ruwanki kiyi min biyayya a matsayina na mahaifiyarki… Zaɓinki ne ki bi son zuciyarki ta hanyar bijire ma umarnina… Daga sadda kika bi zaɓin zuciyarki ni kuma zan sallamaki har abada in ji da tarbiyar sauran ƴaƴan da Allah ya bani. Ba ke kaɗai na haifa ba Samira, don haka bazan taɓa bari baƙin ciki da takaicin munanan halayenki su zama ajalina ba.”
Tsam! Umma ta miƙe tsaye ba tare da ta ba Samira damar cewa wani abu ba.
Aka ce gudu samun dama tsayuwa samun dama, ga Samira kam ta rasa waƙar farawa a cikin abubuwa biyun. Ta daɗe cikin wani mummunan hali da yanayi na rai kwa-kwai mutu kwa-kwai. Kafin daga bisani kamar an finciko kalaman daga cikin bakinta a fili ta fara maimaita.
“Inna lillahi wa-inna ilaihi raji-unn. Allahumma ajirnee fi musibati, wa-aklifnee khairan minha.”
Ta daɗe tana maimaitawa, kuma cikin hukuncin Allah sannu a hankali tururin da ƙwaƙwalwarta ke yi ya fara sassautawa, don haka ta ƙara ƙaimi tana maimaitawa har zuwa sadda wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Allah sarki Mannira oh oh, Samira kam yadda umman ki ta fada ne ki godewa Allah kawai. Kai kuma Khamis lokacin ka ne ya zo
Khamis fa lokaci ya zo. Allah de ya bamu ikon shuka alkhairi don mu girbi alkhairi a rayuwarmu ta gaba. Sannu da ƙoƙarin comment Sis