“Maman Samira, na ce kin san kuwa yadda ake bayar da maganin ko wane irin ciwo na gargajiya haka ake bayar da maganin Zina da sace-sace?”
Kamar saukar aradu, haka maganar ya dira a kunnuwan Umman Samira. Sannu a hankali take rage ƙarfin kukan da take yi har ta tsaida hawayen tsaf! Kamar ɗaukewar ruwan sama.
“Ban… ban… gane ba Maman Abba. Me kike nufi? Don Allah fahimtar da ni.”
Ta jero maganganun cikin sauri da rawar murya.
Da yanayin tausayi sosai a fuskar Maman Abba take kallon Umma. Akwai aminci sosai a tsakanin su biyun. Shi yasa a wannan gaɓar da gumu tayi gumu Allah ya matsi bakin Umma ta zayyane mata duk matsala da ɗumbin damuwar da zuciyarta ke ciki ita kuma ta sha alwashin taimaka mata saboda Allah da zumuncin da ke tsakaninsu.
“Ƙwarai kuwa! Abinda kunnuwanki suka ji haka na faɗa. Tabbas! Ana bayar da maganin zinace-zinace da sace-sace kamar yadda ake bayar da maganin ko wane irin ciwo da yake damun ɗan Adam. Ni ganau ce ba jiyau ba, sai dai abu ɗaya da bani da tabbaci shi ne ko wane mai maganin gargajiya ne yake bayar da maganin irin waɗannan larorin? Allahu a’alam!”
Da zakwaɗi sosai a fuska da muryar Umma ta sake cewa.
“Ina jin ki Maman Abba. Har yanzu dai baki kaini inda nake son ji ba…”
“Me kike ci na baka na zuba Umma? Ki bi ni sannu a hankali zan kai ki har inda baki taɓa tsammani ba. Zan faɗa miki wannan maganar ne saboda yarda da amincin da yake tsakaninmu, da kuma ganin yadda kika iya ajiye fargaba da tsoron komai kika buɗa min sirrin matsalar cikin gidanki, duk da dai wasu abubuwan ba baƙi bane a gare ni. Amma saboda ke baki taɓa magantuwa ba da kuma ganin yadda duniyar ta juya da yawan iyaye ba sa son gaskiya akan laifin da ƴaƴansu suke aikatawa shi yasa ban taɓa tunkararki da maganar ba.
Kin tuna Yayana Alhaji Bilyaminu da kika taɓa zuwa min biki gidanshi har sau biyu ko?”
“Eh! Na tuna shi.”
“Yauwa! Babban ɗanshi Abdul-Hafiz, wannan mahaddacin Alƙur’anin da kuke ta yabon shi, a farkon ƙuruciyarsa babu irin matan da bai nema ba…”
“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un… Abdul-Hafiz fa Maman Abba? Wannan Hafizin da yake ja ma Sheik Ibrahim Yunus baƙi a gurin tafsiri? Da gaske kike yi ko kuwa dai kina faɗa min wannan maganar ne don hankalina ya kwanta?”
Umma tayi maganganun idanunta a warwaje, hannayenta duk biyu dafe da ƙirji saboda tsananin kaɗuwar abinda kunnayenta suka jiyo mata.
“Hmmm! Ki saurareni da kyau Umma. Bilyaminu yayana ne Uwa ɗaya Uba ɗaya, kin ga kuwa bazan yiwa ɗansa sharri ba. Lokacin da Iyaye suka ankara da ɓarnar da Abdul-Hafiz ya fara ta kan masu aikin gidan, hankalinmu ne ya ɗugunzuma. Duk da halin da nake ciki na talauci akwai kyakkyawar fahimta tsakaninmu da ɗan’uwana. Don haka ba ya ɓoye min komai.
Da farko, babu irin takura da kullen da ba’ayi masa ba, ke in takaice miki har sai da takai duk girman gidan an daina ɗaukar masu aiki gaba ɗaya. Amma sai abin ya fara tsallakawa ga abokan karatunshi ƴan mata. Ke, in taƙaice miki zancen Wallahi har aure Yaya yayi mishi da gaggawa duk da shekarunsa ashirin ne wai ko za’a sami sauƙi, bamu ankara da babu sauƙi a lamarin ba sai da matarshi da iyayenta suka zo da ƙanwar matar da kukansu wai Abdul-hafiz ya lalata ƙanwar matarsa, har ga ciki nan ya ɓulla, kuma an juya ƙanwar dambu da taliya ta ce cikin Mijin yayarta ne.
Mun shiga mummunan tashin hankali a wancan lokacin. Kai ! Kar Allah ya kawo mana abinda bazai wuce ba. Tashin hankalin da muka shiga ya zarce duk yadda kike tsammani, saboda ko misƙala zarratin bamu samu sauƙi ko wani sassauci daga iyayen matar Abdul ba, duk kuwa da kasancewar mahaifinta abokin Yaya Bilya ne na ƙud da ƙud.
Ƙiris ya rage Yaya bai tsine ma Abdul ba saboda masifar da ya jefa shi a ciki. Bayan ruguntsumin shari’a da muka sha Allah ya taƙaita al’amarin ta hanyar zubewar cikin ba tare da ita yarinyar ta sha maganin komai ba. Duk da haka, sai da Alƙali ya tilasta Yaya biyan maƙudan kuɗaɗe ga ita yarinyar, sannan aka raba auren da ke tsakanin Yayarta da Abdul. Bayan gama shari’ar ne rayuwar Abdul ta shiga wala-gigi saboda iyayen duk sun juya mishi baya, ba tare da sanin gurin gudu ko gurin tsira ba na ɗauki Abdul-Hafiz na tafi da shi can ƙauye gurin ƙanin Kakanmu. A niyyata ya zauna a can, bayan ƙura ya lafa iyayensa sun huce sai ya dawo cikin gari.
Inda Allah ya taimake mu shi ne ko da naje sai ban ɓoye musu komai dangane da abinda yake faruwa ba. Ashe kaya ne ya tsinke a gindin kaba, a taƙaice dai acan ƙauyen Ƙanin Kakanmu wanda muke kira da Ɗanbaba shi yayi ma Abdul magani. Kuma wani abin sha’awa da burgewa shi ne Wallahi maganinsa sam babu shirka ko saɓon Allah a ciki, rubutu ne yake yi sai ya zuba garin magani a ciki yaba Abdul ɗin ya sha.
Kamar wasa sa’adda muka je ɗakko shi ni da direban gidan Yaya Ɗanbaba ya tabbatar min in dai ba matar aurensa na halal ba, in Allah ya yarda Abdul bazai sake kusantar zina ba, ko da kuwa tsirara mace za tayi a gabansa in dai ba halaliyarsa bace bazai taɓa kusantar ta ba.
Ko da muka dawo na faɗa ma su Yaya abinda Ɗanbaba ya ce da farko duk basu ɗauki maganar da muhimmanci ba, sai da suka ga sannu a hankali abubuwa suna ta juyewa yadda basu taɓa tsammani ba. Cikin hukuncin Allah kamar yadda Ɗanbaba ya faɗa haka ne ya tabbata, domin sun gwada shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.
Sai ma wani nutsuwa da hankali na musamman Abdul ya ƙara akan wanda yake da shi a baya. Ya nemi yafiyar iyayensa, ya mayar da hankali sosai kan karatu har zuwa yanzu da ya zama abin alfahari ba ga mu iyayensa kaɗai ba, har ga al’ummar musulmi gaba ɗaya…”
Tun kafin Maman Abba ta dire numfashin maganganunta har Umma ta zube gwuiyawunta biyu a ƙasa. Ta haɗe hannayenta duk biyu alamun roƙo idanunta na tsiyayar da zafafan hawaye ta fara cewa
“Ki taimaka min! Don Darajar Allah da fiyayyen Halitta SAW ki taimaka min kamar yadda Allah ya taimake ku ko ni ma kuka na zai zo ƙarshe. Ki taimaka min ki kaini gurin Ɗanbaba in karɓa ma Samira magani, duk da maza sun ja baya da nemanta har yanzu bata san Annabi ya faku ba. Ina tsoron abinda zai je ya zo a can gaba.
Wallahi tallahi wannan halin da yarinyar nan take ciki shi ne babban ƙalubalena a yanzu, ko ɓatan mahaifinta ba ya ɗaga min hankali kamar yadda mummunan halin da take ciki yake ɗaga min hankali. A wannan karon, na sha alwashin yin amfani da ƙarfina na mahaifiyarta in aurar da ita ko tana so ko ba ta so. Amma babban abin tsoro da fargabata shi ne, kar in aurar da ita ya zama an gudu ne ba’a tsira ba, tsorona yadda ta saba tu’ammali da maza kala daban-daban ta kasa tsayuwa ga mijin aurenta, ina fargabar ta dinga bin mazajen banza da igiyar auren wani a kanta. Wannan firgitaccen tunanin, shi ne abinda yasa kike ganina a zawarce Maman Abba.
A mafi yawancin lokuta ƙwaƙwalwata tafarfasa take yi, a yadda nake ji a jikina kamar zuciyata gab take da bugawa… Don Allah don Annabi ki taimaka min kamar yadda Allah ya taimake ku kuka samu waraka kan ciwon Abdul-Hafiz a lokacin da baku taɓa tsammani ba…”
Hannu biyu Maman Abba ta sa ta ɗaga Umma ta zaunar da ita akan kujera. Ita kanta idanunta ciccike suke da hawayen tausayin Umma, idan ta tuno irin tashin hankalin da suka shiga lokacin matsalar Abdul matsayinsa na namiji da bahaushe ke yiwa kirarin duk abinda yayi ado ne lallai Umma tana ma da ƙarfin zuciya, da ita ne, bata ma san irin halin da za ta shiga ba.
“Kar ki damu Maman Samira, ki kwantar da hankalinki don Allah. Tun farko ni nayi alƙawarin taimaka miki, shi yasa har na baki wannan labarin. Yanzu dai ki koma gida, gobe idan Allah ya kaimu ki shirya da wuri mu kama hanya, ƙauyen da nisa sosai…”
‘Mafarin lamarin kenan.’
Maganin da Umma take tilasta ma Samira sha a cikin ƙwarya shi ne maganin da Ɗanbaba ya haɗa mata, kuma ya faɗa ma Umma yadda za ta dinga ba ta maganin. Bayan wannan maganin kuma yayi ma Umman alƙawarin zai dage mata da addu’ar Allah ya nutsar da zuciyar Samira guri ɗaya, ta yadda ko da anyi auren in dai ba wani ƙaddara da ba’a fata ba babu abinda zai hana ta zama cikin lumana da ƙan-ƙan da kai ga mijinta.
Sannan ya ƙara ma Umma wasu muhimman addu’o’i akan waɗanda ta sani ya ƙara jaddada mata dagewa da yin ibada tana kai kukanta ga Rabbil-izzati. Domin faɗin Allah Ta’ala ne duk wanda ya dogara gare shi haƙiƙa ya isar masa.
Tabbas da gaske ne, duk wanda ya dogara ga Allah mafificin dogaro zai ga biyan buƙata a cikin ƙanƙanin lokaci. Sannu a hankali kamar yadda muka bayyana a baya, Umma da kanta ta fahimci lallai kwalliya tana biyan kuɗin sabulu. Don haka ta ƙara dagewa da ibada a gefe guda kuma ta fara sakar ma Samira fuska tana jan ta a jiki, har ma take amfani da hikimarta na mahaifiya tana nusar da Samira muhimman abubuwa dangane da rayuwar aure waɗanda in dai ta riƙe su kuma tayi amfani da su sannu a hankali za ta kai ga tsanin nasara.
Asibitoci uku Umma da ƙaninta da ƙanin mahaifin Samira suka kai ta aka yi mata medical chek-up. Cikin hukuncin Allah duk wani gagarumin ciwo da zai iya kawo tarnaƙi ga batun auren Samira da Isiya ba’a same ta da shi, ciwon sanyi kawai take da kuma shi ɗin ma ba wani mai tsanani bane, tuni ƙwararriyar likitar mata ta ɗora ta akan magunguna masu kyau.
Bayan kai sakamakon ga Iyayen Isiya su ma basu yi ƙasa a gwuiwa ba gurin tura shi asibiti domin yayi gwajin Genotype da HIV, ba wai don suna zarginsa da neman mata ba sai don share duk wani tantama da ka iya jewa ya dawo. Shi ɗin ma dai lafiya lau ne, jininsa A-A ne ita kuma Samira A.S, a shawarar da likita ya basu kuma lafiya kalau ne za su iya aure ba matsala. Kuma ba’a same shi da cutar Ƙanjamau ba.
Ta ko wane ɓangare dai sai Hamdala, aka tsayar da batun aure bayan Samira ta gama Istibra’i da sati biyu.
*****
Wani ƙaƙƙarfan nishi mai tafe da gurnani aka ja aka sauke a kunnuwan Khamis. Kamar baza ayi magana ba daga can ɓangaren, shi kuwa har lokacin bai gaji da jera kalmar Hello, hello, hello cikin rawar murya da ɓare-ɓaren baki ba.
Sai can aka furta cikin tsawa daga can ɓangaren da wata gwarjejiyar murya mai barazanar fasa dodon kunne
“Kai dalla banza dakata ka ishi mutane da Hello hello kamar wanda ya warke kurumta… Kai ne mahaifin Mannira?”
“Eh ni ne! Wallahi ni ne!! Na rantse da Allah ni ne!!! Mannira Khamis Abubakar ba? Ƴata ce halak-malak! Ni na haife ta…”
Ya jero maganganun a ruɗe tashin hankalinsa na ƙara ninkuwa daga hamsin zuwa ɗari.
“To madaalllaah… Lallai ka iya haihuwa…!”
Aka sake furtawa daga can ɓangaren da yanayin maganar dabanci. Khamis ya buɗe baki zai sake magana aka katse shi da cewa
“Keke b… gefen sabon maƙabarta, ƙarƙashin gadar ƴan keke napep… kayi gaggawar zuwa ka ɗauki ƴarka a gurin… Domin yanzu haka tana cikin mummunan hali, sabuwar yankar rake ce… Mun gama kwasar rabonmu, idan baka yi gaggawar zuwa ba tabbas wasu gayun ne za su tsinci dami a kala… domin gurin matattarar ƴan holewa ne. Allah ya maka albarka Dagus, lallai ka iya haihuwa… Mun daɗe bamu samu yarinya ɗanya sharaf da nunannun kayayyaki irin ƴarka ba… A huta gajiya Dagus…”
Ƙit! Aka katse wayar daga can ɓangaren ba tare da an bashi damar cewa komai ba.
Tsayuwar bugawar zuciya saboda wani abun firgici da aka ji ko aka gani, abu ne da Khamis bai taɓa ganin ya faru a gaske ba sai dai a film ko a labaran littafi. Sai ga shi a yau ya faru da shi a zahiri.
Allah ne ya tsare shi ta hanyar shigowar Uncle Jamilu cikin falon kamar an jefo shi, da yayi mummunar faɗuwan da in dai ba tsarewa da kiyayewa ta Ubangiji ba babu abinda zai hana shi kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki.
“Subhanallahi… Khamis! Khamis lafiya kuwa? Me yake faruwa ne?”
Ya jera mishi tambayoyin a ruɗe bayan ya taro shi da gaggawa a lokacin da yake daf da kaiwa ƙasa.
Khamis kam ba baka sai kunne, ga dai idanunsa a buɗe, amma bayan idanun da ke buɗe babu abinda ke motsawa a jikinsa. Saboda tsananin ruɗewa Uncle Jamilu ya ma manta shi ma’aikacin lafiya ne, ya kai gwauro ya kai mari a tsakiyar falon, daga bisani tunanin sheƙawa Khamis ɗin sassanyar ruwan sanyin cikin frige ya faɗo mishi arai.
Bayan jan nannauyar ajiyar zuciya, da buɗe idanu a firgice, kalaman da ya iya maimaitawa a fili kawai cikakken kwatancen da aka bashi na inda zai je ya ɗauki ƴarsa Mannira ne, a bayan haka bai ƙara cewa uffan ba ya sake afkawa duniyar suma a karo na biyu.
Aka ce ranar wanka ba’a ɓoyon cibi, an riga an zo wani gaɓa da duk yadda Jamilu ya kai ga riƙewa Khamis sirrin cikin gidansa ya zama dole ya janyo wani na jikin Khamis ɗin cikin wannan mummunan al’amari mai rikitarwa da ban firgici.
Ya san Yaya Yusuf a matsayin mafi kusanci ga Khamis, amma sam ba shi da lambar wayarsa. Kuma bai san gurin aikinsa ba, balle kuma gidansa.
Kuma ko da ya ɗauki wayar Khamis da take yashe a ƙasa sam ya kasa buɗe ta balle har ya duba gurin lambobi ya ɗauki lambar wayar Yaya Yusuf. A dole ya mayar da wayar ya ajiye.
Har ya naɗe hannun riga zai ɗauki Khamis don ya saka shi a mota ya kai shi asibiti sai Nauwara ta faɗo masa arai. Da saurin gaske ya ɗauki wayarsa ya lalubo lambarta ya danna mata kira.
A can ɓangaren kamar baza ta ɗauka ba, domin lokacin tana tsaka da shafe Alhajinta don faranta masa rai a karo na barkatai ne kiran ya shigo wayarta, sai kuma taja tsaki a fili sannan ta ɗaga wayar, murya a cushe tace,
“Uncle ina class ne fa…”
“Nauwara ba lokaci. Ki turo min lambar wayar Yayan mahaifinku Alhaji Yusuf yanzunnan, ke ma duk halin da kike ciki ki tabbatar ana tashinku ki same mu a asibitin Garkuwa, Daddynku babu lafiya.”
Ga abin da ake gudu Innalillahi Khamis ya ja wa kansa da iyalan sa masifa