Skip to content
Part 53 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Nannauyar ajiyar zuciya Ziyada taja ta sauke, jikinta a sanyaye ƙwarai. Sannu a hankali tana jin yadda damuwarta ke ƙara ninkuwa.

Ta kalli Aunty Rukayya fuska damalmale da damuwa ta ce,

“Wallahi Aunty lafiyata ƙalau kamar yadda na faɗa miki. Kawai dai yau ɗin gaba-ɗaya na rasa sukuni da nutsuwar zuciya, tun da na wayi gari da asubah. Zuciyata ta ƙi min daɗi sam! A gefe guda ga faɗuwar gaba da nake yi akai-akai.

Hankalina duk yayi gida, tunanin Mannirah da Nauwara yana ta faɗo min akai-akai. Ban sani ba ko lafiya?”

“Uhmmm!”
Aunty Ruƙayya itama ta sauke ajiyar zuciya. Kafin ta ƙarasa cikin ɗakin ta nemi guri kusa da Ziyada ta zauna.

Hannunta guda ta kamo ta riƙe a cikin nata, da taushin murya ta fara magana idanunta cikin na ƙanwar nata da take yiwa wata matsananciyar ƙauna mara algus.

“Dama ai dole ki damu Auta. A matsayinki na mahaifiyar da ba ta tare da yaranta ai dole ki kasance cikin damuwa da tunaninsu kusan a ko da yaushe. Da wannan dalilin yasa nake tunanin ko don su Mannirah ba za ki haƙura haka nan ki koma gidan mahaifinsu ba?”

Cikin ƙanƙanin lokaci damuwar fuskarta ta yaye, baƙin ciki da tsana suka bayyana ƙarara, ta kalli Aunty Rukayya da idanunta da suka canza launi lokaci ɗaya zuwa jajaye ta ce,

“Wallahi Tallahi in anyi duniya don Manzon Allah SAW ni da auren Khamis har abada. Ko da kuwa mu biyu kaɗai za muyi saura a duniyar nan bazan taɓa koma wa aurenshi ba. Yaran da suke tsakanina da shi Allah ya raya su yayi musu albarka.

Idan kuma kuka matsa akan dole sai na koma mishi to wallahi za ku neme ni ku rasa har abada!”

Ire-iren alwashin da ta dinga sha kenan tun lokacin da ta dira a gidan Aunty Rukayya da ke birnin Lagos tare da sauran ‘ya’yanta uku da ta samu nasarar tafiya da su ba tare da sanin mahaifinsu ba. Haka taje musu ziƙau babu komai a tattare da ita bayan yaran, hatta da wayar hannunta ma ta cire layukan ciki ta lalata wayar da hannunta don ma kada tsautsayi ko ƙawa-zuci ya kai ta ga kunna wayar har ta tuntuɓi yaran ta sanar da su inda take. Domin ta tabbata suna jin inda tayi mafaka, to kuwa lallai kamar mahaifinsu ne ya ji. Ita kuwa ko da Khamis shi ne Autan maza ta haƙura da aurenshi har Abada.

Duk yadda Anty Rukayya ta so ta lallasheta akan ta haƙura ta sanar da mutane inda take, idan ma auren Khamis ɗin ne ba ta so za ta iya shige mata gaba a matsayinta na babbar Lauya anan Lagos, su shigar da ƙara domin a ƙara tabbatar da rabuwar auren.

Sam Ziyada ta ki.

“Uhmmm! Aunty ki barni kawai in samu nutsuwa, in gama Iddah hankalina kwance kamar yadda Addininmu yayi umarni. Ina da tabbacin matuƙar ɗaya daga cikin su Nauwara ko dangin mahaifinsu suka san inda nake suka taso ni gaba da magiya da roƙon in koma gidan Khamis ba lallai in iya tuburewa ba. Faruwar hakan kuwa kamar na jefa kaina da kaina a mahallaka ne. Kuma dai kina tune da Yaya Yusuf, ina matuƙar jin nauyinshi saboda irin tsayuwar dakar da yasha yi a zamantakewar aurena da ɗan’uwansa. Na fi son kowa ya san inda nake bayan na gama Iddah, kin ga a lokacin babu batun tilastawa in koma sai dai shawara a tsakanina da ko wanene. Karɓar shawarar komawa gidan Khamis kuwa daidai yake da ranar da jaki ya fidda ƙaho a kansa.”
Irin maganganun da take yi kenan aduk sa’adda Aunty Ruƙayya ta bijiro mata da zancen ta taɓo yaran su san inda take.

Ko a yanzu, kallon Ziyadah take yi cikin sigar lallashi da lallaɓawa
“Banda ke da abinki Auta, ta ya za ayi ki ce kin tsani mijinki Uban ƴaƴanki? Akan wani dalili? Kar fa ki manta, tun a farkon fari Khamis zaɓin zuciyarki ne. Saboda Allah ke ba kya tunanin yaranki da kika baro da kuma waɗanda kika taho da su yanzu? Idan fa baki manta ba, har yanzu da auren Khamis a kanki tunda saki ɗaya ne. Kuma su yarannan da kika kwaso yana da hakki a kansu kamar yadda waɗanda kika baro a can suke da hakki a kanki. Ina kuma son ki tuna da cewa, hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Khamis ko kina so ko bakya so kun riga kun zama ɗaya, ko kun rabu a daidai wannan gaɓar kamar an gudu ne ba’a tsira ba.”

Sanin da tayi Aunty Rukayya ba za ta taɓa fahimtar matsanancin halin ƙunci da baƙin cikin da ta shiga a gidan Khamis ba tunda har yau bata buɗe baki ta faɗa mata abubuwan da suka faru na yasa ta girgiza kai kawai. Ta buɗe baki a hankali ta ce
“Ni dai yanzu Aunty duk ba wannan ba. Wayarki nake so ki bani aro in kira Yaya Yusuf in tambayi halin da yaran nan suke ciki. Har yanzu hankalina ya ƙi nutsuwa, jin yadda suke zai sa hankalina ya kwanta. Sauran maganganun komawa auren Khamis ko rashin komawa zamu yi daga baya, amma ba yanzu ba.”

Sanin halin Ziyada na taurin kai yasa Aunty Rukayya bata matsa ba, ta ɗauki wayarta ta miƙa mata. Aunty Rukayya na kallo ta sanya lambar Yaya Yusuf da yake haddace a kanta ta danna mishi kira, sannan ta sanya wayar a hands-free.

Bugu ɗaya, biyu, aka ɗaga can ɓangaren. Yayi sallama da muryarshi mai cike da kamala da haiba, amma duk a sanyaye, kamar ba Yaya Yusuf da ko wani lokaci ake jin jajurcewa da mazantaka a muryarsa ba.

Sai jikinta ya ƙara sanyi, har ta kasa buɗe baki ta amsa sallamarsa. Duk ta bi ta diririce. Sai da ya sake yin wata sallamar sannan ta iya amsa mishi cikin sanyin murya da saluɓewar jiki.

Shiru yayi kamar wanda yake son ya tabbatar da wani abu. Zuwa can kuma ya ce
“Ziyada? Ziyada ke ce?”

Bai jira ta amsa ba ya cigaba da magana da sauri da yanayin da ke bayyana jin daɗin kiransa da tayi a daidai wannan lokacin.
“Allahu Akbar! Ma Shaa Allah!! Don Allah kina ina Ziyada?”

Haka kawai sai ta ji hawaye sun cika mata idanu. Ta kai hannu tana ɗauke ƙwallar tare da gyara zama tana russunawa cikin girmamawa kamar tana gabanshi ta fara gaishe shi.

Ya amsa mata cikin natsuwa. A ɗokance ya cigaba da jefa mata tambayar tana ina ne? Tana lafiya? Kuma yaushe za ta dawo?

Sanin da tayi rabin tambayoyin nashi bata da amsarsu yasa ta dinga kauce musu. Ta dai amsa da cewa lafiyarta lau kuma tana hannu mai kyau amma yayi haƙuri ba zata iya sanar da shi inda take a halin yanzu ba. Ta ƙara da cewa yanzun haka ta kira ne kawai ta ji ko ya su Mannirah suke saboda duk yinin yau tunaninsu ya hana ta samun kwanciyar hankali.

Daga can ɓangarensa, shiru yayi yana juya tambayar tata a cikin ranshi. Yana so ya faɗa mata takamaiman abinda ya faru, saboda yasan da cewa a matsayinta na uwa idan har taji abinda ya faru da ɗiyarta tabbas duk inda take za tayi gaggawar dawowa. Sai dai wani ɓangare na zuciyarsa kuma na tsoron irin damuwa da tashin hankali da fargabar da zai iya jefata idan har ta ji gaskiyar abinda ya faru.

Da wannan dalilin na ƙarshe yasa shi sanar da ita rabin gaskiyar maganar
“Maganar gaskiya yanzu haka ma muna asibiti ne Mannirah ba ta da lafiya…”

A gaggauce ita da Anty Rukayya suka yi musayar kallo. Sannan ta dafe ƙirjinta da take jin bugawar ya ƙaru fiye da da cikin kiɗima da tashin hankali ta ce
“Yaya lafiya? Me ya same ta? Me yake damunta haka?”

Yayi ɗan jim kafin yace
“Hatsarine ya ɗan rutsa da ita, amma dai tana nan lafiya lau sai ɗan abinda baza’a rasa ba. Amma fa akwai maganganu da yawa game da mas’alar da ke faruwa waɗanda ko kusa ba za su faɗu ta waya ba. In da so samu ne dole ne sai kin zo kin gani da idanunki, don haka nake so in ji inda kike a halin yanzu. Idan da halin tahowa to lallai gobe kiyi sammako ki taho, idan kinyi nisa da yawa ko da wata matsala ta daban, ki sanar da ni zan ita turowa a ɗaukeki a duk inda kike a faɗin nigeria.”

Yayi shiru yana sauraren abinda zata ce. Ita kuma ta hau girgiza kai kamar yana kallonta hawaye wasu na korar wasu a fuskarta. Cikin kuka take cewa

“Kayi haƙuri Yaya, amma ba zan taɓa dawowa gidan Khamis ba. Don Allah kada ka tambaye ni dalili ko kuma ka tursasa min akan in koma, Wallahi ba zan iya ba!”

Jiki cike da kasala da damuwa Yaya Yusuf ya laluba kujera ƙwaya ɗaya da take ajiye gefen gadon da Khamis ke kwance ya zauna. Da sauri ya gyara riƙon wayar jin da yayi kamar za ta suɓuce a hannunsa. Yasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi, amma abinda ya tsorata shi shi ne rantsuwar da Ziyada tayi saurin shatawa tun ma kafin ya roƙeta koma wa auren Khamis.

“Ziyada, Khamis ƙanina ne, nasan halinshi ciki da bai. Ina kuma sane da irin abubuwan da yake aikatawa na cutarwa a gare ki. Sai dai a yanzu ba wai ina neman alfarmar ki komawa Khamis da aure bane, saboda nasan idan na ce ki koma ɗin, za ki koma Ziyada. Amma ba zan zalunceki ba.

Sai dai ina roƙonki a duk ranar da kika ji zuciyarki ta yi sanyi, kika dawo, to muna maraba dake. Idan kuma kika ga ba zaki iya ba, wallahi zan shige miki gaba in jajirce har sai rabuwar aurenku ya tabbata, duk da ba na fatan hakan. A yanzu dai ina neman alfarmar idan kin ga da hali ki zo ga yaranki, saboda suna matuƙar buƙatarki musamman a wannan yanayin da ake ciki. Ba don kowa ba, don su ɗin kawai Ziyada, don Allah ki dawo gare su.”

Kuka take yi mai matuƙar ban tausayi da karya zuciya. Su dukansu shiru suka yi suna saurarenta jikinsu a sanyaye. Sai da tayi kukanta ma’ishi kafin ta buɗe baki daƙyar ta ce,

“Yaya kayi hakuri, amma a yanzu, ba zan iya zuwa inda suke ba… Ba zan iya ba. Don Allah idan Mannira idonta biyu ka haɗa ni da ita, ko kuma ka haɗa ni da Nauwara…”

“Mannira har yanzu ba a fito da ita ba daga ɗakin tiyata. Nauwara kuma taje ta dawo. Amma zan faɗa mata idan ta dawo sai ta kira ki ta wannan layin. Sannan ina ƙara roƙonki, don Allah ki daure ki zo ki ga yarannan, suna matuƙar buƙatarki a kusa da su, musamman ƙaramar da take cikin ciwo.”
Da waɗannan maganganun na shi suka yi sallama ba tare da ta amsa mishi za ta je ba.

“Ni fa ina ga akwai yiwuwar da matsala wacce sam Yaya Yusuf ba ya son ya faɗa miki ta waya.”

Cewar Aunty Ruƙayya tana ɗauke ƙwallar idanunta.

Ziyada kai kawai ta iya ɗagawa saboda gaba-ɗaya hankalinta yana gurin Mannira. Nutsuwar da ta so ta samu ta dalilin wayarta da Yaya Yusuf ɗin bata samu ba, sai ma hankali da ya ƙara tayar mata ba tare da sanin takamaimai me yake damun ɗiyarta ba da har ake mata tiyata.

Ta kalli Anty Rukayya idanunta sun kaɗa sunyi jajur.

“Ban san me zanyi ba Aunty, gaba-ɗaya kaina ya kulle wallahi. Don Allah ki faɗa min abinda ya kamata in yi”

Kafaɗarta ta ɗan fara bubbugawa alamar rarrashi, a tausashe ta ce,

“Ki kwantar da hankalinki Ziyada, ki rage ma kanki wannan damuwar don gudun samun matsala. In sha Allah babu wata gaggarumar matsala. Kuma ai yace zai sa Nawwara ta kira, idan ta kira sai muji ko menene daga bakinta. Kuma zan kira Adda Karima, tunda ita tafi kusa da su, Kano da Kaduna ba wani nisa yayi ba. Ko ita zata iya zuwa ta gano mana abinda yake faruwa, idan ta kama lallai sai kinje ɗin sai mu san yadda za ayi ki tafi da gaggawa.”

Hankalinta ya ɗan nutsa da jin kalaman Aunty Ruƙayya. Har ta iya lallaɓawa tayi sallar isha’i, ta tsakuri abinci kaɗan ta ci, kafin ta shiga banɗaki tayi wanka sannan ta kwanta bayan ta sha maganin ciwon kai da taji yana ta sara mata.

Yaran tuni suka yi barci, kuma tasan basa tare da wata matsala tunda yar aikin gidan tana kulawa da su sosai. A taƙaice ma suna cikin walwala sosai fiye da gidan mahaifinsu, domin rana ɗai-ɗai ne Aunty Ruƙayya ba ta saka direba da mai aikinta su kwashi yaran zuwa gurin shaƙatawa daban-daban.

*****

Jikin Nauwara a matuƙar sanyaye yake. Duk da babu wanda yayi mata bayanin takamaiman halin da Mannira take ciki, amma yadda take jin maganganun da nurses masu wucewa suka dinga yi, da kuma yadda ƴan sanda da yan hisba da aka shigo da su cikin case ɗin bisa shawarar shugaban asibitin suke ta kara-kaina a harabar gurin, sai taji duk jikinta yayi mata wani irin sanyi.

Kwananta biyu a gidan Yaya Yusuf, kuma har zuwa lokacin ba a barta ta ga Mannirah ba, duk da cewa kullum suna zuwa asibitin har ma su yini a can idan ba ta da lectures, amma babu mai shiga inda Mannira take sai Yaya Yusuf da Anty Iklima dake zaman jinyarta.

Zamanta gidan Yaya Yusuf takura ce ba ƴar ƙarama ba. Ashe duk tsaurin Daddynsu da take gani, na Yaya Yusuf ya dame shi ya shanye. Duk inda za ta motsa ko ta juya, Anty Zainab yana kanta, duk motsin da zata yi kuwa sai an tambayeta dalili.

Matakai ya zauna ya gindaya mata masu yawa da tsauri, ya kuma bata tabbacin idan ta kuskura ya sameta da karya ɗaya daga ciki ranta zaiyi mugun ɓaci.

Shi yasa tayi matuƙar sanyi, makaranta ma ta mayar da hankali tana zuwa saboda tsoron kada wani lokaci yaje bai sameta ba ya tambaya a faɗa mishi halin da take ciki, tasan ɓacin rai ne zai biyo baya.

Duk yadda Amina ta dinga zuga ta da cewa ta dinga satar jiki tana fita kamar yadda take yi a gidan Daddy kasawa tayi. Ta riga ta gama tsorata da warning ɗin Abba Yusuf. Don haka kullum sai dai tace mata ta dakata tukunna abubuwa suyi sauƙi.

A kwana na huɗu ne aka barsu suka shiga ganin Mannira. Tana ganin yadda ƙanwar tata ta koma cikin ƙanƙanin lokaci kawai sai ta zube ƙasa tana ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka. Dama damuwa ce ta tara ta kwana da kwanaki, da wannan dalilin yasa ta dinga rusa kuka tun Abba Yusuf yana mata faɗa Aunty Ikilima na rarrashinta har sai da shi da kanshi ya koma rarrashinta da tausasan kalamai.

<< Lokaci 52Lokaci 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×