Ɓacin rai da damuwar da take gani a fuskar mahaifiyarta ya zarce ace damuwar duk akan ciwon mahaifinsu ne.
‘To me yake faruwa? Ko akwai wata sabuwar matsala ce a tsakaninsu kamar yadda suka saba? Domin iyayen kusan kullum cikin rikici suke. Wani irin zama ne suke yi kamar na ƴan dadiro.
Yanzunnan za’a gansu cikin farin ciki da soyayya. Anjima kaɗan kuma sai a gansu cikin ɓacin rai da jin haushin juna. Sai kuma ta tuna gigitaccen tsawan da suka ji ɗazu Daddy ya daka ma Mummy, wataƙila shi ne har yanzu abinda yake ƙona ma uwar rai. Taɓe baki tayi, sai kuma ta ja zanin da take rufa ta lulluɓa har kanta, ta lumshe idanu zuciyarta cike da saƙe-saƙe mabanbanta.
A can tsakar gida cikin wani irin matsanancin murna da har ya gaza ɓoyuwa a fuskar Khamis, ya sake lalubo lambar Big Aunty ya danna mata kira.
Yana fara ƙara ta ɗaga da gaggawa, da karaɗin murna a muryarta ta fara cewa
“Da girman kujerarka ƙanina Khamis babbar harka, kar dai ka ce min har ciniki ya faɗa?”
Da yanayin jin shi ɗin ya kai wani shege ya ce
“Ahhh! Aka ce miki ni na wasa ne Aunty?”
“Inaaa.. ai na san ka wuce duk yadda ake tsammaninka ƙanina. Yanzu dai ya ake ciki? fesa min da ɗumi-ɗuminta.”
“Kamar dai yadda kika yi tsammani, ciniki ya faɗa…”
“Ayyiririri…”
Ta katse shi ta hanyar rangaɗa wata zazzaƙar guda kamar a can gurinta ba dare bane.
“Ina jin ka Ƙanina, ciniki ya faɗa. Allah yasa dai babban kifi ka sake kamo mana.”
“Ƙatoto kuwa Big Aunty. Yanzu dai ayi gaggawar yi musu wani ɗanyen shiri wanda marabarsa kaɗan ne da yadda uwayensu suka suntulo su zuwa duniya.”
A tare ita da shi suka fashe da dariya. Sannan ya cigaba da cewa
“Amma fa ni bazan samu zuwa in kai su ba…”
“Me yasa ƙanina? Me yasa haka? Na zaci za ka zo ka fara ɗan tattaɓa nunarsu ka saka musu albarka?”
Ta ƙarasa maganar da damuwa a muryarta.
“Kar ki damu Aunty. Zuwan nawa bazai yiwu bane a wannan lokacin, na ɗan samu ƙaramin hatsari ne amma da sauki. Ke ma kin san ko ba’a min tayi ba ina ɗanɗanawa balle kuma abinda ya zama da kaso na a ciki? Za mu jame ko ba yau ba. Yanzu dai ayi gaggawar shirya su kamar yadda na ce, zan tura ma Zabari kwatancen inda zai kai su, ayi gaggawar shirya su Aunty. Oga ya tsani ɓata lokaci.”
“Angama Kanina, ba ka da matsala. Yanzu za’a cika aiki, sai na ji alert kenan?”
“Eh! Kar ki damu.”
Ya amsa yana dariya.
“Dole in damu Kanina. Na san halinka fa, yanzu dai faɗa min. Ya tsarin rabon zai kasance?”
“Zan ja hamsin, ki ja talatin, kan ta waye su ja ashirin…”
“Ban yarda ba, wallahi ban yarda ba. Ka san irin kuɗaɗen da na kashe musu a ɗan yinin nan kawai kafin su fara ƙyalli yadda za’a so su kuwa? Idan ka yarda kai arba’in ni arba’in yaran su tashi da ashirin-ashirin?”
“Ke dai Aunty kin cika masifaffan son kuɗi. Ban san me za kiyi da maƙudan kuɗaɗen da kike tarawa ba”
“Eh na ji dai. Ka amince ko kuwa a fasa kowa ya rasa?”
Tayi mishi tambayar da yanayin da ke tabbatar mishi da gaske take yi.
Da sauri ya daina dariyar da yake yi, ya san halinta sarai. Yanzunnan sai ta ɓata al’amarin bayan ya daɗe rabon da ya samu irin wannan damar.
“Shi kenan Big Aunty. Ke ai tawa ce, ni da ke kuma ba ta ɓaci. Na amince da yadda kika ce.”
Nan take ta saki murya suka ƙarasa maganar da za suyi. Ya katse wayar ya tura mata cikakken kwatancen gidan baƙin da Honourable Ɗanlabaran Usman Sabon kuɗi ya ce a kai masa kayan da aka tallata masa.
Saboda ɓadda kama yasa Khamis adana lambar Honorable ɗin da suna Babbar harka
Dare aka ce mahutar bawa. Ga Ziyada kam wannan dare bai zama hutu a gare ta ba, duk da ba yau bane lamari makamancin irin wannan ya fara aukuwa ba amma har yau ta kasa sabawa.
Duk tsawon lokacin da Khamis ya ɗauka fiye da awa biyu da rabi zaune a tsakar gidan yana waya da maza da ƴanmata daban-daban tana tsaye ne a jikin windon falonsu tana kallonshi.
Babu abinda ke tsiyaya a idanuwanta sai zafafan hawaye. Wani dunƙulallen abu ne yazo ya tsaya mata a wuya, shi bai faɗa ciki ba shi bai fito waje ba.
Idan ta kalli Khamis uban ƴaƴanta a idanuwanta, ta kuma saurari irin munanan kalaman da ke fita daga bakinshi. Sai ta ƙara ji a ranta lallai kam tayi asara.
Saboda maɗaukakin tashin hankali da damuwar da take ciki ta ƙura ma inda yake zaune idanu har bata san sa’adda ya taso da ɗingishi ya shigo cikin falon ba.
Mamaki sosai ne ya bayyana a fuskarsa ganinta tsaye a gurin.
“Uhmmm”
Ya faɗa a fili haɗe da taɓe baki.
Ya taka a nutse har ya ƙarasa inda take tsaye, hannunsa guda ya ɗaga ya ɗora a kafaɗarta.
Firgigit ta dawo cikin hayyacinta haɗe da waigawa, karaf idanunta suka faɗa cikin nashi.
A karo na biyu ya sake taɓe baki, sai kuma ya ɗan saki murmushu cikin rashin damuwa da hawayen da yake gani dama-dama da fuskarta.
“Ziya! Har sai yaushe iska zai daina wahal da mai kayan kara? Ki sauƙaƙa ma kanki mana ta hanyar ajiye komai gefe ɗaya ki rungumi irin tsarin da nake so…?”
“Khamis..!”
Ta katse shi ta hanyar kiran sunansa da wani irin rauni a muryarta. Ta ja shessheƙar kuka sau biyu, a raunane zuciyarta na wani irin zafi ta cigaba da cewa
“Ƴaƴana Khamis! Ya za ka ji a ranka idan juyin juya hali irinna LOKACI ya hurga mu ɓigiren da za su fara girbar abinda su basu san hawa ba balle sauka a kanshi?”
“Ke dallah saurara min. Bakinki ya sari ɗanyen kashi. Ke dai da an fara magana ta arziki da ke yanzunnan za ki saki ki kamo wani shirmen wanda ko kusa hankali bazai ɗauka ba. Duk ƴan matan da nake ta’ammali da su ba ni nake musu dole ba, ba ni nake janyo su cikin harkokina ba. A taƙaice ma harkarmu babbar sana’a ce irinta ba ni gishiri in baka manda. To a cikin wannan harkar ina wata sakayya da zai bibiyi ƴaƴanki bayan ni ɗin ba wani zalunci nake aikatawa ba. Ki kiyayeni fa Ziya, kar ki kuskura ki sake min irin wannan zancen, ba na so.”
Yana gama faɗin haka ya wuce cikin ɗakinsu ya barta tsaye a gurin.
Kamar mutum mutumi, haka ta bi bayanshi da kallo har ya ɓace ma ganinta.
Maganganunsa da ba yau ya fara faɗa mata makamantansu ba ko kaɗan basu samu matsuguni a zuciyarta ba. Ta yaya za’a ce bawa na aikata saɓon Allah sannan ya ce bazai girbi mummunar shukar da yake yi ba?
Ƙafafuwanta ne suka yi wani irin sanyi. Idan ta fara tunani kan al’amarin Khamis, ta hanga ta hango ɗan’uwansa ɗaya ne ƙwallin ƙwal da suka fito ciki ɗaya. Sannan shi ɗan’uwan nasa ƴaƴansa maza ne ƙwara biyu.
Ita kuma ƴaƴanta duk mata ne namiji ƙwara ɗaya. Sai ta ji wani irin matsanancin tsoro da firgici ya ƙara lulluɓeta. A lamarin Khamis idan aka tashi girbe shukar da yake yi ita da ƴaƴanta sune a ciki dumu-dumu.
Ƙasa ta durƙushe ta sake fashewa da kuka. Matsanancin da na sanin auren Khamis da ba yau ta fara yi ba ya ƙara lulluɓe ilahirin jikinta. Menene laifinta? Ita menene ya kai ta ga dagewa da cijewa akan son sa har sai da ta aure shi?
To ko dai nata sakayyar ce ta fara bibiyarta tun yanzu? Mahaifiyarta ta faɗa ta ƙara faɗa cewa za tayi kuka a lamarin Khamis, maganganun ne suka dawo mata rangagaɗau a cikin kunnuwanta kamar a lokacin Ummansu take faɗa mata.
Waiwaye ya kasance ado ne a cikin ko wace irin tafiya. A cikin rayuwar ko wane bawa akwai ƙaddara mai kyau ko akasinta da aka rubuta tun fil-azal za ta faru da shi. Amma wasu wahalhalun mu da kanmu muke janyosu cikin rayuwarmu. Aka ce muji tsoron wata fitina wacce idan ta zo za ta shafi har waɗanda basu ji ba basu gani ba a cikinmu. Taya bawa zai yada sharri a baya sannan yayi tunanin tsintar alkhairi a gaba?
Ziyada ƴa ta uku a gurin mahaifiyarta Hajiya Khadeeja da mahaifinta Alhaji Auwal. Babbar ɗiya a wannan ahali Karimatu ce, sai mai bi mata Rukayya, Ziyada ita ce auta.
Ziyada tana da shekaru goma sha biyu a duniya Allah ya ɗauki ran mahaifinsu Alhaji Auwal. Rashin mahaifi tamkar rushewar wani babban bango ne da gaba ɗaya iyali suke jingine da shi, amma kasancewar kafin rasuwarsa Allah ya sa yana da rufin asirinsa sai rayuwarsu bata tagayyara sosai ba.
Hajiya Khadija jajurtacciyar macece mai kamar maza da ko bayan rasuwar mijinta tayi tsayuwar daka kan al’amarin ƴaƴanta. Duk yadda dangin mijin suka so ƙwace ƴaƴan sam ta ƙi yarda da haka, a ƙarshe ma sai da ta maka su a kotu sannan suka shafa mata lafiya.
Duk da dukiyar da Alhaji Auwal ya bari bata zauna ta naɗe hannuwa ba. Sana’a goma aka ce maganin mai gasa, kayayyaki take saidawa a cikin unguwa tun daga kayan miya har zuwa zannuwa dangin leshi, atamfa, shadda, da yadiddika na maza da mata.
Saboda kasuwancinta da iya tafi da jama’a yasa gidanta ya ƙara fice sosai a unguwar, kusan duk matan unguwar suna cinikayya da ita, sun santa ta sansu. Bayan ciniki akwai kyakkyawan mu’amala a tsakaninsu. Ko kaɗan bata ɗauki girman kai ta ɗora ma kanta ba, duk inda abu ya faru na daɗi ko akasin haka da gaggawa take shiga tayi murna ko jaje.
Da wannan dalilin yasa duk gidajen da suke kusa da ita sama-sama ta ɗan san halin da suke ciki sun san halin da take ciki.
Akwai gidaje biyu tsakanin gidansu Khamis da na su Ziyada. Baza’ace babu kyakkyawar alaƙa tsakanin gidajen biyu ba, amma alaƙar bata yi irin mugun zurfinnan da za’a kirata da kusa-kusa ba.
Hajiya Hauwa mahaifiyar Khamis halinta na son yin abu kai tsaye da gadara da isa ba ɓoyayye bane a gurin maƙwaftanta, sannan ko kaɗan ba ta da haƙuri, ba ta da uzuri musamman idan abu ya biyo ta kan ƴaƴanta. Amma fa tana da kirki, ga kyauta, abin hannunta da na mijinta sam basu rufe mata idanu ba. Wancan halin nata ne dai yasa mata irinsu Hajiya Khadija ke ɗan ja baya da ita, domin idan abu ya haɗo ku yanzunnan za ta rufe idanu tayi ma mace wankin babban bargo, kamar dai wani abu na mutunci bai taɓa haɗa ku ba.
Ƙulluwar zazzafar soyayya tsakanin Khamis da Ziyada wani al’amari ne da duk gidajen biyu babu wanda zai ce ga sadda ta samo asali. Kawai wayan gari aka yi Khamis yaje ma Hajiya Hauwa wacce suke kira Ammi da zancen yana so tayi ma mahaifinsa magana aje nema mishi auren Ziyada.
Itama a ɓangaren Ziyada kamar haɗin baki cire kunya da fargaba tayi ta tunkari Ummanmu da zancen tana son Khamis, shi take so a aura mata, har sun tsayar da magana a tsakaninsu zai turo iyayensa.
Ɓulluwar wannan al’amari yasa duk gidajen biyu shiga wani irin hali na tashin hankali. Can gidansu Khamis duk yadda iyayen ke son shi ko kaɗan basu goya mishi baya ba, saboda shi ɗin yaro ne ƙarami, ga yayansa Yusuf nan da ya girme mishi da shekaru bakwai ko budurwa ba shi da, balle har a kai ga fara zancen aure.
Acan ɓangaren Ziyada kam ita ta fi ɗaukar lamarin da zafi-zafi. Mutsuke idanu tayi duk yadda uwar take ta mata karatun dalla-dalla ta toshe kunnuwanta ta ƙi gane abinda ake nuna mata. Tun ana magana ta sunkuyar da kai tayi shiru fuskarta a ɗaure, har aka fara kaiwa matakin zumɓura baki, da kawar da kai gefe ɗaya ana gunguni.
Daga ƙarshe ta ƙeƙashe idunta ta fara fito na fito da yayunta da mahaifiyarta. Ana faɗe tana mayar da amsa cikin rashin kunya da bushewar idanu.
A wannan lokacin Karimatu mai shekaru ashirin da uku ita ce aka sa ranar aurenta. Ruƙayya ma tana da manemi, amma ba’a tsayar da maganar aure ba.
Cikin fushi Yayyin nata suka so haɗuwa suyi mata dukan kawo wuƙa ko za ta dawo cikin hayyacinta da gaggawa uwar ta hana su. Cikin fushi da ɓacin rai ta nuna su da yatsa manuniya tana cewa
“Ku ƙyale min auta ta. Ni da ita tun tale-tale akwai fahimtar juna. Kuma cikin ku biyun babu wacce ta isa ta ratsa tsakanin fahimta da ƙaunar da ke tsakanina da Autata. Zo nan ki zauna kusa da ni kin ji Ziyadar Umma.”
Bakinnan a gaba tana ƴan harare-harare da fisga irinta wacce take jin kanta a tsakiyar kogin soyayya ta ƙarasa daƙyar ta zauna kusa da mahaifiyarta.
Murmushi Ummanmu tayi, ita lamarin wani lokacin dariya yake bata. Hannun Ziyada ɗaya ta kamo ta fara mata magana a tausashe.
“Autata, kin ga har yanzu ke yarinya ce. A cikin tafiya irinta soyayya har yanzu baki fara ba balle har a ce za ki iya rarrabe farfaru da barbaƙu a cikinsa. Shi Namiji ba’a mishi irin wannan zazzafar soyayyar a wanye lafiya. Kiyi haƙuri ki bi umarninmu, za kiga da kyau in dai kin bi abinda ni mahaifiyarki da yayyenki muke so.
Amma ina tabbatar miki ko rantsuwa nayi babu kaffara matuƙar kika dage sai kin auri wannan yaron a daidai wannan gaɓar za kiyi kuka nan gaba, Wallahi sai kinyi kuka Ziyada. Baza ki taɓa cimma abinda ke a ɗan ƙaramin tunaninki kike hangen za ki cimma a aurensa ba…”
“Ummanmu. Ni dai shi nake so. Idan ba Kham ba sai rijiya, rijiyar ma gaba dubu mai cike da fasassun kwalabe.”
Ta faɗa ma uwar cikin tsantsar raini da fitsara, ta ƙara da kawar da kanta gefe ɗaya ta cigaba da murguɗa baki.
“Hmmm! Ta yaro kyau take ba ta ƙarko. Auta shi wannan yaron da kika nace ma mecece sana’arshi? Ba ya sayar da komai fa. Yaron da ko makarantanr sakandire ya ƙi tsayar da hankali guri ɗaya ya kammala ta ina kike tunanin zai iya riƙon aure? Da me zai riƙe ki idan anyi auren?”
“Ummanmu shi arziki ba na Allah bane? Dare ɗaya fa Allah kanyi bature. Kika sani ko shi ɗin da kuke rainawa shugaban ƙasa ne a gobe? Ni dai ko bazai zama wani abu ba ma dinga bara muna cin abinci, a hakannan shi nake so, kuma shi ɗin dai zan aura.”
Kama haɓa Ummanmu tayi tana kallon Ziyada da mamakin yadda duk ta inda ta ɓullo sai yarinyar ta ɓulle.
Duka duka Ziyadar nawa take? Yaushe ta haife ta? Ita har yanzu a idanunta kallon wannan ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da take ta-ta-ta a gabanta take ma Ziya. Har yanzu bata cika shekaru goma sha bakwai ba, ta ina tayi saken da har zuciyar ƴar ƙaramar yarinyarta ta kamu da irin wannan matsananciyar soyayyar da har take iya tsayawa a gabanta suna kallon juna cikin ido ta faɗa ta mayar mata da martani?
Shi kanshi Khamis ɗin nawa yake? Da waɗanne irin kalamai ne yake amfani har ya samu nasarar mallake zuciyar Ziyada haka? In dai ba ta manta ba shekarunshi sha tara ne da wasu ƴan watanni.
Ta ina aure tsakanin ɗanyen kai na tsantsar ƙuruciya irinna Ziyada zai haɗu da zafin kai da tashen balaga da samartaka irinta Khamis? Ita ko ba ma wannan ba sam yaron baiyi mata ba, wasu daga cikin ɗabi’unsa tun a yarinta sam-sam basa mata daɗin gani.
Yaro ne da ya taso a shagwaɓe, a sangarce. An samu haihuwarsa ne a lokacin da ake neman ƙarin haihuwar afujajan! Da wannan dalilin yasa Hajiya Hauwa mahaifiyar Khamis ta shagwaɓa shi sosai kamar tsoka ɗaya a miya.
Irin yadda take nunawa babban ɗanta Yusuf yaro mai haƙuri, hankali, hangen nesa kamar ba ita ta haife shi ba. A fili yake ba mutanen gidansu kaɗai ba hatta ƴan unguwa sun shaida Khamis shi ne ɗan soyayya a gidan.