Wa ya gaya maka tsare tarbiyar ƴaƴa wayau da dabarar iyayensu ne? Sannan bayan ka take dokokin Allah kake tunanin ganin yadda kake so? Bayan ka keta haddin ƴaƴan wasu kuma ka ce kai baza a keta haddin ƴaƴanka ba? Ai wallahi ina tabbatar maka waɗannan munanan ƙaddarori biyun da ka gani somin taɓi ne matuƙar baka tuba ka shiga taitayinka ba."
Khamis dai ya kasa magana, domin ya san duk maganganun ɗan'uwansa babu komai a ciki sai tsantsar gaskiya. Sai kuka kawai yake yana ƙarawa, a zuciyarsa ji yake 'Ina ma ace. . .