Skip to content
Part 60 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Wa ya gaya maka tsare tarbiyar ƴaƴa wayau da dabarar iyayensu ne? Sannan bayan ka take dokokin Allah kake tunanin ganin yadda kake so? Bayan ka keta haddin ƴaƴan wasu kuma ka ce kai baza a keta haddin ƴaƴanka ba? Ai wallahi ina tabbatar maka waɗannan munanan ƙaddarori biyun da ka gani somin taɓi ne matuƙar baka tuba ka shiga taitayinka ba.”

Khamis dai ya kasa magana, domin ya san duk maganganun ɗan’uwansa babu komai a ciki sai tsantsar gaskiya. Sai kuka kawai yake yana ƙarawa, a zuciyarsa ji yake
‘Ina ma ace ya mutu kafin wannan mummunar ranar? Ganin Nauwara a yanayin da ya ganta abu ne da bai taɓa tsammanin zai faru a rayuwarsa ba.’

Tsakanin ɗan’uwa da ɗan’uwa sai Allah. Irin kukan da yake yi kamar ƙaramin yaro, tun yana ba Yaya Yusuf haushi har ya koma bashi tausayi. A ɗan tausashe ya ce
“Yana daga cikin abinda aka rubuta a kundin ƙaddararka. Sai kayi haƙuri, ka karɓeta da hannu bibbiyu kamar yadda ka sanya dubbunnan mutane a ciki su ma suka karɓa da tawakkali.”

Har yayi shiru sai kuma ya cigaba da cewa
“Uhmmm! Kai ne fa don bin mata har da yiwa ƴaƴan wasu asiri don kawai ayi ta aikata zina da kai Khamis! Kaicon ka! Wallahi Kaicon ka Khamis!! Na zaci ƙaddarar da ta afkawa Mannira zai zama sanadiyyar shiryuwarka. Saboda rashin rabo ka sake komawa ruwa, gashi nan yanzu ka ɗauko ta ka ɗiyar, bin mazan take yi hankalinta kwance, ba kuma tare da wani yayi mata asiri ko ya tursasata ba. Hakan ya yi maka daɗi ko?”

Ya juya ya kalli Nauwara fuskarsa a ɗaure, da ɓacin rai ya fara mata magana
“Kin ba ni kunya… Na rantse da Allah ban taɓa tsammanin haka daga gare ki ba. Saboda a iya gani na mun ba ki tarbiyar da ta da ce, mun kuma yi iyaka bakin ƙoƙarinmu wajen ganin cewa muna fitar miki da hakkinki, kuma muna kulawa da buƙatunki. Ashe duk hakan bai ishe ki ba Nauwara?”

A haukace ta ƙara fashewa da wani irin kuka wanda ya sanya zuciyar su duka biyun karyewa, Khamis ya biye mata suka yi ta rairawa kamar wasu ƙananun yara.

Daƙyar ta iya buɗe baki cikin kuka ta fara magiya tana basu hakuri da neman afuwarsu.

“Duk wani neman yafiya da za kiyi babu abinda za ta mana Nauwara. Bazai taɓa goge mummunar ganin da idanuwanmu suka yi ba, kin ci amanarmu, sannan kin ci amanar tarbiyar da muka ɗauki tsawon shekaru muna gina ki akai. Idan har da gaske kike kin tuba, to ki tubarwa Allah ki kuma koma zuwa gare shi.

Abu na farko da zan faɗa miki shi ne, daga yau, na hana duk wata fita da zaki yi zuwa ko’ina, na yanke miki karatun da kike fakewa da shi kina aikata iskancin da kika ga dama. Sannan magana ta biyu ita ce, yanzunnan kafin ki fita ki aje min jakarki da wayar hannunki. Abu na uku shi ne daga yau kin fara istibra’i, nasan kin san abinda hakan yake nufi. Bayan kin gama kuma zaki ji sauran matakan da zasu biyo baya.

Fice min daga nan mutumiyar banza sakarya kawai, ina ganinki kamar mai hankali da nutsuwa ashe kura ce da fatar akuya. Kin ji kunya!!!”

Cikin kuka ta aje jakarta da waya a ciki ta fice daga falon tana rangaji kamar za ta kifa ƙasa.

Ya sake mayar da kallonshi kan Khamis ya ce,

“Duk sana’o’i da neman kuɗin duniyar nan ba ka da babbar sana’ar da ka riƙa a matsayin sana’a kuma hanyar samun kuɗi sai Kawalci. KAWALI ne kai Khamis. Ka ɗauki yarinya daga gaban iyayenta ka kaita gurin ƙattin banza mutanen banza, ayi zina da ita, kuma ka san zinar za’a yi da ita. Bayan kuma an gama aikata Zinar a biya ka kuɗin kai ta ita kuma a biya ta kuɗin zinar da aka yi da ita. Ƴar wasu ce fa kake ɗauka ka kai ta ayi lalata da ita ta yaya kake tsammanin ta ka ƴar za ta tsira Khamis?

Baya ga haka abincinka haram! Abin shan ka haram! Suturarka haram! Ka ciyar da iyalanka da haram. A hakan kake tsammanin Allah zai tsallakar da ƴaƴanka daga munanan ƙaddarori?

Allah ya sani, kuma yana ji yana gani na fita hakkinka Khamis. Na yi iyakar ƙoƙarina a kanka, duk wani abu da ya kamata inyi don ka shiryu na yi iya yi na Khamis. Allah ne shaida, amanar mahaifiyarmu na riƙe. Ko a yanzu na mutu muka haɗu a barzahu ba ni da kunyarta…”

Yana zuwa nan a maganganunsa muryarsa ta fara rawa. Sai ga hawaye sharr.! A hankali yasa hannu ya share wasu suka sake gangarowa, da raunin murya ya cigaba da magana.

“Ka kwashi tsumman ƙafafunka ka bar min gidana yanzu. Na rantse da Allah ba na ko son ganin fuskarka Khamis, ka je kawai. Ban taɓa ji a zuciyata ina maka mummunar tsana irin na yau ba. Ka tashi ka fice tun kafin inyi maka baki, domin tabbas zai kama ka.

Kaje kawai, duniya ce. Wanda bai zo cikinta ba ma jiran zuwansa take yi. Idan ka ga damar shiryuwa ka shiryu, don kanka, idan kuma baka ga dama ba, duka dai kanka. Amma ka sani, daga yau, duk wani hukunci da uba zai zartarwa ƴaƴan da ya haifa na cikinsa, shi zan zartar akan su Nauwara. Saboda har yanzu ba ka cancanci zama mahaifi a gare su ba.”

Kamar bazai tashi ba, sai kuma ya miƙe zumbur! Har lokacin hawaye na tsiyaya a fuskarsa ya fice daga cikin falon da saurin gaske kamar zai tashi sama.

A ɓangaren Nauwara kuwa ko da ta shiga ciki kai tsaye banɗaki ta wuce. Duk da Allah ya sa babban abu bai kai ga afkuwa tsakaninta da Duwan wanda gayu da canjin zamani yasa ya maida sunan nashi D. Boy ba. Kai tsaye wankan janaba ta fara yi don dai ta samu nutsuwar zuciyarta. Har lokacin hawaye ya ƙi tsayawa a idanunta, tana wankan tana rusa kuka.

Allah ya sani, tun da uwarta ta haife ta bata taɓa shiga cikin kunya, baƙin ciki, nadama, da na sanin duk irin abubuwan da ta daɗe tana aikatawa irin na yau ba. Ita me ma ya kai ta? Tsautsayi, aka ce zagin mahaifa.

Ta tsine ma matsiyaciya kuma shaiɗaniyar ƙawa irin Amina ya fi sau dubu.
Tun a farkon fari sanadiyyar haɗuwarta da Amina a facebook yasa tarbiyarta ya fara gurɓata sannu a hankali.

Sai kuma ta fara tunanin tun tana ƙanƙanuwar yarinya me ma ya kai ta ta uzzura ma Daddy har ya siya mata waya? Duk a lokacin ta tuna irin yadda Mummy ta nuna matsanancin ɓacin rai akan wayar da Daddy ya sai mata, ta tuna yadda ita da Daddyn suka nace suka ƙi bin ra’ayin Mummy. Haka nan Mummyn ta haƙura ba don zuciyarta ya so ba.

‘Yanzu wa gari ya waya? Duk a yawon barikin da take yi me ta tsinana ma kanta kuma me ta tsinana ma rayuwarta? Ita da take yawon barikin ma a tsorace? Eh a tsorace mana, domin tana tsoron ta mallaki abubuwa masu bala’in tsada Daddy ya ramfo halin da take ciki.

Hatta akawun ɗin ta na banki ta gagara sakin jiki ta loda wasu maƙudan kuɗaɗe a ciki saboda tsoron kada tsautsayi yasa wata rana Daddy ya gani. Duk irin manyan kuɗaɗe da dalolin da take samu kaso tamanin cikin ɗari yana hannun Amina da Mummy. To gara ma Mummy kuɗaɗen da take bata da sunan balance ɗin da suke biyanta ne a matsayin uwar ɗakinsu.

Amina kuwa tana bata kuɗaɗen ne a matsayin ta tara mata, amma ita da kanta ta san yaudarar kanta take yi, ko da ta nemi kuɗaɗen idan ma har ta samu ne ta samu kashi ɗaya daga cikin ɗari na abinda ta bata ajiya. To me yawon bariki ya tsinana mata?

Irin kukan da ta daɗe tana yi da zazzafan tunanin da ya addabi zuciyarta yasa cikin ƙanƙanin lokaci kanta ya fara wani fitinannen ciwo, mintuna kaɗan tsakani kuma zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe ta.

*****

Tsananin firgici da tashin hankali yasa Khamis bai damu da mutanen da yake wucewa suna kallonshi kamar mahaukaci saboda kukan da yake yi ba. Wasu masu ƙarfin hali da suka san shi a unguwar kuwa har tsayawa suke suna tambayarshi
“Malam Khamis lafiya kuwa? Ko wani abu ne ya samu Ɗan’uwan naka?”

Ko kallonsu ba ya tsayawa yi, haka yake gifta su ba tare da ya ce musu uffan ba. A yanzu tunanin da ke zuciyarsa ɗaya ne, kafin su isa hotel ɗinnan Oga ya faɗa mishi Big Aunty ita ta sama ma su Duwan ƴan matan da za su huta da su. Don haka a yanzu kai tsaye gidan Big Aunty ya nufa, gara yaje ya fara cin kutumar… kafin yayi takakkiya har garin Kano ya lahanta Duwan.

Ko ɗazu ya ƙyale shi ne saboda Yayanshi da ke gurin ba don ya haƙura ba. Tun akan Mannirah yasha alwashin idon shi idanun wanda ya haiƙewa ɗiyarshi lallai sai ya guntule mishi mazakuta. Sai dai duk abinda zai faru ya faru.

Yana isa kan titi ya tare acaɓa ya hau
“Muje, Unguwar dosa za ka kai ni. Malam so nake ka ƙure malejin gudunka a ɗari biyu mu isa a gaggauce, duk kuɗin da ka yanka min zan biya ka.”
Haka ya faɗa ga mai mashin ɗin.

Wani ma yai rawa bare ɗan makaɗi? Mai mashin da ya kasance ƙwararren ɗan shaye-shaye kuma tun safe ba shi da ko sisi sai yanzu abokinsa ya bashi mashin ɗin da cewar ya taɓa aiki zuwa shida na yamma zai karɓa. Nan take ya fige mashin da bala’in gudu tun kafin Khamis ya gama daidaita zamansa, in banda Allah yasa yayi gaggawar riƙe ƙuƙumin mai mashin ɗin tabbas babu abinda zai hana a watsar da shi.

“Allah dai ya tsare.”
Cewar wasu dattawa su uku da suke tsaye a gefen titi suna kallon duk abinda ke faruwa.

*****

Tun bayan fitar Khamis da Yayansa, Oga ya zauna jaɓar akan doguwar kujerar da take cikin ɗakin hotel ɗin. Har wannan lokacin nutsuwarsa bai dawo daidai ba. A gaskiya tun da yake aikata baɗala iri-iri a bariki bai taɓa cin karo da abinda ya tsaya mishi a zuciya irin wannan ba.

Tsakani da Allah Khamis ya bashi tausayi. Babu abunda yake hasasowa a zuciyarsa sai idan da shi ne ya kama ƴarsa a irin wannan yanayin da suka tarar da Nauwara da ya zai yi? Ai kila ma da yanzu ya mutu. Ya sani a yadda yake da masifar son ƴaƴa zuciyarsa bugawar farat ɗaya za tayi. Lallai Khamis yana da jarumta da ƙwarin zuciya.

Da wannan dalilin yasa sanin irin saɓon da yake aikatawa zai iya bibiyarshi da zuri’arshi bai saki jiki ya tara ƴaƴa da yawa ba. Ɗa ɗaya kacal namiji da ya mallaka tun yana ƙarami ya kai shi Sa’udiyya, acan yake karatu da komai, izuwa yanzu har ya shiga jami’ar Madina. Mahaddacin Alƙur’ani ne gangaran ka fi gwani. Kallon ɗan kaɗai a matsayin jininshi yana saka shi jin wani matsanancin alfahari.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da hankalinshi kan Duwan ya ce
“Kwana a Kaduna bazai yiwu ba Duwan. Wannan shirmen da ka aikata ya rusa plan ɗin komai. Kira Hadi ya sallami yarinyar da take tare da shi mu kama hanyar barin garinnan tun kafin Khamis ya sake waiwayarmu. Ka san shi dai da bala’in zuciya da rashin haƙuri, dole muyi gaggawar komawa a miƙa sunanshi gurin Malam ya shafe abin a ƙwaƙwalwarshi idan ba haka ba bazai taɓa bari ka cigaba da rayuwa cikin nutsuwa ba.”

Duwan da tun bayan ficewarsu ya haɗa kai da gwuiwa hankalinsa a tashe zuciyarsa cike da tsanar kansa daƙyar yayi ƙarfin halin ɗaga kai ya kalli Oga.

“Wallahi sam ban san ƴarsa ta cikinsa bane. Ko kusa ban ga kamanni ba. Ina ƙaunar Khamis, da na san ƴarsa ce babu yadda za’ayi in bari irin wannan harkar ta haɗo mu da ita…”

“Na sani. Ƙarasa shiryawa bari in kira Hadi.”

Kira uku yayi ma Hadi a waya bai ɗauka ba, da yake duk ya san ɗakunan da suke ciki, a taƙaice ma shi ya kama ɗakunan, don haka ya miƙe da kanshi ya fice zuwa ɗakin Hadin don sanar da shi komawar gaggawa da za suyi.

Wannan batun komawa ko kusa baiyi ma Amina da Hadi daɗi ba, haka nan dai suka rabu ba don zukatansu sun so ba. Ya cika mata jakarta dam da maƙudan kuɗaɗe sannan suka yi musayar lambar waya a tsakaninsu. Yayi mata alƙawarin zai sake dawowa kwanaki kusa, idan kuma bai dawo ba zai kira ta har Kano ta kai mishi ziyara.

Saboda saurin da suke yi nan ƙofar hotel ɗin suka barta tana takawa a ƙasa zuwa inda za ta samu Keke napep su kuma suka kama hanya. Oga bai faɗa mishi dalilin da yasa ya ce sun fasa kwanaki biyun da za suyi a kaduna ba sai da suka ɗanyi nisa da cikin gari.

Shi kuwa Hadi ko don ba a gabanshi al’amarin ya faru ba? Dariya yayi ta ƙyalƙyatawa yana ƙarawa. Ko kusa abin bai bashi tausayi ko kuma ya tsaya mishi a zuciya kamar yadda ya tsaya musu ba.

“Wato wannan shi ne sata ta saci sata. Taɓɗijan!!! Ina ma dai ace a gabana wannan diramar ya faru? Na rantse da Allah da sai nayi Vid in yaɗa ma duniya.”

Sai kuma ya sake kwashewa da dariya yana dukan sitiyarin motar da shi yake tuƙawa.

*****

Ko da ta tare mai keke napep, da farko har ta ce mishi ya kaita gida, amma kuma sai ta canja shawara tace mishi ya kaita gidan Mummy. Cajin da tayi ma kanta da magungunan mata har yanzu bata samu nutsuwar da take buƙata ba. Ga kuma giyar da ta ɗaɗɗaka ma cikinta har yanzu bai gama sakinta ba, gara ta je gidan Mummy, in yaso zuwa can da yamma sai ta wuce gida.

Jakarta ta buɗe ta zaro wayarta ta lalubo lambar saurayinta Ikhlass ɗan shawalwalin yaron da take bala’in so da dukkan zuciyarta kuma take riritashi kamar tsoka ɗaya a miya amma sai tayi rashin sa’a wayar tayi ta ringing bai ɗauka ba. Ko da ta kira sau biyu ba amsa, wayar ta mayar cikin jaka tana jan tsaki a ƙasa-ƙasa.

A zuciyarta bari tayi idan ta isa gidan Mummy sai ta kira shi. A irin wannan yanayin da take ciki shi kaɗai ne zai tafi da ita yadda ya kamata. Idan kuwa bai ɗauki waya ba duk inda yake za ta kira abokansa biyu na kurkusa su nemo mata shi.

Suna isa ƙofar gidan Mummy bata ɓata lokaci ba ta sallami mai napep ta shige gidan ba tare da ta tsaya sauraren mai keke da yake ta zuba mata godiyar bar mishi canjin ɗari uku da tayi ba. Wani abin mamaki da yasa ta tsayawa idanunta warwaje shi ne ganin haɗaɗɗiyar mashin ɗin Ikhlass wayyo kuɗina fake a rumfar aje motocin gidan, ita da kuɗinta ta siya mishi mashin ɗin sabuwa dal, shi yasa duk inda ta ga mashin ɗin take gane ta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 59Lokaci 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×