“Ikky yana gidannan ke nan?”
Ta tambayi kanta a fili.
Rashin samun amsar tambayarta yasa ta ƙara sauri don shiga falon gidan, a lokacin kuma sai take tunanin to ko dai kiran da tayi mishi a waya yana gaf da isa gidan ne shi yasa bai ɗauka ba?
“Haka ne ma.”
Ta amsa tunanin a fili tare da sakarwa kanta lallausan murmushi. A zuciyarta take jin yadda ƙaunar Ikhlass wanda take kira Ikky a gayance yana ƙara tumbatsa. Bala’in son shi take yi, kishin shi take na bala’i kamar wani mijinta na aure. Ta tare gaba ta tare baya a cikin zuciyarsa. Shi ma da yake ɗan alƙawari ne a gabanta da bayan idanunta ita ɗin dai ita ce ƙwallin-ƙwal.
Sun shirya nan da shekaru biyu masu zuwa za suyi aure. A lokacin ita da shi duk sun gama karatu sun fara aiki, za suyi aurensu hankali kwance a yadda ta gama tsarawa. Duk da dai a yanzu duk wata mu’amala ta auratayya ita ke gudana a tsakaninsu.
A mafiyawancin lokuta cikin ƴan kwanakin idan tana buƙatarshi ta fi zuwa da shi gidan Mummy inda take da ɗaki guda a matsayin nata, saɓanin ɗakunan hotel da ta fi kama musu a baya.
Ko da ta shiga falon, rarraba idanu ta fara yi don ganin ta inda za ta hango Ikky a zaune yana jiran ƙarasowarta. Amma wani abin mamaki shi ne babu shi, sai ƴanmata uku da suke zaune da ƴan ɓingilolin riguna a jikinsu suna buga lido, ga kwalaben lemu nan birjik a ajiye a teburin kusa da su.
“Zury ina Ikky?”
Ta tambayi ɗaya daga cikin ƴanmatan da suke buga Lido ɗin har lokacin yanayin mamakin rashin ganinshi a falon bai bar kan fuskarta ba.
Firgigit suka yi duk su ukun! Da alamun ma basu san da shigowarta ba sai da suka ji muryarta a tsakiyar kansu kamar daga sama.
“Iye! Na’am! Aunty Amna kin dawo ne? Daman ba kwana za kiyi acan ba?”
Zuri tayi maganganun a daburce. Sai kuma suka fara kallon kallo a tsakaninsu alamun rashin gaskiya ƙarara a fuskokinsu.
Bata fahimci komai ba daga yanayinsu, domin ita kanta ba a nutse take ba. Don haka ta sake maimaita tambayarta ta farko bayan ta amsa ɗaya daga cikin tambayoyin Zury.
“Eh! Na dawo. Ina Ikky? Na ga mashin ɗin shi a waje?”
“Aunty Amna wallahi ba ya nan. Ki duba shi a tsakar gida. Tun da ya shigo ya tambayi ina kike muka ce mishi bakya nan ya fita, mu mun zaci ma ya wuce. Kila ya zagaya ta bayan garden yana jiranki.”
Ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗi haka a gaggauce tun kafin Zury ta amsa.
“Ok!”
Ta amsa a taƙaice.
Har ta kama hanyar fita daga cikin falon don zuwa garden ta duba shi sai kuma ta canja shawara. Cikin falon ta koma, bata sake kallon ƴan matan da suka miƙe a firgice suna kallonta ba ganin ta fasa fita kai tsaye ta nufi hanyar da zai sada ta da ɗakin da yake a matsayin nata.
‘Gara in watsa ruwa ko na ji dama-dama. Duk inda Ikky ya shiga a faɗin gidannan bazai ɓace min ba.’
Maganar da take yi a zuciyarta.
Har ta gitta ɗakin da ke kusa da nata wanda yake mallakin Mummy ne da take barcin rana a ciki sai kuma ta dawo sannu a hankali ta tsaya a saitin ƙofar. Jin kamar ana biye da ita a baya yasa ta waiwaya, ƴanmatan nan ne da ta bari a falo suka biyo bayanta suna kallonta idanunsu a warwaje.
A tsorace ɗaya daga cikin ƴanmatan ta fara cewa,
“Aunty Amna…”
Da sauri ta ɗaga mata hannu alamar dakatarwa.
Kanta ta kara a jikin ƙofar tana sauraren sautin sambatun da ke fita da muryar da ko giyar wake ta sha bazai taɓa ɓace mata a cikin ƙwaƙwalwarta ba.
Ƙirjinta ne ya buga daram! Tsananin firgici yasa bata san sa’adda ta saki jakar hannunta zuwa ƙasa ba duk da kyakkyawan riƙon da tayi mishi saboda maƙudan kuɗaɗen da ke ciki.
Ba tare da wani jinkiri ba ta buɗe ƙofar ɗakin a haukace ta shiga ciki don gane ma idanunta zahiran abinda kunnayenta ke jiyo mata sama-sama ba tare da neman izini ba.
Mummunan ganin da tayi wanda bata taɓa tsammani ba yasa idanunta rufewa ruf! Sai kuma a daburce ta ba abinda idanuwanta suka gani baya tare da ƙwalla wani firgitaccen ihu da ya ratsa lungu da saƙo na cikin ƙaton gidan.
Wannan ihun nata shi ya dawo da su daga nisan duniyar da suka afka basa ji basa gani sai kawunansu da nishaɗin zukatansu kaɗai. Tsoro da firgicin da suka shiga su biyun, kamar ma ya ninninka wanda ita da ta gansu ta shiga.
Da wani irin bala’in sauri Ikky ya zare jikinshi daga na Mummy yayi wani irin wawan tsalle sai ga shi a ƙofar bayin da ke cikin ɗakin, ai kuwa bai tsaya wata-wata ba ya afka cikin bayin da bala’in gudu haɗe da danno ƙofar da ƙarfi ya murza key ta ciki.
Ita kuwa Mummy… Da fari ta ma rasa abinda za tayi saboda tsananin ɗimaucewa da firgicin da zuciyarta ta shiga. Domin ta fi kowa sanin irin yadda Amina take masifar son Ikky da matsanancin kishinsa da take yi.
Wani tunani da ya ɗarsu a zuciyarta kuma yasa tayi niyyar gyagijewa ta watsar da firgicin ta hanyar gwadawa Amina salonsu na tsoffin ƴan bariki da suka ga jiya da yau kuma har gobe ana kan damawa da su. Da saurin gaske ta miƙe zaune daga kwancen da take, ta ɗaga hannu biyu sama alamar sallamawa tana kallon yadda Aminar take tunkarota hannayenta biyu nannaɗe a baya idanuwanta jajur kamar an watsa barkono a ciki.
“Amina…”
Ɗif! Sautin maganar da ta fara ya tsaya cak! Sakamakon jin saukar wani abu a bazata mai tsinin gaske da bala’in ƙarfi ya huda ƙirjinta a guje ya caki daidai saitin ƙahon zuciyarta.
Wani azababben zafi da raɗaɗi da ya fara ratsa ta yasa lokaci ɗaya idanunta suka kaɗa suka yi jajur! A wahalce ta ɗago idanunta tana kallon saitin hannun Amina da yake riƙe da sabon wuƙar da ita da kanta ta ɗauko a kicin bayan ta zubo ma Ikky kayan marmari a cikin wani ɗan madaidaicin faranti ta kai mishi har ɗakin da ta sauke shi.
Babban kuskuren da ta tafka shi ne ko da suka gama ciyayyar kayan marmarin ta hanyar bani in baka kamar wasu masoya na gasken gaske sai bata kwashe komai ta mayar da su kicin ba. Tattare komai tayi ta ajiye a gefe ɗaya suka fara wasannin banza da taɓe-taɓe a tsakaninsu, har zuwa sadda komai ya kankama suka afka ninnisan duniyar da suka shagaltu a ciki har basu ji ƙaran kiran wayar da Amina tayi ma Ikky har daki biyu ba.
Wasu zafafan hawaye ne na tsananin azaba suka silalo daga idanun Big Aunty wacce juyin zamani yasa ta maida sunan zuwa Mummy a gurin sabbin ƙyanƙyasar ƴan matanta da suka zama hanyar shigowar kuɗaɗenta.
“Mummy ni za ki ciwa Amana?”
Amina ta tambayeta da wani irin murya kamar ba nata ba tana sake danna wuƙar ciki tare da murzawa yadda zaiyi daga-daga da sassan zuciyar Mummy.
“Irin wannan hukuncin shi ne sakamakon duk wata maciya Amana. Kin karɓi na ki, saura shi bunsurun yanzu zai karɓi kason sa bayan na tabbatar na dagargaza zuciyarki.”
Tsananin azaba da raɗaɗin fitar rai yasa Mummy ta kasa magana, sai wani irin kakari da gurnani take yi irin na azabar fitan rai. Ga wasu ƙananun hawaye da suke gangarowa ta gefe da gefen idanunta. A wannan ɗan tsakankanin lokacin da mala’ikan mutuwa ke ƙoƙarin zare ranta, kamar a faifan bidiyo haka take kallon duk irin munanan abubuwan da ta aikata a cikin rayuwarta suna wucewa ɗaya bayan ɗaya.
“Amina… kin kashe ni…”
Su ne kalmomi biyu da suka zama na ƙarshe da ta samu nasarar furtawa daƙyar a maimakon kalmar Shahada. Daga haka ɗif! Mala’ikan mutuwa ya zare ranta daga gangar jikinta.
Duk da haka Amina bata zare wuƙar ba sai da a karan kanta ta tabbatar rai ya bar gangar jikin Mummy. Sannan ta zare wuƙar da gudu ta nufi ƙofar bayin da Ikky ya shiga ta fara murɗa hannun ƙofar da nufin buɗewa tana sambatun ya buɗe ya karɓi sakamakonshi kamar yadda tsohuwar kilakin ta karɓi nata sakamakon.
Duk wannan abinda yake faruwa, su Zury suna tsaye a bakin ƙofa suna kallon komai, idanuwansu a warwaje, hannayensu bi-biyu ɗore a kawunansu da matsanancin tashin hankali a fuskokinsu.
Sa’adda Amina ta shammaci Mummy ta caka mata wuƙar nan a tsorace Biba ta buɗe baki za ta yanka ihu da saurin gaske Sholy ta toshe mata baki da ƙarfin gaske. Akan idanuwansu tayi ta murza wuƙarnan duk suna jin maganganun da take yi har Mummy ta garzaya barzahu. Ganin ta nufi ƙofar bayin da Ikky ya shiga da irin maganganun da take faɗa babu alamun wasa a fuskarta yasa cikin sauri Sholy da ta kasance mai ɗan shekaru fiye da Zury da Biba ta janye hannayensu da gudu suka fice daga ɗakin.
Basu ko tsaya neman sutura ta mutunci ba suka fice daga falon a guje suka nufi hanyar fita daga gidan.
Har suka buɗe get suka fita basu ga mai gadi ba, sun ɗan fara nisa da gidan suka hange shi ya fito daga masallaci, yana ta sauri ya koma gida. Don ya san ƙa’idar Mummy na tsanar ya tafi sallah ya bar mata get babu kowa a gurin.
Kai tsaye gurinsa suka nufa jikinsu na rawa kamar ana kaɗa musu ganga.
“Baba Mai gadi ina za ka je? Na rantse da Allah kayi ta kanka ka ceci rayuwarka. Yau gidan Mummy babu lafiya, ga Amina can ta cakawa Mummy wuƙa a ƙahon zuciya tana ta murza wuƙar bata zare ba sai da Mummy ta daina motsi. Yanzu haka tana can tana bubbuga ƙofar bayin da Ikky ke ciki tana ihun ya fito shi ma ta kashe shi. Mu kam mun yi ta kanmu.”
Sholy na gama faɗa ma Mai gadi haka suka sake fyallawa a guje suna gudun ceton rai, babban burinsu suyi nisa sosai da unguwar tun kafin Amina ta kashe Ikhlass ta dawo ta kansu su da tun farko suka ɓoye mata gaskiyar abinda ke faruwa.
Ai kuwa Mai gadi shi ma nan take ya ranta ana kare, duk yadda hankalinsa ke kan gidan saboda ƴan kuɗaɗensa da suturunsa da suke cikin ɗakinsa yana tsoron komawa ajali ya rutsa da shi.
Abinda basu sani ba shi ne duk waɗannnan maganganun da suka faɗa ma Maigadi sun faɗa ne a kunnen wasu Matasan dattijai da gidansu ke maƙwaftaka da na Mummy.
Kuma daman sun daɗe suna takaici da baƙin cikin irin yadda gidan Mummyn ya zama matattara karuwai manya da ƙanana. Sun daɗe suna kai shunen gidan ga hukuma amma saboda ɗaurin gindin da Mummy take da shi na manyan masu kuɗi da ƴan siyasa tun kafin bincike yayi nisa ake watsar da case ɗin.
A yanzu da suka ji magana har ta kai ga yin kisa a cikin gidan, kuma ba kowa aka kashe ba face Mamallakiyar gidan har ana ƙoƙarin sake kashe wani basu ɓata lokaci gurin kiran lambar ƴan sanda ba. Cikakken kwatancen gidan suka ba ƴan sanda sannan suka je ƙofar gidan da matasan layi suka yi dako-dako don kar wacce ake tuhuma ta gama aikata ɓarnar ta fito ta gudu ba tare da an sani ba.
A can cikin gidan kuwa, a haukace Amina ta cigaba da bubbuga ƙofar bayin da ƙarfin gaske tana ihun Ikky ya buɗe mata tun kafin ita ta buɗe da kanta. Ta rantse da girman Allah idan ya bari ta buɗe ba tare da shi da kanshi ya buɗe mata ba sai tayi mishi gunduwa-gunduwa da gaɓɓan jikinsa kamar yadda ake yiwa kaza a maimakon sassauƙan kisan da za ta mishi idan ya buɗe ƙofar salin-alin.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah na tuba ka yafe ni. Wayyo Allah na… Wayyo uwata… wayyo ubana.. Na shiga uku na lalace ni Ikhlas! Allah ga bawanka mai yawan saɓonnan ka ceceni ba don hali na ba…”
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin kalaman da Ikhlas yake maimaitawa ƙasa-ƙasa a bayi cikin kuka na fitar hankali.
Yayi kashi yayi fitsari duk a tsaye ba tare da ya san yana yi ba. Idan yayi gaba yayi baya sai ya duƙa a ƙasa ya sake fashewa da kuka muryarshi ƙasa-ƙasa yana tuna yadda a kullum mahaifiyarshi take mishi nasihar ya ji tsoron Allah. Ya daina amfani da kyawun da Allah ya bashi yana yaudarar ƴan mata a matsayinshi na maraya kuma ɗan talakan tulik.
Amma yasa ƙafa ya shure duk maganganunta. Tana faɗa yana shiga ta kunnen dama ne ya fita ta kunnen hagu. Kyau da iya ɗaukar wankan da yake da su ne jarinshi, duk wata ɗawainiyarshi na duniya ƴan mata suke ɗauke mishi saboda tsananin farin jinin da yake da. Haka suke kashe mishi kuɗi kamar me, sun mai da shi kamar wani ɗan manyan mutane don irin tsadaddiyar rayuwar da yake gudanarwa.
A cikin mintuna goma sha uku da yayi a banɗakin sau talatin da bakwai yana gwada haurawa ta ƴan ƙananun windunan bayin sai yaga abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba cire wando ta ka.
Ya haɗa zufa yayi kashirɓin, kamar an sheƙa mishi ruwa aduk jikinsa. Ga kukan da yake yi, ga majina da hawaye, miyau sunyi jaga-jaga da fuskarsa.
Izuwa wannan lokacin Amina ta gaji da buga ƙofar daga can waje ta tafi kicin ɗinsu a haukace ta ɗauko taɓarya tazo ta fara buga ma ƙofar bayin. Duk a ƙoƙarinta na buɗe ƙofar ta ƙaddamar masa ta ko wane irin hali.
Saboda tsabar tashin hankali da rarrafe ya ƙarasa jikin ƙofar tana buga taɓarya yana sake danna ƙofar da dukkan ƙarfinsa. Ya wage murya yana kuka yana haɗa ta da girman Allah da na iyayenta tayi mishi rai, ya bi Allah ya bi ta. Don Allah ta yafe mishi daga yau zai zama kamar bawa a gare ta, bazai ƙara gigin cin amanarta ba.
Suna wannan budurin yana roƙanta tana auna mishi zagi ta uwa ta uba tana rantsuwar ko zai mutu sai ta kashe shi, kwatsam! ba zato ba tsammani sai ga ƴan sanda sun zagayeta.
“You are under arrest.”
Ɗaya daga cikin ƴan sandan wanda da alama shi ne Ogansu ya faɗa da ƙatuwar murya yana saita ta da bakin bindiga.
Cak! Taja ta tsaya tana rarraba idanu a tsakaninsu. Da alamun sai a yanzu ne ta dawo cikin hankalinta, tsoro da firgici kwance ƙarara kan fuskarta. Sai rarraba idanu take yi cikin rashin gaskiya tana ji tana gani suka maƙala mata ankwa a hannuwanta duk biyun, wuƙar da ta kashe Mummy tana gani Ogan ƴan sandan ya buɗe hankici a hannunsa sannan ya ɗauki wuƙar, wasu kuma suka nufi gawar Mummy suna ɗaukarta hoto.
Ikhlass bai buɗe ƙofar bayin ba sai da ya tabbatar da gaske ƴan sanda ne suka iso. Yana buɗewa zai ruga a guje saboda tsoro Ogan ya daka mishi tsawa. Ba shiri ya tsaya a guri ɗaya yana makyarkyata, kallo ɗaya za’a mishi a gano firgici kwance ƙarara a fuskarsa.
A wulaƙance kuma a ƙyamace suka hurga mishi kayanshi ya saka bayan ƴan sanda biyu sun tsaya a kanshi da bindiga ya tsarkake jikinsa sama-sama saboda duk ya ɗume ɗakin da warin kashin jikinsa. Sannan aka maƙala mishi ankwa yana ji yana gani aka tisa ƙeyarsu zuwa Ofishin ƴan sanda.
interesting