Skip to content
Part 66 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Wata ƙaƙƙarfan dariya Nauwara ta tuntsire da shi daga can ɓangaren tun kafin Mannira ta ƙarasa ba ta labarin yadda suka ƙare da Abban na su ta fara mata tsiya.

“Iyyeh iyyeh Ƙanwata ki ce kin kusa shigowa daga cikinmu ke ma ki sharɓi irin romon da muke sharɓa. Ina jin ki, sai aka yi Yaya?”

Shiru tayi kamar baza ta cigaba da bata labarin ba, amma tuna irin jan kuɗin da ake tsakanin Saudiyya da Nigeria yasa muryarta a sanyaye ta cigaba da faɗa mata yadda suka yi.

“Hmmm! Duk da wata irin faɗuwar gaba da ta same ni lokaci ɗaya bai hana ni amsawa da eh, Abba!”

Ya ce,

“Ma sha Allah. Yanzu dai zancen cika alƙawarin ne ya taso. Akwai wani bawan Allah da yayi min maganar yana da sha’awar aurenki tun da daɗewa. Ina tunanin ma za ki gane shi, Wannan likitan ne da yayi miki aiki lokacin da mummunar ƙaddara ya afka miki.

Daman tun a wancan lokacin kafin a sallameku ya neme ni da maganar, duk da cewa na yaba da hankalinshi da kuma jin irin kyakkyawan shaidar da ya samu a cikin asibitin na mutuntaka. Sai ban bashi wata sahihiyar amsa ba na dakatar da shi a hikimance, domin a lokacin babban burina ki warke ki samu nutsuwa ki cigaba da rayuwarki kamar babu abinda ya faru da ke.

Abinda ban sani ba ashe tun a wancan lokacin ya cigaba da bibiyar al’amarinki a ɓoye. Ni kuma bai ƙara tunkara ta da maganar ba sai dai lokaci bayan lokaci yana aiko min da gaisuwa. Sadda mahaifinku ya rasu ya zo har gida da abokai da iyayenshi sunyi mana gaisuwa.

To Allah cikin ikonsa dai sati huɗu suka wuce sai ya turo min da magabatanshi yana sake roƙon don Allah in bashi dama a karo na biyu, shi dai har yanzu yana nan akan bakanshi.

To kafin dai in amsa musu sai da nasa aka min sahihiyar bincike akanshi da iyayenshi, kuma Alhamdulillah, ya samu kyakkyawar shaida ta ko wane ɓangare. Da wannan dalilin yasa na sake kwashe sati guda ina istikhara akan lamarin kuma a kullum ƙarin nutsuwa nake ji a zuciyata. Don haka na bashi damar turo magabatansa.

Wani ƙarin abin daɗin kuma shi ne, yanzu haka yana nan Madina, ashe ya samu aiki da babban asibitinsu dake nan. Kuma ya tabbatar min idan kun yi aure, kin gama karatunki, za ki iya cigaba da zama anan tare da shi har ma ki cigaba da karatu idan kina ra’ayi duk zai yarje miki.

Duk da mun gana da magabatansa har ma na karɓi kuɗin na gani ina so, na kafa musu sharaɗin idan har ya zo gare ki kika ga baki aminta dashi ba, to babu takura, zan mayar musu da kuɗinsu. Me kika ce Mannirah? Duk da ina da cikakken iko a kanku Allah ya sani ba ni da niyyar yi muku auren dole…”

Tun kafin ta aje numfashin maganarta Nauwara ta katse ta da cewa
“Allah dai yasa baki watsa ma Abba ƙasa a ido ba. Don Ina mai baki tabbacin baza ki taɓa yin da na sani a zaɓinsa ba. Ni kam ina cikin alkhairi dumu-dumu.”

“Ke ma kin san bazan taɓa iya ƙin zaɓin Abba ba. Na amince na ce mishi. Daga haka ya cigaba da min nasiha da saka albarka waɗanda sam ba na wani fahimtar me yake cewa. Domin Allah ya sani al’amarin maza ni gaba ɗaya tsoro suke ba ni.”

Ta ƙarasa maganar jikinta a sanyaye.

“Ke ba komai fa, Ki kwantar da hankalinki don Allah. Ba duka maza ne mugaye ba, kawai dai ki tsayar da zuciyarki guri ɗaya ki cigaba da addu’a, ni ma zan taya ki. In Allah ya yarda baza ki taɓa yin da na sani ba.”
Haka Nauwara ta sake ɗaukar lokaci tana yi mata nasiha da bata shawarwari masu kyau, daga bisani suka yi sallama.

Ko da suka yi sallama ta jima zaune a wajen, har sai da shayin da aka kai mata ya huce. Tana shirin tashi ta wuce wajen darasinta na gaba, ta ji saukar wata murya mai cike da kwarjini a kunnuwanta yai mata sallama kafin ta amsa kuma ya ja kujerar dake fuskantarta ya zauna.

Ta ɗaga kai da niyar ganin mai ƙarfin halin zama a inda take tun kafin ta amsa sallamarsa ko tayi mishi umarnin zama, amma wani ikon Allah idanunta na faɗawa cikin nashi sai ta ƙame ƙam kamar mutum-mutumi.

Kallo ɗaya ne tak tayi mishi, amma sai taji zuciyarta na wani irin luguden daka kamar wacce tayi arba da abinda ta jima tana bilayin nema. A zaune take, amma sai take ji kamar wani jiri-jiri na nema ya kifar da ita. Lokaci ɗaya wani sanyi-sanyi da ta rasa na menene ko kuma daga ina sanyin ke zuwa ya lulluɓe gaɓɓan jikinta gaba ɗaya. Daƙyar ta iya janye idanunta daga fuskarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa, haka kawai ta samu kanta da haɗe yatsun hannayenta guri ɗaya tana ɗan matsawa kamar wacce aka umarta.

A karo na biyu, ya sake buɗe bakinsa yayi mata sallama da muryarsa mai ɗauke da kwarjini irinna ƙasaitattun mazaje.

A sace, ta sake ɗago ƙwayoyin idanunta ta kalle shi a fakaice, ba za’a sanya shi a sahun maza masu masifaffen kyau ba, amma yana da wani irin cikar zati da kwarjini na musamman, ga wata irin kamala da take bayyana nutsuwarsa a fili. Da ganinshi irin matasan nan ne da ilimin boko da na Addini ya gama ratsa jinin jikinsu, a shekaru kuwa ko ya haura talatin to bazai wuce da biyu ba.

Ta rasa dalilin da yasa ko da ta buɗe baki da niyyar amsa mishi sallamar sai ta samu harshenta da lanƙwasa murya, amsawar tata sai ta fita a sanyaye kuma a tausashe.

Lallausan murmushi ya fara sakar mata, kafin ya buɗe baki kai tsaye ya fara kora mata cikakken bayanin wanene shi, ba tare da wani kwana-kwana ko ɓata lokacj ba.
“Sunana Doctor Nasir Muhammad Dabo. Kiyi hakuri da dirar kai tsaye da nayi a gabanki ba tare da neman izinin zuwa ba. Zuciyata ce… ta kasa cigaba da jumirin hakurin da ta ɗauki tsawon shekaru tana yi wajen dakon jiran lokacin da za ta samu tsayayyiyar dama a kanki. Allah dai yasa ban takura ki ba Manneee?”

Irin yadda ya yanke sunanta a gayance kuma ya kira ta da wani irin salo mai rikirkita zuciyar mai saurare ba ƙaramin tsuma ta yayi ba. A kunyace ta ƙara sunkuyar da kanta a ƙasa, kamar an sa supa glue an manne mata baki sam ta kasa amsa tambayarshi.

Lura da yanayin da ta shiga yasa shi ƙara sakar mata murmushi a karo na biyu, ya cigaba da cewa

“Ina roƙon alfarmar kafin ace min na takura, a taimaka a ɗan ba ni lokaci a fara fahimtar halaye da ɗabi’una. Daga nan ne za ki yanke ma kanki shawarar tafiyar za ta yiwu ko baza ta yiwu ba? Ni dai Allah ya sani na daɗe ina dakon matsananciyar ƙaunarki da soyayyarki a zuciyata. Ina kuma ganin lokaci yayi da zan ɗaukaka soyayyar zuwa mataki na gaba, daga ɓoyewa zuwa bayyanawa ga wacce zuciyata ke tsananin ƙauna da muradin kasancewa tare da ita ako wane lokaci, ko ya kika ce Manneee?”

Kalamai yake yi daki-daki, cike da nutsuwa da kamun kai. Ta kuma rasa dalilin da yasa, nutsuwar da yayi wajen furta kalamansa masu bayyana abinda ke zuciyarsa kai tsaye suka taka muhimmiyar rawa gurin samar mata da nutsuwa na musamman a tare da shi ko yaya?

A wannan karon, ta kasa ɗagowa ta kalle shi. Sai ta ɗauki wasu lokuta cikin shiru kamar baza ta amsa ba. Shi dai ya ƙure ta da kallo yana karantar yanayinta, a bazata, sai kawai ya ga ta saki wani ƙayataccen murmushi.

Bai san lokacin da wata nannauyar ajiyar zuciya ta ƙwace masa ba. Domin wannan murmushin da tayi kaɗai ya isa gamsar da shi a amincewar da yake nema a gurinta ya samu rabi, kuma yana da tabbacin rabin in sha Allah bazai gagara samuwa ba.

Har sannan idanunta na ƙasa, ta buɗe baki a tausashe ta fara magana ba tare da tana kallon fuskarsa ba.

“Bayan abinda ya faru da ni a baya sanadiyyar yaudaran saurayin da zuciyata ta gama amincewa da shi ɗari bisa ɗari. Na ɗaukarwa kaina alƙawarin duk sa’adda wani saurayin yazo min mijin aure zan riƙe shi ba saurayi ba… Don haka idan baka shirya ba don Allah kar ka nemi ɓata min lokaci domin ba ni da wannan lokacin…”

“Na shirya… Na rantse da Allah a shirye nake. Ko yanzu kika ce kina buƙatar a tura da komai da komai zuwa sati mai zuwa a ɗaura aure ni ba ni da matsala.”

Ya amsa da matsanancin murna a fuskarsa bakinsa na ɗan rawa-rawan da ke bayyana zumuɗin da zuciyarsa ke ciki. Bai jira cewarta ba ya ƙara da

“Kin san darare nawa na kwashe ina addu’ar Allah ya nuna min ranar da zan samu damar fuskantarki in bayyana miki asirin zuciyata kuwa?”

A wannan lokacin ma bata amsa ba. Domin har ga Allah kalaman soyayya daga bakin namiji ya daɗe da sanewa daga zuciyarta. Ta ji fiye da haka a bakin Muhsin, daga ƙarshe ta tsinci mummunan sakamakon da ko a mugun mafarki bata taɓa tsammani ba. Ita kam wane tsautsayi ko ganganci ne zai sa ta sake yarda da daɗin bakin maza?

Ko shi wannan likitan don ya biyo ta hannun Abbanta ne. Kuma daga yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata da yana da haiba da kwarjinin da ko babu soyayyarsa a zuciyarta za ta iya rayuwar aure da shi. Da wannan dalilin kuwa yasa bata ga abinda zai sa ta ɓatawa kanta lokaci wajen sauraran kalaman soyayyar da take da tabbacin kaso casa’in cikin ɗari cike suke da ƙare-rayi.

“Ka san abinda ya faru da ni a baya… A taƙaice ma kai ka gyara ɓarnar da wani ɗan’uwanka namiji yayi min…”

“Na kuma ɗauki hakan a matsayin mummunar ƙaddarar da babu bawan da ya isa ya tsallakewa. Sa’annan tunda ba mu muka halicci kanmu ba balle mu tsara ma kanmu abinda zai faru a rayuwarmu na farin ciki ko akasinsa, me zai sa mu dinga yawaita tunanin abinda ya wuce wanda ba mu muka ƙaddara faruwarsa a rayuwarmu ba?

Don Allah mu daina tunawa Manneee… Zan karɓe ki aduk yadda kike, zuciyata cike take da alfaharin samunki a matsayin mata zan kuma raine ki da soyayya maɗaukakiya in Allah ya yarda.”

Gamsuwa ta sake samu ɗari bisa ɗari daga amsoshinsa. A wannan karon, murmushin da take yi ba idanunta na kallon ƙasa bane. Cikin ido take kallonshi sannan ta sakar mishi ƙayataccen murmushin.

“Ya kuma bayanin iyali? Mata da ƴaƴanka nawa? Ka fahimce ni don Allah. Ba don komai yasa nayi maka wannan tambayar ba sai don mu samu cikakken fahimtar juna, domin ba na jin daga wannan lokacin za mu sake samun damar tattaunawa mai tsawo irin haka. Sati mai zuwa za mu fara jarabawa, bayan jarabawar kuma za mu samu hutun sati huɗu. idan komai ya tafi a yadda nake so a cikin wannan hutun zan wuce nigeria kuma bazan dawo ƙasar nan ba sai a matsayin matar auren wanda Allah ya zaɓa a matsayin mijin Mannirah…”

“In Allah ya yarda ni ne wannan mijin.”
Ya amsa yana murmushi da ƙwarin gwuiwa sosai a muryarsa.

“Ba ni da mata. Shekaru huɗu da suka gabata saura sati biyu a ɗaura aurena da ƴar’uwata Allah yayi mata rasuwa. Tun daga wancan lokacin nake ta ragaita har zuwa sadda Allah ya haɗa ni da ke na kuma ji farat zuciyata ta kamu da ƙaunarki. Shekaruna talatin da biyu ne a duniya, ƙiris ya rage in cike talatin da uku. Allah yasa dai ban miki tsufa ba?”

A tare suka yi musayar murmushi. Kafin ya cigaba da ba ta labarin duk wani abu da ya kamata ta sani a kanshi, iyayenshi, ƴan’uwanshi, aikinshi. Iyayenshi Haifaffun garin Kano amma aiki ya kai mahaifinshi kaduna sai kuma zama ya ɗore duk aka haife su a kaduna.

Sun ɗauki lokuta masu tsawo suna maganganu na fahimtar juna a tsakaninsu har bata fahimci tafiya mai tsawo da lokaci yayi ya barsu zaune a gurin ba.

Kwaɓe fuska tayi da yanayin shagwaɓa kamar za ta sa kuka lokacin da ta kalli agogo ta ga yayi tafiyar da har ana gab da gama darasin da za ta ɗauka na gaba.

“Ka gani ka sa na rasa darasin da zan saurara ko?”
Tayi maganar a shagwaɓe.

“Yi haƙuri… Allah ya huci zuciyar Gimbiyar Nasir. Ni fa a ganina bamu fi minti goma muna magana ba. Yanzu dai faɗa min, me zanyi in fanshi waɗannan tsadaddun lokutan da aka sadaukar musamman domin ni?”

“Kar ka ƙara zuwa ka cinye min lokacin karatuna.”
Ta amsa kai tsaye.

Idanun da ya bubbuɗe gaba ɗaya alamun maganar bata gamshe shi ba yasa ta ƙara mishi bayani da cewa
“Ka manta na faɗa maka za mu fara jarabawa sati mai zuwa? Ka ga ina buƙatar isasshen lokaci wajen karatu da bin komai a nutse. Na baka dukkan damar da kake buƙata. Zanyi magana da Abba in tabbatar mishi na amince maka, sauran aikin kuma ya rage naka. Ni dai don Allah ka bani lokaci kar in raba hankalina biyu a sadda nake matuƙar buƙatar nutsuwa…”

“To amma za muyi musayar lambar waya ko?”
Ya jefa mata tambayar da yanayin marairaita a fuskarsa.

“Don wannan kar ka damu.”
Ta amsa tana sake haske shi da murmushi.
“Amma duk sadda ka kira ban ɗauka ba don Allah kayi min uzuri. Yanayin karatunmu akwai buƙatar nutsuwa da mayar da hankali wajen bincike da karance-karance don ƙara faɗaɗa ilimi… Idan ka kira ban ɗauka ka turo min saƙon kar ta kwana ma ya isa.”

Haka nan ba don ranshi na so ba ya amince da tsarin nata. Don ya san tana da gaskiya, kuma ma shi da ta sauƙaƙa mishi irin wahalar da yake tunanin zai sha a farko kafin ya tunkaro ta ya kamata ya bata duk wata dama da take buƙata.

Zai daure, ya kuma ƙara jurewa, ya ƙara haƙurƙurtar da zuciyarsa har zuwa sa’adda za ta zama mallakinsa. Lokacin da karatu da binciken da take yi a hostel tana zaune a cinyarsa za ta dinga yi, idan yaga ta gaji ya ruƙunƙume abarsa yana shafa gashin kanta zuwa gadon bayanta har barci ya ɗauke ta.

Da murmushi a fuskokinsu suka rabu bayan musayar lambar waya, hatta ita da take jin bai wani samu shiga na musamman a zuciyarta ba sai da ta dinga ji kamar kar su rabu a daidai wannan lokacin.

<< Lokaci 65Lokaci 67 >>

2 thoughts on “Lokaci 66”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.