“Ziyada?”
Aunty Ruƙayya ta sake kiran sunanta a karo na uku da wani irin maɗaukakin mamaki a fuskarta.
“Wai da gaske ke ɗin ce kuwa?”
Ta sake jefa mata tambayar a mamakance tun kafin Ziyada ta amsa kiran da take mata.
A gaban Yayyen nata biyu, jin ta take kamar wata ƙaramar yarinya sa’ar Batula ɗiyarta.
Don haka kafin ta amsa sai ta tura baki gaba kaɗan, da yanayin shagwaɓa ta ce
“Kin ga dai Aunty ki bari… Ba na son irin wannan…”
“Uhmmm! E ai dole ki ce ba kya son irin wannan. Na ga dai bawan Allah nan ba irin wahalar da shi da bakiyi ba, babu irin rarrashi da kalaman ban haƙurin da bamu yi miki ba ni da Oga da Aunty Karima amma kika baɗawa idanunki toka kika ce sam! Bazai yiwu ba, sai yanzu kwatsam! Rana ɗaya, lokaci ɗaya kizo min da zancen kin amince? Don Allah me ya canja tunaninki cikin sauƙi haka? A yanzu kin shirya rabuwa da yaran naki kenan?”
“Hmmm!”
Ta faɗa a takaice da ɗan murmushi a fuskarta.
“Addu’a ne ya canja tunanina cikin sauƙi Aunty. Kuma yara dai na san ko ba daɗe ko ba jima tunda Abbansu na raye bazai taɓa bari in cigaba da riƙe su har zuwa aurensu ba.”
Tayi ɗan shiru kafin ta cigaba da cewa
“Ko da nake cewa ni da aure har abada na sani abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Duk ɗan sunnah bazai ƙi bin hanyar da aka bi wajen samar da shi ba. Bana fatan Allah ya ɗauki rayuwata ba tare da igiyar aure a kaina ba. Sati guda na kwashe ina addu’ar Istikhara kan Allah yayi min zaɓi na alkhairi tsakanin Barr Muhyi da Alh Hassan to a kullum lamarin Alhajin shi nake ji yana ƙara kwanciya a cikin zuciyata. Shi yasa kawai na yanke shawarar amincewa sai ku cigaba da taya mu addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairin da ke tsakanina da shi.”
“Amin! Amin! Amin ya rabb! Eh lallai sai yau na ƙara yarda Autar Ummanmu ta ƙara hankali. Wannan Albishir ne mai girma da na tabbatar zan samu gwaggwaɓar tukwuici a gurin Oga, don haka bazan yi sanya gurin isar masa da saƙon albishir ɗin ba.
Kin san irin shaƙuwa da amincin da yake tsakaninsa da Alh Hassan kuwa?”
Ta tambayi Ziyada tana daddanna wayarta da nufin kiran maigidanta. Bata jira amsawar Ziyada ba ta cigaba da cewa,
“Abokinsa ne na ƙud- da ƙud! irin abotar nan da ta haura zuwa matakin aminta da ƴan’uwantaka. Kin ji dai ana cewa ɗan Adam tara yake bai cika goma ba ko? To babban Yayanki ya sha ce min Alh Hassan ya cika sha biyu cif! Saboda tsananin yardar da yayi da shi…”
A daidai lokacin maigidanta ya ɗaga waya daga can ɓangaren, don haka sai ta yanke labarin da take ba Ziyada ta mayar da hankali kan wayar da take yi da mijinta.
Ita dai Ziyada bata tsaya sauraren kabbarbarin da taji Babban Yayan na yi daga can ɓangarenshi ba ta saɓe jikinta ta gudu ɗakinta ta kulle ƙofar. Domin ta san a ƙarshen wayar da wahala idan bai ce a bata yayi mata godiya ba, ita kuwa wani matsanancin kunyarsu take ji shi da abokin nasa da yake shirin zama mijin aurenta.
*****
“Da gaske kake yi Abbansu?”
Ta jefa mishi tambayar da mamaki a muryarta. Duk da ta san babu wasa a tsakaninsu amma samun labarin auren Mannira a irin wannan lokacin abu ne da bata taɓa tsammani ba.
‘Bayan tabbatuwar komai na maganar aure tsakaninta da Alhaji Hassan har an yanke ranar ɗaurin auren sati uku masu zuwa. Yana da gidaje a Kano, Kaduna, Abuja da Lagos. A ciki ya bata damar zaɓin inda take so ta zauna, matarsa ɗaya da yaransa huɗu a Lagos suke zaune don harkokinsa sun fi ƙarfi anan. Don haka ta zaɓi Abuja, domin bayan Lagos inda yafi gudanar da harkokinsa Abuja ne.
Da wannan dalilin yasa ta yanke shawarar kiran Abba Yusuf domin sanar da shi halin da ake ciki tun kafin ya tsinci labarin aurenta a gari. Tun lokacin bikin Nauwara ya faɗa mata cewa zai bar su Batula a gurinta ne kaɗai zuwa sadda ita ma za tayi aure, a wancan lokacin, a wauta irin nata har tana ganin ashe babu ranar rabuwarta da ƴaƴanta, domin ita da sake aure har abada.
Sai kuma ga shi cikin hukuncin Allah zancen auren nata ya taso ko shekaru uku ba’ayi da yin wancan maganar ba.’
Tana lalubo lambarsa za ta danna kira sai ga kiranshi ya shigo cikin wayarta, haka kawai ba ya kiranta sai da dalili. Don haka ko da ta ɗauki wayar sai bata katse mishi hanzari ba ta hanyar faɗa mishi ita ma kiranshi take niyyar yi, bayan gaisuwa saurarawa tayi ya gama faɗa mata dalilin da yasa ya kira ta wanda labarin auren Mannira ne da ya taso gadan-gadan.
Da ɗan murmushi a fuskarsa kamar tana gabansa ya amsa da
“Ƙwarai kuwa. Kin yi mamaki ko?”
“Eh to ai abin mamakin ne Yaya. Ko da yake ba’a mamaki da ikon Allah. A ina ta samu mijin?”
Ta sake tambaya da yanayin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a muryarta.
“Likita ne… iyayensa da kowa nasa suna nan Kaduna amma asalinsu ƴan jihar Kano ne.”
“Ma sha Allah! Allah yasa mahaɗin arzikinta ne.”
“Amin ya rabb”
Ya amsa a tausashe.
“Amma Yaya ina fatan dai ka faɗa ma shi yaron mummunar ƙaddarar da ya taɓa afka mata?”
Ta tambaye shi tana jin wani irin faɗuwar gaba na musamman.
Daga can ɓangarensa, ɗan shiru yayi kamar bazai amsa ba. Can kuma sai ya ce
“Ziyada? Wai mene ne hikimar ki ta nacewa da maganar a faɗawa duk wanda ya fito da niyyar auren yarannan ƙaddarar da ta afka musu? Kar fa ki manta… Yanzu muna cikin wani zamani ne da mafi yawancin maza basu ɗauki budurcin matar da za su aura da wani muhimmanci ba…”
“A’a Yaya.!”
Ta katse shi da sauri. Kafin ya amsa ta cigaba da cewa,
“Ba abinda ke faruwa a zamanance za mu duba ba. Addininmu shi ne gaba da komai, ko a addinance, yana kyau iyaye su sanar ma da yaron da zai auri ƴarsu duk wani naƙasu da yarinyar take da shi don gudun yin kitso da ƙwarƙwata. Ka ga ko da daga baya ya tarar da abinda bai tsammata ba bazai ce an zalunce shi ba, wannan shi ne kaɗai dalilina Yaya, don Allah ka fahimce ni.”
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga can ɓangarensa. Ya fahimce ta ƙwarai, kuma ya san ta fi shi gaskiya. Da a ɗaura auren a sakar mishi yarinya don an same ta ba yadda ake tsammani ba gara tun farko ace ba’a ma ɗaura auren ba. Allah zai kawo mai iya aurenta aduk yadda take. Amma a al’amarin Mannirah Allah ya kawo musu komai a sauƙaƙe, shi ne likitan da yayi mata aiki lokacin da ƙaddarar ta faɗa mata. Don haka ba buƙatar a sake sanar da shi, amma duk da haka dai zai sake tuntuɓarsa da maganar.
“Ki kwantar da hankalinki Ziyada. Na fahimce ki ƙwarai.”
A taƙaice ya kora mata bayanin wanda zai auri Mannirah ya san duk wani abu da ya taɓa faruwa da ita.
“To Alhamdulillah! Allah yasa albarka a taraiyarsu.”
Da farin ciki ya amsa addu’ar na ta. Sannan ya ƙara da sanar da ita lokacin da ya tsara na gudanar da ɗaurin aure da shagalin bikin, idan Mannirah ta samu hutu ta shigo Nigeria, a lokacin bai fi saura sati biyar ba.
Addu’ar dai ta sake yi da fatan alkhairi. Har za tayi shiru ba tare da ta faɗa mishi maganar aurenta ba sai kuma taga shirun bai da amfani, mene ne abin ɓoye abinda ba fasawa za’ayi ba?
A kunyace, ta faɗa mishi maganar na ta auren da za’a ɗaura shi kafin na Mannirah, sai ta ƙara mishi da cewa,
“Amma in Allah ya yarda za’a bar batun tarewa har zuwa bayan bikin Mannirah…”
“Ai ba buƙatar haka ma Ziyada.”
Ya katse ta jikinsa a sanyaye sosai saboda tunanin Khamis da ya karaɗe ilahirin zuciyarsa lokaci ɗaya da jin maganar auren da Ziyada za ta sake yi.
Tun bayan kwaranyewar zaman makokin Khamis wasu daga cikin ƴan’uwansu da abokan arziki suka yi ta ba shi shawarar ya nemi auren Ziyada ko don su haɗa kan ƴaƴan Khamis waje ɗaya. A gurinshi wannan ba komai bane face cin amana duk da kuwa babu haramci a addinance.
Da sauri yake kore zancen, a ganinsa da wani ido zai kalli Khamis su haɗu ranar lahira Ziyada da yake matuƙar so shi shaƙiƙin ɗan’uwansa ya aure masa ita?
‘Ko da ni da Ziyada kaɗai za mu rage a duniya bazan iya aurenta ba.’
Da wannan amsar yake kashe bakin kowa.
To gashi dai yau ƙarshen tika-tiki ita Ziyadar da kanta take mishi zancen za ta auri wani, har ma saura sati uku ɗaurin auren. Kenan za ta tashi ranar lahira ba’a matsayin matar Khamis ba kenan? Nan da nan idanunsa suka kaɗa suka yi ja, muryarsa ta cushe sosai kamar wanda yayi mummunan shaƙewa da abinci.
“Kayi haƙuri Yaya. Allah ya gafarta ma Khamis.
Ta faɗa a tausashe kamar ta san tunanin da yake yi.
Duk da haka, ya kasa ce mata komai a karon farko, ya kuma kasa amsa kyakkyawar addu’ar da tayi ma ƙaninsa. Sau huɗu yana buɗe baki da nufin yin magana sai ya kasa, sai da yai ta jan addu’o’i a cikin zuciyarsa kafin da ƙyar ya iya cewa,
“Me kika shiryawa rayuwar su Batula?”
Ya tambayeta duk da ya san sun daɗe da yin maganar idan za tayi aure zai amshi yaran ɗan’uwansa.
“Na san dai baza’a barni in tafi da su agolanci wani gida ba duk da shi da kansa yayi min tayin zai riƙe su. Amma idan za’a bar su nan hannun Aunty Ruƙayya zan ji daɗi, sai su cigaba da karatunsu a nutse ba tare da samun matsala ba…”
“Bazai yiwu ba.”
Ya katse ta aɗan fusace.
“Gidan Ubansu za su dawo kamar yadda su Mannirah suka zauna anan, ki shirya musu dawowa Kaduna gaba ɗaya nan da kwanaki bakwai.”
Ƙit! Ya katse wayar ba tare da ya saurari ko za ta sake cewa wani abu ba.
Sagalau tayi da baki tana kallon wayar kamar mai kallon fuskar Yaya Yusuf ɗin a ciki.
Lokaci ɗaya itama jikinta yayi sanyi, ɗan murnar da take yi na samun mijin auren da Mannirah tayi nan take ya bi rariya.
Ta daɗe cikin shiru tana tunane-tunanen da ta rasa inda suka nufa. Sai kuma ta aje wayar a gefen gado, ta fice daga ɗakin zuwa gurin ƴar’uwarta don ta faɗa mata yadda suka yi da Abban Yara, kamar yadda suke kiranshi.
“Ƙyale shi. Kar ki wani damu kanki, ɗan’uwansa yake tayawa kishi. In banda abin Abban yara ya muka iya da abinda tun kafin a haifo mu aka rubuta zai faru a cikin rayuwarmu?”
Maganganun da Aunty Ruƙayya tayi mata kenan bayan ta gama ba ta labarin yadda suka rabu a waya.
Maganganun da suka ɗan kwantar mata da hankali, har tayi ƙoƙarin watsar da tunanin komai ta mayar da hankali wajen kama ma Auntyn girkin da take yi suna hirar yadda bikin Mannirah zai kasance.
Ko da ta koma ɗaki kuma ta ɗauki wayarta sai taga ya sake kiranta har sau biyu, da saƙunan ban haƙuri guda biyu ɗauke da kalaman ban haƙuri na yadda ya amsa mata maganar aurenta. Kuma Kamar yadda Aunty Ruƙayya ta faɗa, bai ɓoye a cikin saƙonnin ba cewa yana taya ɗan’uwansa jin babu daɗi ne.
Amma yana mata fatan alkhairi da addu’ar Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi. Sai saƙon banki na naira dubu ɗari da Abban ya tura mata a cewarsa ga gudummuwa nan ta sayi tsintsiya.
Ɗan murmushi tayi tana ƙara jin nutsuwa a ranta sannan ta tura mishi da saƙon godiya da addu’ar Allah ya ƙara girma. Ta kuma sake tabbatar mishi in Allah ya yarda kamar yadda ya ce, za ta harhaɗa komai na sauran yaran da suke gurinta za ta karɓi takardar transfer a makarantarsu zuwa sati mai zuwa in Allah ya yarda ita da kanta za ta kai mishi su.
*****
Tun bayan rasuwar Khamis da sati ɗaya, kafin Ziyada da ƴan’uwanta na kusa su bar gidan Yaya Yusuf ya kira malamai suka raba gadon Khamis kamar yadda addininmu yayi umarni.
Ziyada ba ta da gadonsa, don tuni ta gama iddar aurensa. Ƴaƴansa su ne masu gado tunda uwa da ubansa duk sun rasu. Sai aka yi arashi kuma da Ziyada da Yaya Yusuf shawararsu tazo ɗaya na cewa a sadakar da kaso mafiyawa daga cikin dukiyar, tunda dai duk sun san ba ta hanyar halas ya tara dukiyar ba.
Duk da dai garin banza a farau-farau ɗin banza yake ƙarewa. Kuɗaɗe ne da ake samunsu ta hanyar haramun, ko kaɗan ba su da albarka. Bai mutu ya bar wani abin azo a gani ba, daga gida, sai mota, sai kuɗaɗen da basu taka kara sun karya ba a cikin asusun bankunan da yake ajiyar kuɗi guda uku.
Cikin ƙanƙanin lokaci Yaya Yusuf yasa aka binciko mishi unguwar da suke fama da matsananciyar rashin ruwa ya bada kwangilar yi musu bohole aka zuba kawunan famfo har huɗu, da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Khamis.
Gida da motar duk saidawa aka yi, aka bi hanyoyin da suka dace wajen sadaukar da kuɗaɗen a aikin masallaci da makarantun islamiyyu. Duk da nufin su kasance sadaƙatul jariya ga marigayin.
“In Allah ya yarda, nauyin ƴaƴan da Khamis ya bari bazai gagareni ɗauka ba.”
Cewar Abba Yusuf cikin ƙwallah da faffaɗar damuwa damalmale da fuskarsa.
Yanayin yadda jinyar Khamis ta kasance har zuwa mutuwarsa ya ƙi barin zuciyarsa, wai ma fa tun a duniya kenan? Ina kuma ga in an je lahira? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!! Irin tsoron da ya dinga jiye ma Khamis kenan ya matsa mishi da nasihar ya tuba, ya daina aikata miyagun laifukan da yake yi tun kafin lokaci ya ƙure masa, domin gaba ɗaya rayuwar bawa ba’a hannunsa take ba. Amma da yake Khamis ɗin rabonsa ƙalilan ne bai tuba ba sai da Lokaci ya ƙure masa, ko ga yadda suka dinga biya mishi kalmar shahada ya gagara amsawa shi yasan bayan tiya akwai wata caca. Allah dai ya jiƙan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya, idan ta mu ta zo Allah yasa mu cika da imani.
****
Kamar yadda Ziyada tayi alƙawari, kwanaki tara a tsakanin maganarta da Abba Yusuf ta gama harhaɗa duk wasu kayayyaki na yaran suka kama hanyar zuwa Kaduna.
Kwanaki biyu tayi a daddafe ta wuce Kano wajen Aunty Kareema da ta matsa mata dolen-dole ko tana so ko bata so sai ta je anyi mata gyaran jiki kamar yadda ake yi ma ko wace Amarya.
Duk yadda taso zille ma al’amarin gyaran jikin ya gagara, don itama Aunty Ruƙayya ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari, har da ƙarin gudummuwar maƙudan kuɗaɗe ta tura ma Aunty Kareema tana sake jaddada lallai ayi ma Ziyada gyaran da idan Alh Hassan ya ganta bazai gane ta ba, idan kuwa ya shiga gonarta zai iya rantsewa da Allah budurwa ce ya ɓare a leda ba wacce ta zazzage ƴaƴaye har biyar ba.
A kunyace ta rufe fuskarta tana ɗan murmushi, sai kuma can ta buɗe fuska tana tura baki ta ce ma yayyin nata.
“Ni dai Aunty Kareema da kun ƙyale ni…”
“Ai wallahi baki isa ba. Gyara ne za’a yi miki mai sunan gyara wanda ko yarinyar mace albarka. Kin san irin kuɗaɗen da na zubewa Hajiya Futuha kuwa? Ai gyaran da aka yi ma Nauwara nafila ne akan wanda za’a miki, domin yanzu an samu ƙarin kayayyaki na musamman daga ƙasashe daban-daban. Ana gama naki gyaran takanas-ta kano zan je in taho da Mannira ita ma a sulle min ita. Ba’a bori da sanyin jiki yarinya…”
******
Komai yayi farko zaiyi ƙarshe… haka zalika ba’a bori da sanyin jiki. Kwanan Ziyada goma a Kano suka wuce Kaduna ita da Aunty Karima. Da wani irin canji na musamman ta ko wane ɓangare a jikinta wanda ita da kanta duk kushewar da take ma gyaran ba ƙaramin daɗin jikinta take ji a yanzu ba. Ta canja gaba ɗaya ɗari bisa ɗari, kamar yadda yayyenta suka sha alwashi, gyara ne aka yi mata na musamman aka yi ƙara’i har da na lokacin auren farkonta da ba’ayi ba.
Sun sakarwa Hajiya Futuha maƙudan kuɗaɗe ita kuma ta baje ƙololuwar basira gurin cancaɗe musu ƙanwarsu kamar wacce za ta auri Sarkin Sa’udiyya.
A can Kaduna suka haɗe da Aunty Ruƙayya. Ko da ganin Ziyada haɓa kawai ta riƙe tana kakabi da mamaki ganin irin canjawar da tayi a cikin kwanaki ƙalilan.
Minti ɗaya biyu sai ta shafa gefen fuskar Ziyada da lallausan murmushi a fuskarta ta ce
“Fatabarakallahu Ahsanul Khaliƙeen. Wallahi Auta kinyi kyau ƙwarai da gaske, yadda kika san an zabge shekaru ashirin a cikin shekarunki.”
Duk da basu yi wani gayyata na azo a gani ba, Ƴan’uwa da abokan arziki dan-ƙam suka cika gidan ranar ɗaurin auren Ziyada da Alhaji Hassan. An ci, an sha, anyi hani’an. Sannan aka rarraba kyaututtukan na musamman ga duk waɗanda suka halarci bikin ɗaukar nauyin Babban Yaya.
Washe gari aka ɗauki Amarya da tawagarta a jirgi zuwa tamfatsetsen gidan mijinta da ke Abuja. Da alƙawarin tun ana saura kwanaki huɗu bikin Mannira za ta dira a Kaduna ayi komai da ita.
Sati uku tsakanin auren Ziyada aka ɗaura auren Mannira da Angonta. Alhamdulillah! Ƙayataccen bikin da ya bar ɗinbin tarihi saboda manyan malaman da suka samu halartar ɗaurin auren.
Idan baku manta ba, Mannirah gangaran ɗin mahaddaciyar Alƙur’ani ce da ta halarci musabaƙa da dama, don ma dai soyayya da ta saka a zuciyarta a wancan lokacin yasa ta nemi komawa baya. Malamanta na tsananin alfahari da ita, su suka yi gayyata na musamman, sannan suka haɗa mata gagarumin walima da ya samu halartar manyan malamai mata da ake ji da su a faɗin ƙasar nan.
A wannan rana, Abba Yusuf tun yana dariyar farin ciki da alfahari bai san lokacin da ya shige ɗakinsa ya fashe da kuka.
“Allah ya gafarta maka Khamis. Lallai daga cikin mutacce ake fitar da rayayye. Ina ma kana raye ka ga duk irin miyagun abubuwan da ka aikata a cikin ƴaƴan da ka haifa an samu yarinyar da Addinin musulunci da Manyan malaman musulunci ke alfahari da ita? Allah ya gafarta maka Khamis”
Cikin kuka yake wannan maganar yana fyace majina kamar ƙaramin yaro.
*****
Tammat bi hamdulillah! Duka anan na kawo ƙarshen wannan labari nawa mai suna LOKACI. Ina roƙon Allah ya yafe min kura-kuran da suke ciki, faɗakarwar da ke cikin labarin kuma Allah yasa mu amfana. Allah ya shirye mu ya bamu ikon tuba tun kafin LOKACI ya ƙure mana.
Jinjina da godiya ta musamman ga BAKANDAMIYA Hikaya da duk ahalinta, ina addu’ar Allah ya ƙara ɗaukaka BAKANDAMIYA. Jinjinar ban girma ga gwanata LUBNAH SUFYAN.
Sai mun haɗu a wani sabon labari nawa mai suna… BAYAN TIYA, AKWAI WATA CACA!!
©FAREEDA ABDALLAH
Godiya me yawa