Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Lullubin Biri by Halima Zakariyya

April 20th, 2021

American Hospital, Dubai; 2:30pm

“hey don’t move, we are us navy seals…God! Damn it…we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!…great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one.”

sautin dake fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin dake manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf dake juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. “ohh dammm it!”

“ai na faɗa maka sai sun kama shi”. Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa’ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru.

Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,”ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba”.

“hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne…kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai”.

“kuma wataƙila ya suɓuce masu ba”.
“ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa”.

“wannan ai ba mace ba ce”.
“bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba”.

shirun Kalid ɗin ya haɗe da sanda sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon.

“get the mask!!…there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe’s breath.”_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba.

lokacin da Yusuf ya buɗi baki zaiyi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma’aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali.

cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. “Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu”. ta faɗa sanda ta ke harɗe hannayenta zuwa baya.

“ta farka ne?”. Yusuf ɗin ya tambaya a sa’ilin da yake buɗe fayel ɗin yana dubawa.

“ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta”.

shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin daya manna na bin rubutun dake cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa 1,2 Yusuf ya ɗago kansa akan fayel ɗin, ya kai hannu ya shafo goshinsa sannan ya jinginar da kansa jikin kujera yana mai sauke gajeran numfashi.

“huuuuhh”._ hucin iska ta fita daga bakinsa. *”EXOGENOUS DEPRESSION”.* ya faɗa cikin amon sauti na tausayawa haɗe da kulle murfin idonsa. furucin nasa kuma yasa Kalid maido da kallonsa gare shi.

“tana cikin matakin biopolar kenan?”.

Yusuf ya jijjiga kansa tabbacin hakan ba tare daya ce komai ba, na tsawon wasu sakanni ya ɗaga ido ya kalli Nurse ɗin yace,”kuma iyaka binciken da jami’an tsaro suka yi babu wani danginta a ƙasar nan?”.

“ƙwarai ranka ya daɗe sun bada tabbacin hakan…ni kaina lamarinta na ɗaure min kai”.

Kalid yace,”gaskiya da sake a wannan lamarin, su ƙara bincike domin idan ba zaman ƙasar nan take ba to waya kawota ya ajiyeta kuma ya tafi ya barta cikin wannan mawuyacin yanayin?”.

Yusuf ya ƙara fitar da iska daga bakinsa kamin yace da nurse din,”Ƙarƙashin kulawar wa ta ke?”.
“Ranka ya daɗe tana ƙarƙashin kulawar Dr Nameer, sai dai gaskiya tana fuskantar matsala”.

“wanne irin matsala?”.
“Dr Nameer yana da zafi, so kuma shi yace muddin babu wani nata ba zai bata wani kulawan daya dace ba…infact yanzu ma yaƙi rubuta alluran da suka kamata ayi mata saboda wai ko ya rubuta bata da me saya mata”.

karo na babu adadi Yusuf ya ƙara girgiza kansa tausayi fal ransa, sannan ya ɗauki ƙaramar takarda yay signing a jiki ya miƙa mata tare da fayel ɗin.

“kije Pharmacy Sumayya, ayi dukkan abinda ya dace akan matar nan, zan saka maki kuɗi a account, dan Allah ki kula da ita ni kuma nayi miki alƙawarin biyanki da kauri”.

ta rissina ta ɗauki fayel ɗin tana yi mishi godiya sannan tai musu sallama ta fice daga ofishin.
bayan fitarta da wucewar minti uku Yusuf ya miƙe yana kafa hular zanna bukar a gashin kansa, fuskarsa na bayyana ainihin damuwar dake cikin ransa.

“tashi mu tafi Kalid”.
“a’a ba kana da sauran aiki ba?”.
“ba zan iya komai ba Kalid, kaina ciwo yake. zan yiwa Dr Yusrah magana”.

Kalid ya miƙe tsaye shima, suka nufi ƙofa yana cewa da Yusuf. “Dr ka rage saka damuwar wani a ranka…”. kuma bai ƙarasa maganar ba Yusuf ya tari nunfashinsa da cewa.

“Kalid idan har matar nan tana da miji a raye to ya cika azzalumi, idan ma yana raye ne ko ya mutu to tabbas ƴaƴanta salwantattu ne, basa neman albarka kwata-kwata, basu san darajar uwa ba, domin ko kaffara ba zanyi maka ba ta dalilinsu ta shiga wannan bala’in rayuwar, kuma duk sanda nai tozali da wani ɗa nata sai nayi shari’a da shi”. maganar yake cikin zafi rai kamar zai kaiwa bango duka.

“tabbas ba zai wuce takaicin miji ko na ƴaƴanta ne ya zama silar wannan ciwon nata ba…amma ni abun mamakin ace tana cikin wannan mawuyacin halin kuma babu kowa nata a tare da ita”.

Kalid yay maganar a sanda suke sauka daga kan steps suna ƙarasowa cikin reception kamin su sa kai su fita gaba ɗaya daga asibitin. kuma har suka isa bakin mota cikinsu babu wanda ya sake magana.

on their way to hotel wayar Yusuf tayi ƙara, ya kai hannu ya cirota daga aljuhunsa, ya ɗaga vedio call ɗin daya shigo yana mai raba hankalinsa gida biyu, ɗaya ga tuƙin da yake, ɗaya kuma ga fuskar matarsa da ta bayyana a cikin wayar.

“You Excellency what am i seeing on your face?, whats wrong?, are you oak?, wani abu ya faru ne?, what is the problem?”. tarin tambayoyin da suka fito daga bakin Nuratu kenan zuwa ga mijinta, cikin kiɗima da bayyanuwar tashin hankali na farat ɗaya, dalilin damuwar da ta gani a tare da shi ta haddasa ma ta ruɗewa na neman fitar hayyaci.

kallo ɗaya na yanayin da take ciki zaka yi kasan macece dake tsananin so da ƙaunar mijinta, gami da tausayinsa, wanda bata so ko da ƙuda ɗaya ya taɓa mata shi, kan kace kwabo hawaye sun fara reto akan kuncinta, cikin ƙanƙanen lokaci kuma ta fashe da kuka, kukan daya haddasa wani duka a ƙirjin Yusuf.

“Sweety”. sai a yanzu laɓɓansa suka buɗe da kiran sunanta, ta ɗago kanta da ta duƙar tana kuka ta zuba idonta cikin nasa. sai kawai ya sakar ma ta wani kyakykyawan murmushi, irin murmushin nan da zai tsayar da kukan nata. amma me? kamar yanda ya riga ya sani ba zata yi shirun ba, hasalima kamar ma ya ƙara tunzurata ne, dan kawai ɗora hannu tai akan fuskar ta ƙara fashewa da kuka, kuka sosai kamar ƙaramin yaro me neman shan nono, sautin muryarta na fita cikin kuka na shagwaɓa da damuwa take ƙara cewa.

“ni ba irin wannan ba, bana son wannan ka jefar da shi. indai murmushin ƙarfin hali ne a tare da kai your Excellency bana ƙaunarsa, kuma ba shi zai sa na sami sassaucin raɗaɗin damuwar dana riska a tare da kai ba”.

tuƙin yake amma gaba ɗaya attension ɗinsa ya koma gareta, kyawawan idanuwanta na kan wuyansa tana bin wani dunƙulallan abu dake wucewa ta maƙogoronsa, muryarta ta ƙara narkewa tana cewa.

“please tell me what is the problem?, Did you do something that you did not succeed on it?”.

ta riga ta san waye mijinta, yawancin damuwarsa na ta’allaƙa ne akan rashin cimma nasararsa akan abu musamman ma ta ɓangaren aikinsa, amma da mamakinta sai taji yace,”keep calm Sweety”. voice ɗinsa ya fito very cool.

sai ta gwaɓe kamar ƙaramar yarinya tana cewa da shi. “to ni dai ka dawo gida idan Allah ya kaimu gobe. ka bar komai da kake yi ka dawo, otherwise i will keep crying”.

“Sweety isn’t a big deal faa, please don’t bother your self kinji”.
“ni ban yarda da kai ba”.

sai kawai ya tsarate da wani kallo daya sa ta saki wani murmushi daya fito da annurin fuskarta, sannan kamar sai a yanzu ne ma ya lura da irin shigar dake jikinta wanda yasan ta kira ne dan ta nuna masa, dan haka ya kanne mata ido guda ita kuma sai ta cije gefen leɓenta kaɗan.

kuma gaba ɗayansu sai murmushinsu mai ƙarfin sauti ya fito a tare. wucewar daƙiƙa 2 suna aikawa junansu saƙo ta irin kallon da suke ma juna kamin Nuratu ta ɗan cukule fuska tace da shi.

“this time around idan ka dawo sai nayi shari’a da Kalid”.

yanda tayi maganar da gaskiyarta yasa shi yin murmushin daya bayyanar da haƙoransa, Kalid dake gefe yana charting ya saki dariya yana faɗin. “yi haƙuri Madam tuba nake”.

“i will not accept your apology tunda kai dai har yanzu ka kasa koyon yanda zaka kula da amanar da aka baka”.

“wani abu ya faru ranki ya daɗe?”. ya tambayeta cike da zolaya da kuma son ƙara kunnata.

“au kana ma tambayana ne me ya faru ko?, Allah dai ya dawo daku lafiya zaka min bayani daki-daki. lawyer nake, kasan abunda zan aikata da wanda ba zan aikata ba”.

No 3. Shongo Housing Estate, Gombe State

17:00 pm

gidaje guda 5 ne aduk girman estate ɗin, kuma a kallo ɗaya zaka yiwa gida me lamba na uku ka gane ba ɗaya yake da sauran gidajen ba, tun daga girmansa zuwa tsaruwar ginin da yanda aka fitar da fasalinsa. anyi tsarin ginin gidan da ado da kwalliya irin na gidan sarauta, idan har ba sani kayi ba zaka tsammaci wata babbar masarauta ce. duk jikin bango da zaka kalla birjik yake da ado na ƙawa cikin nau’i iri-iri don burge idon me kallo.

daga cikin gidan, second part dake kallanka a yayinda daka shigo cikin haraban gidan, acikin tamfatsetsen parlon na alfarma wanda yake shaƙe da kayan alatu na more rayuwa, me ɗauke da royal italian cushion.
sautin waƙa ne ke tashi acikin wata mp3 dake manne ajikin wani glass kamar drower.

Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday, happy birthday to you.

waƙar dake fitowa kenan acikin sautin kiɗan, yayin da ƴan mata da yaran dake kewaye da shi ke tafi da hannayensu cikin murna da annashuwa, suma suna bin sautin waƙar fararan haƙoransu duk a waje.
yana tsaye ne a gaban ƙaton cake ɗin da akai masa kwalliya da tsari me kyau an saka +1 ajiki, ga candle guda ɗaya a kunne a saman cake ɗin.

irin yanda fuskarsa ke washewa da murmushi ba zaka taɓa ganewa hakan ba a kallo 1 zuwa biyu da zaka yi masa. lokacin da sisters ɗin nasa suka gama bin waƙar sai ya sunkuyo da kansa yayi blowing wutan candle ɗin sannan ya ɗago yayin da idanuwansa ke a lumshe yana yiwa kansa adu’a acikin ransa, for few seconds ya buɗe yana sauke ganinsa akan ɗaya daga cikin sisters ɗin nasa wadda duk ta fi sauran matan haske da kuma dogon hanci.

kyakykyawan murmushi suka sakarma junansu lokaci ɗaya. da ido yay mata alama ba tare da yay magana da baki ba, hakan yasa ta matso kusa ta riƙe hannunsa ya yanka cake ɗin, laɓɓansa na talewa da murmushi mai faɗi. ya yanko cake ɗin yana juyowa ga hannun damansa inda wata farar dattijuwa kyakykyawa ke tsaye sai murmushi ta ke, haƙoranta sunƙi rufuwa saboda irin farin cikin da take ciki, jikinta sanye da tsadadden less brown and black colour, tasha ɗauri kace budurwa me ji da tashen ƴan matanci.

bakinta ya nufa da cake ɗin daya yanko ya saka mata, ta karɓa tana faɗin. “Happy birthday Son. wish you long life and prosperity”.

“Use miyyete Mama, midon nana beldum joddaki emada eder duniyaru am”. (Amin na gode Maama, ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata).

ya faɗa yana yanko wani cake ɗin, sai daya kalla duka sisters ɗin nasa su huɗu sannan ya sauke kallon ƙarshen nasa akan Zaituna, kallon da yay mata ne kawai ya fahimtar da ita mai yake nufi, dan haka ta matso kusa da Maama, ta buɗe baki itama ya saka mata cake ɗin a baki, ta karɓa tana faɗin.

“Mi seyake be yaltugo nyandere danyeki ma Hamma am. Allah ɓeddane njamu be jutal balde barkante jo”. (Barka da zagayowar ranar haihuwarka Yayana. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana masu albarka.)

fuskarsa ta ƙara washewa da annuri, ƙwayar idonsa na haskawa da wani ƙyalli na farin ciki. sai ya dangwalo icing cake ɗin ya lakuta mata a hancinta da gefen kumatunta kamar itace birthday girl ɗin, yana faɗin. “Special thanks to you Sweetest”.

daga nan kuma ya dinga yankar cake ɗin yana sakawa sauran sisters ɗin nasa a baki, suma duk suna binsa da wishing. haka ya gama basu sannan suma kowacce ta yanko ta nufo bakinsa da shi, sai dai bai karɓi na kowa ba sai daya fara amsar na Maama da Zaitoon tukunna.

suna haka Kalil ya shigo aka ɗora da shi, gaba ɗaya shi sai ya koma ma kamar shine me birthday ɗin, dan gaban cake ɗin ya zauna yana ta ci. kuma zuwansa wurin sai yau sauya ƙaramin birthday partyn da Maama ta haɗa zuwa babba. cike da murna gami da so da qauna for one another suke ta abinsu, kowa jikinsa ya ɓaci da cream na jikin cake.

Ɓangaren Masu Aiki

17:40 pm

“Fillo karki zauna dan Allah”. wata ƴar tsohuwa fara ƙal dake zaune a gefen katifa tana cura fura ta faɗa. “Kaka am debbo ba zan jima fa yanzu zan dawo”. ta faɗa tana zura hijab kalar c-green wanda ya ɗauki farar fuskarta matuƙa.

ta zura siririyar ƙafarta cikin takalmi sannan ta nufi ƙofa tana faɗin,”sai na dawo Kaka”. Can bayan gidan ta nufa, kasancewar yamma tayi hayaniya ta ɗan ɗauke ba kamar da safe ko rana ba, mafi akasari a irin wannan lokaci masu hidimar gidan sun tafi don hutawa kasantuwar ayyukan da suke sha tun sanyin safiya.

da yake gate ɗin gidan biyu ne, kuma gate ɗin baya ta nan ma’aikatan gida ke shige da ficensu, shi kuwa main gate na masu gidan ne. a bakin bishiyar da Amir ya saba tsayuwa duk sanda yazo anan ta same shi yanzuma, ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya jingina da jikin bishiyan yana jiran isowarta. tun daga nesa daya hangota ya kafeta da ido, kuma kamar kullum sai Fillo ta tsaya da tafiya tana ɗan turo baki gaba.

ganin hakan yasa Amir ɗauke idonsa daga gareta yana fitar da siririyar dariya a fuskarsa. sannan yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa. bai san da ƙarasowarta wajen ba sai jin maganarta yay acikin kunnensa tace.

“ja66ama”. (barka da zuwa) tai maganar a hankali.

sai a yanzu ya buɗe fuskar ya juyo da fuskarsa zuwa gefen damansa inda ta ke a tsaye, bai ce mata komai ba sai wani sanyayyan murmushi daya ɓalle masa a saman fuska. irin kallon da yake mata yasa taji nauyi ta rufe fuskarta tana ƙara faɗin.

“awari jam?”. (anzo lafiya?) nan ma shiru yay bai amsa mata ba, itama kuma bata jira ƙara cewarsa ba ta kuma ɗorawa da faɗin. “noi him6e sare?”. (ya mutanen gidan?)

Amir ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da jan leɓensa na ƙasa zuwa cikin bakinsa ya tsotsa kaɗan. a shagwaɓe  tace,”wai yau ba za’a min magana bane?”. har yanzu murmushin dake kan fuskarsa bai ɗauke ba yace,”mi tawi on jam?” (na sameki lafiya?)

“lafiya lau”. ta faɗi hakan tana ƙara yin ƙasa da fuskarta da alamar dai macece ita mai kunya sose.

“Inna vi mi hofnuma”. (Inna tana gaisheki)
“mi ja6i”. (ina amsawa)

“shine kika barni na daɗe a tsaye haka ko?”.

ta ɗan cije leɓenta kaɗan tana kallonsa sannan tace,”kayi haƙuri. na tsaya ƙarasa aiki ne, kasan me Martaba baya nan, to kuma duk sanda zai dawo Kaka ake bawa aikin fura, shi ne yau bamu gama da wuri ba sai yanzu. yanzu haka ma na taho na barta tana ƙarasa curawa ita ɗaya. da ta gama zamu tafi can masarautar mu kai”.

“Allah sarki Kaka…Allah dai ya kawo min arziƙin da zanzo na ɗauke ku nan bada jimawa ba”.

ta haɗe girarta alamun son ƙarin bayani akan abinda yace.
sai ya ɗaga tasa girar yana cewa,”ehh mana, ai idan na aureki ba ke ɗaya zan ɗauka ba. har da Kaka zamu tafi…Halimatu indai na aureki to lokacin hutun Kaka ne yayi”.

wannan furucin na Amir zuciyarta taji ya ƙara burgeta, ta kuma ƙara yin amanna da shi. muryarta mai sanyin nan ta fito a hankali da cewa,”Allah ya buɗa ya bada arziƙi mai yalwa da albarka. ya kaimu lokacin”.
“ameen ƴar aljannah”. ya faɗi hakan sanda yake sunkuyowa daidai fuskarta.

“yanzu bari na barki kije kici gaba da taya Kaka aiki, nasan yana da yawa. gobe in Allah ya kaimu na dawo”.
“tom shikenan Allah ya kaimu. ka gaida min da Inna idan ka koma”.

ya sunkuya ya ɗauko wata ƙaramar baƙar leda daya aje a ƙasa ya miƙo mata. “ga wannan. mangoro ne da bai nuna ba irin wanda kike so”.

tasa hannu biyu ta amsa cike da jin daɗi. “amma kam na gode. dama ranar nan Maijidda ke ce min ta ganshi a kasuwa da suka je, ina ta kwaɗayinsa tun ranar ashe da rabon zan sha”.

“nima na fito zan taho wajenki naga ni a bakin hanya, nace to ba zanzo haka ba hannu na dukan cinya, sai na siyawa farin cikina wani abun”.

yatsun hannunta na naɗe acikin ledar tai murmushi da ƙara yi masa godiya. sai data juya ta nufa cikin gida sannan shima ya juya ya tafi.

“Fillo! Fillo!!”. muryar Maijidda dake fitowa daga nasu ɓangaren ke ƙwala kiran sunan, sunan da kusan kowa ke kiran Halima da shi acikin gidan idan ka ɗauke Kaka wadda ba ko da yaushe ta cika faɗa mata hakan ba, tafi kiranta da Halimatu. jin kiran yasata dakatawa daga tafiyar da take tana yatsina fuska har lokacin da Maijidda ta ƙaraso wajenta.

“na rasa me ya shiga kunnenki ya toshe miki ji akan cewar bana son irin wannan kiran sunan na mafarauta”. Halimatu ta faɗa tana ɗan hararta. “ke kuma gaki kullum acikin ƙorafi”. “nayi ɗin”. Halimatu ta faɗa tana sake ɓata rai.

Maijidda ta taɓe baki tana cewa,”ke dai kika sani. daga ina kike? mene wannan?”. ta jera mata tambayoyin tana ƙoƙarin amsar ledar hannunta.
“daga inda kika aikeni Kaka”.

Maijidda tai gajeriyar dariya bata ce komai ba. wanda tuni har ta buɗe ledar ta ɗauko mangwaron ta fara gatsa. hakan kuma yasa Fillo jan tsaki tai gaba abinta, dan idan da abinda ta tsana a halin Maijidda shine cin abu ba tare data wanke ba, ita dai data ga abunda bakinta yake so ba ruwanta da tunanin wankewa zata afashi cikin baki.

sun shigo tsakar gidansu suka ci karo da Masu aiki nata zubewa ƙasa suna aika gaisuwa da kirari.
Halimatu ta ɓata rai sosai ta kama hannun Maijidda ta dakatar da ita daga tafiyar da suke.

“lafiya?”. Maijidda ta tambayeta.
“mu juya dan Allah”.
“saboda me?”.
“ni wannan gaisuwar sarautar har ga Allah ba ƙaunarta nake ba. ko waye ma haka a ɓangarenmu oho”.
ta ƙarasa faɗa da jan tsakin ƙorafi tana ƙoƙarin juyawa.

Maijidda ta fizge hannu tana cewa,”ai idan kinga na koma to tabbatarwa nayi ba wanda nake zato bane ya shigo wajen nan. haka kawai kiyi mana buƙulun ƴan silallan da zai bayar”.

“banza mayyar kuɗi, wallah idan ba kiyi wasa ba da wannan shegen son kuɗin naki za’a cuceki”. Fillo ta faɗa tana barin mata wajen ta fice da sauri gudunma kar Kaka ta hango inuwarta ta ƙwala mata kira.

tana fita ta nufi famfo ta wanke mangoro, ta dawo ta zauna kan wani ɗan tudu tana sha. kusan tsawon minti biyar tana zaune a wurin, kuma zaman na dole, duk gudun kartai gaisuwar da bata da niyya.
a wajen Maijidda ta dawo ta sameta, ta zauna itama tana cewa,”kin gani, dubu biyu ce ya bawa kowa. kema ga naki na karɓo miki”.

kallo ɗaya taiwa kuɗin ta ɗauke kai, kuma tana juyawa gefe idonta ya sauka akansa, yana tafiya cikin takun isa, taƙama da cikar izza. duk tsayin zamanta a gidan bata taɓa ganin me kalar halittarsa ba, hakan yasa ƙananun laɓɓanta taɓewa kan ta dawo da kallonta ga Maijidda tace da ita.

“waye wancan ɗin. tunda naga ke babu wanda baki sa ni ba acikin gidan nan saboda shegen shishshigi…cikin masarauta ma idan aka je yanda kike faɗar sunan jama’a kamar kece uwarsu”.

“kanki ake ji. yanzu amsar tambayarki zan baki ko na jira ki gama neman maganar?”. Maijiddan ke maganar tana ta shan mangwaronta.

“ki riƙe amsarki karki faɗa ai ba damuna yayi ba. dama naga ne ban taɓa ganin irin halittar bane acikin gidan nan tsawon zamana”.

“to sunansa Turaki”. jin sunan da Maijidda ta ambata ya ƙwala ƙarar sautin wani abu acikin kanta, babu shiri ta miƙe a zabure tana gyara ɗaurin zanenta.

“me kika ce?”.
“baki ji me nace bane hala? to nace Turaki ko”.

lokaci ɗaya idon Halimatu ya manne a bayan Turaki dake tafiya yana kusan kaiwa ga barin harabar ɓangaren masu aikin gaba ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki dake jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa.

“tashi muje Maijidda”.
“zuwa ina?”.
“ina wannan baƙar ledar dana baki ranar bikin gimbiya Safiyya?”.
“tana ɗakin Yami”.
“je ki ɗaukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dan Allah”.

Till we meet in the next page! Your comment will make me to continue or stop.

Don’t forget to rate and share to other groups please.

1 thought on “Lullubin Biri 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×