Zaune ya tarar da ita bakin gado ta yi tagumi zama yayi dab da ita yarik'o hannunta cikin taushin muryar yace, "Ki yi hak'uri Insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba kinji?"
Murmushi mai sauti tayi kafin tace, "Karka damu yawuce."
"Alhamdulillah, nagode farin cikina. Bari naje na d'auro alwala."
Ya cire babbar rigarsa da agogon dake d'aure a hannunsa ya ajiye akan gado ya fad'a toilet.
Bayan sun gabatar da nafila raka'a biyu kamar yanda Manzon Allah S.A.W ya hori sababbin ma'aurata su yi, ya yi mata tambayoyi gameda. . .
Ah lallai ai tun farko ki fadawa Daddy din ai ba a shiru da Irin abu haka. Allah ya kyauta