Zaune ya tarar da ita bakin gado ta yi tagumi zama yayi dab da ita yarik’o hannunta cikin taushin muryar yace, “Ki yi hak’uri Insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba kinji?”
Murmushi mai sauti tayi kafin tace, “Karka damu yawuce.”
“Alhamdulillah, nagode farin cikina. Bari naje na d’auro alwala.”
Ya cire babbar rigarsa da agogon dake d’aure a hannunsa ya ajiye akan gado ya fad’a toilet.
Bayan sun gabatar da nafila raka’a biyu kamar yanda Manzon Allah S.A.W ya hori sababbin ma’aurata su yi, ya yi mata tambayoyi gameda addininta ta bashi amsa dai dai. A ransa ya godewa Ubangiji hak’ik’a tun anan suna da banbanci da Ruk’ayya wacce tun a daren farkon su ya fahimci bata san komai ba game da addinin ta ba, kuma duk yanda yaso ya koyar da ita ko ya samu mata malami tak’i tabashi had’in kai. Ba abunda ya sauya daga zamanta agidan Fahad wulak’anci na yau daban na gobe daban. Yanzu harta kai yana d’auko ‘yan matansa suna kwana agidan Fad’ima kuwa ko yaushe cikin hidimarsu take.
Zaune take a falo tana sauraren karatun alk’ur’ani mai girma a wayarta itama tana bi. Memy sabuwar budurwarsa wacce yau satinta biyu agidan ta shigo d’akin tare da jiho mata tare mama da fanti ajikinta.
“Ke gasunan ki wanke mun kuma ki tabbatar sun fita.”
Kallo d’aya Fad’ima ta yi mata saboda banzar shigar da ta yi banbancinta da tsirara k’alilan ne.
Mik’ewa tsaye tayi zata bar wajan, Memy ta rik’o rigarta ta baya, k’iris ya rage ta fad’i ta baya.
Cikin tsawa tace, “Ke dan ubanki me kike nufi zansa ki aiki ki yi tafiyanki?”
“Dan Allah ki kyale ni bana son fitina.”
“Ank’i a kyale ki d’in. Dan uwarki zaki d’auki wankin ko sai na nad’a maki na jaki!”
Murmushi Fad’ima ta yi kafin tace, “Ki yi ta zagi kanki kika zaga wanki kuma ba zanyi ba. Ki bari abokin shashancin naki yazo ya wanke maki.”
“Kutumar uba dan kin ga bayanan zaki kawo mun iskanci to wallahi zaki sani bari ya dawo gidannan sai kin san kin mun rashin mutunci marar zuciya kawai da naci. Yace baya sonki baya k’aunarki amma kin nace masa. Ni wallahi da nice ke da tuni nabar gidan nan.”
“Uhm wannan ba matsalarki bace aljannata ce nake nema bauta ce dai bazan sake yiwa k’adangarun bariki ba.”
Daganan tai shigewarta uwar d’aki tare da sawa k’ofar key aranta tace, “Mijina zan yiwa biyayya saboda umurnin Ubangiji, amma na daina d’aukar wulak’ancin ku.”
Memy tace, “Zaki sani ne yarinya wallahi sai kin yi da nasanin fad’amun Magana!”
*****
Da yamma tana kitchen tana kwashe tuwo tajiyo hargowar Fahad gabanta ya bada ras! Ta sani mai rabata da shi sai Lillahi.
“Ke kina ina dan Uwarki?” Dama tana malmalar k’arshe zubawa tayi cikin cooler tarufe cikin sauri ta fito tayi kicib’is dasu abakin k’ofar kitchen zasu shigo d’auketa da mari ya fara magana cikin masifa.
“Wato samun waje ta saki aiki kik’iyi, kuma zageta ki zageni dan kin raina iyayanki ko? To bari kiji wannan da kike gani ta fiye mun ke tafiki matsayi da k’ima a idona maza kije kiyi mata wankin da ta saki ko na b’abb’allaki anan dabba!”
Cikin muryar kuka tace “kayi hak’uri idan kayanka ne ko sun kai kala nawa zan wanke ma amma bazan yiwa wacce take zaman dadir….”
Naushi ya kaiwa bakinta sai da jini ya fito yace, “Ni zaki fad’awa magana dan Uwarki!”
Cikin tsananin kuka da jin azabar ciwo tace, “Duk abinda zaka mun Yaya Fahad sai dai kamun amma wallahi bazan wanke mata ba. Kai ne dole na ba ita ba. Idan kuma tilastani wallahi ka ji na rantse yau zan je na fad’awa Dady duk abunda kake mun.”
Daga haka bata sake cewa komai ba, ta bi ta gefensa tawuce.
Memy cikin jin takaici tace, “Yanzu kenan baza ta yi ba?”
Cikin k’awafa yace, “Baki ji abunda ta fad’a bane. Kawai ki yi hak’uri, amma zata san nafita iya iskanci!”
Memy tabar wajan cikin jin haushi shima d’akin ya nufa kayansa ya kwaso da masu daud’an har wankakke da gugarsu ya nufi d’akinta yana zuwa ya watsa mata su ajiki. “Gasunan ina so ki wanke su tas ki gogesu ayau nake buk’atarsu”.
Hannu tasa ta share hawayen dake fuskarta kafin tace, “To.”
Haka taci wahalar wanke ranar sallah kawai ke tashinta bata samu barci ba har k’arfe ukun dare. Bayan ta gama tayo alwala ta fuskanci gabas dan yin nafila.
K’arfe bakwai na safe ya shigo d’akin ya tarar da ita kwanci kan darduma tana barci da alama barcin d’auketa yayi awajan Dan ko hijab d’inta bata cire ba.
Murmushin mugunta yayi kafin daga bisani ya fita d’akin bai jima ba ya dawo hannunsa rik’i da goran ruwa masu sanyi har sun fara k’ank’ara.
Yana zuwa kanta ya bud’i marfin ya kwarara mata ruwan ajiki firgice ta tashi tana ajiyar zuciya dan kuwa ruwan ba k’aramin sanyinsu taji ba.
Ganinsa tayi tsaye kanta fuska ba annuri yace, “ke wato samun wuri barcin safe to ubanwa zai girka mana abincin?”
Cikin sanyi tace, “kayi hak’uri jiya ban samu nayi barci ba saboda wankin da nayi kuma sallah ma na idar barci ya d’auke ni.”
Cikin harara yace, “Wannan ke ya shafa ina kayan?”
Mik’ewa tayi taje ta d’auko masa, “Gasu ina kwana.”
Harara ya danna mata kafin yace, “karki raina mun wayau yaushe kika wankesu har kika goge?”
“Wallahi na wanke kuma ka duba kagani.”
Fizgar kayan yayi yafita yana tsaki aransa yana mai jin haushin yanda tayi wankin so yayi ya tarar bata gama ba yaci ubanta.
Cire kayan jikinta tayi ta sauya wasu aranta tana mamakin irin k’in da Yaya Fahad ke mata ko zumuncin su baya dubawa.
Haka ta shiga kitchen dan d’aura masu abinci duk kuwa da barcin da ke idanunta.
Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)
Ah lallai ai tun farko ki fadawa Daddy din ai ba a shiru da Irin abu haka. Allah ya kyauta