Malam Hasan d’ane ga K’asim su biyu ne rak ga iyayansu shi da d’an uwan haihuwarsa Husaini ‘yan Asalin jahar Katsina ne suna zaune a Magamar Jibiya dukkaninsu suna da ilimin Arabik dana boko Alhaji Hasan yana zaune a cikin katsina d’an kasuwa ne dake fita k’asashi waje saro kaya. Yana da Mata d’aya Hajiya Hauwa suna da yara hud’u.
Fahad shine babba sai Maimuna, Suwaiba, Mujahid sai auta Atika.
Fahad a katsina yayi karatunsa sai da zai shiga makarantar gaba da sakandiri, Jami’a aka kai shi Engila a inda ya had’u da abokanai marar tarbiya suka rugaza tarbiyar sa ta gari da Iyayansa suka d’orashi akai a can ya fara shaye shaye da neman mata ya kammala karatunsa ya so ya nemi aiki a can Abbansa bai yarda ba dole yadawo ba dan ransa yaso ba yana tai makawa Dady harkar kasuwanci ba abunda ya sauya daga halayensa sai dai yana matuk’ar taka tsantsan kar iyayensa su sani.
Husaini yana zaune a Magama da matarsa d’aya Inna Asma’u malamin makarantar boko ne yana da rufin asiri dai dai gwargwado Inna tana da son Sana’a wannan yasa take sayar da d’an wake ba dan sun rasa ci ko sha ba.
Sun dad’e da aure kafin Allah ya basu haihuwar ‘ya mace Fad’imatu Zahara tana da shekara Goma ta samu k’anwarta Zainab.
Yaran sun taso cikin tarbiya tagari suna zuwa islamiya da boko anan cikin Magama. Fad’ima tayi hardar alk’ur ani mai girma har wasu littafan addini tafara karatu. Yarinya ce mai sanyin hali sam bata da hayaniya tana da hak’uri sosai har ta gama sakandiri bata da tsayayye badan babu masoyan ba. Kawai bata kula su ba ne shiyasa suke mata kallon mai wulak’anci.
Zaune suke tsakar gida tanawa Zainab karatu Inna na tsefan kanta, suka jiyo sallama. Zainab ta tashi da gudu ta rungume Ummy tana “Oyo yo Ummy.”
Dariya Ummy tayi kafin tace “fushi nake Zainab daga ke har Fad’ima kun daina zuwa mana hutu.”
“Ayya Ummy Allah ki tambayi Abba har tambayarsa nayi idan anyi Hutu zanje.”
“To na yarda yaushe ne hutun naku?”
“Saura sati biyu.”
“Allah ya nuna mana.”
“Amin.”
Fad’ima tace “sannu da zuwa Ummy.”
“yawwa ‘yar gidan Ummy karatu ake?”
“Eh” ta bata amsa a tak’aice Inna ta shimfid’a tabarma tana fad’in “Yaya zauna kinyi tsaye kina biyewa surutun Zainab da baya k’arewa.”
Zama tayi tana dariya bayan sun gaisa Fad’ima ta kawo wa Ummy abinci da ruwa tace “Ummy ina su Yaya Atika?”
“Lafiya k’alau suke. Ta so zuwa kanta ke ciwo shiyasa bata zo ba amma tace agaishe ki har sak’o tabani na baki.”
“Allah sarki Allah ya bata lafiya.”
Dukansu suka amsa da “amin.”
Dai dai lokacin Dady ya shigo Fad’ima tayi saurin shimfid’a masa tabarma bayan sun gaisa ya kalli Fad’ima yace “Hussain ya fad’a mun kin gama makaranta ko?”
Cikin ladabi tace, “eh Dady.”
“Masha Allah Allah ya taimaka. To yanzu cigaba da karatun za ki yi ko aure z aki yi?”
Tashi tayi tabar wajan da sauri cikin dariya Ummy tace “ina ruwan Fad’ima akwai kunya.”
Washe gari Dady da Abba ne zaune a d’akin Abba, Dady yace, “Hussain akwai shawarar da na yi wanda shine mak’asudin zuwana garin nan. Ka ga mu biyu iyayen mu suka barmu gashi ba awaje d’aya muke zaune ba zumuncin mu zai yi rauni. Hakan yasa na yi shawarar me zai hana mu had’a yaran nan aure Fahad da Fad’ima saboda zumuncin mu ya k’arfafa, amma me kagani?”
“Haba Hasan yaran nan duk ‘ya’yan ka ne duk abinda ka yanke akansu dai daine. Hakane na yi farin ciki, Ubangji Allah yasa alkhairi aciki.”
“Amin summa amin kira mun Fad’iman naji ko bata da wani tsayayye”.
“Bana tsammani ban tab’a ganinta da wani ba.”
“Duk da hakan dai kira mun ita naji.”
Abba ya shiga cikin gida ya kira ta.
Sake gaishe shi tayi bayan ya amsa yace, “Fad’ima acikin masu sonki akwai wanda kika tsayar?”
Cikin jin kunya tace “A’a Dady.”
“Madallah. To mun yi shawarar had’aku aure da d’an uwanki Fahad, amma idan kin san bakya so karki b’oye mun.”
Tunani ta dinga yi sam Yaya Fahad bashi da kirki ga shaye-shaye da neman mata duk tasha kamashi ad’akinsa amma bata dai tab’a fad’awa kowa ba. Ya zata yi baza ta iya musawa Dady ba.
Nisawa tayi kafin tace “na amince Dady duk hukuncin da ka yi dai-dai ne. Kai mahaifina kana da iko akaina.”
“Masha Allah nagode Allah yayi maki albarka tashi kije.”
Sanda Dady yayiwa Fahad maganar wai tashin hankali wannan bak’auya kullum cikin zumbulelen hajib zai aura tab ina da sake.
Ummy ta katse masa tunani, “Ya ka yi shiru Fahad?”
“Gaskiya Dady Ummy ku yi hak’uri amma bana sonta.”
Dady ya harare shi kafin yace “to ubana ba shawara nake nema ba umurni nake maka.”
Zai yi magana Dady ya daka masa tsawa “zaka tashi kabani waje ko saina sab’ama!”
Tashi yayi ya bar falon ransa b’ace “mtsw ana masa gata yana bultsewa” cewar Ummy.
Sati na zuwa dubban jama’a suka sheda d’auren auren Fahad da Fad’ima. A ranar aka kaita gidanta dake ‘yar aduwa road kowa ya watse sai ita kad’ai ango bai shigo ba sai k’arfe biyun dare.
Har Fad’ima tayi nisa cikin bacci ta ji an afka mata. Firgice ta tashi zaune jikinta sai rawa yake. Mari biyu lafiyayyu ya kai mata lokaci d’aya. Ta sa ihu, kafin tadawo hayacinta ya afka mata acikin halin maye, ya mayar da ita cikakkiyar mace wanda ya nuna mata rashin tausayi zallah.
Sai da ya dawo hayacinsa yace “ba dai kin nacewa aure na ba! To ki shirya zama dani ke da farin ciki sai dai hange.”
Ya d’auki kayansa yabarta cikin yanayi na wahala haka ta ja jiki ta shiga toilet ta tsabtace jikinta da shiga ruwan zafi ranar kam tasha kuka harta godewa Allah.
Duk wulak’anci da tozarcin da yake mata bata tab’a fad’awa kowa halin da take ciki ba.
Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)