Malam Khamis d’an asalin Zamfara ne cikin gusau suna zaune a Samaru wajan gidan Np yaransa biyar mata ukku maza biyu Habib shine k’araminsu yayi karatun sa anan cikin Gusau inda yayi jami’a B.U.K Kano ya samu aikin sa anan cikin Gusau ya had’u da Ruk’ayya a wajan bikin Abokinsa. Ruk’ayya na cikin k’awayen amarya gani d’aya ya mata Allah ya jarabce shi da sonta. Tun anan yayiwa abokinsa magana ya bashi kwatancen gidansu.
Bayan kwana biyu ya shirya yaje unguwar su Ruk’ayya da ke Tudun wada bayan tsohon gidan yari wajan gidan sharifai da tambaya ya gano gidansu yasa yaro yayi masa sallama da ita. Ya jima tsaye awajan kafin ta fito cikin kwalliya atamfa ce ajikinta amma fa Tasha d’inkin zamani riga da sikit ne sun matseta sosai sai d’an yalon mayafi.
Tana zuwa ba ko sallama sai cewa tayi, “Gani kai ke nemana?”
Cikin murmushi yace “Eh ina fatan ban shiga hakk’in ki ba na zuwa ba da izininki ba?”
Cikin ya tsinar fuska tace, “A’a ba damuwa. Allah yasa dai ba laifi nayi ba?”
“Haba, ai manya kuke ba kwa laifi.” ya gyara tsayuwarsa tare da jingina bayansa jikin motarsa “duk da dai baki tambaye ni sunana ba ko waye ne zan yi karambani na fad’a. Ni dai sunana Habib. Ganin farko da na yi maki awajen bikin Sadeek na ji ina sonki, soyayya ta gaskiya wacce nake burin ta kaimu ga raya sunnar Ma’aiki S.A.W. Ina fatan Ruk’ayya zaki karb’i k’ok’on barata da hannu biyu?”
Nan take ba ja, ta aminta da soyayyar Habib domin ya iya d’aukar wanka gashi kyakyawa. Ganin motarsa kad’ai ya tabbatar mata da yana da kud’i. Wannan yasa bata wani ja masa aji ba tace, “Na’amin ce, kuma fatana Allah ya tabbatar mana da alkhairi, sannan Allah yasa bada yaudara kazo mun ba?”
“Ruk’ayya ban zo gunki da yaudara ba, kuma zaki tabbatar da hakan. Nagode sosai da kika amin ce mun.”
Bai wani jimawa ba yayi mata sallama bayan ya cikata da abun arzik’i.
Da murna ta shiga gida tana kwalawa mahaifiyarta kira “Kubura! Kubura!”
Da sauri ta fito d’akin tana gyara d’auren zaninta, “Ke lafiyar ki wannan kira haka?”
Kujera ta janyo ta zauna kafin daga bisani tace, “uhmn… bari ke dai Kubura, tsuntsu ne ya fad’o daga sama gasasshe! Kalli kayannan.”
Kubura da ta samu kujera ta zauna kusa da ‘yarta, ta bud’e ledar les ne da shadda sai mayafi da takalmi da turare da sabulan wanka duk masu tsada sai dubu biyar.
Cikin mamaki tace, “Wad’annan kayan fa duk na waye?”
“Nawa ne wanda aka ce yana sallama dani ne wai sona yake da aure.”
Gud’a ta rangad’a kafin daga bisani tace, “Kai Ruk’ayya wallahi dama na fad’awa Malam ke d’in mai sa’a ce kin fi k’arfin yaku bayi irinsu Sunusi kafinta da wani yama sunansa?”
Cikin tab’e baki Ruk’ayya tace, “Wai Lawal mai gashin tsire kike magana?”
“Shifa ai sune dai Malam yana ce ki fitar da d’aya daga cikinsu barshi yaga abun arzik’i.”
Ruk’ayya d’iya ce ga Malam Haruna mai kayan miya yana auren Khadijatu Kubura kuma yaransu ukku duka mata ne, Ruk’ayya ce babba.
Kubura mace ce marar Hak’uri, masifaffiya kuma gata Allah yayi mata kwad’ayi da dogon buri, sab’anin Malam Haruna mutum ne mai hak’uri da wadatar zuci. Idan aka cire Safiyya da ke bin Ruk’ayya wacce ta dauko halin babansu, bata biyewa mahaifiyarta da ‘yan uwanta.
Ruk’ayya da auta Saratu sam basu da tarbiya ba, inda suka dauko halin mahaifiyarsu. Daga makarantar boko har islamiya basa zuwa sai yawace-yawacen banza. Biki kuwa duk inda akeyin sa ko an gayyace ta ko ba a gayyace ta ba sai ta je ko yaushe.
Malam kullum cikin fad’a da nasiha yake amma kamar ba ya yi. Ko yaushe burinsa ta samu miji ya aurar da ita ga manema amma tak’i ta fitar saboda dogon buri sai mai kud’i sai gashi Allah ya kawo mata Habib dai dai burinta.
Sosai suke nunawa juna so cikin k’ank’anin lokaci iyayensa suka nema masa auren ta, ba asa lokaci mai tsawo ba. Mahaifinta yayi farin cikin samun nagartaccin miji, addu’an sa ko yaushe Allah yasa kartaje ta nuna masa halin.
Habib kuwa duk da ana ta kawo masa sukanta k’in d’auka yayi yasa a ransa ko da gaske ne tunda tana son sa zai sauya halinta cikin k’ank’anin lokaci. Iyayensa basu tsaurara ba kasancewar su masu sauk’in hali.
Bayan Aure
Ko sati basu yi da aure ba suka fara samun matsala bayan ya gama shiri zai je gidan Hajiya zasu fita da Alhajin sa, ya ce, “Madam, ya kamata ki fara girki ina so na ci girkin amaryata.”
Fari ta yi da idanu kafin tace “Habibi ni fa Indomie kad’ai na iya sai kuwa dafa ruwan zafi, kuma banda abunka ba Hajiya na aiko mana abinci ba.”
Kallonta yake cikin mamaki kafin yace, “Haba Ruk’ayya, yau kwana biyar da auren mu kullum Hajiya ke kawo mana abinci a wuni sau uku. Gaskiya ina jin kunya. A gidana ya kamata ana girkawa akai mata dan haka ki ma daina zancen baki iya ba na san da wasa kike.”
D’aura kanta ta yi ak’irjinsa tace, “Ni fa da gaske nake tunda hakane ka sa a nemo mana ‘yar aiki.”
Janye ta yayi daga jikinsa ya mik’e tsaye yana gyara hularsa yace, “Kin ga bar zancen ‘yar aiki dan bana ra’ayinsu. Ni da abokaina zan zo da azahar ki kammala da wuri.”
Cikin k’osawa da zancen tace, “Ni fa gaskiya ta na fad’ama dan ma karka kwaso angayar abokan ka, ka ga wayam, kuma ‘yar aiki kam dole ka d’auko ta dan ba ‘yar wahala nake ba da zan zauna ina maka girki da gyaran gida.”
Ta fita d’akin a fusace. Ya jima awajan yana mamakin Ruk’ayya kafin ya fita gidan jiki asanyaye.
Sam bata zuwa gidan iyayensa sai can ba a rasa ba gidajan ‘yan uwansa kuwa bata tab’a zuwa ba. Idan sun zo babu tarbar arzik’i sai kallon banza, shiyasa suka yi zuciya suka daina zuwa. Bata da aiki sai kallo da yawan zuwa gidajen k’awaye, ga yawan bani bani ga k’azanta. Ya yi nasiha, ya yi nasiha a banza duk abun da take masa bai tab’a zuwa ya kai k’ararta gun iyayenta ko wani nashi ba.
Ku biyo ni a babi na bakwai in Allah Ya so.
Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)